Skip to content
Part 19 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Fyaɗe! Amma kuma sai nake ga kamar hukuncin baiyi mata tsauri ba kuwa, ai gara mutuwa da fyaɗe a wajen mace, amma maganin Mutum mai shiga abinda babu ruwansa kenan, hakanma yayi, amma dai nasan dole zataji tsoro ta amince kuyi aiki tare Saboda tasan zaki iya aikata abinda kika furta.”

“Koma bata amince ba Hajiya Mansura bani da matsala da ita domin kuwa babu abinda zata iya, Asali ma ni ce wacce zan iya kawo ƙarshenta.”

“Hakane ni nasan zaki iya fiye da haka ma amma dai mubi komai a sannu, yanzu dai ki bata nan da 1 week idan bata amsa tayin ba, kiyi duk abinda kikaga ya dace, bara na ajiye waya anjuma zamuyi Magana.”

Da to Aunty Amarya ta amsa tana katse kiran, fuskarta babu wani alamun tsoro.

Ita kuwa Ablah tunda Aunty Amarya ta fita hankalinta ya gagara kwanciya domin kuwa ta fara tsoron lamarin Aunty Amarya duk inda take tunani matar ta wuce nan sai dai abinda ya kulle mata kai ta rasa wani daliline yasa take neman rayuwarsu, gashi dai sun gama yarda da ita, amma cutar su take ta ƙarƙashin ƙasa, ta yadda ganota zaiyi musu wahala, koda an sanar dasu bazasu yadda ba, numfashi ta saki ganin bata da amsar da zata bawa kanta, lallai tana buƙatar taje ta samu Umma ta sanar da ita abinda ke faruwa ko zata taimaka mata, miƙewa tayi tsaye ta shige bedroom ɗin Inna da sallama tana kwance ta sameta gefenta Ablah ta zauna murmushi Inna Jumma tayi tare da cewa.

“Shalele na, kin shigo kenan.”

Sunkuyar da kanta Ablah tayi jikinta da mungun sanyi tace.

“Eh Inna na shigo, Inna kuyi haƙuri bisa abinda na aikata ɗazu naga duk ranku baiyi daɗi ba, ba da nufi nayi hakan ba gani nayi kamar kyankyaso cikin abincin saboda karya ci ya cutar dashi yasa naje na zubar da abincin kuyi haƙuri dan Allah.”

Murmushi Inna Jumma tayi tare da tashi ta zauna.

“Na sani Ablah baza kiyi da nufi ba, nasan halinki sosai kuma ai wannan maganar ma ta wuce karki kuma tayar da ita ki saki ranki kinji.”

Kanta Ablah ta ɗaga alamun to ta kuma cewa 

“Sannan Inna dama nace ina son na sanar dake ina so zanje na duba Umma na anjuma da yamma tunda bani zanyi girkin ba Ladiyo ce, kuma akwai kayana da nake son na ɗauko idan naje.”

Murmushi Inna Jumma tayi tace.

“To shikenan ba damuwa ki shirya sai drever ya kaiki, idan kin tashi tafiya kizo zan baki saƙo.”

Da to Ablah ta amsa tana tashi ta tafi shiryawa, bata wani juma ba ta fito cikin hijabinta ta dawo wajen Inna Jumma, kaya Inna Jumma ta bata atamfa Uku da less biyu sai kuɗi tace Umma tayi ɗinki dubu goma sosai Ablah taji daɗin abinda Inna Jumma ta yiwa Umman ta, fita tayi drever ya Kaita.

Shi kuwa Al’ameen tunda ya fita yayi garden cike da ɓacin rai Ɗaya daga cikin kujerun robar dake garden ɗin ya zauna tare dayin shuru yana nazarin Ablah, duk da yasan halin Yarinyar bata abu sai da hujja sai dai a yau baiga hujjar ba, wannan ai kamar raini ne yana tare da iyayensa tazo ta masa wannan rainin hankali, numfashi ya saki tare da runtse idanunsa yana jin zafin marin daya mata, bai so ya saka hanu jikinta, bai san sanda ya mareta ba.

