Skip to content
Part 2 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Biyu (Zalunci Gimbiya Juhiaina)

Gudun da lokaci ke yi baya hana rayuwa da abunda rayuwa ta ƙunsa tafiyar da al’amurransu, tsawon shekaru ashirin da biyar kenan da haihuwa Zinariya, in da ƙaddara ta zaɓar ma Zinariya zama a duniyar jinnu wanda ba lallai hakan ya zame mata abu mai sauƙi ba. Cikin shekarun nan Zinariya ta rayu ne har ta kawo yanzu cikin tsanani da wahala dan rayuwa na yi mata Matuƙar wahala a ƙarƙashin inuwar waɗanda ba jinsinta ba.

Zaune take akan wani dutsi mai matuƙar girma da faɗi, an ƙawata dutsin da magudanar ruwa da kuma furanni da aka killace a duk wata kwana da za a iya tsugunnawa ko a zauna, lilo take yi da ƙafafunta tayi shiru da alama ta zurfafa cikin tunani. Wata Ƙatuwar mage ta bayyana gabanta, a ɗan razane ta ja baya jin magen gefenta, ta zuba mata ido tana sauke ajiyar zuciya. Magen ta matse jikinta sosai nan take jikinta ya rikiɗa zuwa bil’adama.

“Wai yaushe ni ɗin nan zan daina tsorata Zinariya ne?” Magen da ta Rikiɗa zuwa suffar bil’adama tayi maganar, murmushi Zinariya ta yi ta ce “na yi dogon tunani akan hakan amma amsa ɗaya nake samu samu”, “wace amsa ke nan? ” ta tambaya, Zinariya ta numfasa ta ce “ babu ranar da zaki daina firgita ni matuƙar kina zuwa min ba Sanarwa”, dariya tayi ta ce “o  ni Jamina  taya kike so na sanar miki “, Zinariya ta ce “umhm! Ina kika shige tun ɗazu nake cigiyarki”, “ina fada yau Sarauniya ta hana kowa zama. Kin san ta wasu lokutan sai a hankali “, gaɗa kai Zinariya tayi alamar e, sannan ta ce “ ya maganar tafiyar da ta ce zata yi”, “wai ta fasa ” Jamina ta taɗa.

Zinariya ta sadda kanta ƙasa tana lilo da ƙafarta kamar ɗazu. Jamina ta dafa kafaɗunta wanda hakan ya saukar mata da wani mugun nauyi duk da ta saba da jin nauyin amma hakan bazai hana ta jin ciwo ba idan har wani a cikin ƴan masarautar ya dafa ta “me yake damun ki? “Jamina ta tambaya, Zinariya ta ɗago ta kalle ta ce “ban san me yake damu na ba, amma dai ina jin ban da lafiya a ƴan kwanakin nan, hancina yana zubar da jini, kuma gefen ƙirjina yana matuƙar min ciwo”, ido Jamina ta zuba ma Zinariya tana kallon cikin ƙwayar idonta sannan ta rufe idon da sauri ta buɗe wata wuta mai hasken gaske ta fito daga idonta, kaifin hasken yasa Zinariya rufe idonta dan hasken yayi wa gangar jikinta haske. Miƙewa Jamina tayi, Zinariya ma ta miƙe ta bi bayanta.

Juhaina tana zaune akan wata doguwar kujera ta miƙe ƙafafunta da hannayenta hadimai suna mata tausa Jamina ta shigo cikin ɓacin rai “Juhaina miye dalilin zaluncin nan? ” Juhaina ta sauke hannayenta ƙasa tare da miƙewa tsaye tana faɗin “zaluncin me nayi?”, “me Zinariya ta miki? “, Juhaina ta ce “ta shiga gonata ne”, “ba wata gona da Zinariya ta shiga taki, kawai kin ɗauki karan tsana kin ɗora mata hakan bai dace ba ” ta faɗa , “to ko zaki kashe ni ne saboda Zinariya, duk yaushe aka haife ki har kike da bakin faɗa min abunda ya kamata nayi da wanda bai kamata ba, to bari ki ji na rantse da tsarkin mulkin Mahaifiyata zan iya kawar da duk wata halitta a duniya dan ganin na gaji Mama, bazai taɓa yuwuwa a ce daga zuwanta garin nan a ce ita ce magajiyar Mama ba, idan ta kama na kawar da numfashinki a doron duniya zan yi hakan, ballanta Zinariya da ba jinina na ” ta faɗa cikin tsananin fushi, Jamina ta ce “zaki iya kawar da kowa amma ba ni, kuma zan yi iya ƙoƙarina na tabbatar baki yi sarautar garin Gimatuwa ba” tana faɗin haka ta juya zata wuce amma wata igiya ta sarƙafe mata ƙafa, idonta ta buɗe sosai ta ware hannayenta ta nuni igiyar nan take ta katse, ta juya ta kalli Juhaina ta ce “idan zaki naɗe min ƙafa sau dubu dan ki kai ni ƙasa ba za ki taɓa yin nasara ba ” tana gama faɗin haka ta ɓace ɓat.

