Skip to content
Part 3 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

“Sa’adatu”

Tahir ya kira cikin muryar nan tashi, wannan muryar da kunnenta ya bambanta mata da sauran muryoyin da ta taba ji, kamar hakan take jira, kamar kukan da tayi a kwanaki takwas din nan bakomai bane ba, sai yanzun da taji ya kira sunanta da sanyin murya da wata irin tausasawa da bata tabaji a tare dashi ba, sai kuwa hawaye masu zafi suka zubo mata, wannan nauyin da take ji a kirjinta ya sake danneta.

“Babu wanda ya fadamun, da na taho, jiya ma na kira Abdallah ne, sai yake sanar dani.”

Har yanzun cikin wannan tausasawar yake mata magana da take kara sa hawayen da bata ko kokarin gogewa zubo mata.

“Ban san ya kike ji ba, kuma tsakanin ranar zuwa yau, nasan babu kalar abinda ba’a fada miki ba, duka dai karshen zancen kalmar hakuri ce…”

Kamar ya sani, babu wanda zai fahimci abinda take ji sai wanda ya tsinci kanshi a yanayi irin nata. Yanayi na rashin mahaifin da bai kwanta jinya ko ta rana daya ba. Asalima Alhamis din sun tashi lafiya kalau, tun asuba ba zatace ga wani canji da ta kula dashi ba. Ranace kamar kowacce rana, ya kamata ace tunda safen taji a jikinta, ko yaya ne ta ji a jikinta. Da tayi shirin makaranta, sauran wainar da akayi musu da dare, kwara biyu data rage ita taci, tana hadawa da ruwan Lipton. Ta saka hijabinta ta nufi dakin Habibu, ko sallama bata yiwa Abida ba saboda tayi mata fadan jalof din taliyar da Asiya ta kawo mata. Da sai abin kwadayi ne Asiyar take kawo mata, amman yanzun kusan kullum da dare tana da kwanon abinci a gidan Hajiya, saboda anfi yi musu tuwo, ita kuma ta dorawa kanta. Kuma hasashen Abida yayi dai-dai, ita ta roki Asiya tace dan Allah kome zasu dafa da daddare ta dinga kawo mata.

Abinda Sa’adatu bata sani ba, shine ita kanta Asiyar a boye take kawo mata abincin, Hajiyarta na da kirki, amman akwai abubuwan da ba zata dauka ba. Ciki kuwa harda kwadayin Sa’adatu, idan abin kwadayi ne, Hajiyar bata damuwa, wani lokacin ma da kanta zatace mata ba zata dibarwa kawarta ba. Amman ace abinci, kuma duk dare, Hajiya ba zata dauka ba, ita kuma Asiya ba zata iya batawa Sa’adatu rai ba. Ranar da duk bata kai mata ba tun bayan da ta roka, har hakuri take bata idan sun hadu ta kuma gabatar da tarin uzurori. Fadan Abida ya batawa Sa’adatu raine ba kadan ba, tunda bata ga dalilin yin shi ba. A ganinta Abida tafi kowa sanin bata kaunar tuwo, ita ba kudi zata bata dan ta siyi wani abin taci ba, ko kudi gareta idan ta siyo haka zata dinga yi mata fada tana mata wa’azi kamar wadda ta kafurce saboda tace bata cin tuwo.

Bayan har yau bata ci karo da abinda ya hada musulunci da tuwo ba, ko son jin dadin da Abida bata gajiya da yi mata magana akai. Itama fa randa duk Habibu zai siyo nama, tana kula har wani lumshe ido zakaga tanayi, wanda yake ba Sa’adatu dariya, a ranta takan ce.

“Amma ashe ba bakina kadai ke son cin dadi ba.”

Shisa da asuba ma can kasan makoshi ta gaishe da Abidar, bata damu ba dan bata amsa ba, gujewa wani fadan ne yasa ta gaisheta ba wai wani abu ba. Itama fushin takeyi, shisa data gama shirinta batayi mata sallama ba ta wuce dakin Habibu kai tsaye tanayin sallama a bakin kofa ya amsa yana fadin ta shiga, labulen ta daga, bakin nan ta dage shi sama saboda fushi.

