Skip to content
Part 13 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Murmushi ta saki tana saka kayan da aka dawo mata dashi daga wanki a cikin drower, tace.

“Ehh har yanzu ya kasa fahimtar shine wanda zuciyata keso, mtsss! Na fara gajiya Maimu, ji nake tamkar soyayyata babu Nasara, da ana sanja zuciya wallahi dana sanja wannan lusarar zuciyar tawa, wacce ta kasa cire wanda bai damu da ita ba a cikin ta, kullum sonsa ninkuwa yake sama da ninki huɗu a zuciyata, ina tsoron kar ciwo ya shigeni.”

Maimu Numfashi ta saki tana duban Rufaida tare da cewa.

“Zuwa yanzu ya kamata ace ya Haidar ya fahimci kina sonsa, amma da gaske shine ya miki alƙawarin samun Nasara a soyayyar ki, sannan ya tabbatar miki da bazaki faɗi, zai tsaya miki.”

Rufe drowern Rufaida tayi tare da zama gefen Maimu tace.

“Ƙwarai kuwa shine yamin wannan alƙawarin, mtsss amma ina ji a raina cewa bazai iya cika min ba, Soyayya zata makantar dashi ya manta da wannan alƙawarin, na shiga Uku Maimu anya soyayyar Ya Haidar bazata kasheni ba kuwa.”

“Soyayya bazata kasheki ba Rufaida ni kaina lamarin Soyayyar ki yana damuna, amma karki damu insha Allah Ya Haidar zai soki, ke dai ki dage da addu’a da kuma kyautata masa, ki dinga isar masa da sakon ki, ko ta hira ne, na rasa dame wannan tsinanniyar Nafeesan ta fiki da har yake hangota take dusashe hasken ki.”

“Ni kaina Maimu ina tunanin meta fini dashi a rayuwa da ta rigani ƙwace ya Haidar, ban sani ba wataƙil ko kyau ta fini ko kuma kyawun hali, ko iya magana ta fini, na kasa gane wanne ta fini a ciki.”

Maimu cikin tausayawa Rufaida tace.

“Bazaki gane abinda ta fiki dashi ba, Saboda baki da alaƙa da ita, da wannan tunanin zaifi kyau ki cika komai, ki kuma ɗauki ɗamarar ƙwato farin cikin ki.”

“Hmmm! Sanin kanki ne nayi duk wani ƙoƙari domin na dawo da hankalin sa gareni amma abun yaci tura, mtsss kema fa kin sani.”

“Na sani amma hakan bashi yake nufin ki sakankance ba, kamata yayi ƙoƙarin ki yafi na baya, saurin sarewa ga cimma Nasara wannan ɗabiar lusari ne, bana son ki zamo lusara, nafi so ki kasance tsayayyiyar jaruma mai ƙoƙarin ƙwato nasarar ta.”

Numfashi Rufaida ta saki tare da cewa.

“Shikenan insha Allah zan ƙara iya ƙoƙarina sai kema ki tayani da addu’a, bara na ƙarisa haɗa kayan sai muje.”

Da to Maimu ta amsa tana jawo wayarta.

Zaune suke a tsakiyar gadon su Nafeesa, kowa hankalinsa yana kan wayarsa, Amnat duban Nafeesa da ta zubawa wayarta idanu tayi tare da cewa.

“Nafeesa!”

Ɗago idanunta tayi ta kalli Amnat.

“Ina jinki.”

“Ba Maganar kina jina bane magana ce ta zuwa wajen malamin nan saboda kina buƙatar abinda kike samu a wajensa yafi wanda yake baki yanzu.”

“Hmmm! Amnat nifa kibar Maganar zuwa wajen wannan malamin domin kuwa na riga na gama mallake zuciyarsa, samun abin hanunsa kuwa, abune mai sauƙin gaske, a halin yanzu Haidar zuciyarsa ma nace masa ya ciro ya bani Wallahi zai cire kuma ya bani, ke wawan fa ya riga ya gama afkawa tarko, a yanzu ba Maganar zuwa wajen malam, sai dai kuma idan gaba naga tazo da tangarɗa sai mu ziyarci Malam, ni yanzu haka ma tashi zan na tafi, hotel zan shige Atiku Naira yana jirana, kuma shima kinsan ina samu garesa wanda nake samu a wajensa shi nake bawa Mama.”

“Mtsss! Ke matsalarki kenan, saurin yadda da kanki, ya kamata kijeki saboda riski amma tunda kince bazaki ba ai shikenan, ni yanzu so nake ma ki bani aron 50k next week akwai birthday ɗin Samy, ina so na kashesu a BIRTHDAY ɗin.”

