Skip to content
Part 3 of 6 in the Series Addininmu by Salis M. Reza

… Allah ya bata ilimi ga dogon tinani, in har ta bugo ‘kasida tofa sai tayi dad’i, haka dai shima ya tafi cike da son jin wannan sabuwar’kasidar.

A J. VOP

Mai Okada bai sau’keshi a ko inaba sai ‘kofar gidan su Salis. Bayan ya sallami mai mashin d’in ne ya nufi bakin get d’in gidan cike da kwarin gyiwa, yana zuwa ya bubbuga cikin ‘kan-‘kanin lokaci mai gadin ya bud’e. kafin A J yayi magana mai gadin ya ce “Kaine AJ ko? Da sauri AJ ya ce “Eh nine.

Ai kuwa take ya bashi hanya had’i da cewa “yace in kazo ka shiga ciki. Tin daga harabar gidan AJ yake sake bin gidan da kallo sai yaga gidan kamar ya ‘kara kya u, kamar ba gidan da suka zo shekan jiyaba, sai da yaje ‘kofar palorn kafin ya danna abun da yaga Salis ya danna wancen lokacin kafin ya nemi guri ya tsaya kamar dai yanda sukayi wancen karan d’in.

‘Yar aikin gidan ce tazo ta bud’e kamar wancen lokacin, yana shiga ya hango Hajiya zaune a d’aya daga cikin kujerun dake cikin palorn, da sauri AJ ya fara kwasar gaisuwa. Hajiya ta amsa sannan ta ce “Tashi daga ‘kasa ga guri ka zauna, babu musu ya zauna yana kallon hanyar da zaiga Salis ya fito.

Hajiya ta ce “Salis baya nann dama nice na sa ya kiramin kai, tin ranar da na ganka agidannan kaida my son naji ina son in d’aukeka wani ai ki mutu’kar zaka iya? Cike da mamaki AJ yake kallon hajiya kafin ya ce “Hajiya ni in dai zan samu kud’i kuma ADDINIMU bai hana ba Wallhi ko menene zanyi. Cike da jin dad’i hajiya ta ce “Ok tom kazauna cikin shiri nann da wani lokaci zan fad’a maka wani irin aikine zakayi, kuma zaka samu kud’i sosai domin kuwa in har ka yarda to daga ranar bakai babu ta lauci.

Jin abun da hajiya ta ce ne yasa AJ cewa “To hajiya a fara sanar dani aikin mana tin yanzu sai na fara shiri? Hajiya tayi dariya tana kallon sa cikin burgewa ta ce kar ka damu yanzuma kanada wani babban kaso daga cikin kud’in aikin na ka ina zu. Hajiya ta mi’ke tsaye ta nufi d’akin ta, shikuwa sai bin ta yake da kallo har ya daina ganin ta. Ai kuwa take ya saki wani dariya yana cewa “kai Yasin AJ ni na daban ne, irin wannan farinjini hk! Yana cikin hakane hajiya ta dawo. Ta mi’ka masa bandir din yan dubu-dubu guda d’aya wato dubu d’ari kenann.

Cikin rikicewa AJ ya ce “Haji hajiya Wann wann Wannan nawaye? 

Hajiya ta ce “Ko baka sone?  

“Ina so wallhi inaso sosai makuwa. Kai hajiya na gode sosai Allah ya saka da alkairi. Amma hajiya wannan wani irin aikine? 

Hajiya ta ce “Aikin bashi da wani wahala kaide ka zauna cikin shiri. “Ai kuwa hajiya a shirye nake wallhi. Haka AJ ya bar gidan cikin tsan-tsar farin ciki, kasuwa ya fara zuwa ya musu siyayar kayan sakawa shida Nana da innah kafin ya tsaya a gurin mai kaza ya seyo musu ko d’aya, yaje ya siyo musu yourgot kafin ya nufi gida cike da farin ciki.

ZAHRAH VOP

Fitowa da kud’in tayi ta girga taga dubu d’ari harda tara, aikuwa ta bud’e baki da hanci tana mamaki me yasa ta d’ebo da yawa, take ta saka a cikin jakar school d’in ta, sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa gamida sau’ke abun da ta tara a cikin ta tsabar far gaba. Riga da wando ta saka na Adidas sannan ta nufi kiching domin samun abun da zata ci, tana shiga tayi karo da Mommy a ciki tana had’a musu abincin yamma.

Cike da mamaki Mommy take kallon ta, cikin yaran su Mommy ta ce “Daga ina kike?

“Mommy nadawo tin d’azu zan shiga gida naga kun rufe gidan shine na koma sai yanzu nadawo. Mommy ta bud’e baki zatayi magana taji muryar Samuel a d’akin Daddy yana ihuu ai kuwa suka nufi gurin da gudu. Cikin fushi Daddy ya ke cewa “I see wer is my money? Samuel na kuka yana cewa “Daddy banine na d’auka ba Allah nima yanzu na shigo.

Mommy ta shiga tsakanin su sannan ta  mi’kar da Samuel ta ce 

“Samuel what happened?

“Mommy I don’t know.