“Waya taba munke da sanyin safiyar nan?

Sake kumbura fuska tayi tana saka shi yin dariya, kafin tayi masa gaisuwar daya amsa da.

“Sa’adatu rigima.”

Yana saka hannu a aljihun shi ya ciro Naira dari da hamsin, ya mayar da hamsin din ya bata Naira dari, ta kuwa yi murmushi ganin kudin, daman wani lokaci yana kara mata akan Hamsin din da ake ba kowannen su, yasan halin rikicinta, kuma kamar yanda Abida take yawan yin mita akan halinta, yana kula adan zaman da yakeyi dasu, kawai yafi dora abin akan hankalin da bai gama zauna mata ba har yanzun. Yana kara mata kudin makaranta ne, ko ya bata dan na kashewa a boye, a nufin shi na kauda mata kai daga hangen wasu. Saboda kowanne mutum da halin shi, haka cikin yaran ma, bukatunsu da halayensu sun bambanta, yana kokarin ganin ya bama kowannen su irin kulawar da zata dace da halin shi.

“Sai na dawo Abba”

Ta fadi

“Allah ya tsare hanya, a kula dan Allah”

Ta juyo shi yana cewa bayan ta saki labulen dakin, bata ko amsa ba ta fice. Rashin amsawar da yanzun yake damunta. Me yasa bataji a jikinta wannnan bace maganarsu ta karshe? Bama ance mutane kan nuna alamu da suke zama bankwana kafin mutuwarsu ba? Suna yin wasu maganganu da sai daga baya idan an natsu ake kula duk nasiha ce. Ya akayi shi duk baiyi wannan ba? Ta tafi makaranta, kuma ko da taje a ranar sai ta kwantar da kanta akan benci ta fara bacci, baccin da yayi mata wani irin dadi har tayi karyar ciwon kai don duk Malamin daya shigo ya sama mata lafiya. Tunda ta shiga aji hudun nan, ta zabi bangaren kimiyya da fasaha (science). Sai taga kamar anfi maida hankali wajen koyar dasu fiye da sanda take jiniya, don Malamai na shigar musu sosai. Kuma karatun nayi mata saukin fahimta tunda turanci ya fara zauna mata babu laifi.

Ko da ta tashi ma, babu komai a tunaninta, sai Tahir daya fado mata a rai. Ba zatace ga abinda ya faru tun ranar da suka zo tana gyaran waken nan ba, ya dai dawo washegari, tana zaune tana nazarin wasu kalmomi da Asiya ta rubuta mata da fassararsu, da yake a tsakar gidane sai yaja kujerar daya gani ya zauna, ta kuma tsinci kanta sa gaishe dashi, bayan gaisuwar suka fara hira, hira kamar sun jima da sanin juna, sosai suke hirar kafin Asabe ta fito ta kare musu zagi daga ita har shi, ganin damuwa da kunyar da take shimfide a fuskar shine ya sata yin murmushi tana ce masa.

“Ta iya fadan rashin dalili, mun rigada mun saba, kaima in kana zuwa sosai ba zai dinga damunka ba.”

Da turanci tayi maganar tana bashi dariya hadi da mamaki a lokaci daya

“Ni zaki zaga da turanci Sa’adatu?”

Asabe ta fadi.

“Ba zaginki tayi ba Mama, karatun da na koya mata ne take maimaitawa inji ko tayi dai-dai.”

