Skip to content
Part 4 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Ɗauke wuta kawai Latifa ta yi ta juya zuwa ɗakinta ta rufo ƙofar da karfi, na wuce a hankali na haura sama. Kamar yanda nayi zato ya kashe duk fitilun wurin sai hasken bed side lamp ita taimaka mini na hango shi gefen gado ya yi tagumi da duka hannayensa.

Ina shirin zama wayarsa tayi ƙara ya kai hannu ya ɗauka cikin dakusashshiyar murya ya soma Magana “Kana ji na Usama? al’amarin Halima yana neman sha mini kai,
ina duba mata saboda ganin al’amuran da muka keto ni da ita har muka zo yau.

Amma ita bata sani ba gani take isarta ke sa ni kyaleta.” Ya yi shiru ya ɗan saurara
kafin ya cigaba “Wallahi nake gaya maka bayan fama da nake da ciwon Basma
Latifa ma na fama da ciwon ido, wai ciwon shi ya zama abun kishi wurin Halima, yanzu ta tsare ni ta nemi in bata wasu ubannin kuɗaɗe tun da ina kashe kudi kan matana.

Ta bar ni ma in ji da damuwar da nake ciki yau tun isowar mahaifin Basma yake nuna mini gazawata kan ciwon ƴarsa.” Shiru ya yi ya cigaba da saurare sun ɗauki lokaci yana bayyana ma wanda suke wayar damuwar da yake ciki, a raina ina ta tunanin ko ya manta ina dakin.

Da ƙare wayar tasu ajiyeta ya yi ya koma ya rafka tagumi tashi nayi daga inda na lafe gabana na harbawa zuwa inda yake ƙirjina na haɗa da bayansa sai na rungume shi, cikin sanyaya murya na riƙa ba shi hakuri.

Mun ɗauki wani lokaci a haka ba tare da ko motsi ya yi ba, har na sare na janye hannayena zan koma inda na taso in kwanta, na ji ya waiwayo gaba ɗaya sai ya rungume ni, kwanciya ya yi ina maƙale a jikinsa sai ya ja mana bargo.

Zuwa safiya na yi duk abin da zan yi dan ganin na rage mishi damuwar sa kuma sosai na samu nasarar hakan. Da zai fita sallar asuba ma umartata ya yi da kar in koma ɗakina nan na zauna bayan na idar da tawa sallar, nayi azkar da karatun Alkur’ani har gari ya soma haske. Da ya shigo kwanciya muka kuma yi da nayi yunkurin zare jikina in tashi dan in je in haɗa abin karyawa sai ya kuma maƙale ni dole na haƙura,
sai tara da rabi muka tashi kofin shayi guda ya ce in kawo masa sai ƙwai cikin sauri na kammala na kawo masa dan ban ga alamar zai sauko ba, su ma matan ban ga kowa ba,

Haɗa mishi na yi na daidaita mishi zafin hada danbun naman da nayi na haɗo masa.
Sai na koma kitchen su ma mutanen gidan ruwan zafi na dafa musu na soya kwai na jere komai bisa dinning. Ɗakina na wuce wanka na yi na gyara jikina ina ƙamshi, doguwar riga ta atamfa da ɗinkin ya zauna mini dam a jikina na saka na yi ɗauri me kyau sai na fito.

Latifa na hango zaune a dinning tana break past na ƙarasa ina mata ina kwana ban tsaya ba na wuce dan yanda na ga tana bi na da kallo, saman na haura na samu Tahir yana aiki a system ɗinshi, murɗa ƙofar da sallamar da nayi yasa shi ɗago kai ta cikin farin glass ɗinsa yana kallona tafukan hannayena na sa na rufe fuskata, neman wurin zama na yi ba tare da na yarda mun haɗa ido ba ta wutsiyar ido na saci kallonsa karaf idanuwanmu suka haɗu tsadadden murmushinsa ya ke jifana da shi.

Nima murmushin na yi dan tsantsan kyan da ya mini ya sha wanka cikin jallabiya me guntun hannu, mun jima zaune shiru shi yana aikinsa ni kuma ina famar ƴan tunane tunanena na dalilin da ya hana masa zuwa asibiti yau dan sammako yake yi, kamar in masa maganar zuwa asibitin dan makaranta ba kullun yake shigaa ba, sai dai na ja bakina.