Dariya Nafeesa tayi tace.

“Gaskiya sai dai ko na baki 20k dan gaskiya ina tsoron baki 50 kizo ki hanani in tafka miki tsiya kiji haushi na, dan wallahi bazan yafe miki har 50k ba.”

“Kinyi asara da tsinannan son kuɗin tsiya, ni 50 zaki bani Saboda bazan hanaki kuɗin ki ba, domin nasan kuɗi bazasu ciyu ba.”

Tayi Maganar dai-dai Nazifa tana shigowa, kallon banza ta watsa musu cike da ƙyamar halinsu ta ɗauki cup zata fita taji muryar Nafeesa na cewa.

“Wai Nazifa me kike ɗaukar kanki ne dan ubanki, yanzu har rashin mutuncin naki, ya kai ki dinga min kallon banza, to wallahi ki fita sha’anina kafin naci ubanki dan naga kinyi mungun raina ni.”

Murmushi Nazifa ta saki tare da juyowa ta kalli ƴar Uwar tata tace.

“Allah ya kiyashe ni taɓewa, meye abin raini yanzu kuma kinga ban kulaki ba, dan haka ki daina takalata da masifa, sannan karki kuma zagin ubana domin kuwa ni ƴace ta gari ina ganin mutuncin ubana duk lalacewarsa, ki kiyaye, ban taɓe ba nasan mutuncin kaina.”

Zaro idanunta Nafeesa tayi tare da nuna kanta da yatsa tace.

“Nazifa ni kike gayawa magana, ni ce ƴa bata gari ba, ni ce ban san mutuncin kaina ba lallai Nazifa yau kin gaya min baƙar Magana.”

tayi Maganar tana ƙoƙarin miƙewa da nufin ta yiwa Nazifa mungun duka, Amnat riƙo hanun Nafeesa tayi tare da girgiza mata kai alamun karta je, murmushi Nazifa tayi ta fice daga ROOM ɗin.

“Kina jin abinda Yarinyar nan take faɗa min fa Amnat sannan ki hanani dukan shegiya kai amma Nazifa tayi mungun raina ni wallahi.”

“Kinga Nafeesa ki rabu da ita Domin ba kunya gareta ba, yanzu haka ne take ta cakaleki kuyi masifa har Baba yazo ta miki tonan asiri tunda kinga yanzu haka ma yana gidan nan, ki dinga haɗiye fushinki a wajenta.”

Numfashi Nafeesa ta sauƙe tare da zama tana cewa.

“Kuma hakane, kin san na manta ma da yau Baba yana gida, kinga ni tashi ma mu tafi kafin ya fito ya hanani fita.”

Dariya Amnat tasa tare da miƙewa ta ɗauki bag ɗinta suka fita.

Tunda ya zauna a Office ɗinsa ya kasa aikin komai gabaki ɗaya zargi da tunanin accident ɗin Ashfat ya cika masa ƙwaƙwalwar sa gashi dai yau kimanin wata biyu da accident ɗin amma ya kasa yarda da cewa daga Allah ne gani yake haɗa musu accident akayi duk da bashi da wata hujja da take nuna hakan, ya kasa fahimtar komai, tsuka yaja tare da miƙewa ya ɗebi wayoyinsa ya fita Office ɗin Haidar ya shiga ya samu Faruq na zaune suna tattaunawa game da ayyukan Companyn, gefe dasu ya zauna tare da yin shuru, Haidar kansa ya ɗaga ya kalli Al’ameen yace.

“Wai lafiya kuwa Al’ameen naga ka zauna kayi shuru.”

Faruq juyowa yana kallon sa shima, tsuka Al’ameen yayi tare da cewa.
“Mtsss! Wallahi Haidar har yanzu tunani nake akan accident Ashfat zuciyata taƙi amincewa da wannan accident ɗin gani tamkar haɗasa akayi duk da bani hujjar abinda nake zargi.”

“Oh my God wai yanzu Al’ameen abinda ya wuce wata biyu kake ƙoƙarin bawa tunaninka wahala akansa, wannan accident kowa ya sani Allah ne ya aikosa ba wani ba amma ka kasa fahimtar haka, dan Allah ka bar wannan tunanin domin kuwa tunaninka ba gaskiya bane.”

Faruk ne shima yace.

“Hmmm! Al’ameen dan Allah kabar wannan maganar ta wuce domin kuwa babu gaskiya cikin hasashen ka, tunaninka shirme yake baka.”

Shuru Al’ameen yayi cike da nazarin kalamansu domin kuwa sun fishi GASKIYA, numfashi ya saki tare da ɗaga kafaɗarsa, Haidar ne yace.