Tahir ya fadi yana sa Sa’adatu kunshe dariyar da take neman kubce mata

“Rufe mun baki, sakarai kawai, kai har zaka shigo gidan nan ka tsaya wajen wannan fitsararriyar”

Shirun yayi, sun dai sake hada ido tayi masa murmushi. Sai ranar ta bude musu wani sabon shafin, yayi zuwa fiye da yanda zata iya kirgawa a hutun karshen zangon da yazo. Dama ya gane lokacin tasowar su daga Islamiyya, sai yazo ya jirata a kofar gida, su sha hira, da an kira Magriba ya wuce, ita kuma ta shige gida

“Kinga ba zan iya masifar Asabe ba, ki rage shigewa yaron nan, ban hanaku gaisawa ba, amman ki rage shige masa”

Abida tace mata tun rana ta biyu da ta shigo da Magriba ta tsareta da tambayar daga inda take, ta fada mata suna kofar gidane ita da Yaa Tahir, kamar yanda take kiran shi, duk kuwa da kannen shi Hamma suke ce masa, kyaleta yayi, data fada yayi masa dadi. Ta kunnen dama maganar Abida ta shiga ta fice a kunnen haggu. Masifar Asabe wacce iri ce basu gani ba? Ita tana jin dadin hira da Tahir, har ya tafi, har ta kwanta sai wasu abubuwa a cikin hirar su ta dinga dawo mata tana sakata murmushi. Labarai basa kare masa, na makaranta, na rayuwa dama abubuwa mabanbanta, gashi yana kamshi mai dadi, ya iya gayu, yana da hasken fatar Asabe, sabanin dan uwan shi da yake baki, kuma tasan ba idanuwanta bane ba, har Asabe yafi kyau. Cikin jerin abubuwan da take so tare da Tahir harda kyautar da yake yi mata, duk da ba wata ta azo a gani bace ba, yana yi mata din.

A cikin shekara dayar da sanin shi sunyi wata irin shakuwa da tana zaune tunanin shi zai fado mata. Ta tambaye shi me yake karanta a makaranta yace mata turanci. Taso ta tambaye shi idan ya gama a ina zaiyi aiki, sai ta kasa. Amman da yake tambayar tana cin ranta, bata kuma san wa zata tambaya inda wanda suka karanci turanci suke aiki ba, ta tambayi Asiya tace mata.

“Anya na sani kuwa, ba dai zai wuce aikin koyarwa a jami’a ba.”

Sai ta shashantar da maganar, saboda in ta hasaso Tahir a matsayin Malamin makaranta sai taji hasken da yake dashi a wajenta yana dishewa batare da wani kwakwaran dalili ba. Shisa sai take hasaso shi da wani babban aiki, take hango shi cikin mota babba, da gida irin wanda take gani a fim. Yanda duk Asiya ke ce mata.

“Yaa Tahir dinki na da kyau.”

In ta hango shi a Malamin makaranta sai wannan kyawun ya dishe a idanuwanta. Tunda Asiya ta fara kiran shi da “Nata” bata taba kokarin gyara mata ba, ba kuma don Tahir din nata bane, sai dan bata son yanda Asiya take yawan yabon kyawun shi da sanyin halin shi, kamar in da ba na Sa’adatun bane zai wahala bata je ta tallata masa kanta ba. Ko da take hanyar komawa gida ma, tunanin Tahir din ne fal a ranta, sai dai in ya kira Abdallah wasu ranakun yana gida ya bata su gaisa. Yanzun kuma kacokan hankalinta ya koma kan mallakar waya, ba yar karama irin ta Abdallah ba, data tambaye shi.

“Wayarka na 2go?”

Haka yace mata

“Wannan ai yar karama ce Sa’adatu”

Cike da rashin fahimta tace,

“Amman Meenar ajinmu Nokia gareta, kuma tana yin 2go da Facebook”

Murmushi yayi

“Watakila irin symbian din nan ne da nake ganin Auwal na siyarwa, ko kuma manyan Nokia din nan da nakan gani”

Bata san wanne yake magana akai ba, amman tabbas cikin irin su take da buri. Wannan kafar sada zumuntar da aketa magana, bata so yayinsu ya wuce bata shiga ciki ba. Sai dai kullum da burin mallakar wayar yake karuwa a ranta, da yanda hanyar samunta take kara yi mata nisa. Bata da wanda zai bata wannan makudan kudaden ta sani, idan tace ma zata tara wanda take dan samu, to dole zata daina cin kayan kwalam da makulashen da a wajenta sune rayuwa. A kafa ta tako, ta hada duk kudin ta siyi kifi da nufin kome aka dafa da ranar saita hada da kifin taci, bama zai wuce mai da yaji ba ta sani. Kanta tsaye ta sha kwanar da zata sadata da gidansu, haka kawai zuciyarta ta doka, ta sake dokawa ganin Asabe, Abida da Abdallah a tsaye a kofar gidan. Kafafuwanta suka kara sauri, tabbas lafiya ba zata sa su tsayuwa kofar gida ba.

