Skip to content
Part 48 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Da idanuwa Aisha take binshi tunda ya koma asibitin, tana zaune akan gado ta mike kafafuwanta, da kofin shayi a hannunta da take kurba a hankali saboda zafin shi, yanayi mata dadine sosai, saboda ya sha kayan kamshi, kuma data tashi hadawa sai bata saka madara ba, ta zuba Milo mai yawa dan ko sikari bata saba. Yayi sallama, ta amsa masa, bai kuma kalleta ba, ya karasa yaja kujera ya zauna. Fuskarshi take kallo, gabaki daya kamar shine yake jinyar, yayi wani irin zuru-zuru da ko a lokuttan rashin lafiya bata taba ganinshi haka ba. 

“Me kaci duk yau?”

Ta bukata, Jabir ya girgiza mata kai.

“Bana jin cin komai, dan Allaah karki ja maganar.”

Ya karashe cike da roko da wata irin gajiya da take fitowa tun daga zuciyarshi. Batace masa komai ba, ta cigaba da kurbar shayinta. Jabir kuwa babu abinda yake so yayi banda kwanciya, kwanciyar ma a wani waje da babu kowa, da zai samu gida zai koma, ya shiga daki ya kashe fitila, watakila duhun dakin yayi tarayya da wanda yakeji a zuciyarshi ya sama mishi wata yar natsuwa koya take. Yau kwana nawa kenan yake cikin rashin natsuwa? Bayan ya kamata ace ranakun na daga cikin ranakun farin cikin rayuwar shi. Abinda suka dade suna nema ne fa suka samu, abinda suka cire rai daga samun shi harya sa su yanke hukuncin gayyato Sa’adatu cikin rayuwarsu. Amman tun ba’a kwana ba da jin labarin, tunanin makomar Sa’adatu a cikinsu ya danne farin cikin da yake ciki, ya turashi can wani waje da yake neman ya bace masa gabaki daya ma a yau.

Haka ya dinga bin ‘yan uwanshi da murmushin da bayaji a zuciyarshi, yana kallon farin cikin da yake kan fuskokinsu, yanda wasu a ciki har suke kasa hakura sai sun rungume shi, ko babban yayansu da son girman shi da kuma gudun raini yake hanashi nuna musu kulawa irin haka sai da ya bubbuga bayanshi yana ta binshi da murmushin daya kasa dainawa. Balle kuma Hajiya Hasina, da ana fada mata cewar cikine da Aishar saita kasa tsaida hawayenta. Farhana kuwa shi ya rike hannunta, ta kasa magana, data kalle shi ta kalli Aisha sai hawaye ya sake balle mata, lokacin data samu bakin magana lokaci zuwa lokaci zatace

“Wanda bai mika lamurran shi ga Allaah ba aiya shiga uku…”

Ubangiji Mai kyauta da kari, kuma a kwanakin nan duka hankulan kowa yana kan Aisha da ganin tabi duk wata ka’ida da likita ya gindaya mata. Shisa banda Aishar da yake mamakin yanda akayi a cikin tarin abubuwan da suke gabanta harta samu sararin kula da yanayin shi.

“Wani abu yana damunka Jay.”

Ta fadi cike da tabbatarwa kwanaki biyu da suka wuce, shiru yayi. Tunda idan ya bude bakinshi ma baisan me zaice mata ba, ba kuma zai fara karyar babu abinda yake damunshi ba tunda Aishar ta sanshi fiye da kowa. Babu abinda yake kissimawa a cikin kanshi daya wuce babu wannan dalilin daya shigo da Sa’adatu cikin rayuwarsu, daman ko tare da dalilin ma zaman nata yana da lokaci.

Ya dai rasa dalilin da yasa zuciyarshi takeyi masa kamar ta manta da wannan lokacin da Sa’adatun take dashi, kamar taso ta hango masa kasancewarta a cikin rayuwar shi na lokaci mai tsayi, lokacin da bayaso yasan iyakarshi. Kamar har abada zuciyarshi take son raya masa yana yakicewa. Sai dai daya kalli Aisha sai yaji wani abu na dukan zuciyar tashi, wani abu da ya girmi rashin gaskiya. Ya shagala da Sa’adatu harya dauke hankalin shi daga kanta, har bai kula da bata da lafiya ba, ko da babu ciki, baisan ranar da zai yafewa kanshi wannan rashin kulawar daya nuna mata ba.

