Skip to content
Part 2 of 5 in the Series Wani Rabon by Deejasmaah

Chapter Two (Life after)

A hankali na fara regaining consciousness d’ina yayinda komai ya fara dawo min tiryan tiryan wani mugun kuka ya taso min duk yanda naso tare shi na kasa dan haka na bud’e baki na bashi daman fitowa hakan ne ya ankarar da mutanen d’akin da farkawa ta.

A guje suka rufu a kaina suna masu rarrashi na “assha!! farkawa da kuka kuma? haba Faheemah shin baki yarda da k’addara bane?” Ammi ta fad’a tana mai fitowa daga toilet matsowa tayi gaban gadon tana mai rik’e hannu na

Banyi shiru ba amma na d’an rage k’aran kukan nawa a cikin kukan nace ” Why always me Ammi ?!, Why me ?! mai yasa ni lamari na ya banbanta na kowa?, mai yasa kowa yana cikin farinciki amma bandani?, shin wani laifi nai ma Allah da yake punishing d’ina da hakan?”

“Kulll!! Faheemah kar in sake jin kin fad’i hakan! Shin so kike imanin ki ya raunana? ” Ammi ta katse ni daga abinda nake fad’i kana tace ” These are trials sweetheart, kiyi hak’uri ki jure domin ki samu ikon cinye jarabawarki and I assure you that Allah zai kawo miki naki rabon soon or later” ta k’are maganar cikin lallashi

Hawayena na share kafin nace ” ni na yafe may be bana cikin wa’inda zasui aure a wannan rayuwar dan hak’a na hak’ura ban san me Allah yake nufi da wannan jarabawar ba dan haka na daina soyayya domin na san bazai taba kaini ga dokin da nake hange ma kaina ba ” kai Ammi ta dafe ganin har yanzu ban k’arbi abinda tace ba don haka cikin sanyin jiki tace ” kina ganin bazaki sake soyayya ba? Saboda Mas’ud shine autar maza ko me?”

Girgiza kai nayi kana nace ” Aa ni dai kawai na hak’ura ne ” ganin na kafe ne yasa ta k’yaleni bawai dan ta hak’ura ba aa sai don cewa ta lura that I’m still not myself toh zata bani lokaci in komai ya lafa sai ta k’ara zama dani domin tasan cewa bana karaya a rayuwa so magana dani a wannan lokacin baida maana ko kad’an

Juya akalar maganarta tayi kam Mamie da take zaune “Tunda yanzu ta tashi ai sai kici abinci ko?” Murmushi Mamie tayi jin yanda tai maganar da zolaya domin Mamie bata iya kawaici ga duk wani abu da ya shafemu dukda kasancewar ta fulani amma ko kad’an bata iya kara ko d’auke ido ga lamarin da ya shafemu hakan yasa bamu da wanda muka shak’u dashi fiyeda ita

Kallon idonta nayi a lokacin da ta kalle ni idanuwan nan kaman an gasa k’arfe a wuta saboda ja ga kuma damuwa da fargaba dana karanta a idanunta hakan yasa duk Wani yanayin da nake ciki naji ya fara wucewa damuwar Mamie itace gaba da tawa girgiza mata kai nayi a hankali na furta ” issokay Mamie kar ki damu kinji ko” gyad’a min kai tayi sannan muka d’unguma muka nufi cikin gida domin cikin umarmin Hajiya Ammi Areefah da Noosrah ne suka kama ni sai Fadeel ya rufo mana baya

D’akin mu muka shiga akan sofa suka zaunar dani sannan bestie ta nufi toilet ta had’a mun ruwan wanka kamani tayi ta kai ni toilet d’in sannan ta mik’o min towel kafin ta bar toilet d’in na dʼan dad’e a toilet d’in domin kuwa gasa jikina nayi sosai kafin na samu ya d’an sake sannan nai wanka tare da brush da alwala kana na fito yanzu kam naji k’arfin jikina ba kamar d’azu ba

Koda na fito na samu har an fito min da kayan da zansa banyi zura kawai nayi ba tare da na shafa ko mai ba hijab na janyo na tada sallah a zaune saida na rama wainda na rasa kafin na fuskanci abincin da suka kawo min teaʼn da Ammi ta had’o min na d’an sha na ture don banjin dad’in bakina potato porridge d’in da yasha kifi da vegetables na fara sha ba laifi akwai d’an yaji kad’an a ciki shine yasa ma na saki jiki na sha da d’an yawa….

Cikin dauriya nake komai don banso suga alamun cewa Ina da damuwa duba da yanda suke nuna min kulawa da kuma yanda suke damuwa in na shiga matsala don haka duk na amshi k’addara ta hannu biyu na tabbatar akwai abinda Allah yake nufi da hakan

Saidai duk yanda naso in mance hakan na kasa musamman da na ga an dawo da kayan da aka kaisu Zaria wani sabon kuka muka dasa wannan karan harda Mamie saida mukayi mai isan mu kafin muka hak’ura fitar da furnitures din akayi aka saida su sukuma kayan kitchen d’in aka ajesu a store d’inmu bayan anyi wrapping d’insu da ledoji da badan tare aka siya mana da bestie ba da ita zaa barwa kasancewar bikinta nan da wata shida bayan mun kammala final exams din da take gabanmu.

2 Weeks Later

Shirye shiryen komawa school mukeyi duk wani damuwa na ajiye shi gefe tareda k’udurce cewa na gama soyayya a rayuwata tunda dai bana morar ribar soyayya ban tab’a kaiwa gaci a soyayya ba ranar asabar muka had’a kayan mu muka koma school ni da Nusrah (bestie) inda muka maida hankalin mu kan abinda mukeyi dukda Mas’ud ya addabi rayuwata da kira da kuma izuwa duk inda zai had’u dani ware rana d’aya nayi na fuskance shi

Duk maganganun shi kame kame ne domin baida abinda zai kare kanshi a gare ni lumshe idona nayi tareda cewa ” ni fa banda damuwa akan rabuwar mu, cos Allah yayi cewa kai ba mijina bane so banga abin jayayya ba, Allah yasa hakan ne alkhairin mu ni da kai amma dan Allah ka daina bibiya ta don hakan baida wani ma’ana da fa’ida please ka rabu dani.”

Babu yanda ya iya ganin cewa ban da buk’atar shi yasa ya kwashi k’afafuwanshi ya bar wurin tun daga nan ban k’ara jin d’uriyar shi ba inda hakan yafi mun kwanciyar hankali
Maida hankalina nayi kan karatuna dan na tabbata da cewa a rayuwar nan banda gatan da yafi karatu yayinda samari kuma suka fara yo min caa kamar na kirawo su duk wanda yazo koran shi nake yi da kalma d’aya watau anyi mun miji ko kuma na kusa aure domin banson abinda ya faru ya kuma faruwa

A hankali ranaku suna shud’ewa har muka fara final exams d’inmu cikin nasara komai yana tafiya daidai ba tareda muna fuskantar wata matsala ba har muka kammala exams din inda muna kammalawa dama kamar a kan k’aya nake muka tattara kayanmu tass muka baro Zaria muka dawo gida karatu an k’are sai shirin biki da yake tunkaro mu…

Deejasmah

<< Wani Rabon 1Wani Rabon 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.