Skip to content
Part 25 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Ban ƙara shiga tashin hankali ba sai da na ji abu ta kasa na yana bi na, dubawar da zan yi jini na gani, kuka na fasa na sauka kasa, ciwon mara ya sauko min ina ta mukurkusu na ji muryar Laila ta window da ta saba leƙo ni.

Nishin da ta ji yasa ta tambayar me ya faru na ce “Ki zagayo kofar a bude take” ai kuwa sai ga ta da gudunta ta shigo ta rungume ni, tana fadin “Me ya same ki? Cikin zafin ciwo na ce “Ina jin bari zan yi.”

Wayarta ta janyo jikinta na rawa, kawarta Dr Fati ta kira, wadda na san ta saboda yawan zuwan da take wurin Aunty Laila, halin da nake ciki ta fada mata ta kuma nemi taimakonta.

Muna nan ina fama “Dr Fatin ta iso ta shiga taimaka min, cikin hukuncin Allah na haihu da Namiji, kuma sannan ne Tahir ya iso daga kiran da Aunty Laila tayi mishi a waya. Ya shigo ya iske Dr Fati tana taimaka min zan shiga bathroom, Laila ta nade babyn a zanena, hawaye hawaye shabe shabe take yi dan bai zo da rai ba, ta mika wa Tahir, duk da bai iya daukar jarirai ba haka ya fito falon, ko da yake bakwaini ba dan karami bane, sambalele ne.

Bai iya cewa Aunty laila komai ba wadda ke kuka da gaske, shi ma ban da yana namijin duniya da kukan zai yi da alhakin yarinyar nan? Me yasa ya biye wa zuciyarsa ya yi ta cuta mata, bayan ya rabota da iyayenta? Ya ƙara duban yaron tausayin kansa na ƙara kama shi, yau ya samu abin da ya dade yana fatan samu amma kuma ba rai.

Wayarsa ya zaro Hajiyarsa ya kira, jin yanayin muryarsa yasa ta ce “Lafiya? Ina Ummu” wata iska ya furzar me zafi, idonsa na kan babyn, ta haihu Haj, sai dai yaron bai zo da rai ba, dan bai kai watannin haihuwa ba.”

Kukan da Haj ta fasa, ya kara jagula zuciyarsa, cikin kukan ta ce “Ka faɗa ma iyalan Attahiru, su kula da ɗiyar mutane, ka da ta mutu, a garin kabilu, da ta yi kwari ka kawo min ita, ko har sai yaushe zan ga kwanka? Ina take ka bani ita.Ya lumshe idanuwansa “Wanka ake mata.” Sai yanzu ya tuna ya kamata ya sanar ma uban goyon nasa.

Tare da mutane Kawun ya iso, da Aunty Kulu, wadda ta same ni kwance bayan yin wanka na, zama tayi daf da ni ta cire kaina ta dora saman cinyarta, “Sannu kin ji yarinyata, jarabawa ce, kowane bawa da irin jarabawar da ake mishi, mu kin ga ma ko barin ba bamu taba yi ba, ke kuwa har ga dan ma kin gani, Allah yasa masu ceto ne, Allah ya kawo rayayyu.”

Su Aunty Laila suka ce “Amin”. Ita da Dr Fati wadda za ta wuce, sai na ji tausayin Aunty Kulu ya kama ni. Aunty Kulu na ma Dr Fati godiya, ni ma na ɗago nayi mata. Suna tsaka da rarrashina in tashi in sha tea da Aunty laila ta haɗa min, Tahir ya shigo duk ya yi wani iri, kallona ya yi kafin ya maida duban ga Aunty Kulu, “Aunty, Baba, ya ce da ita za ku tafi, za ta fi samun kulawa a wurinki.”

Ta ce “Kwarai kuwa ni ma nayi tunanin haka.” Suka shiga haɗa min kaya, Anty Laila na share ido wai za ta yi kewa idan na tafi, Aunty Kulu na bata haƙuri. Mijin Aunty Laila shi ya dauke mu a motarsa, Tahir ya tafi sawo magungunan da Dr Fati ta rubuta min.