“Tabbas ban kyauta ba.”

Ya furta a fili yana danasanin marin daya mata, yana nan zaune cikin tunani shima Haidar ya kwaso tasa damuwar ya shigo garden ɗin ko kaɗan bai zaton Al’ameen yana wajen ba, shi dai kawai yazo ne ko zaiji sauƙin damuwar dake ransa na Rufaida domin kuwa ta ruɗasa ta sashi cikin tashin hankali, sanda yazo daf da Al’ameen sannan ya gansa zama yayi ransa a cunkushe tare da huro iska mai zafi daga bakinsa Al’ameen duban yanayin Haidar yayi tare da cewa.

“Haidar anya kuwa kana lafiya?”

Ɗago kansa yayi ya kalli Al’ameen tare da cewa.

“Meka fuskanta kamin wannan tambayar?”

“Yanayinka ne naga ya sauya ba kamar yadda na saba ganinka ba kullum da alamu dai kana cikin matsala meke faruwa?”

Numfashi Haidar ya sauƙe tare da fuskar Al’ameen yace.

“Tabbas ina cikin matsala Al’ameen, mtss! Matsala ta banbancin zuciya, na rasa gane meyasa zuciya take muradin yin kwaɗo, takan zuwa inda ba’a gayyaceta ba, bata fuskantar mai sonta sai tace ita lallai muddun taso wata zuciyar dabam da bata sonta, to fa wai dole ita wannan zuciyar ta sota, na rasa meyasa take haka *DA ACE BA ZUCIYA* da wata damuwar baza’a shiga ba na rasa nutsuwa ta tun ɗazu.”

“Duk da kamin zancen a dunkule sai dai na fahimci matsalar Soyayyace amma *DA BABU ZUCIYA* da rayuwar ma babu ita Saboda zuciya itace numfashi, shin abokina kun sami matsala da Nafeesa ne?”

“Nafeesa ba matsala bace a rayuwata maganin damuwata ce ita, wata ce can daban matsalata, zuciyarta ta kamu da tsananin soyayyata Soyayya ta gaskiya, nine shaida akan hakan, kuma tana cikin mawuyacin hali akaina, mtsss! Sai dai ni sam babu ita a zuciyata bana mata Soyayya ta Aure, wannan abun shi yake damuna na rasa ya zanyi ina tausayawa Yarinyar matuƙa, saboda zata iya shiga wani hali muddun ta rasani ni kuma bazan iya bata zuciyata ba, na riga da na daɗe da KYAUTAR ZUCIYATA

Nafeesa itace mallakin zuciyata.”

Murmushi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Na fahimta to amma Haidar, mai zai hana ka faɗa mata gaskiya cewa kana da wacce kake so tayi hkr idan so cuta ce, haƙuri ma ai magani ne, ko da ka sota a dole bazata samu cikakkiyar farin ciki ba, Saboda ba ita bace a ranka, zuciyarku bata haɗu ba ka fahimtar da ita.”

“Bazata fahimta ba Saboda tayi nisa zuciyarta a makance take soyayyata itace kawai muradinta.”

“Lallai kuwa tana tare da wahala Allah ya yaye mata, kaga Abokina dan Allah karka ɗagawa kanka hankali akan wannan maganar, tunda har ta kasa fahimtar ka, ka rabu da ita kawai ita da wahalarta, ba dai kai kam ka samu mahaɗin zuciyarka ba, yauwa ni yaushe ne zaka kaini naga wannan nafisar taka?”

“Itama tace tana son ganinka insha Allah gobe sai muje harda Faruq ma, shima yana son zuwa.”

“Hakan ma yayi Allah ya kaimu.”

Da ameen Haidar ya amsa tare da cewa.

“Ya akayi yau na ganka Anan zaune kai ɗaya?”