Saboda da yana tare da Sa’adatu, yana kallon kiranta bai daga ba. Wannan wani abune da zai jima yana cin zuciyarshi. Duk zagayen daya dingayi a kwanakin, jiyane ya gama sanin cewa nesan da bayason hangowa ce tazo kusa. Lokacin da Sa’adatu zata fita daga rayuwarsu yazo, tunda babu wani dalili da zata cigaba da zama kuma. Daya fita ko zai samu ya sha iskar da yaji tayi tsaye waje daya a cikin asibitin, saiya tsinci kanshi da komawa gida, batare da dogon tunani ba ya dauki takardun gidan da Sa’adatu take ciki. Daya fito ya sake shiga mota baya ganin komai sai ranar farko daya fara ganin gidansu Sa’adatu, wannan tsukakken gidan da ya dinga juyayin yanda suke rayuwa mai cike da walwala a cikin shi, gidan da ma ya fahimci duk kankantarshi ba nasu bane ba, haya suke biya. Ko ya rabu da ita ba zai taba samun natsuwa ba sanin wannan gidan zata koma. Gara ya mallaka mata wanda daman ya siya da sunan ta zauna a cikin shi.

Bai dauki lokaci ba, saboda yana da Lauyan da yake yi masa irin abubuwan nan. Haka yaji envelope din da takardar take ciki tayi masa wani irin nauyi. Saiya barta a cikin mota, yinin ranar dai duka yoghurt ya dinga kafa kai yana sha, sanin cewa ko bashi da dandano, ko da baiji yunwa ba jikinshi yana bukatar abinci. Daya tashi da safiyar yau din kuwa, daman ba bacci ya samu yayi ba, wasu abokan wasan Aisha dinne sukazo asibitin su biyu, sai yayi amfani da wannan damar yace mata zaije gida ya watsa ruwa acan, daga gidan kuma zai shiga kasuwa, akwai abubuwan da zaiyi, idan tana bukatar shi ta kira. A gabansu ya taka ya sumbaci goshinta da gefen fuskarta, kafin yayi musu sallama ya fita, suna binshi da kallo, suna kuma jinjinawa yanda shekaru basu dishe ko kadan daga kulawar da yake nunawa Aisha ba.

Bayan yayi wankan, ya dauko littafi da biro, ba zaice yana jimawa baiyi rubutu ba, saboda a lokacin da yan kasuwa da suka taka matakan nasara irin wadanda ya taka, da kuma yanda zamani yazo, komai yake kara saukaka, suke amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen adana muhimman abubuwa da kuma wasu lissafe lissafen, yafi gane yaga komai a takarda, ko da za’a adana din, to yana son ya zamana yana da copy, saboda kamar yanda mota take da rashin tabbas, ka fita da ita lafiya kalau taja ta tsaya a tsakiyar titi, haka yake kallon na’urorin nan, duk da har yau basu taba fuskantar irin wannan matsalar ba, shi dai yafi son yagani kuma yaji takardu a hannun shi. Duk wani mai aiki a karkashin shi kuma yasan da hakan. To kusan kullum ma a cikin yan rubuce-rubuce yake. Yau dai gashi rike da biron da yake yawan amfani dashi, amman yanajin yayi masa wani irin nauyi, kamar an dauke biron an musanya masa da wani katon icce.

Fallen takarda kuwa, hasken shi bai taba shigar masa ido irin yanda yayi a lokacin ba. Ya dora biron akai yana cirewa yafi a kirga. Jikinshi baya rawa a zahiri, saboda hannunshi tsaye yake qam, amman wata irin kaduwa zuciyarshi takeyi da bai taba tsintar kanshi a ciki ba. Sai ya sake dauke biron yana so ya tsara kalaman da zai rubuta, amman kuma akwai wata kwaskwarima da akeyiwa saki ne? Idan zai cika takardar da surutu, karshenta dai takardar saki za’a kirata

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ya tsinci kanshi da furtawa a hankali, ashe haka sakin yake da firgici da tashin hankali? Ta ina mutanen dake auri saki suke samun karfin gwiwarsu? Idan shi dama can akwai sakin a tsarin shi kafin yin auren yanajin tashin hankalin nan, to wanda kuma babu wannan tsarin fa? Wata irin zufa na keto masa kamar babu na’ura mai sanyaya daki ya rubuta

“Ni Jabir na saki Sa’adatu saki daya”