“Yaa Abdallah…”

Ta kira tana kallon fuskokin su, ga mamakinta, kuka Asabe takeyi, hijabin jikinta ma a bai-bai take, sai ta maida dubanta kan Abida, da abinda zai taba ranta harya saka mata zubar hawaye ba karami bane, basu zubo ba kam, amman zaka iya hangen kyallinsu. Zuciyar Sa’adatu ta kara dokawa.

“Me ya faru?”

Ta tambaya cikin rawar murya.

“Ki shiga gida Sa’adatu, yanzun zamu dawo”

Cewar Abdallah.

“Abbanku ne yayi hatsari”

Asabe ta amsa mata tana sake rushewa da kuka, taji me Abdallah yace, maganar Asabe ce tayi mata wani irin duka da bata taba sanin irin shi ba a tsayin rayuwarta, lokaci daya taji wani abu da ta tabbatar ba jiri bane ya dibeta, saboda da jiri ne da tuni ta kai kasa. Kafin ta samu damar cewa wani abu, sai ga Sadiya da Jidda sun dawo suma.  Ita Sadiya saita biya ta taho da Jidda da take firamari sannan su taho tare. A cewar Sa’adatu ai Jiddar tayi girman da zata iya zuwa kuma ta dawo daga makaranta da kanta, me yasa zata tsaya wahalar sai sun taho tare? Kuma ita bama kullum take takowa da kafarta ba. Shisa daga wajen zuwa har dawowa kowa tafiyar shi daban ita da ‘yan uwan nata, basa jiranta kamar yanda bata jiransu. Abdallah ne yayi musu magana yace su shiga gida, zasu je su dawo. Ba kuma suyi musu ba suka shige. Sa’adatu sai da ya sake yi mata magana tukunna ta shiga gidan bayan taji suna cewa asibiti Aminu Kano. Jidda ta mikawa ledar kifin data siyo, ta karba da mamaki.

“In ajiye miki?”

Ta tambaya dan tasan in dai abin dadine, to zai wahala ma kasan Sa’adatu tana dashi balle harta sammaka, kuma ta ga kifi ne.

“Ki cinye”

Ta fadi tana shigewa dakinsu, ta cillar da jakar makarantar, ta nufi ta islamiyya, inda ta dauko dari biyu a tsakiyar littafin hadisi. Ta fito, bata kula su Sadiya da suke tambayar inda zataje ba, ai shima Abdallahn yasan babu yanda za’ayi ta zauna. Mashin ta tare suka yi ciniki ta hau, tana jin yanda iska ke dukan fuskarta da wani irin yanayi har suka isa asibitin, ta sallame shi bayan ta sauka. Sai kuma tayi tsaye a bakin kofa cikin rashin madafa, da tazo ina zata nufa? Wa zata tambaya? Ba zatace ga mintinan da ta kwashe tsaye tana taraddadi ba sai jin Abdallah tayi ta riko hannunta.

“Sa’adatu?”

Ya kira cikin mamaki da alamar tambayar me takeyi, bata amsa ba, bai kuma sake cewa komai ba. Kai kawai ya girgiza yana janta suka nufi cikin asibitin gabaki daya. Ta san ta rigasu zuwa saboda ita mashin ta hau, bata san inda suke nufa ba, ta dai rufe idanuwanta yafi a kirga saboda kamar bangaren yan hatsari ne, ko muma emergency, bata dai sani ba, kamar yanda bata san sanda Abdallah ya saki hannunta ba, ita kuma taja tayi tsaye a inda ya barta, duk a hargitse take jinta, duk wani labari na hatsari da take ji bai shirya ma zuciyarta tashin hankalin da take gani yana faruwa a wajen ba. Jini, ta ko’ina jini ne, ma’aikata na ta bada taimako, duka dakin a kacame yake, in ba gizo idonta yayi mata bama harda ‘yan sanda ta gani, bata dai san inda suka nufa ba.