“Am maganar ɓatan kuɗin nan, munyi bincike akai Sosai, Abbas muka samu da hanu cikin rage kayan.”

“Okay Abbas shine ya rage mana kaya, ba damuwa, a dakatar da salary nashi na wata shida sannan zanyi Magana dashi yayi kuskure sau ɗaya karya kuma na biyu.”

Yayi Maganar yana miƙewa yabar Office din, Faruq ne ya dubi Haidar tare da cewa.
“Yau yaushe zamuje ka kaini naga Nafeesa”?

“Yau Inna Jumma tace zan rakata unguwar Durmi, gidan su ABLAH, da sai muje yau amma insha Allah, sai muje gobe ko.”

Murmushi Faruq ya saki yana cewa.

“Gaskiya Yarinyar tana bani tausayi gata da hankali, ranar kaga wulaƙancin da Al’ameen ya mata kuwa Allah sai da naji tamkar na ɗaukesa da mari .”

“Hmm! Ni na rasa dalilin da yasa Al’ameen ya tsani Yarinyar nan, haka ya mata sanda ya bigeta ma daƙyar na samu na taushesa, na rasa dalilin da yasa Al’ameen baya ƙaunar mata shi ko irin ɗan felling ɗin ma bashi dashi, gashi kuma Inna Jumma tace zata ɗaukota ta dawo da ita part ɗinsu, gaskiya akwai matsala haɗuwarsu waje ɗaya.”

Dariya Faruq yasa yace.

“Umm! Allah dai ya kyauta, bara na koma gida kawai sai kun dawo.”
Har bakin mota Haidar ya rakasa sannan ya koma.

*****

Misalin bakwai na dare ya shigo room ɗin mahaifin nasa yana zaune da system a gabansa zama yayi ya tanƙwashe kafafunsa kusa da mahaifin nasa yace.

“Barka da hutawa Daddy.”

Ɗago kansa Daddy yayi fuskarsa cike da fara’a tare da tsantsar ƙaunar ɗan nasa yace.
“Yauwa Barka Zakina, har ka dawo daga Office din kenan.?”

“Ehh Daddy na dawo tun ɗazu, ban ganka a falo bane ma na tambayi Khalifa yace min kana bedroom ɗin ka, amma Daddy yaushe ne zaka koma American.”

“Eh to da next week nake son zamu koma Saboda nabar ayyuka da yawa acan, Zakina ya kamata fa ku fitar da matan Aure, zamanku haka bazai yiwu ba, ka duba Buhari ɗan gidan tsohon ministar sa’an kune fa, amma yanzu yaransa biyu ku kuna nan ko matar ma baku fitar ba, gara ma Haidar naga shi yana nema, amma kai da Faruq baku da niyya.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da sosa kansa yace.

“Amm Daddy! Nifa yanzu ba wani aure bane a gabana, mubar Maganar Daddy idan lokacin Auren yazo dole ai zanyi.”

“Abinda kake cewa kenan kullum idan lokaci yayi zakayi, sai yaushe lokacin zaiyi shifa lokaci tafiya yake baya jira, dan haka bazan zuba maka idanu ba, na baka nan da na sake dawowa ka fito min da mata, idan ba so kake sai ka dawo tuzuru ba kafin kayi Aure.”

Murmushi Al’ameen yayi cike da ƙaunar mahaifin nasa ya miƙe yace.

” nikam Daddy na gaishe ka da alamu yau hirar baza tayi daɗi ba, gara naje nayi da Inna Jumma.”

Yayi Maganar yana dariya tare da ficewa, shima Daddy dariyar yayi yace.

“Ai dole ka gudu tunda na maka maganar Aure.”

A falo ya samu Inna Jumma, ita da Aunty Amarya sai Maimu gefe kuma Ashfat ne kwance Aunty Amarya ta fito da ita tasha iska, Al’ameen jikin Inna Jumma ya faɗa tare da cewa.

“Wash Allah makashin kakata! Inna Jumma na gaji sosai kimin matsa.”

Ranƙwashi Inna Jumma ta kai masa tare da cewa.

“To dan ubanka ni dai gani ban mutu ba, sai dai kuma idan Uwar Uwarka ce zata mutu, dallah tashi min a jiki ni karka karya ni, da wannan murɗaɗɗen jikin naka, tausar taci gidan su.”

Dariya Aunty Amarya tasa tare da cewa.

“Haba Inna ya da faɗa haka kamar wacce kike jiransa, na dai ga alama kin samin ɗa a gaba.”

