Skip to content
Part 16 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Kanta ta sunkuyar ƙasa, wata zuciyar na cewa ta sanar dashi wata zuciyar kuma na hanata idanunta ta runtse zuciyarta na mata zafi, cikin sanyin jiki ta ɗago ta zuba masa idanu still dai hawayen ne ya fara gudu saman fuskarta, cikin sanyin murya mai ban tausayi Rufaida ta buɗe baki zatayi Magana, Al’ameen ya yi Sallama, juyawa Haidar yayi yana amsa sallamar, Rufaida sosai taji haushin katse mata hanzari da Al’ameen yayi, zama yayi gefe dasu yana kallon Rufaida bakinsa ya taɓe tare da cewa.

“Ita kuma wannan meya sameta, naga tana cuna baki kamar shantu?”

Ya jefawa Haidar tambaya, Rufaida takaicin baƙar Magana da Al’ameen ya faɗa mata ne yasa ta kuma jin zafi cikin zuciyarta ƙara tura bakinta tayi , sai kuma kamar wacce zuciyarta ke jira a ƙara ɓata mata rai ta saki kuka mai cin rai, zaro idanunsa Al’ameen yayi yana kallon ta, sosai ya fuskanceta cikin tsawa yace.

“Kee! Dakata haka bana son iskancin banza, da rainin wayo kukan Uban me kike, zaginki akayi ko dukanki akayi yau naga mahaukaciya, dallah tashi kibar nan, karki sa kaina yayi ciwo.”

Rufaida sautin kukan ta ƙara cike da jin haushin Al’ameen, da yayi mungun takurawa rayuwarsu, mutum kullum yana nan Kamar kububuwan maciji kowa tsoronsa yake ji, jin sauƙar sautin muryar sa a kunnenta ne ya sanyata miƙewa a firgice.

“I say get out! Ko bakiji bane sai na miƙe na ɓallaki shasha.”

Cikin sauri Rufaida ta bar wajen, tana cigaba da kukanta, Haidar dubansa yayi tare da cewa.

“Al’ameen wai meye hakane kam, ina ruwanka da ita kasan meye damuwarta baka rarrasheta ba, shine zaka dinga mata wannan ihun kana zaginta babu laifin tsaye bare kuma na zaune, Yarinyar nan tana cikin matsala na ijiye ta domin naji damuwarta, kazo ka korata tare da ƙara mata damuwa akan wanda take dashi, wannan ba dai-dai bane wallahi, ya kamata ka dinga saussautawa yaran nan.”

“To ubana tashi ka dakeni sai nafi jin maganar taka, kaga ni fa ba wannan shashancin bane ya kawo ni, jiya naje gaishe da Daddy, kasan kuwa Maganar da Daddy yamin?”

Girgiza kansa Haidar yayi tare da cewa.

“A’a meya ce maka, Allah dai yasa ba laifi mukayi ba?”

“Ai ni da wannan maganar da ya min gara ma ace laifin mukayi, wai Daddy cewa yake muje mu nemo Mata, Aure yake son muyi nan da wasu kwanaki kaɗan mtsss! Kuma da alamu Daddy serious yake wannan maganar.”

Dariya Haidar yasa harda riƙe ciki yana nuna Al’ameen da yatsa, Al’ameen buɗe baki yayi yana masa kallon mamaki, cike da haushin dariyar da Haidar ke masa yace.

“Kai dariya ma kake min, Oh ga mahaukaci ko yayi kyau.”

Sassauta dariyar Haidar yayi tare da cewa.

“To ai dole nayi dariya Al’ameen Saboda abun dariya ne, Al’ameen kaine fa a ruwa domin kuwa ni na samu matar Auren ko yau tace na fito a shirye nake, shi kuma Faruq baida matsala domin kuwa yana da niyyar Neman matar Aure, kaine dai baka da bukatar Mace, kaga kuwa kaine a ruwa kusa da kada ma.”