Murmushi Al’ameen yayi cikin ɓoyewa Haidar damuwar sa domin kuwa shi Mutum ne mai haɗiye abubuwa da yawa a zuciyarsa, duk damuwar da kaga Al’ameen ya sanar da su Haidar to Tabbas ba ƙaramar damuwa bace murmushi ya saki tare da cewa.

“Yanayin wajen kawai yau nake so.”

Yayi Maganar a taƙaice,. Kafin suka ci-gaba da zancen duniya.

Ita kuwa Maimu ganin miss Call ɗin Rufaida ya sata nufar part ɗin su Haidar momma ta samu zaune tana kallon BBC News, gefenta Maimu ta zauna.

“Sannu da hutawa Momma.”

“Yauwa Maimu kece tafe ya Ummin naku?”

“Tana lafiya, ke kaɗai ce momma, Madina fa?”

“Kin ganni ni kaɗai nake zaune sai Su’udah ita kuma ta kama aikinta tayi kitchen, Madina taje gidan Hajiya Suwaiba na aiketa, Rufaida ce kawai tana sama.”

Ɗan murmushi Maimu tayi tare da cewa.

“To bara na haura Wajen Rufaida kafin Madina ta dawo.”

“Okay sai kin fito”

Da to Maimu ta amsa tana haurawa sama bedroom ɗin su Rufaida ta nufa tare da tura door ɗin ta shiga shashsheƙar Rufaida ne ya fara dukan kunnenta, da sauri Maimu ta ƙarisa tana furta.

“Subahanallah! Rufaida meya sameki haka?”

Ɗago idanunta tayi da yayi jajur tamkar gaushi ta miƙe da sauri tare da faɗawa jikin Maimu sai kuma ta saki kuka mai ban tausayi, maimu tsinkewa zuciyar ta tayi cikin tashin hankali da tsoro tace.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Rufaida meya sameki ki sanar dani mana, kin sa zuciyata sai tsinkewa take Please tell me what happening?”

“Na shiga Uku Maimu! Soyayyar Ya Haidar zata kasheni! Maimu bazanyi tsawon kwana ba a duniya mutuwa zanyi bazan iya rayuwa babu shi ba, Na shiga Uku.”

Numfashi mai nauyi Maimu ta saki cike da tausayin Rufaida, ita kuma tata ƙaddarar kenan ta son maso wani, tsuka Maimu taja tare da cewa.

“Bazaki mutu ba Maimu Saboda soyayya komai yayi zafi maganinsa Allah, kuma duk zafinsa wata rana zaiyi sanyi, ki dakatar da kukan haka ki sanar dani meya faru.”

Sake Maimu Rufaida tayi ta zauna tana fuskantar ta, cikin shashsheƙar kuka tace.

“Na sanar dashi yau cewa shine wanda nake so, sai dai faɗar tawa bata amfane ni da komai ba sai ma baƙin ciki da ta ƙara min, Ya Haidar yaƙi amincewa da soyayyata, ya sanar dani cewa, bazan samu matsuguni a zuciyarsa ba, rayuwarsa ta Nafeesa ce kawai, Maimu zuciyata tana min nauyi baƙin ciki da damuwa sun isheni, gashi Soyayyar sa ƙaruwa take a zuciyata, na kasa ciresa a zuciyata, Maimu ina ji a raina Soyayyar Ya Haidar itace ajalina.”

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wace irin mummunar Magana kike faɗa haka, Rufaida soyayya bazata kasheki insha Allah Ya Haidar zai soki, kar kiyi gaggawa kibi komai a hankali insha Allah burinki zai cika Rufaida ni kaina ina tausaya miki, duk da bansan zafin Soyayya ba amma na fahimci zafin da kike ji a zuciyarki, wai ni wannan Nafeesan kan ya take ne da Ya zurfafa. A cikin Soyayyar ta, wallahi na tsaneta na tsani a kira koda sunanta ne, shifa da kansa ya miki alƙawarin yaƙi akan soyayyarki to meyasa yanzu zai karya alƙawari bayan komai yana hanunsa bansan Ya Haidar da ƙeta ba?”