“Matsa dalla can”

Aka fadi ana hankadeta harta kusan kifawa, bayan shi ta gani yanata sauri, sai kuma wani matashin kamar shi da yake bin shi yana fadin.

“JB…”

Sai taji zuciyarta ta maimaita sunan, idanuwanta kuma sun bisu da kallo har suka bacewa ganinta.

“JB”

Ta sake maimatawa tana kallon hanyar da suka bace.

Batare da ta san kaddara zata sake hada su ba.

Ganin sai tureta akeyi yasa ta samu kusurwar wani bango daga can bakin kofa ta rakube tana ta raba idanuwan ganin ta inda su Abdallah zasu bullo, tun tana tsaye har kafafuwanta sukayi sanyi, dole ta tsugunna, karshe ma zama tayi a kasa, sanyin tayil din wajen na ratsata. Tana hango Abdallah tayi saurin mikewa, sai dai gani tayi ya durkushe a wajen cikin alamar dake nuna kuka ne ya ci karfin shi, sai taji ta kasa karasawa inda yake, ya kusan minti biyu sannan ya dago yana sa hannu ya share fuskar shi. Wani abu yaso ya gaya mata sun zama marayu, amman sai taki bashi dama, tana kallon shi ya fita, ya dawo yana nemanta, tana tsaye harya ganta, baice mata komai ba ya kama hannunta, batayi musu ba ta bi bayan shi, fita yayi da ita ya sakata a cikin napep ya sake komawa, saiya fito da Asabe da yake rike da nata hannun itama ya sakata a cikin napep din, bata ji me yace masa ba, saboda hankalinta na kan Asabe da fuskarta ta kara yi mata haske.

Tayi wani irin fayau kamar takarda, idanuwan nan sun sake fitowa, sun kuma rine mata, wani yanayi ne da Sa’adatu bata jin zata manta. Har kofar gida ya kaisu bayan da Sa’adatu ta dinga nuna masa hanya tunda suka shiga Bachirawa. Ita ta fara fita, maganar duniya tayiwa Asabe, amman kamar bata jinta, sai da ta kamo hannunta sannan ta biyota kamar wadda bata cikin hayyacinta. Suka shiga gida inda Asabe ta nufi dakinta, sai ta kasa shiga, anan kofar dakin ta kwanta, a kasa, yanda duk Sadiya tayi da ita ta tashi ko tabarma ce a shimfida mata kiyawa tayi. Ta tambayi Sa’adatu ko bata da lafiya ne ta amsata da bata sani ba. Haka sukayi cirko-cirko har Jidda da take karama ta san gidan nasu yau ba lafiya. Zuciyar Sa’adatu kuwa babu abinda bata kitsa mata ba amman banda rashin da tayi. Saboda Habibu ba zai tafi bai nuna wata alama ba.

Ba yanda za’ayi ta rasa shi haka rana daya, ai da taji a jikinta. Ko da safe da taje karbar kudin makaranta, zai nuna wata alama, zata shiga cikin dakin ta zauna, abinda ta jima batayi ba, zasuyi hirar da zata rike a ranta ta dinga juyawa idan kewar shi ta addabeta, daya yi mata maganar karshen nan ai da zata koma ta daga labulen ta amsa shi. Shisa ko da aka shigo da gawar cikin gidan ma take jin kamar mugun mafarkine takeyi da wani zaizo ya tasheta.

Ta manta mutuwa ko wanda zata dauka bata jira ta shirya.

Balle kuma har makusantan shi su samu damar bankwana.

Akan idanuwanta gidansu ya soma hadewa da jama’a har babu inda wasu zasu zauna. Ko da aka gama hadashi ma akace suje suyi masa addu’a, kai ta tsinci kanta da girgizawa.