Ƙofar ɗakin da Juhaina take ta bayyana “me yasa kika yi haka?” ta ji sautin muryar Zinariya ta daki dodon kunnenta, cikin ɓacin rai ta ce “ita ce take bibiyarki Shi ya sa na tunkare ta “, Zinariya ta riƙo hannu Jamina ta ce “ba ina cikin rayuwarki dan na ga rashin jituwa tsakaninki da ƴar’uwarki  ba, ina so na kanku haɗe shi ne kaɗai soyayyar da zan nuna muku, da halarcin da mahaifiyarki ta min, bana jin daɗi idan na ga kuna faɗa ta dalilina, dan Allah ki daina”, murmushi Jamina tayi ta ce “hmmm babu wani mai zuciya irin taki, abar bauta ta ƙara miki tsawon rai, zuciyarki mai tsarki ce kamar ta abar bauta” tana faɗin haka ta ɓace ɓat. Murmushi Zinariya ta saki sannan ta juya ta wuce.

Washe Gari Da Safe

Numfashi take yi sama-sama jini yana bin hancinta, runtse idonta tayi tana jin wani mugun zafi yana ratsa tsakiyar kanta, zamewa tayi daga gefen gadon da take zaune tana kuka. Jahida ta shigo ɗakin, da sauri ta nufi Zinariya ganin yadda jini ke gangarowa daga hancinta ta ce “Lafiya kike zubar da jini haka?” Zinariya ta ɗaga kanta sama tana ƙoƙarin riƙe jinin amma Ina abun ya ci tura, yau jinin da ke fita ya fi na kullum, Wulle-Wulle ta fara yi tana ihu, a firgice Jahida ta miƙe ta nufi fadar Sarauniya tana haki ta shiga, tana shiga duk wani bawa dake cikin fadar yayi ƙasa da kansa suna faɗin “Barka da warhaka gimbiya ɗiyar sarauniya, Abar bauta ta taimake ki.” Cikin rawar murya ta ce “mmm… Mama, Ziii… Zinariya ce”, tashi sarauniya tayi tare da kallo wani Bango nan take bangon ya haska mata ɗakin Zinariya. Hannun Jahida kawai ta riƙa suka ɓace tare.

Zinariya na kwance ciki jini Sarauniya Jahiyana ta shigo da sauri ta ɗaga ta “Zinariya ” ta ambaci sunanta, a hankali Zinariya ta fara buɗe idonta sai kuma ta rufe saboda tsananin nauyin da suka mata, daidai lokacin Jamina ta shigo ɗaki da gudu ta durƙusa gaban Zinariya tana faɗin “Wallahi Mama bai kamata a ce Juhaina na irin haka ba.”

Sarauniya Jahiyana ta ce “me tayi ita Juhainar?” “ki kira ta ki ji” Jamina ta faɗa, Jahida ta ce “ba mu da lokacin ɓatawa Mama, ki ceci rayuwar Zinariya dafi ne a jikinta “, cikin zafin nama Sarauniya Jahiyana ta bugi goshin Zinariya da ƙarfi da tafin hannunta, sannan ta buɗe bakinta wani hayaƙi mai matuƙar zafi ya turnuƙe jikin Zinariya ko ganinta ba a yi, ta ɗauki lokaci tana fitar da hayaƙin, sannan ya yi sanyi kamar ba shi ne yake da wannan zafin ba, Zinariya ta sandare, jikinta yayi sanyi kamar babu rai jikinta. Sarauniya ta miƙe tana faɗin “na cire dafin zuwa anjima zata farka, ku turo min Juhaina ɗakina ” tana faɗin haka ta rufe idonta tare da maƙe jikinta ta ɓace. Jahida ta miƙe ita ma ta wuce.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Zinariya 1Zinariya 3 >>

1 thought on “Zinariya 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×