A bedroom dinta Aunty Kulu ta yi min masauki, bata yarda an gyara min daki ba kamar yadda Kawu ya ce. Kwanciya nayi kan tattausan gadonta wanda yake makeke ne, sai kujera guda daya a cikin dakin, gefe ɗaya babbar ma’ajiyar zuba kayan sawa ce, bed side, sai kofar toilet, ɗaki ne yalwatacce yana fidda kamshi me sanyi.

Sai bayan sallar isha’i, lokacin har na kare cin abincin da Aunty Kulu ta kawo min, Tahir ya shigo har bedroom din, ganin sa sai na tashi na zauna har ya yo wanka ya canza cikin kananun kaya, daddaɗan ƙamshinsa na tare da shi. Hannunsa ɗaya na soke a aljihun wandonsa, dayan na rike da leda, ledar ya ajiye saman bed side drower.

“Sannu ya jikin? Ga maganin nan, ya dan yi wuyar samu ne, sai yanzu da na fito na samu.” Shiru na mishi dan wani kishi da ya taso min ganin yanda ya yi kyau, na san shi a daɗin shi da aka ɗauko ni, dama ce ya samu ta sheke ayarsa, kila ma gidan zai rika kawo ta, suna kwana abin su.

Ai da yin wannan tunanin sai na ji hawaye, kwanciya kawai nayi sai na juya mishi baya “Ki tashi ki sha maganin” ya fadi yana bude ledar, yi nayi kamar ban ji shi ba, gajiya ya yi ya fita, suka dawo tare da Aunty Kulu, ita ya mika wa ledar tana cewa in tashi na tashi na karɓa na sha sai na gyara kwanciyata, fita tayi shi kuma ya zauna. Bata jima ba ta dawo ɗauke da wani plate.

“Tashi Ummulkhairi” tun ban tashi ba ƙamshin abin da ke cikin farantin ya sa ni hadiyar yawu ba shiri, plate ɗin ta miƙo min Nama ne, wanda da na ci sai da na rasa gane gasa shi aka yi, koko farfesu ne, ya yi matukar dadi kamar zan tsinke kunnena. Ni fa Aunty, ina nawa?Tahir ya fadi yar dariya tayi “A’a wannan ba gyaran masu jego ne.”

Sai ta fita, ya dan duƙo gabana ba za ki san mini ba? Plate ɗin gaba ɗaya na tura mishi “Dauki abinki ki ci, da wasa nake miki.” Sai da ya maimaita sai na ɗauka, na ci sosai na ajiye plate ɗin, mun ɗauki akalla mintuna talatin sai ya mike a hankali ya fita ya ja min ƙofar.

Da ganin fitar sa sai na tashi zaune na jingina jikin gado, ƙirjina har harbawa yake dan takaicin da ke cin raina. Aunty Kulu ta shigo “Baki kwanta ba? Ta tambaye ni kai na daga mata “Maida hankali ki yi barci.” na ce mata To” ta shiga cire shiryayyar kwalliyar da tayi, ta fada toilet, ta fito ta shiga shafe shafe, shafa wannan goga wancan, ni dai baki na sake ina kallon gayun tafiya wurin maigida.

Wata kyakykyawar rigar barci na zura, nayi saurin rufe idona, ina saƙa abubuwa da dama cikin raina, ta fita ta ja min ƙofar, ban daɗe ba barci ya yi awon gaba da ni. Asubar fari sai ga Auntyn ta shigo tana tambayata yanda na kwana ina cewa lafiya lau” ta ce “To koma ki yi kwanciyarki” na ce “To” Ƙarfe shida na safiya ta ce in tashi in yi shirin wanka. Ita tayi min wankan, ta kuma gasa min jiki sosai, sannan ta sa wani ruwan da ta zuba wani farin ruwa ta ce in shiga sai da ya soma sanyi ta ce in fito, wani ruwan ta kuma haɗa min ta zuba turarukan wanka ta ce in yi wankan sabulu. Da na fito Room heater ta kunna dakin ya dauki dumi, na shirya ta dawo wata humra ta miƙo min “Shafa wannan, ki fito ki karya. Zama tayi ta tasa ni sai da na ci na koshi, Tahir ya iso wanda Aunty tayi ta fadin mamakin da ta ji na isowar sa yanzu a cinkoso irin na Lagos.

