Skip to content
Part 47 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

A aurensu, da bai cika shekara ba har yanzun, sau nawa Jabir ya shafe kwanaki bakwai batare daya nemeta ba? Kamar wasu zasuce abune daya kamata ace ta saba dashi, ita da kanta ma tanajin ya kamata ace ta saba, sai dai sabon da yayi mata da kanshi fa? Ya zatayi da wannan bangaren? Duk wasu lokutta da yake zuwa mata, ta kiyaye su, da safe, ko da azahar, wasu ranakun da yamma likis, a wasu kuma bayan Magriba zuwa Isha’i. Ko abu ta dafa da yake so haka zata dinga jujjuya cokalinta cikin farantin, fuskarshi da yanayinta idan yana cin abincin ya dinga mata reto, sai tayi da gaske take iya samu taci. Wannan karin kuma sai takejin shirun nashi ya hade mata da wata kwantacciyar fargaba da batasan masominta ba.

Yau da ta bude ido ma, ta dauka asuba ce tayi, sai taga hudu da wasu yan mintina ne na safe, haka ta dinga juye-juye har aka kira sallah, to kuma sai ta kasa komawa bacci, tayi wanka, ta sake rigar baccinta zuwa wani riga da wando masu laushi ko a ido, jinta takeyi sakayau, kamar an kwashe duk wani nauyi da take dashi, har tana tunanin inda ace fita zatayi waje, a soma iska, tsaf iskar zata diba harda ita a cikin tarin ledoji da kananun abubuwan da zatayi gaba dasu, bugun zuciyarta ma jinshi takeyi tamkar ya rage karfi. Zuwa takwas na safe ta tabbatar bata da lafiya, sai dai babu inda zata nuna tace shine yake mata ciwon, ko da asibiti zatace bata da abinda zata fada daya wuce bata da lafiya. Batama nemi wahalar da kanta ba, kudi taba Baba maigadi ya siyo musu biredi, ta soya kwai ta hada shayi. Sai dai bata iya cin wani abin kirki ba, sai takejin wani abu ya rike mata makoshi yana hana abincin wucewa yanda ya kamata, shisa ta hakura da biredin da wainar kwan, ta karasa shanye ruwan shayin.

Kan kujera ta kwanta, kujerar da take kallon kofar shigowa, kujera ce mai zaman mutum biyu, shisama bata iya mike kafafunta yanda ya kamata ba, tajasu ta hade da jikinta tana dunkulewa waje daya, yau data dawo daga mikawa Baba maigadi abin karin shi bata sakawa kofar mukulli ba, ta kuma kafa mata ido wani abu na dukan zuciyarta da take cike da rauni, ta kuma dauki lokaci mai tsayin gaske a wannan yanayin, idanuwan nata da taji suna mata zafi cike da gajiyawa da kafesu da tayi waje daya yasa ta lumshe su, tana fatan bacci ya bata hadin kai ko zata samu saukin abinda takeji. Wayarta da take gefen kujera tayi kuka alamar shigowar sako, ko da taga daga bankin da take ajiya ne, wato First Bank, batayi mamaki ba, akwai matar da tace tana son kunun aya roba biyar, zobo roba biyar, to zata tura mata dubu biyar din. Sai dai data bude sakon, mikewa tayi zaune, ta duba, ta sake dubawa.

Lissafi na daya daga cikin darasin da take so, saboda a yayin da dalibai mafi rinjaye suke da tarin korafe-korafe dangane da fahimtarshi, ita tana cikin kalilan din da bai taba basu matsala ba. Sai gashi yau wasu tarin sifili da take gani bayan biyar din na neman rikita duk wata fahimtarta a fannin lissafi, har tana neman sifili nawa ne a cikin dubu, a cikin dubu dari, amman kamar an saka tsintsiya an share, haka take jin kwakwalwarta, sannan sunan wanda ya turo kudin yayi mata kama da irin business name din nan a madadin sunan mutum, duk da tasan ba abu bane mai yiwuwa, amman saita koma Instagram, ta lalubo matar nan, ta kuma tambaya idan ta tura mata kudi

“Ina ta kokari tun dazun, ina fama da matsalar network ne, da ya dan daidaita zan tura miki”

Shine amsar da matar ta bata, amsar data rigada ta sani tun kafin ma ta tura mata da tambayar, ta hadiyi wani abu daya tsaya mata a makoshi, sanda ta mike taje ta dauko robar ruwa ta dawo, hannuwanta rawa sukeyi, dakyar ma ta iya bude robar ruwan da ta kusan shanyewa, saita fahimci bushewar makoshinta bata da alaka da kishin ruwa. Sakon ta sake dubawa, bugun zuciyarta da bashi da karfi tun tashinta na kara raunana. Kuma har zuwa lokacin ta kasa hada lissafi balle ta gane nawane ta shiga asusunta, kamar kwakwalwarta na son kareta ne daga wani abu. Sai ta saka wayar a mukulli ta koma ta kwanta, ta dora wayar kan cikinta, tana jin nauyinta da nauyin kudin da suka shigo sun hade sun danne mata ciki, har numfashinta baya kai mata inda ya kamata. Ta riga ta hakura da baccin ma, ta dai juya kwanciya yafi a kirga tana neman yanda zataji dadi, bata bar falon ba sai da akayi azahar.