“Abba ba zai barni ba wata alama ba, idan kuka tsaya zaku ga ya tashi fa, ku dai ku tsaya.”

Bata san me ta fada da yasa gidan ya sake rudewa da koke-koke ba.

“Ku daina kuka, ku jira ku dai.”

Haka duk wandq yayi kokarin kamata take fisge hannunta.

“Wai akan me zaku dinga bani hakuri kamar na rasa shi? Baku san yanda nake son Abba na ba, ko dan bana nunawa? Ko dan bana fada kuna ji?”

Da gaske take, tana yiwa Habibu wani irin so da ko Abida bata yiwa, duk kuwa da laifinshi da take gani na rashin arzikin da bashi da shi. Da ya koma makaranta bayan ya samu aiki zai samu karin girma, daya hada aikin shi da kasuwanci daya bunkasa sun taso cikin daula, akwai hanyoyi da yawa da Sa’adatu take tunanin ta gano masa da shi ya rufe ido daga gani har talauci ya samu wajen zama a tare dasu. Duk da haka tana son shi, a cikin talaucin nashi, a rashin da sukeyi yau da kullum, inda duk zai sa mata sauki yana nan. Idan wani biki sukaje na ‘yan gayu. Abinda duk za’a bashi ba zaici ba zai boyo ne yazo ya faki idon kowa ya bata. Kamar yanda bata taba fadar tana masa son da batayiwa kowa a duniyarta ba, shima bai fito fili ya fada ba, Sa’adatu nagani. Yana bata muhimmanci da take so kowa da yake cikin rayuwarta ya bata. Bayan shi kuma Abdallah ne kawai yake kamantawa. Rana daya sai ace ta rasa shi? Kuma so ake ta rungumi wannan rashin kamar ta shirya masa?

“Ya rasu.”

Abdallah daya ratso matan da suke ta fama da ita ya fadi, yana saka hannuwan shi duka ya tallabi fuskarta.

“Ya rasu Sa’adatu, kizo kiyi masa addu’a, ke kadai ake jira.”

Sai wani irin sanyi ya ratsata kamar tana tsakiyar korami, wani abu ya rabe gida-gida a cikin kirjinta. Ciwo marar misaltuwa na dukan ilahirin jikinta daya fara kyarma, tayi mamaki data iya bin bayan Abdallah har dakin Habibu, inda aka shirya shi tsaf, sai taga kamar ya kara tsayi, fuskar shi ce kawai a bude, kamar yana bacci, banda wani dan yanka a kuncin shi babu komai. Daga baya taji ana cewa daya fado daga mashin din, wani mashin dinne ya bi takan kirjinshi saiya fasa abubuwa daga ciki, anan ya fara aman jini, sanda aka kwashe su zuwa asibiti ma yana daya daga cikin mutanen da ba’a karasa dasu da ransu ba.

“Abba”

Ta kira tana jiran ya amsa ta da

“Sa’adatu rigima”

Sai wani shiru daya tabbatar mata da komai ya ratsa dakin, bata san sanda ta durkushe ba, da rarrafe ta karasa wajen shi tana rasa addu’ar daya kamata tayi masa. Kallon shi takeyi kamar zaijita ya tashi, batayi wani yunkuri ba ko da Abdallah ya matsar da ita gefe aka dauki gawar Habibu ana ficewa dashi daga dakin da yayi rayuwar wucin gadi a cikin shi zuwa wani dakin nashi da yake jiran kowa. Haka akaje aka dawo, batayi kuka ba, sai da Abdallah ya dawo dakin, ya nufi gadon Habibu ya zauna yana dora kanshi akan gadon hadi da sakin wani gunjin kuka daya fito mata da nata kukan. Sai dai har yayi nashi ya gama ya fice daga dakin ita bata san ta inda zata fara dainawa ba. Har akayi sadakar uku, banda fura da Hajiya ta sa aka daga mata ita aka bata, bata iya sakawa cikinta komai ba. Ko sallah sai ance ta tashi tayi take iyawa. Ba’a ma maganar wani abu wanka balle ta canza kayan makarantar da sune a jikinta har lokacin.