Ƙarfe sha biyu na sauka dan ɗora abincin rana a kitchen ɗin ya same ni ya ce mini zai leƙa asibiti, nayi masa fatan dawowa lafiya tare da yi ma me jikin addu’ar samun sauƙi.

Bai shigo ba sai da aka yi sallar Isha’i gidan daga ni sai Latifa muka wuni wadda na lura cikin nishaɗi take, a kuma ƴan wake waken da take na fahimci zaman ɗakin da Halima take a yau ya yi matuƙar yi mata daɗi.

Yana cin abinci ya ce mu shirya ni da Latifa muje asibiti mu duba Basma, take annurin da ke kan fuskarta ya ɓace ta yamutsa fuska sai dai iya bariki irin nata sai ta yi saurin daidaita kanta. Kowaccenmu ɗakinta ta shiga dan shiryawa, duk da takaicin da abin ya bani fitowata da na samu Latifa ta kame gaban mota kuma girkina sai da na kusa dariya, yanda ta shafa hodar garin sauri a zo a faɗa gaban mota dan tsayawa na yi,
da wani irin kallo ta dube ni tana taunar cingam ɗin da baka raba ta da shi, ta gyara zaman glass ɗinta.

“Lafiya malama kika tsaya mini a kai? Ikon Allah na faɗi a raina bari ka ga matar nan
shiru shiru fa ba tsoro ba ne gudun magana ne sai da na rama kallon banzan da ta mini na ce ,”To ina ruwan kallo da gajiya?

Har da buɗe baki ta yi dan da alama ta ji mamakin mayar mata da na yi, “Amma dai kar ki ce rashin kunya ki ke so ki mini? ta faɗi cikin hayayyaƙowa. “Rashin kunya kuma?

Na tambayeta cike da mamaki ta ɓalle murfin za ta fito muka ga fitowarsa, “Ke fa lafiya ba ki shiga ba? Ya tambayeni da ya iso, “Ba komai yanzu zan shiga.”

Na ce ina kama murfin bayan motar sai da na shiga na zauna shima ya zagaya ya shiga, ko zama Latifa bata bari ya gama yi ba cikin faɗa ta ce, “Darling ka ja wa yarinyar nan kunne ta fita harkata.”

Da mamaki ya dube ta, “Wace yarinyar kenan? Za ta fara bambami, ya ce “Look malama meye a fuskarki? Cammon ki koma ki goge abin da kika yaɓa.” Wani kallo ta dalla mishi kamar me shirin fashewa da kuka, ta ɓalle murfin ta fita ta buga shi da ƙarfi kafin ta wuce ciki kamar me shirin tashi sama.

Mun zauna kusan minti goma ba Latifa ba labarinta, ya kira wayarta bata ɗaga ba
Ƙwafa ya yi ya ce mini, “Dawo gaba.” Ba bata lokaci na koma sai ya ja motar muka bar gidan, muna tafiya bisa hanya babu mai magana da wani sai radiyon motar da ya kunna ya tsaya a hanya ya sayi kayan marmari.

Mun shiga ɗakin da Basma take, zaune muka same ta tana shan wani abu a mug wata mata da ta fara shiga shekarun girma ke tare da ita, ita ɗin ce kuma ta yi mana maraba
dan Basman daga ni har ogan ba wanda ta amsa sannunsa, mun jima Tahir ya tafi office ɗin likita sai da ya dawo muka yi musu sallama.

A hanya mun kusa gida na ji tambayar Tahir, “Me ya haɗa ki da Latifa? Ban tunanin jin tambayar ba dan haka na so daburcewa sai da na daidaita nutsuwata sai na mishi
bayanin yanda muka yi da ita, tsaki ya ja “Ba na so kina biyewa ke ma ana mini faɗa a gida.”

Haƙuri na ba shi, mun samu falon ba kowa. Latifa uwar iya yau dai ba zaman gulma tana ɗakinta. A ranar ko da na kwana turaka ban leƙo ƙasa ba. Mai aiki na yi ma waya na ce ta samar musu abin karyawa, dan Ogan ya ce min yana azumi kuma ranar ma ba zai shiga makaranta ba.

Ina zaune yana shiri zai fita muna ɗan taɓa fira turo ƙofar a ka yi, gaba daya muka kai duban mu ga ƙofar, Latifa ce ta yi ɗaurinta na ture ka ga tsiya tana famar taunar cingam ɗinta na fama, baki na taɓe yayin da ogan ya dube ta cikin hasala.