Tashi Al’ameen yayi yana dariya Inna Jumma ne ta cewa Aunty Amarya.

“To aimaka sarkin son ɗa sannu.”

Dariya Aunty Amarya tayi tana ɓallo magani ta bawa Ashfat, kusa da Ashfat ɗin Al’ameen ya koma tare da dafa kanta yace.

“Ashfat ya kikayi shuru, har yanzu bazaki daina tunani ba ko.”

Kallon sa Ashfat tayi tare da ƙoƙarin tashi zata zauna, Al’ameen hanu yasa ya ɗago Ashfat ta zauna, idanunta ne ya ciko da hawaye wai da ita da take zama da kanta ta tashi da kanta amma wai yanzu sai an taimaka mata, lallai rayuwa ba komai bace, saurin maida hawayen nata tayi gudun kar Al’ameen ya gani tayi murmushin yaƙe tare da cewa.

“A’a Ya Al’ameen ba tunani nake ba, nayi shuru ne kawai ina sauraran hirar ku, ya Al’ameen, zancen wayar tawa, baka kawo min ba.”

Ɗan murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Ashsha! Kinga na manta da zancen wayar nan, amma insha Allah gobe zan dawo miki dashi bazan manta ba.”

Kanta Ashfat ta ɗaga, Al’ameen sosai ya zauna sukayi hira da Ashfat cike da ƙauna irin ta ƴan uwantaka, yana tausayawa Ashfat saboda jarabawar da Allah ya aiko mata, har sai da akayi sallar isha’i kafin Al’ameen ya tafi masallaci, bayan an idar da Sallah tare suka shigo da Faruq da Haidar, Inna Jumma da ta ɗauki mayafinta tana jiran Haidar ne, tana ganinsa ta miƙe tare da cewa.

“Aliyu karka zauna juya mu tafi.”

Taɓe bakinsa Al’ameen yayi tare da cewa.

“To fa wani sabon salo, ina zakuje da wannan daren kin ɗebo hijabi kamar wata matar Liman.”

Harararsa Inna Jumma tayi tare da cewa.

“Inda ka aikemu nan zamuje, Aliyu shige mu tafi ka rabu da wannan uban ƴan gulmar.”
Dariya Haidar yasa yace.

“Au Al’ameen ɗin shine kuma yau ya dawo ɗan gulmar, kaji fa Al’ameen abinda tace.”
“Rabu da ita Haidar zan rama ne bashi taci.”

Inna Jumma dariya tayi tare da shigewa gaba tana cewa.

“Idan baka kamani ba ai ni na kamawa ɗan rainin wayo”

Haidar bayanta yabi yana dariya, Faruq da Al’ameen daining suka shige.

Inna Jumma da Haidar babu inda suka nufa sai unguwar Durmi, kasancewar Haidar yasan gidan, a ƙofar gidan sukayi parking tare da fitowa Haidar nuni ya yiwa Inna Jumma da gidan, da kallo Inna Jumma tabi gidan dashi sai kuma ta maida kallonta ga Haidar tare da cewa.

“Aliyu yanzu a wannan gidan mutum yake rayuwa?”

“Ƙwarai kuwa Inna Jumma, ni kaina randa na fara zuwa abun ya bani mamaki, haka su suke tasu rayuwar a ciki.”

Numfashi Inna Jumma ta saki cike da tausayi tace.

“Bara na shiga ka jirani.”

Da to Haidar ya amsa Inna Jumma ta shiga da Sallama Umma dake zaune tana wurdi ne ta amsa Ablah kuwa tana zaune gefe tana tilawar alƙur’ani, rufe ƙur’anin tayi tana murmushi tace.

“Inna Jumma sannu da zuwa, Umma Inna Jumma ce.”

Murmushi Umma tayi ta nunawa Inna Jumma wajen zama.

“Bismillah ga waje ki zauna, sannu da hanya kece da dare haka.”

Murmushi Inna Jumma tayi tana zama kan taburmar tace.

“Yauwa sannu, Ni ce nan, naji kince kina wuni gidan aikinki ne, shiyasa nace gara nazo da daddare zanfi samunki.”

“Ayya aikuwa kam, ina wuni.”

“Lafiya lau, ya hidima.”

Da alhamdulillah! Umma ta amsa tana murmushi, Inna Jumma gyara zamanta tayi tare da cewa.

“To alhamdulillah muta waya sai yau Allah ya ƙaddara za’a haɗu, to fa ina ƙara bada haƙuri akan abinda Aminu ya yiwa Shalelena.”

Murmushi Umma tayi tace.