“Mtsss! Kaga ni fa yanzu dan Allah ba wannan maganar bace ta kawo, ni zuwa nayi na roƙeka ka rufa min asiri idan Daddy ya kira ka kan wannan maganar dan Allah karka ce masa ka samu matar Aure, wallahi muddun kace masa ka samu, to fa na shiga Uku domin kuwa ko zan mutu Daddy sai ya sani nemo mata dole, idan naƙi kuwa yamin Auren dole, ka taimakeni ɗan uwana dan Allah.”

Dariya Haidar ya kuma sheƙewa dashi, cikin dariyar yace.

“Babu wannan alfarmar bazan iya maka ba, babu karya domin kuwa ni Aure nake so na gaji da zaman gauranci, kawai malam nemo Mata idan kuma baka da idon kallon mata, sai mu mu nemo maka.”

Yayi Maganar cikin dariya da tsokanar Al’ameen, haɗa fuska Al’ameen yayi domin kuwa yaga Haidar kamar ya maida Maganar wasa,.

“Haidar Please stop funny! Magana fa nake maka na gaskiya amma naga kana maida abin na wasa, dan Allah na roƙi alfarma gareka.”

Numfashi Haidar ya saki tare da ɗaga kafaɗarsa yace.

“Okay amma dai, gaskiya ya kamata ka maida hankali domin kuwa Aure shine cikar mutum, sai kana nuna kai baka ma ƙaunar Auren kwatakwata, gask…”

“Dan Allah dakata da wannan maganar ni kaga tafiyata ma abinda ya kawoni kenan, idan momma ta fito kace ina miƙa gaisuwa.”

Yayi Maganar yana miƙewa tare da ficewa daga part ɗin, da kallo Haidar ya bisa tare da girgiza kansa.

Kwana biyu da dawowar Ablah gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA ta gama fuskantar halin kowa a cikin gidan, sosai jininsu yazo ɗaya da Maimu, sosai take son Ablah tsakani da Allah, inda yanzu Ablah tabar bedroom ɗin Inna Jumma ta koma nata dake gefen room ɗin Inna Jumma, sai dai kuma cikin ikon Allah a cikin wannan kwana biyun Allah bai haɗa fuskarta dana Al’ameen ba, saɓani suke, sosai taji daɗin hakan domin kuwa bata ƙaunar haɗuwa dashi.

Yau tunda sassafe Ablah da Ladiyo suka gama haɗa breakfast saboda akwai yau Monday ihsan zata school, ganin yayi Safiya sosai yasa Ablah bata ci nata abincin ba, ta koma bedroom ɗin ta ta kwanta, Ladiyo ce ta yiwa ihsan komai ta wuce school, shima yau Al’ameen da wuri ya tashi ya yi shirin Office saboda yana da general meeting, koda ya sauƙo ƙasa babu kowa bedroom ɗin Ummi ya shiga, ya samu ta fito daga wanka murmushi ya saki tare da zama gefen bed ɗinta yana murmushi yace.

“Ummi Barka da tashi kin tashi lafiya.”

Zama Ummi tayi tana murmushi cike da ƙaunar ɗan nata tace.

“Lafiya Alhamdulillah! Har ka fito kenan, kayi sammako yau.?”

“Ehh Ummi muna da general meeting ne da Companyn Ahmad St rice, sun buƙaci na saka hanun jari a Companyn nasu, na duba na gani idan har na saka hanun jarin, za’a samu ribar da takai 5.2b so shine yanzu zamuje da Haidar mu tattauna sannan mu bada hanun jarin.”

“Masha Allah, indai har za’a samu wannan ribar to ai yana da kyau ku saka hanun jarin, sannan naji kana cewa sun buƙaci ka saka hanun jari, it means kaine kenan zaka saka ba tare dasu Haidar ba?”