“Lafiya za ki fado wa mutane wuri ba sallama ba neman izini.” Noƙe kafaɗa ta yi irin nasu na ƴan duniya, “Magana nake son yi da kai.” Shi ne ba ki haƙuri in fito
daga kin san akwai wata a ciki, ko na taɓa fita ban shiga ɗakin wata ba?

“To ai magana nake son yi da kai ina ruwana da wata ko…

“Stupid Latifa” Ya faɗa da ƙarfi wanda har ni sai da yan hajina suka kaɗa. Ki fita kuma kika sake gwada mini irin haka matakin da zan ɗauka kanki.” Ya yi ƙwafa ta juya fuu!
Ya bi bayanta da mugun kallo. Tashi nayi na soma gyara wurin na wanko toilet,
kasa na sauka zuwa ɗakina, wanka na yi zuciyata cike da tunanin wannan rikice rikice na wannan gida, sai da na ƙare shirina sai na koma falona na kunna TV na kwanta,
murɗa ƙofar da aka yi yasa ni daga kai.

Tahir ne bai shigo ba sosai yana daga tsaye yasa hannunsa aljihu kuɗaɗe ya ciro masu kauri ya ajiye min a hannun kujera, godiya na yi masa sai ya juya na bi shi da a dawo lafiya. Halima ce ke da girki a ranar sai uku na fito dan yunwar da ke sakaɗata
ganin wayam teburin yasa na gane bata girka komai ba, kitchen na wuce Latifa ma ciki na gan ta sai mai yin aiki Indo, ko da na yi sallama bata amsa ba, a yanda na gan ta na gane daga unguwa ta dawo kuma da alama tana tare da shegiyar dan sai masifa take wa Indo, me yasa da Halima bata fito ba ita bata girka komai ba, ita dai sai haƙuri take bayarwa.

Indomie na dafa da ƙwai biyu na juyo a flate, kallonta ta yi sai ta ja tsaki raina ya sosu amma sai na danne na sa kai na bar kitchen ɗin, a dinning na zauna ina kallon wani programme da ake gabatarwa a tashar Arewa 24 a ƙatuwar flasmar da ke falon.
Latifa ta fito da nata abincin a hannu ɗakinta ta wuce ni ma da na kammala nawa ɗakin na koma txt na tura wa Tahir zan shiga gidan Kawu Attahiru.

Shi nake so in gaido dan ya shigo garin duba Basma. Washegari da safe ina gama karyawa ɗakina na gyara nayi wanka da kwalliya cikin wata doguwar riga mara nauyi
sai na bi lafiyar gado, barci me daɗi na shiga yi har ina mafarki.

Kukan wayata da na riƙa ji yasa ni kai hannu na lalubota a hankali na buɗe idanuwana, sunan Maman Ummi matar yayan Tahir kuma wadda muka fi shiri lokacin da na zauna gidan su Tahir da na gani kan screen ɗin yasa ni yunkurawa ina ɗaga kiran, bayan sallama gaisuwa ta biyo baya da tambayar jama’ar gida ta ce “Yanzu fa za mu ɗauko hanyar garinku.”

Dan murmushi nayi

“Lafiya? Ta ce “Za mu zo duba kishiyar ki ne” Na ce “Allah ya kawo ku lafiya, kuna da yawa ne? ta lissafa mini su shida ne, yayyen Tahir biyu sai matan yayyensa dan kowa an ɗauko matarsa ɗaya. Kai na gyaɗa “Tahir kuwa ya san da zuwan.”

“A’a kam dan an ce ba a samu wayar tasa ba.” Nayi masu addu’ar Allah ya kawo su lafiya.” Muna ajiye wayar sai na nemi barcin da nake ji na rasa, miƙa nayi sai na fito zuwa kitchen ban samu kowa a falo ba sai Indo tana daɗa gyara shi, ina shiga kitchen din sai ga ta ita ma ta shigo, “Haj za a taimaka miki ne? Ta tambaye ni da girmamawa,
kallonta na yi “E jama’ar gidan su oga ne za su zo.”

