Yini Na Shida
Da gari ya waye, tun kafin lokacin da aka yi tsammanin fitowar Basaraken ya fito. Kodayake, duk irin sammakon da ya yin wurin fitowar ya riski ‘yan gaban goshin fadar tasa a wurin. Da isowarsa, kafin ma ya zauna su kai ga kwasar gaisuwa, Kahuhu ya ce. “Madalla da adalin Sarki!” Sannan bayan zaman nasa suka yi gaisuwa kamar yadda aka saba. Gama karbar gaisuwar kuma ke da wuya ya juyo ya dubi Kahuhun yana murmushi ya ce.
“Alaramma na ji yau ka yi kirarin da ba ka saba yi ba.”
Kuhuhu ya risina ya ce.
“Allah Ya kara maka yawan rai, dama dai salon milkinka yana burge ni kwarai, to kuma yau din sai ka kara yi min birgewa ta musamman, yadda na ga ka yo sammako haka ba yadda ka saba fitowa ba. Kuma na yi tunanin ganin ka tauye zaman jiyen ne ya sa ka yi wannan fitowar, don ka biya bashi.”
Basaraken ya yi murmushi tare da cewa.
“Kahuhu birnin sani.”
Dila ya yi farat ya dora:
“Eh, ilimi mai tafiya, ilimi mai tashi, a sama karatu, a kasa karatu, kadan da babban aiki. Ba jikin ba, kan!”
Dukkansu suka yi dariya, sannan Kahuhun ya kalli Dila yana cewa.
“Kai fa dama an sosa maka inda yake yi ma kaikayi.”
A daidai wannan lokaci kuma suka hangi dakarunsu cikin wani shirin atisaye na musamman. Tururuwai ne a sahun gaba, suna tafiya jere a kan layi. Sai bayan sun zo kofar fadar suka hade wuri guda. Sannan wasu tsirari daga cikinsu suka fara wata tafiya mai shataletale da kwan- gaba -kwan-baya, wanda kafatanin dabbobin wurin babu wanda zai iya bugar kirji ya ce ga dalilin yin ta. Bayan sun kai wani bigire sai kuma dukkansu suka bude fukafukai suka tashi, suka koma wurin da suka tsaya na farko. Daga nan sai suka kara matsawa can baya. Yayin da su kuma Zomayen nan suka matso gaba, bayan sun kafa hancinsu a kasa sun yi wani dan sansane-sansane sai nan da nan suka ci gaba da bin dukkanin wurin da wadancan Turwai suka bi dazu, ba tare da saba ko daya daga shataletalen da suka yi ba.
Dila ya juyo hannunsa na hagu, ya ce.
“Ka kuwa fahimci me suka son nunawa a nan?”
Kahuhun ya ce. “Ba inda Tururuwar ta bi suke bibiya ba?”
Ya ce. “Ashe ka fahimta. Ka san daga cikin abubuwan da ta yi alwashin yi, har da samar da wannan sinadari, wanda zai zama tamkar wata taswira da dakarun za su bi zuwa duk inda ‘yan’uwansu suke.”
Kahuhu ya ce. “Kwarai an yi haka kuwa.”
Hankalinsu ya kara komawa kan Zomayen, wadanda a yanzu suka sukwano cikin wani gudu mai ban mamaki zuwa bigiren nan da suka fara tsayawa.
Jin kadan su ma suka sulale suka koma baya. Sannan Kuregai suka maye gurbin, ta hanyar shigowa gaba. Daki-daki, sai da dukkanu suka shigo, kowanne ya nuna irin tasa gwanintar, har zuwa kan Birai, wadanda su ne na karshe. Kananan Biran, wadanda kallonsu kadai ya ishe dabbobin dake fadar abin mamaki, su ne a kan gaba. Sai wadanda suka dara su girma a bayansu, haka dai har zuwa kan kabilun Banu-dungazau din, wadanda su ne a can karshen baya. Suka dauki lokaci mai tsayi suna wasanni irin na bajinta iri-iri.
Tsawon lokacin da aka dauka ana wannan atisaye fuskar Basaraken cike take da walwala, yayin da can kuma zuciyarsa ta cika da alfaharin samun wadannan dakaru masu tsananin azanci a karkashinsa. Daga karshe, bayan duk sun zo sun jeru cikin ladabi a gabansa, sauran dabbobi suka dauki lokaci suna maimaita wa rundunonin: “Sarki ya gaishe ku!” Bayan nan shi ma da ya bude baki kai tsaye ya ce da su.
“Babu wata daula da za ta samu fasihan dakaru irinku kuma su ji tsoron tunkarar yaki da wani mahaluki.”
Kafatanin dakarun nan suka cika da farin cikin jin batun nasa. Sannan ya kara cewa.
“Hakika ban tuna wani abin alfahari mai girma da ya fara a fadar nan a wannan karnin kaf kamar samuwarku ba.” Ya dan dakata yana bin su da kallo, sanna ya dora: “Kuma ina ba ku tabbaci cewa a shirye na ke da ba ku dukkanin wasu bukatu da za ku nema, kama daga kan abinci har zuwa dukiya.” Muryoyinsu suka rika amo a wurin:
“Muna godiya Rankashidade!”
“Allah Ya kara maka tsawon rai.”
“Ubangiji Ya ba ka rinjaye.” Da sauran kalamai na girmamawa dangogin wadannan.
Zakin ya juya ya dubi inda Kahuhu da Dila suke zauna. Nan take kuwa Dilan ya ce.
“Rankashidade, ba ma sa wadannan wasanni na gwaninta a cikin wasannin idinmu ba?”
Kahuhu ya ce.
“Shawara mai kyau, da fatan fada za ta duba.”
Zaki ya ce. “To ai shi ne silar juyowar da na yi gare ka. Ni ma abin da ke raina kenan, domin hakika na kayatu da lamarin.”
Zaman fadar dai na wannan rana yana daga cikin zama masu matukar nishadantarwa wadanda idan za a yi kididdigar zama masu dadi da wuya a manta da shi. Wanda a karshensa masarautar ta amince cewa washegari da sassafe wadannan dakaru za su zo su nufi hanya, don tunkarar abokan gaba.
Da maraice Basaraken ya kara fitowa don zama da manyan dabbobi, kamar yadda aka saba. Wadanda kaso mai yawa suna zaune a fadar tun kafin isowar tasa. Bayan ya daidaitu a kan karaga kafatanin mazauna fadar suka gurfana suka yi gaisuwa. Sannan da kansa ya fara yi musu bayani:
“Mun tattauna da dakarun da za mu tura wancan artabu, kuma mun yi matsaya a kan cewa gobe da safe dukkansu za su kama hanya. Idan kun so, dukkanku kuna iya hallara mu yi musu addu’o’in nasara da kariyar Ubangiji Al-Karim.” Ya dan dakata, irin dakatawar da ya saba yi ta al’ada. Sannan ya dora: “Muna kara jan hankalinku cewa ku kasance cikin shiri, domin, ba fata muke ba, amma idan abin ya fi karfinsu, to kun tabbata sai manya irinku sun sa hannu kenan.”
Yana bayani dabbobin nan na fama gida kai, har da mafi yawansu suka tabbatar da waccan magana da Dila ya yi musu a kwanakin baya; cewa an bar su a gida ne don kawai tsananin soyayyar Sarkin gare su. A irin wannan yanayi zaman fadar na wannan rana ya tashi. Basaraken ya koma gida, kafatanin al’umar fadar suka tarwatse zuwa nasu gidajen.
Labarin yana ɗauke da darussa masu ilmantarwa Allah Ya ƙara basira