Skip to content
Part 30 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Talatin Da Tara

A wannan yinin tamkar Basaraken ya ji irin jayayyar da sauran dabbobi suke yi a cikin dajin. Da kuma burin da suke da shin a son sanin shin wannan Malami bai fi Kahuhu ilimi ba kuwa.  Kuma anya ma ba zai fi Dila azanci ba. Dan haka, da aka zauna a fadar yau, bai ma saurari kowane koke da ake sa rai sauran dabbobin za su zo da shi ba, sai kawai ya tambayi Dilan,

“Wai kuwa a ganinka wane yankin bil’adama ne a doran kasar nan suka fi ko ina kyautatawa dabbobi?”

Dila ya ce, “Zai yi wuya a duniyar nan a samu wasu mutane masu kyautata wa dabbobi kamar ‘yan Jodan. Domin su ne wadanda da yaki ya ki ci ya ki cinyewa a Siriya, sai suka zo suka debe ragowar dabbobin da ke cikin gidan adana dabbobin dajin kasar. Suka mayar a su can Jodan din. Tare da cewa suna gane bil’ama a cikin wahala a garin. Sai ko ‘yan Baswana da suka haramta farauta kuma suke zama tare a kauye guda da dabbobin, ba tare da tsamgwama ba.”

Da ya gama, ya yi shiru, sai Zakin Ya waiwaya ya dubi Kunkuru: “To Aramma fa?” Kunkuru ya gyara zama ya ce. “Ai duniya kaf babu wata al’uma da ta kai ‘yan kasar Kenya wurin kyautatawa da girmama dabbobi.” 

Zaki ya ce, “Iye?”

Ya ce. “Kwarai ma kuwa. Domin su ne suke da gidan marayun dabbobi, inda ake rainon marayun  kamar yadda ake rainon marayun ‘ya’yan bil’adama!”

Zakin ya ce, “Tirkashi!”

Ya ce, “To ai ba wannan ne kaiwa matukarsu wurin girmama dabbobi ba, Yallabai.”

“Ko?” In ji Zakin.

“Kwarai ma kuwa,” Kunkurun ya fada, “domin su kadai ne duk duniyar nan kasar da suka cire hotunan iyayansu bil’adama daga jikin kudaden kasarsu, suka maye guraben da hotunan dabbobi!” 

“To tabbas na yarda babu wadanda suka kai wadannan girmama dabbobi.” In ji Zakin.

Da Dila ya kara yunkurawa zai yi magana, sai Zakin ya ce. “Ina ganin ya kamata mu takaita haka, dayake muna da wasu tambayoyin.” Dilan ya koma ya zauna cikin tsananin damuwa, amma Zakin bai ko kula da yanayin da ya shiga ba.

Ya juya ga Kahuhu ya ce. “Malam wai bil’adaman nan da muke ta magana, yaya suke ne?  Wataran in ana magana sai in ji kamar suna da kirki, wataran kuma in ji ba abin da suka iya sai mugunta.”

Cikin sanyin jiki kwarai Kahuhu ya fara magana, domin shi ma bai ji dadin yadda aka hana abokinsa magana daga karshe ba: “Yallabai ai wanda duk zai fada maka wane ne dan’adam cikin takaitattun kalmomi, sai dai kawai ya fadi on ransa, ko kuma dai yadda shi bil’adaman suka mu’amulance shi. Ko dai wadanda ya hadu kuma ya yi mu’amula da su.”

“Haka ne?” Zakin ya tambaya.

“Kwarai kuwa,” Ya amsa masa, sannan ya kara; “amma idan so muke mu fahimce su da kyau, to ina ganin kamata ya yi mu fara tun da safe, ba kamar yanzu da muka ci karumin zaman ba. Domin su bil’adama ma’adanai ne, kamar ma’adanan da suke tonowa a karkashin kasa: Mabambanta ne a darajarsu, kamar yadda ma’adanansu suke. Dukkansu kuma, duk girman darajarsu , suna bukatar wani wanda zai kara wanke su, ya saita su kan hanya, sannan su zama mafiya amfani. Kamar yadda in sun hako wandancan ma’adanan dole sai sun gyara sun wanke ko sun tace, sannan yake zama mafi amfani gare su.”