“Lah ba komai Inna Wannan ya wuce ai.”

“To baya ga haka kuma ina neman alfarma ne wajenki Aisha Allah yasa zan samu.”

Murmushi Umma tayi tace.

“Alfarma Kuma Inna, to ina jinki Allah yasa wanda zan iya ne.”

“Wanda zaki iya ne A’isha, dama nace idan babu damuwa mai zai hana ke ki huta ki daina zuwa wajen aikin naki, idan yaso sai ki bani Ablah ta dinga min aiki, zan dinga biyanta dubu talatin duk wata, amma fa zata koma zama a wajena.”

Shuru Umma tayi jin maganar tazo mata a bazata domin kuwa bata tunanin zata iya bayar da ƴarta ta tafi aiki wani waje, bazata iya ba gara mata tana zaune kusa da ita uwa uba ma ita so take Ablah ta koma makaranta duban Inna Jumma tayi tare da cewa.

“To a gaskiya dai Inna sai dai na baki hkr domin kuwa Ablah karatu zatayi, bani da burin tayi aikatau, sannan idan ta tafi nima na tafi nawa gidan aikin waye zai kula da Abdu, kiyi haƙuri Inna bisa neman alfarma da kikayi na kasa miki.”

Murmushi Inna Jumma tayi tare da cewa.

“A’a A’isha, ba dalilin karatu ko kula da Abdu bane yasa zaki hanani Ablah, cewa ZAKIYI kina tsoron bani ita ta zauna a wajena Saboda baki san ya halinmu yake ba, amma ai ina ganin dubu talatin ta isheku buƙatar ku awata ba dole sai ke kinje aikin ba, zaki iya zama a gida ki nemi wata ƙaramar sana’a ki haɗa, sannan ɗawainiyar Ablah na makaranta ai nine nace na ɗauka.”

“Inna Waye zaice bai yarda da tarbiyyar ku ba, babu wanda bai san familyn Ambassador Ahmad Giwa ba, kowa ya sanku da tausayi da karanci babu wanda yake kuka daku sai ma albarka da ake saka muku, ni Tabbata haɗuwa ko zama tare daku wata nasara ce a rayuwa, wallahi dalilina kenan saboda karatun Ablah yasa bana son tayi nisa dani.”

“Idan kuwa hakane dan Allah kimin alfarma ki bani Ablah, na miki alƙawarin zatayi karatu sosai tamkar tana gabanki, zan riƙeta tamkar jikokina, bazan bari ta samu wata matsala ba, ki taimaka.”

Shuru Umma tayi cike da jin nauyin Inna domin kuwa tana ganin girmanta ko ba komai ta haifeta, kuma taimakon ta take son tayi, bai kamata ta watsa mata ƙasa a idanunta ba, cikin sanyin murya badan Umma taso ba tace.

“Shikenan Inna ba damuwa, ki ɗauki Ablah na danƙata Amana a hanunki, dan Allah ki kula min da ita, idan tayi ba dai-dai ba ki nuna mata fushinki, na gode da taimakon da kika min.”

Ablah dake gefe ne tana jinsu suna tattaunawa jin Umma ta amince yasa zuciyarta tsinkewa domin kuwa ita harga Allah bata son zuwa gidan tafi gane tayi rayuwarta yanda ta saba a jikin mahaifiyarta, rayuwar gidan wasu sam baya burgeta tafi gane rayuwar gidan su, Inna Jumma kuwa murmushi ta saki cike da jin daɗi ta yiwa Umma godiya tare da cewa.

“Tafiya da ita nasan yanzu bazai yiwu ba, Saboda zai iya yiwuwa akwai abubuwan ta da zata haɗa a kimtse, insha Allah gobe da azhar zan turo Umaru yazo ya ɗauketa.”

Tayi Maganar cike da jin daɗi ta ɗan juma suna hira da Umma har tara saura sannan ta ajiyewa Umma dubu hamsin tare da mata godiya ta fita, Ablah har bakin mota ta rakata, ganin Faruq tsaye ne Ablah ta gaishe sa, cike da fara’a kuwa ya amsa, har cikin ransa yake yabawa da tarbiyyar Yarinyar, shiga sukayi yaja motar da kallo Ablah ta bisu har suka ɓace mata, runtse idanunta tayi tana tuno da wulaƙancin da Al’ameen ya mata, mutumin daya tsaneta wai kuma ace zata koma rayuwa gidan su, anya kuwa zan yadda na koma gidan su, da zama domin kuwa wannan Uban ƴan baƙin halin zai iya kasheni ma wata rana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita? 12Aminaina Ko Ita? 14 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita? 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×