“Ehh Ummi nine zan saka Banda su ciki, saboda munyi Magana da Haidar akan cewa ko zasu saka suma, to sai yake nuna min cewa, bashi da kuɗaɗen da suke buƙata, ribar da yake samu cikin Companyn mu bai kai ya saka hanun jari ba, dalilin da yasa zansa ni kaɗai.”

Numfashi Ummi ta saki tare da kama hanun ɗannata tace.

“Baza’ayi haka ba Al’ameen, tunda basu dashi mai zai hana kai ka saka musu tunda kai kana dashi, ribar da za’a dinga samu sai suke rabawa shida Faruq amma a matsayin Uwar kuɗin naka ne suna ajiye, kaga kenan kamar ka basu aro ne, idan kayi haka ka taimakawa ƴan uwanka kuma zasuji daɗi sosai zamunci kuma zai ƙara danƙo ka duba maganata da kyau, karka yadda kai ka ta samu su suna baya indai da halin da zaka tallafawa rayuwarsu tafi wadda suke yanzu to kayi domin kuwa ƴan uwanka ne, komai ka musu baka faɗi ba.”

“Hakane Ummi, gaskiya banyi wannan tunanin ba, baizo min ba, kuma naji dadi da kika kawo min wannan shawarar insha Allah idan munje zan saka musu.”

“Da ka kyauta kuwa, jiya munyi Magana da Daddyn ku akan Ashfat yace insha Allah gobe zasu tafi Egypt ɗin zasubi jirgin 11am yace zasuje tare da Auntyn Faruq ta kula da ita idan an mata aikin da tare da amarya zasu sai Abi yace suje da Auntyn.”

“Eh Daddy ya sanar dani, hakan yayi sosai Allah yasa ayi cikin Nasara bara naje nayi breakfast sai na shige Daddy bai tashi ba, zan shiga room Aunty Amarya kafin na shige.”

“Amarya ai tana bedroom ɗin Daddyn ku, kaje kayi breakfast ɗinka kawai ka shige Allah ya bada Sa’a.”

Da ameen ya amsa yana fita, daining yaje tare da jawo kujera ya zauna, Tuwon doya ya ɗiba tare da tea, loma daya ya kai bakinsa daƙyar ya haɗiye saboda azabar yaji da miyar tayi, shi kuwa a rayuwarsa ya tsani yaji a abinci, ai kuwa cikin ɓacin rai ya ture abincin gefe, yana huci, Tabbas yasan babu mai wannan muguntar idan ba Ablah ba, domin kuwa Ladiyo ta juma cikin gidan nan bata taɓa wannan muguntar ba, tea ya haɗa mai kauri yasha, yana tsaka da shan tea ɗin ya hango Maimu tana sauƙowa, kiranta yayi tare da cewa taje ta kira masa Ablah.

Babu jumawa kuwa sai ga Ablah yayin da Maimu tayi shigewarta bedroom ɗin Inna Jumma, Ablah daining ɗin ta nufa cikin sanyin jiki ta tsaya a kansa tace.

“Maimu tace kana kirana.”

“Waye yayi wannan girkin kece ko Soloɓiyo?”

Ya jefa mata tambaya, shuru Ablah tayi cike da mamakin meyasa ya mata wannan tambayar kuma ko dai wani laifin aka masa duk da ita tayi duka girkin ba, ta dai dama kunu ta kuma daka doya sannan ta dafa lipton, to amma koma meye gara ta amsa cikin sanyin muryarta tace.

“Ehh ni ce.”

Murmushin mugunta ya saki tare da juyowa ya kalleta, ɗaya daga cikin kujerun dake daining ɗin ya mata nuni dashi tare da cewa.

“Zauna anan.”

Zaro idanunta Ablah tayi tare da furta.

“Na zauna kuma, ai nan ba wajen zamana bane, kawai koma meye ne ka faɗa min basai na zauna ba.”

Tayi Maganar cike da tsoro Al’ameen tsawa ya daka mata wanda sai da hantar cikinta ya haɗa.

