Saida ta goya Muhd sannan ta yo waje riƙe da tabarma, su Hasana suka amsa suka bi bayanta.
Mutumin yana tsaye daga jikin motarsa, Ummu Hani ta ƙarasa har ƙas ta gaida shi, kamin ta ce, "Ga tabarma can na shinfiɗa a soro." Ba musu ya bi bayanta dan ko yaushe ya zo tun Abbansu na da rai a soro ake masa shinfiɗa.
Kuma gaisawa su ka yi, kamin ya ce, "Ashe kuma abinda ya faru kenan? Allah ya jiƙanta ban sani ba sai da na shigo garin nake jin labari, Allah ya mata rahama."
"Amin. . .