“Na’am,” In ji Zakin; “to amma idan aka ce ka fada cikin takaitattun kalmomi, ya za ka iya bayyana su, masu kirki ko mugaye?”

Kahuhu ya ce. “Masu kirki ne.”

Rufe bakinsa ke da wuya Kunkurun ya zabura, ya ce. “Assha! Wannan magana ta yi muni, domin kuwa ta ci karo da nassi.” 

Kahuhu ya juya ya kalle shi cike da mamaki, ya ce. “Ko?”

Shi ko bai ko kalle shi ba, ya dubi Zakin ya ce. “Rankashidade, idan ka so sai in fada maka dabi’un bil’adama sanannu shahararru, wadanda kuma dukkansu akwai nassi da yake tabbatar da su. Idan kuma Malamin ya musu, in na gama fada ya karyata.”

Kai tsaye kuwa sai Zakin ya ce masa. “Bisimillah.”

Ya ce. “To bil’adama raki gare su. In suka samu abu, rowa gare su. In ka yi musu mugunta, sai sun rama. Masu yawan da na sani. Masu yawan musu. Azzalumai, masu yawan wauta, kuma masu butulcewa Ubangiji.”

Zaki ya rike baki. “Iye!?”

Kunkurun ya ce. “Ai ka ji na bayar da dama in ba haka ba ne a karyata ni.”

Zakin ya ce. “Na ji fa.”

Kunkuru ya kara cewa. “Wai fa wannan ban taba maka bangaren rashin tsarinsu ba; domin su ne suke karar da rayuwarsu a neman kudi, kuma su karar da kudin a neman magani, bayan sun tsufa.”

Zakin ya fashe da dariya.

Bayan yin shiru na dan taki kadan, Kunkurun ya kara cewa: “Idan an yi dace ne a cikinsu ake samun daya daga mutane uku, wanda yake godiya in an ba shi, kuma ba ya butulcewa. Idan ka so sai in ba ka labarin wasu nakasassu uku, daga cikin ingantattun labaransu.”

Zakin ya ce. “Za mu so jin wannan labari kuwa.”

Kunkurun ya gyara murya, sannan ya fara: “Wasu mutane guda uku; da Kuturu da Mai Kora da Makaho, sun kasance cikin matsanancin talauci, bayan wannan nakasa da suke da ita. Watarana sai wani Mala’ika ya zo ya samu Kuturun nan ya ce. ‘Kai kuwa  yanzu me ka fi so a duniya?’ Kuturun nan ya ce ai babu abin da ya fi so kamar ya gan shi ya zama mai kyakkyawan launi, da fata mai kyau, kuma duk wani abu na jikinsa da mutane suke kyamatarsa don shi duk ya gushe. Da Mala’ikan nan ya shafi jikinsa sai nan take ya koma kyakkyawan mutum yadda yake son ganin kansa.  Sannan ya kara tambayarsa: ‘To wace irin dukiya kuma ka fi so?’ Kuturu ya ce Rakuma yake so. Ai kuwa sai Mala’ikan nan ya kawo Taguwa guda daya ya ba shi, ya ce. ‘Allah Ya sa maka albarka a cikinta.’  Ya tafi.

Zakin ya ce. “To fa.”

“Haka nan kuma ya je wurin Mai Korar nan,” In ji Kunkuru; “shi ma suka yi irin waccan magana. Shi ma ya shafe shi, nan take gashi mai kyau ya fito masa, kuma duk wani abu da mutane suke kyamatar sa don shi ya gushe daga jikinsa. Shi ma ya tamabaye shi irin dukiyar da yake so, Mai Korar nan ya ce Shanu yake so. Mala’ikan nan ya kawo katuwar Saniya mai ciki ya ba shi. Shi ma kuma ya yi masa addu’ar albarka a cikinta, ya tafi.”

“Muna biye dai.” In ji Zakin.

Ya ce. “Sannan ya je gun Makaho, shi ma suka yi irin waccan tattaunawa da shi. Ya kuma shafe shi. Idanunsa suka bude. Sannan ya tambaye shi irin dukiyar da yake so. Makahon nan ya ce Awaki yake so. Ya kuwa kawo dakwalwar Akuya ya ba shi, ya kuma yi masa addu’ar albarka a cikinta, sannan ya tafi.”