“Umarni nake baki! Nace kiiii zaunaaa!! Ko bazaki zauna ba sai na tashi na jideki kin faɗa banza wawiya, aini nayi mamaki jiya ace kece kikayi wannan abincin.”

Cikin rawar jiki gami da tsoro Ablah ta zauna jikinta na rawa, kular miyar Al’ameen ya turo mata gabanta tare da cewa.

“Ki ɗauki wannan miyar ki kafa kanki ki shanyeta tass, sannan ki suɗe kular.”

Yayi Maganar yana zaro mata idanunsa fuskar sa haɗe tamau tamkar hadari, da kallo Ablah tabi kular sai kuma ta ɗago ta kalli Al’ameen idanunta sunyi raurau tace.

“Kayi hkr bazan iya shan miya ba dan Allah koma me na maka kayi hkr bazan sake ba.”

“Hmmm! Ashe kin iya bada haƙuri to bana yafewa mungu dan haka dole sai kin shanye miyar nan, ki zaɓi ɗaya a cikin biyu domin kuwa wallahi dole ne sai ɗaya ta Faru kinji na rantse, ko kishanye miyar nan kona ɗauka na watsa miki a fuska sannan na gwale waɗannan idanunnaki mai kama dana mujiya na tsiyaya miyar ciki, ki makance kowa ma ya huta, zaɓi wanda ya fi miki sauƙi kafin na ƙirga Uku.”

Yayi Maganar yana fara ƙirge.

“1…2…”

Sanin halin sa sarai zai iya abinda ya furta yasa Ablah saurin ɗaga miyar ta kai bakinta ta kurɓa wani irin azababben yaji ne da raɗaɗi taji ya gwauraye mata baki cike da azaba ta runtse idanunta ta gagara maida miyar bakinta sai famar shishita take tare da ijiye kular murmushin mugunta Al’ameen ya saki tare haɗe fuska yace.

“Ki ɗauka ki shanye nace wallahi kona watsa miki a idanunki.”

Cikowa idanunta yayi da hawaye ta ƙara ɗauka ta kafa kai hawaye na zuba a idanunta idanunta sunyi jajur tamkar gauta, azaba iya azaba ta jisa bakinta duk ya mele, ganin azabar da tasha yasa Al’ameen ƙwace kular yana sakin dariya tare da miƙewa tsaye ya buga teburin yana sakin murmushin mugunta yace.

“Wannan shine hukuncin ki, gobe ma ki kuma mana abinci da yaji, hukuncinki sai yafi na yau tsauri wawiya.”

Yayi Maganar yana kwasar wayoyinsa da key ɗinsa ya fice, da kuka Ablah ta fashe bakinta duk ya mele azaba take ji har cikin kwaƙwalwarta, miƙewa tayi ta shige cikin bedroom ɗinta prich ta buɗe ta ɗauko ruwa mai sanyi ta kafa a bakinta, sosai tasha ruwan, kafin ta ijiye robar ruwan ta zauna a bakin bed ta saki kuka mai cin rai, Tabbas rashin Uwa a kusa babbar masifa ce, rayuwa ƙasan wani akwai ƙasƙanci da wulaƙanci, meyasa Umma ta yadda aka turo ta gidan nan, gashi tun ba’a je ko ina ba, harta fara fuskantar uƙuba, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wannan wani irin mutumi ne da bashi da imani Tabbas zai iya kashe rai domin kuwa babu Allah a zuciyarsa.

Duk cikin zuciyarta take wannan maganar yayin da take kuka tamkar ranta zai fita tsanar Al’ameen ne ya dasu a cikin zuciyarta, ta juma tana kuka yayin da bakinta bai daina mata raɗaɗi ba, wunin ranar Ablah bata fita ba, yayin yajin da tasha ya sata sakewar ciki ta wuni tana zaga tollet.

Al’ameen koda sukaje meeting ɗin shida Haidar sosai ya yiwa Haidar bazata na saka musu hanun jari shida Faruq ba ƙaramin jin daɗi Haidar yayi ba, koda suka tashi daga meeting ɗin.

