Skip to content
Part 14 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Na dube ta a ina kika samu hotunansa kuma ya aka yi kika san shi ne?

“Su’ada ke sanyawa a DP ko a status, saboda sha’awar da suke ba ni nake cirewa, ita kuma ta faɗa mini yayanta ne da ke zaune a London. Mene ne aibun wannan bawan Allah da Allah ya kawo miki? Maimakon ki kama rawa sai ki zauna kina hawaye.”

Na balla mata harara ai ke da yake yar gayyar son tsofaffi ce dole ki ce haka.”

Wayar ta miƙo hannu ta karɓa tana ƙara kallon hotunan “Yanzu wannan shi ne tsoho Ummu lallai ne, Allah ya yi miki sakayya ya dubi ɗawainiyarki daga abin da ya same ki ya kawo miki miji ɗaya da ɗaya ki nemi yi ma arziƙi ƙulli.

Ki sake shawara wane tsufa ne a nan saboda Allah mene ne a auren yaran dace kawai ake fata.

Kuma ma in don mata da yake da ita masu kuɗin nan ba ma lallai ya haɗa ku ba, kin ce kuma yaransa uku kacal.”

Na dube ta “Su waye waɗannan da yake hotuna da su?

Ta yarfe hannu “Ban san su ba wallahi, na fi tunanin yan Family dinsu ne.

Ki yi addu’a kawai.

Na zubo wasu sabbin hawayen “Shi kenan Abakar Nabila?

Ta dafa kafaɗata “Kowa da ƙaddararsa Ummu Radiyya, ki yi addu’a kawai ƙila ba alheri a ci gaban zaman naku shi ya sa da ya fito bai waiwaye ki ba don Allah ma wane Abakar za ki zauna jira daga zuwa sau ɗaya shi kenan, bai kuma bi ta kanki ba.

In sha Allah wannan zaɓi ne daga Allah ki ba Mama haƙuri.”

Ban ƙara magana ba hawaye na yi ta sharewa ita kuma tana ba ni baki.

Da ta tafi na share fuskata na fita inda Hassana da Mama ke aiki na miƙa hannu don karɓar bokitin da ke gaban Mama in taya ta aikin ta ɗauke na yi sansarai fushi ne mai tsanani kwance kan fuskarta, ɗaki na koma na kwanta.

Kwanakin da suka biyo baya kullum sai Baba Isah ya zo su haɗu shi da Mama da Baba Ali maganar dai ɗaya ce in amince da Bashir Lema.

Sati guda aka ɗauka na aminta da muradinsu na ba zuciyata haƙuri da Abakar ai kam ba a kwana ba magabatansa suka iso da kuɗin da aka sara musu.

Ina kwance bayan fitar Baba Ali da Baba Isah da suka kawo ma Mama kuɗin dubu dari huɗu da hamsin, ta shigo ta ce in tashi zaune gefe na ta zauna kalamai na kwantar da hankali da misalai ta yi ta ba ni na dalilanta na dagewa in yi haƙuri in auri Bashir Lema tana sa rai zai yi mini ruƙo na ƙwarai.

Jin ta nake ina kaɗa kai da ta gama ta ajiye mini kuɗaɗen a kan ƙafata

 “Ga sadakinki nan har da kuɗin da za ki yi sayayya Ummu Radiyya.”

Ta tashi ta fita na yi ta kallon kuɗin kamar a ranar na fara ganin kuɗi masu yawa, ban gushe ina zaune wurin ba Aunty Ya gana da Lubna suka iso murna suke matsananciya Aunty Ya gana ta shigo ta jawo ni ganin kuɗin a kusa da ni ta sanya hannu ta ɗauka muka fita a falo muka zauna suna ƙirga kuɗaɗen, dubu ɗari biyu Aunty Ya gana ta ware bayan ta kira yayarta a Maiduguri ta tambaye ta nawa za a yi ma amarya haɗi na turaruka masu kyau.

Ta faɗi mata ta ce sauran sai a sawo mini suturu in ƙara kan waɗanda nake da su, Lubna ta tashi ta shiga ɗaki akwatunan aurena ta fito da su suka yi ta ciro kayan ciki a cikin kala ashirin da biyar da aka sanyo mini saura kala sha biyar ne ban ɗinka ba.

Lubna ta ce tana ganin in ƙaro kala huɗu masu tsada sun ishe ni na haɗa da waɗannan.

Aunty Ya gana ta ce mutumin nan fa mai hali ne kuma family ɗinsu ma masu shi ne waɗannan kayan ba su yi arha ba? Sai in ga da canzo su aka yi da masu tsada.