Ta juya gurin Daddy ta ce “What happened?

Cikin fushi Daddy ya sanar da ita komai, sannan ya d’ora da cewa… “Dubu d’ari harda wani abufa ya d’auka.

Mommy kuwa ta ce “Amma kuma ai tare da Samuel muka shigo gida, kuma kace ta ciki ka rufe ‘kofar d’akin naka, to tayaya Samuel zai iya shiga? Kafin Daddy yayi magana Zahrah ta ce

“kokuma Daddy bai rufe ‘kofar d’akin da kyu bane shine Samuel d’in ya shigaba. 

Ai kuwa Daddy ya ce “Yes of course hakane ma. Samuel ya harareta yana jin kamar ya kamuta ya fara tattakata. Mommy ta ce “No inda shine da bazai zauna a d’akin ba tafiya zaiyi.

DADDY ya ce “Ya tashi ya dawo masa da kud’i kafin yasa sojojin waje su karkaryashi, Samuel de sai kuka yakeyi, shikuwa Daddy ya kafe akan dole shine ya d’auka. 

Zahrah kuwa take taji ta daina jin yunwar tsabar tsoro, Daddy baya dukansu sai sun kaishi bango, yanzu da ita ya kama haka zaitama wannan dukan! Sai kuma ta fara tinaninn shimafa Samuel d’in tasan dole sukwaso riki dashi in ya warke. Take Kuma ta tuno da rabin ran nata tana jin in ta kai masa wannan kud’in ai za’a daina renashi tin da zai siya babbar waya. Take ta nemo number sa ta ai ka masa da kira.

ABDULLAH VOP

Da sauri ya ‘karasu gurin Abba yana mai d’an du’kawa kad’an ya ce “barka da yamma Abba gani?. Cikin sanyin murya da ta Saba da karanta ALQUR’ANI mai girma Abba ya ce “Abdullha kaga yanzu mutane suna ta magana a kanka akan zaman ka haka, kasan ba mutum baya cika mutam har sai ya ajiye iyali, yanzu fa kai ba ‘karamin mutum bane, duk in da kashiga a ‘kasar nann ansanka, kai harma wasu ‘kasashien, kuma kaga kai ne mai yiwa mutane wa’azi a kan aru’ke sunna a bar bidi’a, Amma kuma kai bakayiba shin hakan zai yu kuwa?…

Saboda haka abun da nakeso dakai shine kafitar da wacce kakeso ka yi aure domin al’umma su sake ganinn ka da kima. Abdullha ya dubi mahaifin nasa ya ce “Gaskiyane Abba, amma Abba duka-duka shekarata nawa da har zan fara maganar aure? Shekara tafa 26 zuwa da 27 Amma Zan fara zancen aure. Abba ya ce “Abdullha ka duba matsayin ka ba shekarunka ba, yanzufa mutane masu shekara. Arba’in ma girmamaka sukeyi, saboda haka nidai yanzu umarni zan baka akan ka fitar da wacce kakeso a cikin wannan shekarar.

Abdullha ya ce “Tom Abba tindadai kace umarnine in sha Allah zan fitar. Abba wato Shek Kabiru Kabuga, malimin sunna wanda yayi suna wajan ru’ko da sunna a fad’in duniya, wanda tin yaronsa wato abdullha Kabir yana ‘karami yake tafiya dashi duk in da zashi kuma yake ja masa a’ya awajan wa’a zi. Har take yanzu shima abdullha yazama jigo ga al’umman dake tare da mahaifin nasa. Abba ya saka masa albarka sannan ya tashi ya tafi.

Abdullha kuwa gidan sa ya nufa yana shiga ya fad’a toilet yayi wanka sannan ya zauna ya fara rera karatun ALQUR’ANI mai girma cikin muryarsa mai sanyin dad’i, saida yayi izufi biyar (5) sannan ya shafa addu’a kafin ya zauna ya shiga tinanin maganar Abba…

To ni yanzu daba soyayya na keyiba ina ni ina wata budurwa! Nann take Aisha ta fad’o masa a rai, amma yayi tsaki yana cewa, wannan yarinyar batada kamun kai, haka dai ya dinga tufka da warwara, harma yayi banza da maganar ya kama har kokin gaban sa.  Take yatina da cewa abokin safa ya gaiyace shi gurin bikin sa, amma ba wa’a zi zaiyiba zaije gurin walimar ne, walimar da uwar amaryar ce ta shirya, haka ya tashi ya shirya domin halartar gurin, kafin lokaci ya ‘kure, domin kuwa abdullha yana kiyaye Al’kawari.

ZAINAB VOP

Washe gari ta shirya tsaffff domin zuwa wani taro biki da a ka gaiyaceta zatayi qasida a gurin, Saida taje gurin Mama suka gaisa, sannan ta ce “Mama ina Aisha ne? Mama ta ce “Sun fita da Isa wai zata rakashi kasuwa. “Ok tom mu zamu je majalisi sai an jima zamu dawo, nann take Mama ta saka mata albarka sannan tamusu fatan nasara kafin ta fita, tabi d’akin mlm shima yasaka mata albarka kafin ta fita. 