Sun fito parking space inda kowa zai hau motar sa, Haidar ya tsaya tare da cewa Al’ameen.

“Na rasa da wani baki zan iya maka godiya, a ko yaushe burinka ka haska rayuwarmu, samun Amini kuma ɗan Uwa irinka abune da yake matuƙar wahala a wannan zamanin, duk da haka dole ne na gode maka, Allah ya saka da alkairi.”

“Nasha faɗa muku cewa bana buƙatar godiya daga gareku, duk abinda na muku a rayuwata ban faɗi ba, bani da wanda ya fiki kaf wannan duniyar idan aka cire Daddy da Ummi, bani da wani gata sai ku, ni dai fatana a rayuwa mu kasance cikin farin ciki har ƙarshen rayuwar mu, bana ƙaunar abinda zai raba kanmu.”

“Al’ameen ba’a halicci abinda zai shiga tsakanin mu ba, koda kuwa shaiɗanne haka zai ganmu ya ƙyale Rayuwar zata kasance cikin farin ciki kanmu bazai taɓa rabuwa ba.”

Yayi Maganar yana duban agogon hanunsa.

“Kaga bara naje Nafeesa na jira na a Amina kitchen.”

Murmushi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Oh da alamu dai wannan Nafeesan ta ɗauke maka zuciya dole nima na haƙura naso zaɓinka, zan iya ganin pictures ɗin ta.”

“Me zai hana kuwa, dama nasan ai dole zakaso abinda nake so, bara kaga pictures ɗinta KYAKKYAWA ce mai hankali da kuma nutsuwa.”

“Hummmm! To yabi zaɓinka, ai sai ka bari idan na gani na faɗa, wataƙil mummuna ce, amma dai bari na gani na yanke hukunci.”

Murmushi Haidar yayi yana buɗe pictures ɗin Nafeesa ya mikawa Al’ameen wayar tare da cewa.

“Gashi yanke hukunci.”

Karɓa Al’ameen yayi yana murmushi tare da zubawa pictures ɗin Nafeesa idanu, na wajen 30second tare da miƙawa Haidar wayar yana taɓe baki tare da cewa.

“Eh to ba laifi tana da kyau, amma dai bata kai ɗan uwana kyau ba.”

Dariya Haidar yayi tare da dukan kafaɗar Al’ameen yace.

“Wannan son kai ne ka nuna, bara naje time na ƙurewa.”

“Okay kace ina gaisheta kafin na kawo mata ziyara saƙo na baka.”

Yayi Maganar yana buɗe motarsa ya shige, shima Haidar tasa ya shiga yana murmushi duk sukaja, Haidar darect Amina kitchen ya nufa tana zaune ta saka lemo a gaba tana kurɓa jikinta sanye da hijabi, hangota ya saka Haidar sakin murmushi, jawo kujerar ya fuskance ta.

“Assalamu alaikum farin ciki na, da fatan duniyarki ya sameki lafiya.”

Ɗago idanunta tayi tana sakin murmushi tace.

“Ameen wa’alaiku mussalam Duniyata, kayi matuƙar kyau, kayiwa kayan kyau.”

“Wow wato nine ma na yiwa kayan kyau.”

“Eh mana Duniyata, ai yanda kyawunka ke haskawa dole su haske kayan, Duniyata kasan me kuwa.?”

“Ban sani ba farin ciki na, bani haske.”

“Ina matuƙar ƙaunar ka, ji nake bazan iya numfashi ba babu kai, kai mutum ne na mussaman a rayuwata.”

Murmushi Haidar yayi tare da lumshe idanunsa yace.

“So So So wannan kalmar tana mungun mini daɗin ji, mussaman idan na tuna da cewa itace ta haɗani dake ina matuƙar alfahari da zuciya domin kuwa da’ace ba zuciya da ba’a halicci SO ba, ina sonki fiye da komai a rayuwata zan iya yaƙi da koma waye akan soyayyarki.”