“Bazai soni ba Maimu muddun Nafeesa tana numfashi, domin kuwa ita kaɗai ce muradinsa ya faɗamin cewa bazai iya mata kishiya ba, Maimu dama na faɗa miki muddun yasan cewa shine nake so bazai iya cika min alƙawari na ba, ki taimakeni Maimu ki taimakeni Ya Haidar ya soni kar na mutu, wallahi mutuwa zanyi idan ban samu Soyayyar sa ba, shine numfashi na, duk wani bugun zuciyata da soyayyarsa take bugawa, shine ABINCIN ZUCIYATA bazan iya rayuwa babu shi ba, idan na rasa shi bazan taɓa Aure ba har abada.”

“Hmmm! Wannan wani irin Soyayya kike masa haka Rufaida ni tsorona ma kar ki haukace domin kuwa naga kinyi nisa hankalinki yana neman gushewa daga jikinki, kawo kunnenki kiji.”

Rufaida hawayenta ta share tare da miƙa kunnenta Maimu tafi 18minute tana faɗa mata Magana kafin ta cire bakinta daga kunnen Rufaida tana cewa.

“Ki gwada mu gani ko Allah zaisa mu dace.”

“To shikenan zan gwada amma zuciyata tana karye.”

“Karki bari zuciyarki ta karye da wuri ki jajurce kamar yadda ya faɗa miki a baya shida kansa ya baki satar amsar da zaki mallakesa.”

“To zan gwada.”

Maimu ta juma tana rarrashin Rufaida harta samu ta ɗan saki jiki, kafin Madina ma ta dawo suka hau hira tare.

Unguwar Durmi

A ƙofar gidan su drever ya sauƙeta ta ɗebi Kayan da Inna Jumma ta bawa Umma tare da cewa drevern ya dawo ya ɗauketa da magaruba.

Da sallama ta shiga cikin gidan, Abdu ta samu yana wasa a tsakar gidan ganinta ya sashi tashi da gudu ya faɗa jikinta yana mata oyoyo Ablah murmushi tayi tare da cewa.

“Kai ɗaya ne cikin gidan, ina Umman take.

“Umma ta zaga bayi yanzu, Aunty kinzo min da alawa da taliyar yara, kinga tamu ta ƙare tun shekaran jiya, wannan Yaya Al’ameen ɗin yazo ya gaishe da Umma jiya ya kawo mata buhun shinkafa biyu da buhun waƙe harda su mai ya bata kuɗi yace wai kina gaisheta.”

Zaro idanunta Ablah tayi cike da mamaki ta furta.

“Al’ameen kuma yazo gidan nan, to kuma meya kawosa, ikon Allah.”

Kallon Abdu tayi tace.

“Naji ɗauko min taburma a ɗaki na zaune zauna kafin Umman ta fito.”Tabarmar ya ɗauko suka zauna ya dinga mata surutu yana faɗa mata abubuwan da suka faru a gidan bayan bata nan, har Umma ta fito ta samesu dariya Umma tayi tare da cewa.

“Wa nake gani haka kamar Ablata, Oh Abdu sarkin surutu tun ina bayi nake jiyo zancen ka.”

Dariya Ablah tayi tare da cewa.

“Labarin abubuwan da akayi a gidan nan bayana yake sanar min.”

Zama Umma tayi tace.

“Cewa zakiyi Abdu gulma yake miki, to kuwa ka kyauta ya kika bar can fatan dai kina jin daɗin zama dasu ba wata matsalar?”

“Lafiya na barsu Umma sai dai fa matsala akwata Umma itace ma ta kawo ni, ga wannan kayan Inna Jumma tace kawo miki da kuɗin ɗinki.”

Karɓa Umma tayi tare da cewa.

“Masha Allah to Allah ya saka da alkairi, babu abinda zance dasu sai godiya ita da jikanta Aminu yaron akwai kirki sosai yakan zuwa sa’i da lokaci ya gaishe ni har ya kawo min abin alkairi jiya ma sai da ya kawo min kayan abinci, amma Ablah wacce irin matsala kike fuskanta a gidan?”