Lubna ta ce a dai yi musu ɗinki haɗaɗde ba mai cewa

Ya gana ta ce shi kenan. Idan zan wuce sai na tafi da su na ba telana za a tsara mata ɗinkuna.

Sun tafi Mama ta ba ni maganin sanyi da ta dafa da kanta dama da ta dafa ma Hassana  tana ba ni ta ce in sha.

Sai daren ranar Bashir Lema ya sake  dawowa wurina rabo na da shi tun zuwan shi na biyu gaishe shi na yi na kame bakina na ɓame.

Ya tambaye ni game da shirina a bikin na ce ba zan yi komai ba, ya ce ya za a yi ba za a yi komai ba? Kuɗaɗe masu kauri ya ba ni na karɓa da godiya sallama ya yi mini na shiga gida.

Mama na tare da Baba hakan ya hana ni nuna mata kuɗin na nemi wuri na adana su na kwanta.

Da safe ban tashi da wuri ba ko karyawa ban tashi na yi ba Hassana ta yi komai suka fita islamiyya ita da Husaini daga inda nake kwance na jiyo shesshekar Mama tana magana cikin kuka “Ban san ya zan yi ba biki na ta ƙaratowa ba komai a hannu na abin da za a ci a bikin kayan gara hatta kayan kitchen ban gama saya mata ba.

Muryar Baba na jiyo yana faɗin”Ki yi shiru ki kwantar da hankalinki in sha Allah zan yi komai, yau ma Kano za ni zan samo kuɗaɗe ki nutsu Hauwa’u.

Bari na fita sai na dawo.”

Jin shiru na tabbatar ya tafin tausayi Mama ta ba ni irin wannan alƙawarin na  zai samo kuɗi ya ba ta ta yi hidima yau na uku kenan na ji ya yi mata.

Na miƙe na fita zaune take a ƙasa ta haɗa kai da kujera, jin motsina sai ta ɗago tana goge fuskarta.

Zama na yi na ajiye mata kuɗaɗen da Bashir Lema ya ba ni ta ce na mene ne? Na ce shi ya ba ni.

Ta ce “Shi wa? Ko da wasa ban ji zan iya ambaton sunansa ba sai na ce mata “Da ya zo da daddare ya ba ni, ki ɗauke su Mama ki rage hidimar da ke kanki . Kayan kitchen ɗina ma ki ɗaukar mata.”

Ta dube ni da sauri “Ke kuma fa?

Na ce “Ba ya ce duka zai saya ba? Ta girgiza kai “Ba zai kyautu a biye maganarsa ba a kai ki zagargar.”

Na ce “Da na san ba zan yi karatun ba da ban biya kuɗina ba da kin ƙara.

Na yi shiru ina jin ciwon kuɗaɗen nawa  da na sha wahalar  ɗinki suka tafi a banza. Albarka Mama ta yi ta sanya mini na tashi na koma ɗaki na kwaso kayana wanki na hau yi sau biyu Mama na cewa ba zan tsaya na karya ba?

Na ce sai na gama.

Na cika igiyarmu don har da na Mama da Hanan, na tafi igiyar wurin su Aya na fara shanya Fa’iza ta fito wani kallo ta jefa mini kafin ta ce “Su Ummu manya, auren ma ba za a gayyace mu ba?

Na waiwayo na dube ta cike da mamaki “Wane aure ne za a gayyace ku Fa’iza?

Ta yi mini wani malalacin kallo”Au ba ki sani ba lallai ma Ummu Radiyya tun ba ki je ba?

Rasa abin da zan ce mata na yi Aya ta iso wurin tambayar ɗyarta ta yi me ya faru tsakanin mu?

Ta taɓe baki tana faɗin bikina ta tambaye ni ban sa ta ciki ba shi ne nake mata wasu maganganu.

Uwar ma ta taɓe baki “Ai daga ita har uwar tun ba ta je gidan mai kuɗin ba sun fara ji da kai.

Saurin kallon ta na yi sai kuma na mayar da kaina kan shanyar har kuma na kammala ban ƙara ko kallon su ba ita da yar ta ta tana ta zubo maganganun da za ka tabbatar tana cikin matsananciyar hassada.

Na ɗauki bokitina na koma wurin mu na iske Aunty Larai ta zo gaishe ta na yi zan shige ɗaki ta ce “Zo zauna.”