Dariya Nafeesa tayi har fararen haƙwaranta suka bayyana.

“Duniyata da alamu yau kana cikin farin ciki meya faru nima na tayaka wannan farin cikin.?”

“Kina fuskantar abinda ke cikin zuciyata, Tabbas ina cikin farin ciki Abu biyu suka sani farin ciki yau, na farko wannan kyakkyawar fuskartaki, na biyu kuma yau ɗin nan ɗan uwana kuma AMININA AL’AMEEN AHMAD GIWA ya sani farin ciki ta hanyar saka mana hanun jari a Ahmad sd rice Wanda zamu samu riba a shekara sama da 5.2b amma mu biyu zamu raba ribar nida Faruq, shima kuma ya saka nasa na kansa wanda shi kaɗai zai mallaki nasa ribar, yau Al’ameen ya sani cikin farin ciki sosai aminine na ƙwarai mai son ganin cigaban mu.”

“AL’AMEEN AHMAD GIWA kuma ban fahimta ba, dama ba cikin ku ɗaya dashi bane, taya zai saka maka hanun jari gani nayi tare kuke business kuma dukiyar nan ta mahaifinku ne?”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Oh wai ke ɗauka kike ciki ɗaya muke dashi, a’a shine ɗan AMBASSADOR AHMAD GIWA na cikin sa, mahaifina ƙanin Ahmad Giwa ne, Tabbas shine ya saka mana hanun jari nida Faruq Saboda ya fimu arziki, ko Companyn da muke aiki yanzu nasa ne wanda mahaifinsa ya mallaka masa, sai dai shi yana ɓoye hakan yana nuna cewa Companyn duka namu ne, sam baya taɓa nuna cewa shi wanine dai-dai yake rayuwarsa data kowa, yama ce na gaisheki, duk da baki san fuskarsa ba, shima sai yau yasan taki fuskar.”

Tunda ya fara Maganar Nafeesa ta saki baki tana kallon sa, ashe dama zaɓen tumun dare tayi, ta gama zaton Haidar shine ɗan AMBASSADOR AHMAD GIWA, ashe abun ba haka yake ba wani ne can ɗan Ahmad Giwa, shima wannan albarkaci yake ciki, to shi Al’ameen ɗin ya yake, numfashi ta saki tare da sakin murmushin yaƙe cikin kissa da ɓoye mamakinta tace.

“Wow gwanin burgewa, congratulations l, na tayaku Murna, amma Duniyata zanso ganin wannan Al’ameen ɗin.”

Wayarsa Haidar ya zaro tare da miƙo mata hoton sa, karɓa tayi ta zubawa hoton idanu, sosai take kallon pictures ɗin ita kaɗai tasan me take ayyanawa a cikin zuciyarta, miƙa masa wayar tayi tare da cewa.

“Ka fisa kyau Duniyata, ka kira min shi a wayarka mu gaisa mana.”

Murmushi Haidar yayi yace.

“Shima haka yace na fiki kyau, shikenan kin rama, bara na kira miki shi.”

Yayi Maganar yana dannawa Al’ameen kira, yana danna kiran Nafeesa tayi saurin karɓar wayar ta katse kiran tana cewa.

“sorry Duniyata na manta ashe Amnat ta kirani wai na tura mata kati, zatayi Amfani dashi da gaggawa na manta sai yanzu na tuna, Please dan Allah taimakeni ka karɓa min katin a wancan shagon kafin mu gaisa, karmu tsaya Magana na kuma mancewa.”

“Hakane farin ciki na, babu damuwa bara na karɓo miki katin nazo.

Yayi Maganar yana tashi ya fita, numfashi mai nauyi Nafeesa ta saki tana dafe kanta cikin gaggawa ta ɗauki numbern Al’ameen a wayar Haidar tare da tura pictures dinsa.

<< Aminaina Ko Ita? 15Aminaina Ko Ita? 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×