Tana kuma ta korafin me yasa bai bari sai ya tashi gudun makara a wurin aikinsa. Murmushi kawai ya yi yana tambayarta yanda na kwana, ganin idonta na gaishe shi, sai da ta fita ya ciro wayata a aljihunsa, ya miƙo min “Ga wayarki nan, na san mutanen gida za su so magana da ke.” Mutanen Aunty Kulu suna ta shigowa daga makota, har zuwa abokan mu’amalar ta, haka mutanen Kawu Attahiru, da abokan Tahir na wurin aiki.

Ranar da nayi kwana uku da daddare ya shigo ya same mu ni da Aunty ina mata kuka, ya karasa shigowa cikin dakin hannayensa zube cikin wandon kayan sanyin da yake sanye da su, fararen riga da wando ne sakar ƙasar Jordan, kasantuwar an fara sanyi.

Tambayar me ya faru ya yi Aunty Kulu ta ce “Ka san saboda ba yaron, nonon sun cika, shi ne suka dame ta”.Juyawa kawai ya yi “Bari a samo magani Aunty.” Shudewar wasu mintoci ya dawo, ni kaɗai ya samu, har lokacin ina goge hawaye, ɓare maganin ya yi ya miƙo min hada ruwa, na karba na sha, Mu gani, in ga yanda suka yi.” Ya faɗa yana wani murza hannayensa, tura baki nayi sai na miƙe, a hankali nake takawa, dan gudun motsi me karfi, zafi suke min, na hau gado ba za ki nuna min ba.” ya fadi yana duƙowa inda nake kwance, ban yi magana ba sai na cigaba da goge idona.Ya ce “Zan tafi in kwanta.”

“Maimakon in yi magana wani kukan na saka “To ina ganin ba nonon kadai ke damunki ba.” Hannuna na daga “Ni ka tafi kar ka bata mata lokaci.” “To! Ya fadi yana wani dan malalacin murmushi, sai ya zauna a kujerar da ke cikin dakin, har Aunty ta kuma shigowa “Allah Sodangi, har yanzu ba ka tafi ka kwanta ba? to mu za mu kwanta. Daga kansa ya yi daga kan wayarsa “Ai zan tafi ta sa kuka, wai bata son tafiyata, dan kar in tafi in je tadi.”

Wani zaro ido nayi jin zancensa kunyar Aunty Kulu ta dabaibaye ni, kudundune jikina nayi “Wane irin zance kuma? Mutun me mata har uku, ko kin manta da abokan zamanki su biyu?

Jin zancen Aunty yasa shi saurin cewa “Ni ma dai shi na gani” “Tashi maza ka je ka kwanta” ta ba shi umarni ta kuma dauki abin da ya kawo ta sai ta fice.”Na tafi Ummulkhairi.”

Ban magana ba, sai dai yana ficewa na soma hawaye. Aunty ta dawo, kusa da ni ta zauna, “Me kike yi haka? Ko so kike a mayar mishi ke? Saurin girgiza kai nayi ina share hawayen, Tahir wanda bai wuce ba yana tsaye jikin ƙofa, ya girgiza kai sannan ya bar wurin.

Na kwanta lamo bayan fitar Aunty Kulu, kafin gwanin iya sata ya sace ni. Ranar da nayi kwana bakwai da haihuwa sai ga Yayana Sani, ya taso matarsa Aunty Rahma wai sun zo duba ni. Maimakon murna kuka na tasa shi ina mishi, ido kawai yasa min yana kallo, Aunty Rahma tana ciki, wurin Aunty Kulu. Shi kuma yana zaune a shiryayyen falon Kawu Attahiru, inda mutanen gidan ke ta shigowa suna gaishe shi. A haka Tahir ya shigo ya iske mu, da alama dawowar sa kenan daga wurin aiki, dan tun ranar da nayi ta mishi kuka, washegari ya dawo gidan da zama, dan dama akwai dakin shi wanda aka shirya komai, duk da ba ma Lagos ɗin ya cika zuwa ba.