Da tayi sallah, saita wuce kitchen, ta dafa farar taliya, tayi sauce din manja mai kifi. Wai kuma dan ta karawa kanta abinyi, saita duba ta dauko sauran lettuce din da take dashi a fridge, harda cucumber, koren tattasai da kuma timatiri, ta yayyankasu dai-dai girman da takeso bayan ta wanke, lokacin da ta zubawa Baba Maigadi nashi, sai taji wata yunwa na mammayarta, tana mika masa kuwa ta dawo ta zuba, bakinta da cikinta sai magiya sukeyi mata kafin ta fara amsa rokonsu, aikuwa taci sosai, dan har karawa tayi. Da ta sha ruwa tayi hamdala, sai taji kaso fiye da goma cikin dari na rashin karfin jikinta ya kau, data kwanta kuma sai baccin da take ta nema ya kawo mata ziyara. Bata dade da bude idanuwanta ba, tana kwancen aka kira la’asar, ta samu ta mike, saida ta sake watsa ruwa dan ta wartsake sosai tukunna ta dauro alwala ta fito, tayi sallah, data idar saita ji tana son sake kayan jikinta, ta kuwa nemi doguwar rigar atamfa ta saka, sai wata hula data shiga da kalar atamfar.

Har mai ta murza a kafafuwanta da hannuwa, ta shafa man lebe, ta fita zuwa falo, tana hango wayarta taji zuciyarta ta buga, lokaci daya kudin data manta da shigarsu suka dawo mata, lokacin kuma saiya hade da bugawar karfe hudu da minti arba’in akan agogon data daga ido ta kalla

“Biyar ta kusa”

Ta furta a ranta
Abinda kuma bata sani ba shine tazarar dake tsakanin bugawar karfe biyar din, tafi tazarar dake tsakaninta da kaddarar da take tunkarota

Kaddarar da Jabir ya turo kofar dakin a dai-dai wannan lokacin, dauke da ita a cikin envelope din da shekaru zasu zo su wuce duk idan taga takadar ruwan kasa abinda yake fado mata kenan. Da sallama a bakin shi ya shigo, Sa’adatu ta amsa a hankali, idanuwanta na yawo a fuskarshi data rame mata, idanuwanshi da suka fada cikin wani yanayi da bata taba gani ba, kuma daya tako cikin dakin har inda takw tsaye sai takejin kamar a cikin zuciyarta yayi yar gajeriyar tafiyar. Daya kama hannunta ya jata kan kujera sai ta soma maida numfashi tamkar wadda tayi gudu saboda nauyin da takejin zuciyarta tayi mata.

“Sa’adatu”

Jabir ya kira yana saka idanuwanshi cikin nata, idanuwan da take gani cike fal da wani abu, wani abu kamar ana farautar nutsuwar shi, batasan lokacin data mika hannu tana tallafar kuncinshi na gefen dama ba.

“Dan Allaah…”

Rokon ya fito mata cikin rawar murya batare data san takaimaiman abinda take roka ba, saiya girgiza mata kai, yana kuma kama hannunta ya sauke daga fuskar shi, kamar wanda aka shake ya soma magana.

“Na nemi duk wasu kalamai dana iya tun tasowata Sa’adatu, a satin nan gabaki daya, amman dana zo hadasu yanda zasuyi mun sauki sai inga ashe babu abinda na iya…”

Cikin wata irin bugun zuciya take girgiza masa nata kan, tana kuma saurin katse shi da.

“To karka fada mana, koma menene, ni ai ba sai naji ba.”

Ba jikinta kadai yake bata kome Jabir din yake son fada ba zataso jinshi ba, harda yanayin shi, harda yanda yake kokawa wajen fito da kalaman.

“Na tura miki kudi dazun…”

Ya fadi, yaja numfashi ya fitar a hankali

“Miliyan biyar din da mukayi ne…wannan.”