“Bamma san yana zuwa ba Umma na ga yadda yake da girman kan nan banyi zaton har zaiyi kirki haka ba, kedai kawai jininku ne yazo ɗaya.”

“Ko kuma ke dai baki fuskance saba, yanzu dai ba wannan ba, Ablah menene matsalar?”

Numfashi Ablah ta saki tare da kama hanun Umma idanunta ne suka ciko da hawaye cikin raurau da murya ta ke sanar da Umma abubuwan da ta gani na Aunty Amarya, sai dai ta boyewa Umma kashedi da zaɓin da Aunty Amarya ta mata, Umma salati ta ɗauka cikin mamaki duk da bata san cikin gidan ba, da yadda suke zaune sai dai tasha mamakin halin Aunty Amarya numfashi Umma ta saki tare da cewa.

“Ikon Allah sai kallo, eh Lallai dole hankalinki ya tashi, dama fa maƙiyin mutum haka yake, baya cutar ka sai ya gama shiga jikinka, yanzu kin san abinda zai faru?”

Girgiza kanta Ablah tayi alamun a’a.

“Ki cigaba da bibiyar lamuranta a ɓoye karki sake ta gane cewa kina bibiyar lamuranta, ki saka mata ido sosai duk wata hanyar da zata cutar dasu muddun kinsan hanyar to ki toshe ta, ko da ta gane kina bibiyar ta, ta miki kashedi dan ta baki tsoro karki yadda ki tsorata, kar zuciyarki ta karye ki zamo kariya a garesu Ablah domin kuwa sun rufawa rayuwarki asiri yanzu haka Maganar da nake miki jiya nan zuwan Aminu yace yaje angama registration ɗinki na makaranta shine ya biya komai sannan yace ya ɗauki ɗawainiyar karatunki, tunda kika fara aiki a gidan su, suke ɗawainiya da rayuwar mu, muka daina tunanin yadda zamu samu abinci saboda suna bamu, akai akai, bayan kuɗin aikin da suke ninka miki, bafa dan sun rasa ƴar aiki bane yasa suke mana wannan hidimar a’a saboda kawai ƙauna ce, da kuma tausayawa a wannan zamanin masu kyakkyawar zuciya irin tasu suna wahala, akwai masu kuɗi da dama waɗanda babu ruwan su da talakawa, koda kaje neman taimako wajen su bazasu muku ba, koda kuwa kana cikin damuwar da zata hallaka kane su babu ruwan su kansu kawai suka sani da ƴaƴansu, amma su waɗannan sun fita daban, sun mana ɗawainiya da kuɗin su, ke kuma ki musu da jikinki.”

“Hakane Umma sai dai ni ina jin tsoron matar Saboda bata da imani bata tsoron Allah zata iya cutar dani Umma, ni Umma da zaki gane kawai na haƙura da aiki a gidan na dawo gida mu riƙe talaucin mu, yafi mana kwanciyar hankali, Umma bazan iya rayuwa cikin RIKICI DA TSORO BA saboda akwai hatsari a zaman gidan Umma…”

