Skip to content
Part 20 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Ya faɗa toilet ya yi wanka ya fito ina zaune bakin gado tambaya ta ya yi akwai damuwa na ce Babu ya ba ni feck ya fita ban ko bi shi da kallo ba wanka na shiga na fito na gyara jikina.

Kamar na sauka ƙasa daga masu gidan ba su nan sai dai na zauna na janyo wayata kiran Husaini ya shigo na ɗaga ina mishi tsiyar bai zo gidana ba, ya ba ni haƙuri na ce To ka zo yau akwai abin da na ajiye maka ya nace sai na faɗa mishi na ce sai ya zo.

Usaini da naci ya ƙi bari na sai da na faɗa mishi tsohuwar wayata na yi niyyar ba shi, ai kam ya ce ga shi nan dariya kawai na yi sanin dama za a yi haka, wayarsa da yake amfani da ita ta tashi aiki da ƙyar ya samu Mama ta ba shi ya sayi  keypad wadda ba a son ransa ya yarda ya riƙe ta ba sai don sanin ba shi da hanyar da zai samu android.

Nan na share zaman jiran shi har aka yi azahar, yunwar cikina ta sauko da ni Basira ta kammala girki, madara na kwaɓa da ruwan zafi na koma sama na sha abina.

Sai uku ya fara kira na yana tambaya ta kwatancen gidan ƙasa na sauko cike da ƙosawa,  ya iso a harabar gidan ya same ni ina jiran shi na ce “Na manta in ce ka taho mini da Hanan.”

Ya yi dariya “Ina zan iya kayan Hanan? Muka shiga ciki muka zauna a falon ƙasa na kwaso mashi abincin Basira yana ci muna hira ya ce “Ki fara ba ni in dafe Aunty.”

Na yi dariya na tashi na hau sama na sauko da ita  ya karɓa duka biyun har sabuwar da aka sawo mini.

Na ce “Wai me ya hana ka zuwa har sai yanzu?

Ya shafa kansa “Ban da ko sisi nake faɗa miki, da ƙyar na samu Mama ta ba ni 300 na haɗa da cin tracking.”

Na yi murmushi “Ashe komawa a ƙafa ya kama ka.”

Ya ce “Haba dai na zo gidanki na koma a ƙasa?

Na ce “Ai ka je gidan Hassana ni kuma sai da na roƙa.”

Ya ce “Bari ki ji, kin san ƙanen Malam Mahir abokina shi ya ja ni gidan.”

Zan yi magana muka ji horn ta glasan window kuma muka ga sulalowar mota cikin gidan.

Muna nan suka shigo Dina ke gaba ta ce mana Sannunku wanda dama shi ke haɗa ni da ita ina kuma jin daɗin rashin raini ko wulaƙanci tsakanina da ita iyaka ta karena ba ni baka ba ni korarka, sauran wucewa suka yi Husaini ya bi su da kallon mamaki har suka shige ya juyo gare ni da zummar magana babansu ya shigo da fara’a ya dubi Husaini shi kuma ya mike yana gaishe shi ya tambaye shi su Mama.

Sama ya yi na ce ma Husaini ina zuwa ya ce shi kam wucewa zai yi, kuɗin da na sanyo a aljihun doguwar rigata na ba shi dubu goma ne na ce ya kai ma Mama biyar ya riƙe biyar, kamar ya goya ni na wuce kitchen ina dariyar irin riƙon da ya yi ma kuɗin na ce ya gaida mini Mama.

Ruwa na ɗaukar ma ogan na wuce sama kaɗan ya sha ya nuna mini ledojin da ya shigo da su na sauka saman carpet ina buɗewa kayan ƙwalam ne irin su bugger na ci iya cina na bar sauran su suka zame mini abincin  dare don ko da ya gayyace ni cin abincin da aka yi order tare da ya’yansa ban fita ba jira na yi suka gama ya zauna kallon labarai suna tare da shi sai da ya gama ya same ni muka kwanta.

Da safe da ya ce mu sauka mu karya na ce a’a ba kamar yadda yake mini ba da na ce a’a yake ƙyale ni cewa ya yi ba zai bari yunwa ta kama ni ba ya kula ban son cin abinci.