Sannu da zuwa ya shiga yi mishi cikin matukar nuna surukuta, sai dai da ganin yanda yake yawan kallona na gane a tsarge yake da ganin kukan nawa yana tunanin ko kararsa na kai. Yaya Sani ya dube ni “Indai idan na zo wurinki haka za ki tasa ni kina min kuka, ba zan kuma zuwa ba.”

Saurin soma share hawayen nayi da bayan hannu “Yawwa, ko ke fa, Ummun Ummanta” Kwana ɗaya, Yaya Sani da matarsa suka yi, da za su tafi ma muna Sallama da Yayan a falon Kawu daga ni sai shi, kudade na ciro a cikin jikina “Ga shi Yaya Sani, ka kai ma Ummata” Duban su ya yi “Na mene ne? Na ce “Masu zuwa ne, suka bani” “To ki bar su za su yi miki amfani.” Wani kukan na soma mishi ya ce,

“To ko dai akwai wata mas’ala ne a zaman naku? Saurin girgiza kai nayi To ki daina kuka, ko so kike in je in ce wa Umma, tun da na zo kuka kike.” Kan na kuma girgizawa, “To zan kai musu dubu sha biyar, su raba su uku, hada Baba, da Gwoggo. Ki riƙe sauran bari ma in kara miki. Ya ciro kudi a aljihu ya miƙo min, na ce “Na gode Yaya.

“Washegarin tafiyar su, muna zaune da Aunty Kulu a falonta, fruits din da ta yanka min nake sha, dan koda yaushe cikin bani su take. Bata daɗe da shigowa gidan ba, kuɗaɗen da akayi ciniki da bata nan aka kawo mata take kirgawa, Tahir ya shigo da sallama, kujerar da ke nesa da wadda muke zaune ya zauna, Aunty na mishi sannu da dawowa ta shiga kiran sunan ɗaya daga cikin masu aikinta, ta iso cikin sauri umarni ta bata ta kawo abincin Tahir, ta kai mishi dakinsa.Ya ce A’a ta kawo mishi nan. Ya harari inda nake zaune “Ke ke shagwaba yarinyar nan Aunty, ga ta zaune, sai mai aiki ta kawo min abinci.”

Daina lissafin da take tayi ta dubi gefenta inda nake, “Allah sarki bata gama warwarewa ba”Ya ce. “Haka ne, bar mata ma garin zan yi gobe”, da mamaki Aunty ta dube shi. “Ina za ka? Ni ma fakare nayi dan jin inda za shi, “Hutu na samu na wata daya, shi ne nake son in wuce Kaduna, zuwana na karshe nayi cinikin wani fili, ina son in gina ma kowaccen su Part ɗinta”Ji nayi hawaye na min zuba tuna tsawon lokacin da na ɗauka ba tare da na je gida ba, Aunty Kulu tana ta mishi addu’a sai kuma ta juyo ta dube ni “Ah kukan me kike?

Ban magana ba cigaba nayi da share hawayen “Ikon Allah, tafiyar da zai yi kike ma kuka, in ya zauna to me zai miki? Kunyar maganarta na ji na mike na shige bedroom dinta kwanta, sai ga ta ta shigo ta zauna tana rarrashina, “Kyale shi, ya yi tafiyar sa Ummu, tafiyar ma za ta yi mana daɗi, mu yi gyaran mu a tsanake.”

Irin maganganun da tayi ta gaya min kenan. Kuma ko a safiyar da zai wuce, da nayo wanka dan yanzu na iya, Atamfa ta kawo min, wadda ta sha dinki me kyau, ta ce in sanya, sosai ta karɓe ni, ita ma da ta dube ni sai da ta murmusa Jegon nan ya karbe ki Ummulkhairi” sunkuyar da kai nayi mayafi ta miƙo min “Je ki ku yi sallama da mijinki na ga har sun yi sallama da Malam.

<< Wa Gari Ya Waya 24Wa Gari Ya Waya 26 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×