Dan murmushi ta yi, “Ya kamata kam a shirya musu abincin tarba.” Fridge na buɗe ina kallon abin da ke ciki nama ne nau’i daban daban sai fitar da sanyin raɓa yake.
Naman kaza na shiga fiddowa wanda kafin ya ƙare ake daɗa lodo wani. Su ma dai ƴan’uwan mai gidan bari in dafa musu su ci yau ɗaya su ma su dangwali arziki,
ba sai waɗannan matan da ya tara ba ya kawo kullun su ci su na ma jama’a kallon banza.

Indo na umurta ta ɗora jallof me ƴan ciki da kayan lambu ni kuma na ɗora pepper chicken. Cikin sauri muke aikin dan in samu mu kammala cikin lokaci, ɗaki na koma nau’in maggi da nake amfani da su curry wanda na riga na bare, sai kayan ƙamshi da nake haɗawa citta da karanfani da kimba da tafarnuwa, ina amfani da su wurin girkina ba ƙaramin ƙarawa girkina ƙamshi da daɗi suke ba su na ɗauko’

Aunty Kulu ta bani wannan dabarar ta ce kar in yarda kishiyoyina su san da kalar kayan dandanon da nake amfani in bar su ranar girkina in haukata su da dandanon girkina.

Na koma mun ci gaba da aikin, muka tsinkayi muryar Halima, “Indo aikin kika soma ban fito ba, me ki ke yi haka gida duk ya… haɗa idon da muka yi yasa ta hadiye sauran maganar, sai ta ƙara tamke fuskar dan ita kullum cikin tsare gida take.

Bata amsa sannun da nake mata ba illa illa Indo da ta duba, “Wa ya ce ayi mini girki ban fito ba? Shiru muka yi duk kan mu, “To aji a sani duk wata kankanba da mutum zai yi ya tsaya iya kan wanda ya kwaso shi.”

Tsayuwa na gyara, “Da yake ma mutum ɗin ba shi ake wa girkin ba, ko kuma isar har ta kai kitchen ɗin ma a hana mutane shigowa? Gaba daya ta taso mini kamar za ta sa duka “Kar ki ce za ki yi mini wallahi duka zan miki.”

Idanu na buɗe “To! Duka?

Ta ce “Me kike nufi?

Shiru na yi ta cigaba da bambaminta kafin ta fita fuu! Dakinta ta zarce ta kira Tahir kan ya ja min kunne me ya kai ni shiga kitchen ina mata girki a ranar girkinta.
Hakuri ya bata ya ce, “Kila taimaka miki ta yi ta ga matsayinki na babba.”

To ban bukatar taimakon ka gaya mata, kuma sai na ji ba’asin rashin kunyar da tayi mini d…..Tsawa ya daka mata, “Kar ki kuskura ki koma wurin yarinyar nan indai kin kawo ƙara wurina dan ina gaba da ku.”

Kit ya katse kiran, gane ɓacin ransa ya sa ta kasa komawa kitchen ɗin, tsaki ta ja ta cillar da wayar ta zauna tana huci. Shi kuma wayata ya shiga kira sai dai har ta karaci rurinta ta katse ba a ɗagawa, ransa ya ƙara ɓaci na san rashin kunyar da na wa Halima shi yasa na ƙi ɗaga kiransa.

Ƙwafa ya yi, “Zan koya miki hankali.” Mun kammala girkin ya yi mini yanda nake buƙata bayan babbar cooler da na cika musu da pepper chicken, na kuma cika wata madaidaiciya wadda nufina zan bai wa Maman Ummi ta kai ma mahaifiyar Tahir.
Duk wani drinks da ke gidan sai da na daukar musu kalarsa
Indo ta fitar mini zuwa wurin mota. Daki na koma na gyara kaina na fito cikin dogon hijab me hannu, wayata sai sannan na ɗauko ta a ɗaki ban ko tsaya duba ta ba na jefa ta jaka, Indo na wurin motar har lokacin sai da tayi mini fatan sauka lafiya sai ta koma ciki, tana me murna a ranta yau Allah ya ceceta da zama da yunwa dan girkin Halima kowa sai ya ji jiki kafin ta gama gara mata girkin Latifa duk da ba daɗi, dan sam bata iya girki me daɗi ba a ƙalla za ta gama cikin lokaci.

Basma kuwa ita take sakarwa girkin duk da sanin da ta yi mai gidan ba ya so.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 3Wa Gari Ya Waya? 5 >>

2 thoughts on “Wa Gari Ya Waya? 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×