*****

“Na sani Ablah akwai hatsari domin kuwa zama da mutum irin Amarya dole da akwai Babban hatsari, amma ki sani rayuwa cikin tsoro yakan karyawa Mutum zuciya, abinda zai ka iya ma sai tsoron yasa kaji ba baka iya ba, ya durƙusar dakai ya hanaka taka rawar gaban hantsi, ba’a Rayuwa cikin tsoro muddun zaki zauna da mutane irin Amarya to fa dole ne ki cire tsoro cikin zuciyarki ki kawo jarunta da rashin tsoro ki dasa su a zuciyarki, ina ji a jikina zakiyi nasara akanta Ablah muddun kika ɗaukk zuciyata babu abinda zai tsorataki a duniya, ki sani ke fa gaskiya kika riƙe akasin ita da ta riƙe zalunci, dole kuma gaskiya itace zatayi Nasara akan ƙarya, bazaki bar gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA ba saboda ƙaramin abu dole zaki zauna domin kare rayukansu, ki sani babu wanda yasan munanan halayyarta sai ke Allah ya nunawa mai yiwuwa hakan yana nufin kece kariyarsu, zan miki addu’a a matsayina ta mahaifiyarki, na Tabbata Allah zai kareki domin kuwa mun dogara ne ga Ubangiji kuma zai zamo gatanki, Ablah bawai saboda muna ƙwaɗayin abin hanunsu ko dan abinda suke bamu ba, zakiyi wannan aikin, a’a zakiyi ne saboda Allah, Ablah karki sake suji halin amarya daga bakinki domin kuwa ko kin faɗa bazasu yarda ba, ta gama ciye zuciyarsu ta shiga jikinsu ta yadda zata cutar dasu ba tare da sun ankara ba, kiyi aikin da zaisa su gani da idanunsu wannan shi zaisa su yarda.”

“Kai Umma nikam bazan iya ba, Umma bazan iya wannan Rayuwar ba, idan har ta cutar da rayuwata Umma kece wacce zakiji ciwo ba suba, su kawai sai dai su mana jaje na lokaci ɗaya daga nan zasu manta su cigaba da hidimar rayuwarsu, amma ke fa bazaki taɓa daina jin ciwon ba, Umma ki gafarceni bazan iya rayuwa cikin wannan gidan ba, ni kawai gobe zan tattaro kayana na dawo gida.”

Numfashi Umma ta saki tana girgiza kanta tare da tuno abubuwa munana da suka faru da ita a Rayuwa wanda sukafi waɗannan haɗari, ta kuma daure zuciyarta ta ƙetare su, amma wai ita Ablah wannan ƙaramin aikin da Zatayi ba tare da sanin kowa ba, tana jin tsoron sa, ina ma ana arawa Mutum zuciya Tabbas da ta sauyawa Ablah zuciyarta da nata.

“Ablah na faɗa miki ki cire tsoro cikin zuciyarki insha Allah babu abinda zai cutar dake mun riƙe Allah bazamu cutu ba, ke dai kiyi amfani da Maganar dana faɗa miki na sani koda kin cutu babu wanda zai kaini baƙin ciki duk wanda yaji ciwo bayana ne, amma a hakan nake baki umarnin kije kiyi aikin Allah ba ƙaramin lada zaki samu ba.”

“Shikenan zan miki biyayya amma sai dai Allah yana gani ina cikin tsoro da fargaba ina ji a jikina akwai abu marar daɗi da zai faru dani a cikin wannan gidan, saboda Aunty Amarya ba Mutum bace mai tsoron Allah, ni damuwata na rasa me take nema a wajen su da take ƙoƙarin cutar dasu, Umma duk mutumin da yayi ƙoƙarin kisan kai babu abinda bazai iya aikatawa ba.”

Murmushi Umma tayi tare da cewa.

“Ƙwarai maganarki gaskiya ce duk wanda zai iya kisan kai to babu abinda zai bashi tsoro, sanin abinda take nema garesu, wannan shi zaki fara bin diddigi, Allah ya rabaki da sharrinta.”

Da ameen Ablah ta amsa sun juma suna tattaunawa da Umma kafin ta tashi ta shiga gidan su ƙawarta Hafsa, ta samu ma bata nan bata wani juma ba ta dawo gidan su da magaruba kamar yadda ta cewa drevern haka yazo ya ɗauketa ta koma.