Kalmomi bakwai ne, da idanuwanshi ya kirgasu, da hannunshi ya rubuta su, amman da ya sake karantawa sai yaji numfashin shi na fita sama-sama saboda tashin hankali. Haka yayi sauri ya nade takardar, jikin shi na bari wannan karin, ninki hudu yayi mata ya mike, da takardar rike a hannunshi, daya fita saida ya tsaya ya dauki ruwan sanyi. Tukunna ya fice daga gidan, haka ya shanye robar ruwan ko zata rage masa bugun zuciyar da yakeji. Daya hau titi sai layukan suka dinga bace masa, saboda kwata-kwata babu wata natsuwa a tare dashi, yawo ya dingayi kamar wanda aka aika duba gari, har aka kira sallar azahar, ya samu waje yayi parking a bakin wani karamin masallaci, inda yayi amfani da daya daga butocin wajen yayi alwala ya shiga sahu kamar sauran jama’a. Ba zaice ga tunanin da yakeyi ba, amman har akayi ruku’u, aka dago aka tafi sujud bai sani ba, kabbarar ladan ta shiga kunnenshi daga can nesa, saiya tafi ruku’u, tukunna ya kula da cewar sujud suka tafi, duk saiya rikice. Ya sallame sallar ya sake tayarwa yana bi, da aka idar ya gabatar da raka’ar farko data kubuce masa.

Yana ta jero Istigfar, wani dattijo da yake kusa dashi yace masa

“Yaro ka ragewa kanka tunani, komai mai wucewa ne kaji ko?”

Daya juya ya kalli dattijon, sai kwarjininshi ya cika masa ido sosai, daga yanayin shigarshi zaka san yana fama da rashin wadata ta bayyane, amman fuskarshi ta nuna tarin wadatar da zuciyarshi take ciki, haka murmushin shi ya nuna tsantar yardar da yake da ita akan Mahaliccin shi

“Nagode Baba”

Jabir ya tsinci kanshi da furtawa, ya kuma saka hannu a aljihunshi yana lalubawa, kudine da ba zaice ga yawansu ba, ya dunkulesu sosai kafin ya fito da hannunshi ya mikawa dattijon kamar maison suyi musabiha yana saka masa kudin a cikin hannunshi hadi da furta

“Allaah Ya kara lafiya”

Ya mike da sauri kafin Dattijon ya samu zarafin furta wani abu, harma Jabir ya fice daga masallacin. Wannan karin tsayawa yayi ya kula da hanya sosai harya karasa gidan Sa’adatu, sai dai ya samu gefe daga tsallake yayi parking din motar, jikinshi kamar wanda aka zarewa duk wani karfi haka ya dingaji, ba zaice ga lokacin daya dauka kafin ya iya tayar da motar ya karkatata ba. Ko daya shiga gidan ma, da murmushin karfin hali ya amsa gaisuwar Maigadi. Ya fito ya dauki envelope din daya hada da takardar ya shiga gidan. Yana sauke idanuwanshi akan Sa’adatu yaji bugun zuciyarshi na neman tsayawa. Saima ya nemi duk wani abu da yakeji ya rasa, wani irin shiru ya ratsa dakin. Lokacin da hawayenta ya fara sauka kuwa kallonta kawai yakeyi yana rasa abinda yakeji. 

Haka duk rokon data dingayi masa da wasu maganganunta suka dinga shiga kunnenshi suna wucewa wani waje cikin kwakwalwarshi kamar an danna recording, amman sunki karasawa zuciyarshi balle ya juyasu yaji tasirinsu, kuma harya kaita kofar gidansu ya ajiyeta, yaja motar ya karasa asibitin haka yakejin shi. Har zuwa yanzun dinma daya tuna baiyi sallar la’asar ba, saiya tashi ya shiga bayin yayo alwala, yanajin idanuwan Aisha akanshi harya idar da sallar, bai yarda sun hada idanuwa ba ya koma kan kujera ya zauna. Haka sukayi zaman jigum, garama Aisha daga baya ta sauko ta dauki tufa guda biyu, da yake an rigada an wanke, ta mika masa koriyar sanin yafi sonta, bai musa ba yar karba, haka ya cinye badon ya gane inda dandanon ya dosa ba. Da aka kira Magriba kuwa sai yace tayo alwala suyi sallar tare, bayajin karfin fita masallaci. Sai Aisha taja musu kafet din zuwa jikin bango, ta zauna ta mike kafafuwanta, sai shikuma ya kwanta, da yake kafet din nada girma, yayi filo da cinyarta, hannunta ta saka tana wasa da gashin kanshi batare da tace masa komai ba.