Yayi maganar yana mika mata envelope din daya shigo dashi

“Takardar gidan nan ne, angama komai sunanki ne akai, sai maganar makarantarki, nace miki zakiyi karatu, kuma zakiyi, zan dauki nauyin komai har kigama…”

Bari jikinta yakeyi, kuma ta tabbata daga ciki harta waje jikin nata yake rawa, ai daman tasan zai dauki dawainiyar karatunta, kudin yin hakan ba wani abin azo a gani bane a wajen shi, ta kuma san zai bata miliyan biyar din da sukace, da ba za’a bata ba akan me za’a ambata mata su, gidan ne, gidan ne bata taba hangowa ba, sai kuma dalilin da yasa yake mata wannan maganganun yanzun bayan ko cikin ma bata rigada ta samu ba balle ta haifeshi, ta dauka saita haifa, ta kuma mika masa, ya mikawa Aisha tukunna za’a fara duk wannan lissafin.

“Aisha na da ciki.”

Ya fadi kalmomi guda hudu da taji sunyi mata irin dirar da maganganun Aisha suka tabayi mata a ranar da tayi mata tayin amincewa da kudurinsu, da ta kalli Jabir wannan karin sai taji rawar jikin da takeyi ta tsaya, zuciyarta ce kawai take kai kawo a cikin kirjinta.

“Tana da ciki, Aisha na da ciki.”

Ya sake maimaitawa, yana janye idanuwanshi daga cikin nata.

“A tare da takardar gidan nan, akwai wata takardar”

Saida ya hadiyi wani abu da shirun dakin yasa taji wucewar shi kafin ya iya cigaba da magana, muryarshi na fitowa da raunin dayasa Sa’adatu taji jiri na kawo mata mamaya.

“Na sake ki saki daya.”

Shiru.
Wani irin shiru da kaifin shi zai iya yanka gilashi
Shine abinda ya gifta a cikin dakin

“Sakinki nayi.”

Haka Tahir yace mata, sai dai a ranar, kuma a lokacin, ba zata taba mantawa ba, wani haskene ya gilma mata, hasken da ya dishe mata ganin Tahir. Sai dai babu wannan hasken yau, tarau take kallon Jabir daya kasa dagowa su sake hada ido, sannan hankalinta bai bar jikinta ba, wancen lokacin ta samu wannan Rahamar, ta bacewar tunani, ta samu ta shiga shock duk dana dan wani lokaci ne, yau kuwa duk wani abu da yake faruwa a cikin hayyacinta take jinta, ko dan daman rabuwar abune da yazo tare da auren? To amman ai ba haka sukayi ba, sai ta samu ciki, saita haihu, ba haka sukayi ba. A cikin abinda yake faruwa, zubar hawayenta ne bataji ba, ko kadan batasan suna zubowa ba har wasu na ture wasu, idanuwanta dai suna mata wani irin zafi da babu kalaman da zasu misalta shi, ta kuma kamo hannuwan Jabir ta rike a cikin nata

“Nasani ai daman, nasan zaka rabu dani, amman saina haihu, haka mukayi da kai, nima idan kabarni zan samu ciki, wallahi zan samu…kaji, kai da ita duka kukace saina haihu na baku dan, ko ka manta? Ka kirata kaji, nasan ita bata manta ba, haka kace saina haihu, me yasa to zaka sake ni yanzun bayan ko ciki bani dashi?”

Tana jin shi yana kokarin zame hannuwanshi daga cikin nata, shisa ta kara rikon da tayi musu, so takeyi ya kalleta amman yaki yin hakan.

“Kaji…dan Allaah, kace ka janye sakin, kabarni in haihu tukunna, kaine kace saina haihu.”

Maganar takeyi tana kukan da batama san tanayi ba, inda wani yana neman cikakkiyar ma’anar rudani, a wannan lokacin Sa’adatu kawai za’a nuna batare da an tsaya wani dogon bayani ba, amman sai Jabir yasa karfin shi da yafi nata yana zame hannuwanshi hadi da mikewa, itama saita mike, sai dai batasan kafafuwanta sunyi sanyi ba saida suka kasa daukarta tajita zaune a kasa, kafafuwanshi ta kama tana rungumewa.

“Dan Allaah, nima zan samu cikin…kaji”

Rankwafowa yayi, ya kama hannuwanta yana bambareta daga jikinshi.

“Sa’adatu, please…”

Ya furta a tsakanin numfashi, sai ta sake kamo kafafuwan nashi

“Jabir….dan Allaah Jabir.”

A karo na farko da ta furta sunanshi a fili, ta kuma ji yanda hakan yasa shi wani irin jan numfashi, ya dauki mintina biyu kafin ya sake rankwafowa yana kama hannuwanta, jikinta yayi sanyi zuwa lokacin, kuma da alama shima din nashi jikin a sanyaye yake, saboda bataji irin karfin dazun a tare dashi ba, daya rabata da jikinshi, ya saketa yana takawa cikin nufin nufar kofar saita kasa binshi, banda numfarfashi babu abinda takeyi

“Ba zaka barni in samu cikin ba nima? Da gaske rabani da kanka zakayi bayan ba haka mukayi ba?”