Washe gari da safe misalin bakwai kafin kowa yayi breakfast, Al’ameen da Daddy suka raka su Khalipa da Ashfat da Auntyn Faruq airport, basu dawo ba har sai da jirgin su ya tashi dawowar su har Ladiyo ta jere breakfast, bayan sunyi breakfast kowa ya kama harkar gabansa, shima Al’ameen wunin ranar yana gida bashi da zuwa Office, Ablah kuwa wuni guda bata fito falon ba, tunda ya zauna a falon yake dube duben ta inda zai ganta sai dai ko gilmawarta bai gani ba rabon da ya ganta tun lokacin daya mareta, haka kawai sai yaji babu daɗi da bai ganta ba, wataƙil ko marin da ya mata ne yasa taƙi fitowa.

“Anya kuwa tana lafiya bata fito ba tun safe gashi yanzu har 3:20?”

Ya furta a zuciyarsa, numfashi ya saki tare da miƙewa ya haura sama.

Aunty Amarya kuwa tana zaune cikin bedroom ɗinta tana tunanin hanyar da zata sake ɓullowa tunda wannan damar ta kufce mata, murmushi ta saki tuno da Ablah tare da miƙewa ta furta.

“Tabbas dole nayi taka tsantsan nasan yadda zan iya takuna Saboda akwai mujiya a cikin gidan nan, nasan dole zatayi ƙoƙarin kawo min farmaƙi, hmmm! Yaro kenan ta yaro kyau take bata ƙargo, bara na ɗan saki zaren naga ta inda zata fara kamawa domin sanin girman hukuncin da zan yanke mata, domin kuwa muddun tace zata ja dani, to kuwa Tabbas zata jefa kanta cikin wuta, *ABLAH* yarinya mai wayo wai dani zata ja, lallai kuwa zarenki zai tsinke baije ko ina ba, ni Amarya murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya, bara mu zuba mu gani, na dai yi nasarar kashe mutum ɗaya na kuma cirewa ɗaya ƙafa duk da ba ƙafar bane naso ta fita ran naso ya fita, bari muga ko zaki yi ƙoƙarin dakatar da nasarata domin kuwa muddun ina numfashi sai na mallaki dukiyar AMBASSADOR babu wanda ya isa ya dakatar dani muddun kuwa wani yayi ƙoƙarin wannan kuskuren shima zan yanke numfashin sa.”

Tayi Maganar tana sheƙewa da dariya, tare da ɗaukar wayarta ta fito falo, Ummi ta samu zaune cikin kujerun falon, zama itama tayi cikin daraja Ummi tace.

“Ummin Al’ameen barka da fitowa yau baki fito kinyi breakfast ba, na aika ihsan ta duboki tace baki tashi daga bacci ba.”

“Tunda mukayi Sallama da su Khalipa na koma na kwanta, ina azumi yau kin san an biyoni guda ɗaya a Ramadan shine yau na ɗauka.”

“Haka fa aini na manta ma, ina Maimu tayi ne ina son aiken su ita da wannan shashar Afnan gidan Hajiya Sauda.”

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Maimu ai tafi Afnan shashanci, yanzu na jiyo muryarta bedroom ɗin ihsan suna can suna game.”

Ummi ta ƙarisa Maganar idanunta na sauƙa akan Ablah da ta fito daga bedroom ɗin ta, idanunta sun ɗan kaɗa sunyi ja, Ummi kira ta ƙwala mata, ta ƙariso tare da sunkuyawa tace.

“Ina kwana Ummi.”

Da lafiya Ummi ta amsa tana dubanta tare da cewa.

“Lafiya kuwa naga idanunki sun sauya kala, tun jiya nake ganin yanayinki ya sauya meke damunki ko dai akan marin da Al’ameen ya miki kike ɗari ɗari damu.?”

Ɗago idanunta Ablah tayi ta kalli amarya domin kuwa itace sanyin jikinta tun jiya, idanu suka haɗa Aunty Amarya ta sakar mata murmushi, kauda kanta Ablah tayi tare da cewa Ummi.

“A’a bashi bane, bana jin daɗi ne kaina yake ciwo.”

 “Subahanallah! Sannu kinsha magani kuwa?”

Kanta Ablah ta girgiza alamun a’a, Ummi cikin kulawa tace.