Haka kuma mutum hudu a gidansu Jabir din suka shigo suka samesu, ko motsi Jabir baiyi ba balle ya nuna alamar zai tashi, suma in akwai wanda ya damu bai nuna ba, yayi kokari wajen shiga hirar da suketa saka shi, abinci suka kawo musu daman, ana kiran Isha’i kuma sukayi musu sallama suka tafi. Yanzun ma a tare suka sakeyin sallar Isha’i shida Aisha, plantain ce soyayya, dankali, sai sauce din kwai, sai kuma lemuka, data zuba musu, haka Jabir ya dinga turawa, lemon ne kadai yasha ta dadin rai saboda yayi masa dadi, ga sanyin kuma yana ta ratsa makoshin shi. Likita ya shigo ya dan duba Aisha, yayi mata yan tambayoyi tukunna ya fita, tunda dai ba wani abu takeji yanayi mata ciwo ba zuwa yanzun, hutun dai suke bukatar tayi, kuma shi takeyi. Tarin bargunan da aka kawo musu, basu taba amfani dako daya ba, ko bude jakar ma Jabir baiyi ba, nasu daya dauko a gida suke amfani dashi, tunda akan gadon nan suke kwanciya shida Aisha, ko tace shi yake kwanciya, tunda ita dai rabinta akanshi take.

Bayan sun kwanta, yanajin Aisha tana addu’o’inta, kamar ko yaushe, sai da ta fara tofawa a hannuwanta tana shafa masa daga kai, fuska har kirjinshi, tukunna tayiwa kanta

“Ka karanta Suratul-Mulk kar bacci ya dauke ka”

Zuciyarshi ta fara fada masa da muryar Aisha, kafin ta maimata masa kalaman da suka zame mata jiki. Sunyi Islamiyya, Hajiya Hasina tayi wannan kokarin akansu, amman yana daya daga cikin yan gidansu da basuyi hadda ba, akwai dai surorin daya haddace, sai dai kafin auren Aisha, Suratul-Mulk da kuma Kahf basa cikinsu, sai bayan aurensu ne, yanda take saka shi karantawa duk dare kafin ya kwanta ya haddace, Kahf kuwa duk juma’a basa fashin karantawa, sai dai in basa tare, ta kuma tuna masa baiyi ba. Haka ya lumshe idanuwanshi yana fara karanto ayoyin, yana kuma jin kamar yana ganinsu ne a kwakwalwarshi. Daya idar bai bude idanuwan nashi ba saima sake rike Aisha da yayi, ko kadan baiyi zaton bacci zai dauke shi ba, sai gashi ya dauke shi, kuma bacci mai nauyi, idan ma yayi wani mafarki bai tuna ba sam.

Bacci yayi har asuba, haka yayo alwala ya saka kaya. Ya fita masallacin cikin asibitin yayi sallah, sai dai me, yana sako kafafuwan shi daga cikin masallacin muryar Sa’adatu tayi masa wani irin duka

“Jabir….dan Allaah Jabir”

Haka ya saka takalmin shi jikinshi na daukar dumi

“Nasani ai daman, nasan zaka rabu dani, amman saina haihu, haka mukayi da kai, nima idan kabarni zan samu ciki, wallahi zan samu…kaji, kai da ita duka kukace saina haihu na baku dan, ko ka manta? Ka kirata kaji, nasan ita bata manta ba, haka kace saina haihu, me yasa to zaka sake ni yanzun bayan ko ciki bani dashi?”

Hannu yakai kirjinshi inda zuciyarshi ke bugawa, sai yakejin zafin da takeyi masa harta cikin rigarshi yana jinshi yana ratsa tafinshi daya dora a wajen. Kokawa ya farayi da numfashin shi, har saida ya durkusa a wajen, mutane da suka zagaye shi suna tambayarshi ko lafiya yasa shi yin karfin halin mikewa, yana dan girgiza musu kai saboda bayajin koya gwada magana zai iya. Haka yake daga kafafuwanshi dakyar yana komawa cikin asibitin, yasan menene rashi, aida wayanshi ya rasa mahaifinshi, ko mahaifiyarshi da baisani ba, idan zaiyi mata addu’a bayan kowacce sallah sai zuciyarshi ta motsa.

Amman wannan rashine da mutuwa ta gifta a tsakani

Rashine da hakuri a cikinshi ya zama dole

Amman Sa’adatu fa? Bashi yasa hannu ya rabata da kanshi ba?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 47Tsakaninmu 49 >>

1 thought on “Tsakaninmu 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×