Bai juya ba, tafiya yaci gaba dayi harya bude kofar ya fita yana rufewa da wani abu tare da Sa’adatu da batasan a bude yake ba. Ba zatace tsakanin rarrafe da tafiya, wanne ne ya kaita daki ba, hijabinta da yake ninke tare da sallaya ta dauka ta saka a jikinta, sai ajiyar zuciya takeyi saboda kukan da yaki tsaya mata har lokacin, silipas din shiga bayi ta saka a kafarta, bata kuma yi tunanin daukar wani abu ba balle kuma wani abu kulle gida, kawai kofar ta kama ta bude, haka bata kula da motar Jabir da bai rigada ya fita daga gidan ba, balle maigadin da yake tambayarta ko lafiya, ganin kukan da takeyi. Da kanta ta fara kiciniya da kofar fita, saiya kama ya bude mata, hanya ta mika kawai ta soma tafiya. Bata damu da hon din da ake dannawa a bayanta kamar idan bata tsaya ba mai motar zaibi takanta ya wuce, ballantana ko juyawa ne tayi, tafiya kawai takeyi batare data san inda take jefa kafarta ba.

Hakan Jabir ya fahimta, shisa ya samu gefe yayi parking din motar ya fita yana takawa da sassarfa ya cimmata, yana kuma riko hannunta, sai dai data juyo taga shine saita fisge hannun nata tana cigaba da tafiya

“Ina zakije?”

Cewar Jabir din yana sake kokarin riko hannunta da ta dago tana buge nashi hannun

“Ka kyaleni”

Ta fadi kamar karamar yarinyar da akayiwa babban laifi

“Gida zakije? Ki tsaya in kaiki”

Wannan karin Jabir yayi magana yana riko hannun nata, ya kuma saka karfi yanda batama yi tunanin zata iya kwacewa ba, hakan yasa ta tsaya

“Ka sakeni, ina ruwanka da inda zanje? Ba ka rabani da kai ba?”

Ta karasa maganar wasu hawayen na zubo mata.

“Kizo in kaiki gidan…”

Kai ta girgiza masa, wani abune yake kadawa a duka ilahirin jikinta.

“Napep zan hau.”

Nashi kan ya girgiza mata

“Ba zaki hau napep ba, kizo in kaiki gida ko kuma ki koma gida, karki sa muja maganar nan Sa’adatu, dan Allaah.”

Batasan me yayi tasiri ba, yanayin muryarshi, fuskarshi, ko kuma rokon da ya karashe maganar dashi, saita bishi, yana rike da hannunta har wajen motarshi, kuma shi din ya bude mata ta shiga, ya rufe murfin ya zagaya ya zauna ya kunna motar, tukunna yaja, wata tafiya da Sa’adatu bata tabayin mai tsayinta ba, har kofar gida ya kaita, sai da ta kalle shi tukunna tace,

“Da gaske ba zaka barni in haihu ba nima?”

Shiru yayi, idanuwanshi kafe da steering wheel din motar, ta bashi dakika, minti, daya, biyu, har zuwa kusan biyar, amman ko motsawa baiyi ba, shirun shi taji ya daketa, wani irin duka da yasa kirjinta daukar dumi, ya kuma kafar mata da hawayen da suketa zubowa, sai kawai ta kama murfin motar ta bude ta fita, ta taka tana shiga cikin gidansu batare data ko juya ba, kanta tsaye ta shiga, har kuma tana mamakin jin sallamar da ta kubce mata, sallamar da take da yakinin sabo dayine kawai yasa ta samu zarafin yinta. Fa’iza da take zaune tana kokarin kunna karamar radio ta amsa, tana kuma dagowa da mamaki bayyane a fuskarta ta kalli Sa’adatu

Wani abu ya faru a lokacin da suka hada idanuwa
Wani abu da babu shi a lissafin Sa’adatu lokacin data karbi tayinsu Jabir

Ta saka hannu a takardar a wancen lokacin, ta kuma rigadata ta yarda zata haihu ta basu yaro ko yarinya su bata kudadenta, a wancen lokacin kudin kawai take kallo ashe, yawansu ne abinda ya rufe mata ido, ko lokacin bikin, yanda taga ‘yan uwanta na tsaye wajen ganin komai ya tafi yanda ya kamata, taji wani iri, taji kamar bata kyauta musu ba, kamar ta dora fatansu kan wani tsani ne da zata kama da hannunta ta kayar, a farko-farko kuma duk idan suna bata shawara akan auren sai tayi dariya a ranta, tana jin auren da yake da lokaci? Auren da yake jiran cikar lokaci ya kare?

To ashe iya nan tunanin nata ya tsaya
Bata hango bayan karewar auren ba
Bata hango me zai faru ba balle kuma ta inda zata fara musu bayani.

<< Tsakaninmu 46Tsakaninmu 48 >>

3 thoughts on “Tsakaninmu 47”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.