Cikina ya kaɗa don sai na ji kamar zancen Nabila za ta yi mini na zauna nesa da ita “Ina son fara yi miki gyara Ummu, don mutanen da za ki shiga cikin su masu wayewa ne ƙwarai, Malam ya shaida mini 300k aka amsa me kika shirya yi da su na mata bayanin yadda su Aunty Ya gana suka yi sauran zan biya kudin ɗinkunan da za a yi mini, zan sayi takalma da mayafai sauran sai a biya kudin gyaran jiki.

Kai ta girgiza “Ba da kuɗinki za ki biya ba.”

Ta janyo jakarta ta fito da wayarta ta yi kira “Yawwa angon Ummu za ka kira mini ina son ganin sa.”

Shiru ta yi ta ɗan saurara sai kuma ta ce “To mene ne don babban Mutum ne? Abin da dai na sani ɗiyata yake so in ba shi don haka ina neman shi kuɗaɗen gyaranta zai ba ni.

Ta ajiye wayar “Ki shirya mu shiga kasuwar ki yi sayayyar.”

Wanka na yi ko karyawar ban yi ba don hakanan nake ji na ban jin yunwa, muka yi ma Mama sallama muka fita.

Kai tsaye kasuwar muka shiga na sayi duk abubuwan da nake so, takalma mayafai sai wasu material da suka burge ni na sayi kala goma muka zauna aka ɗinka mana.

Aunty Ya gana ma ta kira ni ta faɗa mini kuɗaɗen da mai ɗinki ya caza, na jinjina tsadar sai dai fa telanta maye ne, na ce idan na koma gida Husaini zai kawo mata.

Da muka gama da kasuwar gidanta Aunty Larai ta ce mu tafi. Da yamma muna zaune Bashir Lema ya iso tashi na yi na shiga ciki ina sauraren su bayan gaisuwa ta yi mishi bayanin kuɗaɗen gyaran amarya ta tambaye shi ya ce ta ba shi acc no suna shiga wayarta ko razana ta yi da yawan su ta ce “Ba su yi yawa ba Yallaɓai?

Ya ce “Amaryata mai tsada ce, a gyara mini ita da kyau.”

Da ya tafi ta shigo ita ma maganin sanyi ta ba ni ta ce “Kai Ummu ma sha Allah kin yi miji ga shi haɗaɗɗe ɗan gaye ga kuɗi ba ma haɗi da na baya Allah ya kashe ya ba ki.”

Shiru na yi ina duban ta ni kaɗai na san abin da nake faɗi a raina.

A nan gidan na kwana mun yi waya da shi ya ce ya je bai same ni ba me ya sa da ya zo ban fito ba?

Na ce ai wurin Aunty Larai ya zo.

Muka yi yan maganganunmu da shi ne mai yi, muka yi sallama da safe na tafi gida Aunty Larai ta ce sai ana saura sati guda za ta zo ta ɗauke ni a fara gyaran jiki.

Na koma na samu Mama ta haɗa kuɗi za ta ba da a haɗo ma Hassana turaruka, na ce ta bari idan aka kawo nawa sai a ɗibar mata.

Nabila ta shigo wai kuɗinsu fa na yammatan amarya?

Wani kallo na yi mata na ce “Ka ji wani sanabe to me za ku yi sai ka ce wata budurwa?

Ta  juya ido “Shagali, za mu yi wallahi.

Da ya zo da daddare na yi mata waya tare  muka isa falon Baba da ya ce idan ya zo mu dinga hira a can, babban mutum kamar shi bai cancanci a bar shi waje ba.

Tare da ita muka gaishe shi sai na ji Malama Nabila tsit ta kasa faɗin komai duk cika bakin da take, sai da zai tafi ya yi mata kyautar girma da ta gigita ta ta, ni ma ya ba ni.

Sai da ya tafi  muka fita na yi mata rakiya tana ta juya kuɗaɗen “Ke ashe hoto cutar bawan Allan nan yake ga kyau ga Naira tsakani da Allah ya haɗe.”

 Na ja tsaki ina girgiza kai “Kowa dai maganar kenan kyau da kuɗi.”

Ta galla mini harara “To me ake so? Kyan halin ma akwai shi kin sani. Ni yanzu waɗannan kuɗaɗen gobe sai kasuwa na darzo kayan da zan gwangwaje a bikin.”

Na yi yar dariya “A lallai kin caɓa.”

Ta yi yar dariya”Da gaske Ummu, karin maganar hausawa da suke  cewa wani hani ga Allah baiwa ne. Sosai nake taya ki murna Allah ya kaɗe duk fitinar da za ta taso a auren.”

A raina na ce Amin. Sai ta fara tsokana ta tahowar Baba ta sa muka rabu na koma gida.

<< Ummu Radiyya 13Ummu Radiyya 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×