Tana zuwa waje taga halifiyar tata wato Maryam wacce duk wani taro ko mauludi in an gaiyaceta to tare suke zuwa, wani lokaci ma in Bata da time ita take turawa. Maryam tazama tamkar ‘kawace ga Zainab sannan kuma yarinyar ta. In ana cikin hadaya na yabon Annabi Muhammad sallalahu (S.A.W ) girma take bata sosai, in kuma a zahirine ko a gida, zaka gansu acikin wasa da dariya.

Haka suka tafi cikin wasa da dariya. Suna isa gidan, matar da ta kirata tazo da gudu ta rungumeta tana kuka cike da mamaki wai yau gata ga Zainab Ambato. Ta ce “Zainab Ambato wallhi na kasance duk anguwarmu nafi kowa son ki da ‘kasidunki, domin kuwa duk wata sabuwa gasidar ki in tafito sai na d’auko ta, tin kafin yarinyata ta samu mijin aure nayi Al’kawarin sai na gaiyatoki walimar auran kuma, gashi Allah yayi. Matar harda kuka, yayin da yarinyar matar ma tazo ta rungumeta sunata saka mata albarka.

Ita kuwa Zainab Ambato me take in banda mamaki cikeda farin cikin ganinn irin wannan tsan-tsar soyayyar. nann fa al’umma maza da mata suka fara murnar ganinn ta sai zuwa sukeyi ana hoto.

Da kyar aka samu a ka barta ta fara gabatar da majalisinta. Nan fa duk ‘kasidar da ta fara sai kaji muryoyin al’umma tamkar sune sukayi, haka zatayi shiru al’umma sunayi kuma basa mantuwa, uwar amarya kuwa babu kunya ta ce yau ranar farin cikin tane, tafara rera ‘kasidar Zainab Ambato kamar ita tayi. Ana cikin hakane a kazo kan ‘kasidar da ta saka kwanannan wato *GANI ASO*. zokaga al’umma. Ana cikin ha sai ga ango da abokansa…

Angon shi kad’ai ne sai mutum biyu acikin abokannasa… Kana ganinn su kaga malamai aikuwa nannn al’umma suka hango Shek Abdullha d’an gidan Shek kabiru kabuga. Nann fa suka fara mamakin mai ya kawoshi nann bayan bayason wannan wa’ke-wa’ken, tin daga nesa suka fara jin muryar mutane ana jin wa’kar Gani aso, dai-dai gurin da take cewa, ( *narantse da ilahumma ma’aiki bani da wani wanda nakeso ya maa’aiki Allah shine masanin zuci da baki, sanda nakemassa masoyin sa ma’aiki)*.

Nann take abdullha ya tsaya agurin ya kalli angon ya ce “Salim kace min walima za’a yi agurinnan? Salim ya ce “Sorry Shek wallhi nima bansan za’a gaiyato mawa’kiya ba, “Amma ai kasan yarinyar da ganima yar bidi’a ceko? Inji abdullha cikin tsananin b’acin rai. Salim ya ce “Kaga mutane na Kallon mu dan Allah muje muzauna sai muyi magana.

Abdullha ya ce nine zanje na zauna Ina kallon kad’e-kad’e da rare-rare? Salim ya ce “a’a za’a tsaya da shi yanzu please dan Allah?  Saida abdalh yaga mutane sun fara kallon su kafin yabar maganar ya nufi gurin da a ka ware musu wato angwaye.

D’aya daga cikin abokin angon me suna Yusuf ya ce “Wai ita wannan yarin yar ahaka zata ‘kare rayuwarta da kad’e-kad’e da rare-rare bazatayi aureba? Abdalh ya ce “To waye zai auri wannan ai rashin wanda zai aurane yasa kaganta haryanzu. Salim ya ce “Haba kau wallhi wannan da kuke gani ba matar yara bace, ai ba kowane zai iya tinkarar ta da batum aureba sai de manya malamai wallhi. dai-dai lokacin da abdallha ya bud’e baki zaiyi magana ita kuma Zainab Ambato ta kai idonta gurin take idinsu ya had’u a guri d’aya, Saida sukaiwa juna kallon minti d’aya kafin suka kawar da idonsu.

Yayin da abdullha yakejin mugun tsanar abun da takeyi kana take Mata kallon rashin kamunkai. Ita kuwa Zainab idonsu na had’uwa tamai kallon ‘kiyayya kafin ta kalli halifiyarta ta ce “Jeki sakamin wa’kar bagudu bajadabaya, wato wa’kar da abdullha ya musu Randi a kanta jiya.

Ai kuwa dama wa’kar sabuwace kowa soyake a zo kan wa’kar domin kuwa WAQAR tayiwa mabiya shehu dad’i. Ai kuwa ana sawa al’umma suka d’auka, nann take suka fara fitowa da hoton shehu Mata damaza samari da ‘yan mata, ko ganinn Zainab d’in ma bakayi. Saide kaji ana cewa… (BAGUDU BA JADABAYA KAN ‘KWANAR SHEHU MAULANA). 📝

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Addininmu 2Addininmu 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×