Zakin ya ce. “Burun kowa ya cika kenan.”

“Iy mana.” In ji Kunkurun, “Lokaci mai tsayi ya shude, sai ga shi kowannensu kiwo ya yi albarka gagaruma. Wancan ya hada katon garke na Rakuma, wancan na Shanu, wannan kuma na Awaki.”

“Daula ta zauna kenan.” Zaki ya fada cikin murmushi.

Kunkuru ya yi dariya: “Iy, saura kowa ya bayyana launinsa ba.”

“Lallai fa.” Wani tsagi na mazauna fadar suka fada cikin sassaukan sauti.

Kunkuru ya ce. “Katsam watarana sai Mala’ikan nan ya zo wurin Kuturun nan, amma cikin suffa ta Kutare, irin dai yadda yake a baya sak. Ya ce da shi. ‘Ni miskini ne kuma guzuri ya kare mini, gashi ina cikin halin tafiya. Ba ni da wanda zai iya yi min wannan agaji yau sai kai sai Allah. Na hada ka da Ubangiji wanda Ya ba ka wannan kyakkyawan launi, da kyakkyawar fata da dukiya, ka ba ni Rakumi guda da zan yi amfani da shi don karasa wannan tafiya.’  Ai Kuturunka sai ya yi kememe ya hana shi.’

Wasu daga mazauna fadar suka hada baki da Zakin wurin cewa. “Iye?”

Kunkuru ya ce. “Hmmm, ai ba ka ji komai ba tukun Yallabai. Sai da Mala’ikan ya kara tambayar sa: ‘Ni kuwa kamar na san ka, ba kai ne wani Kuturu ba, talaka da mutane suke kyamata, Ubangiji Ya  hore maka?’ Gogan naka sai ya yi mirsisi  ya ce ai sam ba shi ba ne. Shi wannan dukiya ma gadar ta ya yi kaka da kakanni!”

Kafatanin dabbobin da ke wurin daga masu dora hannu aka, sai masu dafe kirji, cikin tsananin mamaki. Zakin ma babu abin da yake yi sai faman girgiza kai cikin wani yanayi mai kama da jimami. Babu kuma wanda ya samu damar yin magana har ya dora.

“Haka kuma suka yi da wancan Mai Kora, kamar yadda sukai da Kuturun. Makahon ne kadai daga ckinsu bai butulce ba. Da aka tambaye shi ya bayar, ba tare da musu ba.”     

Da ya kawo wannan gabar sai ya ce. “Akwai wani tsabar butulci da mantuwa da musu da karyata gaskiya da ya wuce wannan?”

Zakin ya ce. “Kai, babu shi kam.”

Ya ce. “To haka fa suke Yallabai, sai an yi sa’a ne a cikinsu akan samu guda daya tak irin wannan makahon.”

Zaki ya ce. “To Ubangiji Ya kara yi mana katangar karfe da su.”

Mazauna fadar suka hada baki. “Amin.”

Har zuwa wannan lokaci kamar yadda Dilan bai kara cewa ko uffan ba, bayan da aka dakatar da shi, haka shi ma Kahuhun bai ma yi ko yunkurin kara tofa komai ba. Har dai suka kammala kidansu suka kuma yi rawarsu su kadai.

Zakin ya yi sallama, bayan ya lura da cikar lokacin da ya saba tashi, har ya fara tafiya, sai kuma ya waiwayo ya ce wa Kunkurun: “Ina gayyatar ka cin abincin dare a gida!” Sannan ya shiga gida. 

Dabbobin wurin suka cika da mamaki kwarai. Domin sun san wannan gayyatar cin abinci tana daya daga cikin kololowar karramawa da Basaraken yake yi wa dabba. Sannan babban sanadi ne na samun dukkan wata bukata a wurinsa. Kasancewar ana cin abincin ne tare da dukkan iyalinsa. Shi kuwa Zaki babu dama ka tambaye shi wata bukata a gaban matarsa ba tare da ya yi mata ita ba. 

<< Yini Sittin Da Daya 29Yini Sittin Da Daya 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×