‘Yan uwanta mata kuwa da kowa yazo zuwa lokacin, wanda duk suka hada ido da ita sai su fara wani sabon hawayen. Ana rasa wanda zai ba wani hakuri a cikinsu. Ashe haka mutuwa take da ciwo? Tsakanin Abida da Asabe kuwa ba’ama magana. Da gaske ne, kowa zai shaida auren soyayya Abida da Habibu sukayi, ita kuma Asabe bashi ita akayi, amman tana masa son da ba zai misaltu ba, tana jin tafi Abida rasa shi. Soyayyar da take tsakanin Abida dashi rabata za’ayi dai-dai kowa ya dauka a cikinsu, za’a iya cewa cikin rayuwarta Abida ta rasa. Amman Asabe najin duka rayuwarta Habibu ya tafi da ita. Tayi kuka har ta soma gani dishi-dishi saboda zafin da idanuwanta sukeyi. Su duka kafin ayi sadakar bakwai, kallo daya zakayi musu kaga yanda mutuwar ta dake su. Dan da aka gama sadakar bakwai asibiti aka wuce da Hajiya da zazzabi ya rufarwa, idan dubawa za’a tsaya yi, su duka zazzabin sukeyi, Hajiya ya hadar mata ne da jikin tsufa, shisa ya kwantar da ita.

“Nima hakurin dai zan baki…”

Tahir ya fadi, yana sa ta kai hannu ta share hawayenta. Hakurin nan ko an basu, ko ba’a basu ba dole ne, idan ma basu hakura ba ya zasuyi? Tasan inda kuka na dawo da mutum daga lahira da Habibu bai kwana ba, yawan hawayen da suka zubar akan shi za’a doro Habibu a gunguro musu shi.

“Ba zakiyi magana inji muryarki ba?”

Ko tayi yunkurin magana tasan babu abinda zai fito sai kuka, shisa tayi masa murmushin karfin halin daya hado da hawaye.

“Bari inje gida to, zan dawo dana ajiye jakata na watsa ruwa. Kinci abinci kuwa duk yau? Kina son wani abu in taho miki dashi?”

Kai ta girgiza masa a hankali, ko daya aika aka kirata, sam bata kula da jakar da yake rataye da ita ba sai yanzun da yayi magana. Kenan daga tasha nan yayo wajenta?

“Na kasa wucewa gidane, ba zan iya ba sai nazo na fara ganin ki.”

Ya fada yana tabbatar da hasashenta, sai taji wani yanayi ya lullubeta, wani abu da bata taba ji akan kowa ba, hasken da yake dashi a zuciyarta taji ya karu har yana haska mata wasu wajaje daban a cikin kirjinta, tunda akayi rasuwar bataji wani sauki daga ciwon da take ji ba sai yau. Maganganun shi kamar sun fifita mata ciwukanta ne suna sanyaya abinda ke ci da wuta a tare da ita.

“Yanzun zan kara dawowa sai in shiga in yiwa su Amma gaisuwa. Zan taho miki da gurasa da yoghurt ko ba zakici yanzun ba, anjima sai kici kinji? Ki koma gida yanzun, idan kinji zuciyarki na zafi ki cigaba da Inalillahi wa ina ilaihi rajiun.”

Da kai ta sake amsa shi, yanda duk yaso yaji muryarta ta kasa magana. Haka ta koma gida yana tsaye yana kallonta.

Soyayyarta da yake dannewa tayi sama

Maraicinta ya kusanto masa da lokacin da yake jira akanta.

<< Tsakaninmu 2Tsakaninmu 4 >>

6 thoughts on “Tsakaninmu 3”

  1. Har munfara kuka kinan😭 Allah yasani nasan book dinnan hawaye zasu zuba, idan mutu tazu a page kaima irin mutur da akayimaka sai taxumaka sai kuka, madallah Lubna bansan wani irin so nakiyiwa dukkanin abunda Zaki rubutah❤️

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×