Ya tasa ni muka sauka ƙasa, sun hallara muka ja kujeru suka gaishe da mahaifinsu Dina ta ce mini sannu na ce mata ya mura kamar yadda mahaifinta na ji yana faɗi mura take.

Bai taɓa komai ba zuba mini ido ya yi sai da na zuba ya kuma ga ina karyawar, abin da ya dagula ran Amal ba ta gama ba ta tashi da ya tambayi dalilin tashin ta ce phone ɗinta za ta ɗauko sai dai har kowa ya gama ba ko ɓurɓushinta.

Sama muka koma ya kuma kasance tare da ni har aka kammala girki daga ni sai shi da ya sa ma ido sai da na ci muka ci su take away Direbansa ya yo musu, sai la’asar suka nemi ya fita da su su sha ice cream bai yi mini tayin fitar ba suka fita abin su.

Tun daga ranar bai ƙara yarda sun ci abinci ba tare da ni ba duk da su abincin safe kawai suke cin na Basira.

Kwanan su takwas da dawowa na raka wasu baƙi da na yi, don duk nisan gidana ana yawan kawo mini ziyara, zai yi wahala rana ta fito ta faɗi ban yi baƙo ba, Amal da Suhaima su yi ta kallon su suna taɓa baki akwai ranar da na ji Amal na faɗa ma Suhaima ita ba za ta iya zaman garin nan ba gida a takure a yi ta damun su da wasu shara, kullum sai tarkacen mutane sun zo musu ga motocinsu na gidan Haj nan ba filin ajiyewa.

Idan kana son fita sai ka je gidanta ita kuma ta ishe su da faɗa.

Ni dai na raɓa su na wuce sai dare muna cin abinci suka zo ita da Suhaima suka tayar mishi da rikici su ba za su zauna garin nan ba za su koma London ya so lallaɓa su su bari su yi watanni ukun da za su yi hutun Suhaima ya ƙare ta koma ta kammala karatunta da ya rage shekara biyu fir suka ƙi suka yi zuciya suka shige ɗaki.

Kwana biyu aka yi yana rarrashi bai samo kansu ba abin da ya fi ɗaga mishi hankali abinci da suka daina fitowa su nema bai san da ya fita za su aika a sawo musu ni dai na baza ido ina kallon ikon mai sama zarya ya fara wurin Haj yana son shawo kanta yaran su koma Turai ita kuma ta ja ta tsaya in dai ita ta haife shi ya gama zama can ya dawo nan yaransa su yi aure har mutane ya kawo mata kan ta yi haƙuri Suhaima ta kammala karatunta sai su dawo ban san ya suke ciki ba sai da aka yi sati guda na ji an kunna music a falon ƙasa daga saman na leƙo Suhaima da Amal ne ke rawa na rasa

dalilin annashuwar da na gan su ciki na koma dai na zauna har sai da ya shigo ya yi mini bayani su Suhaima za su koma London idan na ce ban ji daɗi ba na yi ƙarya amma a fuska ban nuna ba na yi addu’ar Allah ya kai su lafiya.

Bayan tafiyar su zaman mu ya dawo mai daɗi cikin wata uku da ya yi da ni duk wanda ya gan ni zai ce dama za ki yi ƙiba Ummu Radiyya kin yi kyau matuƙa.

Murmushi kawai nake ni kaina na san na sauya duk da dai ƙibar ba wata ba ce na murje.

Ranar da na cika watanni uku da daddare mun zo kwanciya ya ce na ba shi hankalina na nutsu ganin yadda shi ma ya yi “Da farko zan soma da ba ki haƙuri tun farko ban faɗa miki watanni uku kawai zan yi da ke na koma London.”

Wani iri na ji da ya sa ni saurin duban shi  “Yes. Ya faɗi yana kallona ya kama hannuna ya sanya cikin nashi  “Ki yi haƙuri shekaru biyu kacal zan yi zan ajiye aikina in dawo Nigeria gabaɗaya mu ci gaba da rayuwarmu.

Zan fi son na tafi da ke domin barin ki kamar na bar wani ɓangare na ne, ina son ki so mai matuƙar yawa Ummu Radiyya.

