Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Wani Rabon by Deejasmaah

Dedicated to all the single ladies out there.

Chapter One (The day)

A cikin ranaku masu muhimmanci a rayuwar dan adam kamar ranar auren sa , ranar aure rana ce da babu tamkar ta a tarihin rayuwar halitta, akan yi mata lak’ani da rana d’aya tamkar ya dubu rana ce mai dauke da dunk’ulallen farin ciki da annasuwa mara misaltawa.

Nima a gareni hakan take wani yanayi nake ciki mai tattare da farinciki da nishad’i musamman idan na juya na kalli friends dina a zagaye dani sanye da atamfa wacce sukai ankon ta wai fa duk sun taru ne domin ni, domin su tayani murna da fatan alkhairi murmushi na sauke ina mai kallon bestie wacce ita ma kallo na take yi murmushi tayi min sannan ta furta “Masha Allah”

Sanye nake cikin wata Emerald colored bridal gown wacce aka tanade ta domin ranar nan fuskata dauke da wani kwalliya wanda wata kwararriyar make up artist tayi min ga wani annuri da yake fita daga fuskata hannaye na dauke da wani hadadden lalle da zubona ‘yan hannu da wristwatch da ya k’ara k’awata hannun kafata kuma sanye da wani takalmi wacce muka yo ordern shi daga dubai tare da clutch din kana gani na ka ga amarya kuma yar gata wacce aka dad’e ana jiran zuwar ranar aurenta

Dukda tsantsan farinciki da nake ciki hakan bai hana ni jin wani bahagon yanayi yana lullub’e ni ba wani irin bugu naji kirjina yana yi dafe kirjin nayi sannan na kishingida kadan ina maimaita _”la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimiin”_  babu adadi yi nake ina maimaitawa har na dan ji saukin yanayin da nake ciki duk da dai bai tafi gabad’aya ba amma da sauk’i.

Areefah ce ta shigo d’akin da karad’in ta tsayawa tayi a kaina a daidai lokacin da tayi arba dani “wow Addah amarya _fatabarakallah Masha Allah_ na rasa mai zance wannan had’uwa haka , abeg tashi zaune in miki pics kafin angon nan ya ga wannan had’uwar” hararar ta nayi jin ko miyau bata bari ta hadiye take ta zuba haka.

Turo baki ta yi “please Addah ki zauna” d’an muskutawa nayi na zauna tareda jingina da allon gadon da muke zazzaune nan kowa ya fara ciro wayarshi zai dauke ni hotuna aka fara yi kujera na koma na zauna ana cigaba da d’aukan hotuna k’arar wayata dake hannun Areefah ne ya katse hoton da ake yi
Rufe baki tayi tareda cewa “laaa na manta fa tun dazu uncle Masud yake ta kiranki fa wlh shi ne ma ya aiko wai in kawo miki wayar.”

gabadaya yan matan suka hada baki wurin cewa “Awnnnn see love!!” Niko hararar areepha nayi tareda cewa “silly girl amma kin shigo baki fada min ba sai shiririta kika tsaya yi ” rufe baki tayi tana shirin dariya na jin abinda na fada “sorry Addah na manta ne wallahi.”

Wayar na amsa tana shirin katsewa cikin siririyar murya nace ” Assalamu alaika angon FAHEEMAH gwarzon jarimi basarake ” shewa suka kara saki yayinda Areepha da Noosrah suka turo kunnuwan su dan jin mai zai ce  wata murya mai cike da damuwa ce ta amsa sallamar “I’m Sorry FAHEEMAH I’m really sorry ki gafarce ni wlh an fi karfina ne there’s nothing I can do about it forgive me please.” 

Miyau na hadiye sannan na ce, “wai me yake faruwa Mas’ud kayi min maganar da zan fahimta mana what’s all this? ” ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ” I’m not getting married to u !! I’m not marrying gabadaya! ba yin kaina bane karfi na aka fi but wallahi I love you !! I really do,ki yafe ni FAHEEMAH” kallon Noosrah nayi inajin wani hawaye yana fara taruwa a idanuwa na a hankali cike da dauriya na ce “OK Allah ya bawa kowa RABONshi mafi alkhairi nagode ”  tare da katse kiran gabadaya.

Noosrah ce ta girgiza min kai ganin Ina shirin fashewa kallon mutanen d’akin nayi wa’inda suke bina da kallon son sanin me yake faruwa rik’e hannuna Noosrah tayi tareda dagani mikewa nayi cikeda sanyin jiki fita mukayi izuwa parlor inda abokan arziki suke zaune suna ganin mu suka saki gud’a.

“Masha Allah… ga amarya…amarya an sha kyau… Allah ya sa gidan zamanki ne… Allah ya bada zaman lafiya…” Maganganun da yake fitowa daga bakunan su kenan wanda suke sawa hawaye na kara zubowa.

Da’kin ba’ki dake tsakar gidan muka nufa ba kowa a ciki sai katifa sai kuma doguwar kujera a share yake a gyare saboda biki kan katifar na kwanta tareda sakin kukan da nake bukatar yi kukan nakeyi kamar rai na zai fice daga jikina ji nake kamar karshen duniyar kenan shikenan kuma tawa ta kare kila ma mutuwa zanyi Noosrah ce ta riqoni ta na lallashi rungume ta nayi na sa wani kukan itama rungume ni tayi muka dukufa kukan.

“Wannan wani irin sakarci ne kunzo kun duk’ufa kuka ke da ya kamata ki rarrashe ta amma kin sata a gaba har da tayata.” Ammi ce ta fada tana mai shigowa dakin da muke bamu saurare ta ba muka cigaba da kukan gwara Noosrah ma ta dan rage nata niko wani sautin na k’ara janye ta Ammi tayi sannan ta rungume ni a jikinta tana mai rarrashi na akan k’addara tace” haba daughter kuka ba shi zai yi maganin matsalar nan ba kedin ba matar Masud bace rabon ki yana gaba addua ya kamata kiyi akan Allah ya kawo miki naki RABON nan kusa kuma yasa shine alkhairin ki, take heart dear.”

Ta cigaba da rarrashi na tana kawo min misalai na rayuwa tun Ina kukan har ya dauk’e sai ajiyar zuciya kawai nake yi Areefah ce ta shigo da kaya a hannunta ammi ce tace in cire kayan jikina in chanja body con ce baka karba nayi nasa sannan tasa wipes ta goge min fuskata da ta cude nan mascara can lipstick tas ta goge sannan ta umurce ni inje in wanke fuskar toilet din dakin na shiga na wanko fuska na sannan na dawo dak’in

wani zazzabi ne ya fara rufe ni nan na fara rawar sanyi fita Areefah tayi sai gasu da Anty Sa’adah abokiyar aikin Mamie dubani tayi sannan tayi min allura cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ni a wurin.

Deejasmah

Elegant Online Writers

Wani Rabon 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.