Karatun Suhaima da ya rage shekaru biyu shi zai tilasta ni komawa, idan na ce na tafi da ke rayuwar London ba irin Nigeria ba ce akwai kashe kuɗi sosai zan fi so ki yi mini wannan haƙurin alfarma ce nake nema a wurin ki.”

Bayan hannuna na sa na share idona wasu hawayen suka ƙara tahowa ya kamo ni jikinsa yana shafa bayana da faɗa mini kalamai na lallashi kusan haka muka kwana da safe na tashi ƙozai-ƙozai ya sanya ni na shirya muka tafi gidan Haj

Yana yi mata bayanin komawar shi London ta birkice ta ja ta tsaya kan ba wani karatu da Suhaima za ta ƙarasa a can nan ma akwai makarantu su dawo ta ƙarasa anan. Amma tabbas ba ta yarda ya tafi ya bar ni ba har shekara biyu, sai ya ce mata kama gida a London akwai cin kuɗi amma idan ta yarda ya tafi da ni ya haɗa ni da Farida kamar yadda ya ambaci sunan to gidansa na can akwai Space.

Hannu Haj ta shiga kaɗawa ta ce Haram ni ba azzaluma ba ce da zan bari a kai yarinyar mutane wurin matar nan ita da ya’yanta, amma tabbas ba ka tafiya ka bar Ummu Radiyya.

Cikin dabara na goge hawayen da suka taho mini tashi ya yi ya fita Haj ta ja ni zuwa bedroom ɗinta haƙuri ta fara ba ni, sai ta ba ni labarin matarsa ta ce shi ɗin a da mai son addini ne da ladabi da biyayya ga iyayensa kafin ya haɗu da ita ya zama sai abin da ta kitsa masa ita ta hana shi zama ƙasarsa sai ƙasar nasara, yaransa sun tashi da ɗabi’unsu.

Ta ce in kwantar da hankalina tana kuma so a matsayina na matarsa in dinga nuna masa hanya ta addini tana ta kwatanta mini yadda zan yi.

Bayan fitar ta shiru na yi ina nazarin labarin da ta ba ni kan matarsa ba mamaki don yaransa sun zama yadda na gan su.

Har dare ina gidan da ya tashi dawowa tare da wasu dattawa su biyu ya dawo, ɗaya aminin mahaifinsa ne ɗayan ne shaƙiƙin mahaifin nasa.

Zama suka yi suka ba Haj haƙuri girman dattawan ya sa ta haƙura amma ta yi rantsuwar shekaru biyu suka cika ya ƙara yi mata yadda yake mata ya bi son ran matarsa ta yafe mata shi ba kuma za ta yafe nononta da ya sha ba.

Suka ce in sha Allahu ba za a yi haka ba zai dawo shi ma ya ƙara tabbatar mata da haka.

Hankalinsa ya ji ya kwanta ya kashe wannan matsalar, don ba wai kuɗin da zai sama mini wurin zama a London da ɗawainiyar zaman nawa ne ba shi da su ba kamar yadda ya tsara, matarsa ce ta sha mishi alwashin matuƙar ya kawo ni London za ta tabbatar ta gano inda ya ajiye ni ta sanya ma gidan wuta in ya so a ɗauki hukunci a kanta tun da ƙiyayyar da Haj ke mata sai da ta ga ta cika burin ta an yi mata kishiya.

Daga baya na ji labarin hakan wurin Su’ada ita ma Mama Zulai ta faɗa musu.

Mun koma gida yana ta ba ni kulawa har satin da ya rage ya koma ya cika kafin cikar satin na yi masa rakiya gidanmu da gidan Baba Isah, Haj ta nemi idan ba zan iya zama gidana ba na dawo wurin ta,

na ce zan iya.

Ya tafi ya bar ni cikin kewa da ta hana ni walwala gidan Hajiyar nake samu in tafi in yi wuni anan na saba da mutanen gidan musamman Su’ada sai gidanmu da nake zuwa duk ƙarshen sati mu wuni tare da Lubna da Aunty Ya gana Hassana ce Malam bai faye barin fita ba sai an yi sati uku take zuwa mu wuni tare.

<< Ummu Radiyya 19Ummu Radiyya 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×