“Ya kike wasa da lafiyarki haka, to maza ki shiga bedroom ɗina jikin drowern mirror akwai maganin ciwon kai ki ɗauka kisha, Allah ya baki lafiya.”

Da ameen Ablah ta amsa zata mike taji muryar Aunty Amarya.

“Sannu Ablah Allah ya baki lafiya, Allah Sarki shiyasa yau wuni guda banga kin fito ba, ki daina wasa da lafiyarki ki kula sosai.”

Murmushi Ablah tayi ta amsa mata da.

“Insha Allah zan kula na gode da tunatarwa.”

Tayi Maganar tana haurawa bedroom ɗin Ummi, murmushi Aunty Amarya ta saki tare da Binta da kallo.

Door ɗin ta tura tare da shiga da Sallama, drowern ta nufa sai idanunta suka sauƙa a kansa yana kwance a bed ɗin Ummi yana baccin sa cikin nutsuwa da kallo Ablah ta bisa, kyakkyawan gaske ne, sai dai kuma mugunta da baƙin hali da suka ɓata masa kyawun bakin ta taɓe tare da nufar drowern hanu tasa zata ɗauki maganin bisa kuskure sai ta bige cup ɗin dish dake ajiye saman wadrop, ji kake ƙas…ƙas…ƙas ya tarwatsa tare da yin tsawa, a firgice Al’ameen ya buɗe idanunsa yana ambaton innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Idanunsa ne suka sauƙa akan dish ɗin dake tarwatse a ƙasa daga ƙafafuwan ta ya fara kallonta har sai da ya ɗago idanunsa ya ganta kansa ya dafe tare da tsareta da idanunsa bakinsa ya cije ba tare da yace mata komai ba, ganin bazata iya jurar haɗa idanu dashi ba ya sata sunkuyar da kanta ƙasa zata bar wajen cikin tsawa yace mata.

“Karki kuskura ki fita!”

Turus ta tsaya cike da tsoronsa.

“Ki sunkuya ki kwashe wannan glass ɗin da kika fasa da hanunki.”

Zaro idanunta Ablah tayi tana kallon glass ɗin idan banda rashin imani ta yaya za’ace ɗan Adam ya saka hanunsa a wannan glass mai Uban kaifi, idanunta ta ɗago ta kallesa idanunta yayi raurau har hawaye ya fara taruwa a idanunta, ganin yanayinta yaso bawa Al’ameen dariya, sosai take burgesa idan ta shiga wannan yanayin ita dai kuka baya bata wahala ƙara tsuke fuskarsa Al’ameen yayi tare da zaro mata idanunsa.

“Bazaki sunkuya ki kwashe bane kike kallona, idan kika yarda na tashi sai na danna ƙarfarki cikin glass ɗin, tunda a rayuwarki bakya ƙaunar kiga ina hutawa.”

“Al’ameen dan Allah kayi hakuri zan ɗauko tsintsiya na kwashe, idan na saka hanuna zai yankeni kuma bada sanina ya fashe ba.”

“Au dama kina tsoron ya yankeki shine kika fasa shi, to kuwa tunda kika tasheni daga bacci, dole sai kin kwashe da hanunki oya maza fara.”

Tura bakinta Ablah tayi cike da fara jin haushin sa tace.

“To kai nan ɗakin kane da zakazo ka kwanta ni wallahi bazan saka hanuna ba naji ciwo.”

Ta ƙarisa Maganar hawaye na sauƙa daga idanunta, tare da ficewa da gudu ganin da gaske yake sai ya ji mata ciwo, dariya Al’ameen yayi har fararen haƙwaransa suka bayyana miƙewa yayi da kansa yaje tollet ɗin Ummi ya ɗauki tsintsiya da faka yazo ya kwashe glass ɗin ya juye a dosbin, ya koma ya kwanta na sakin murmushi.

Da la’asar lis Haidar ya shigo cikin shirin fita hanunsa riƙe da key ɗin motar sa, sama ya haura bedroom ɗin Al’ameen, ya sunkuya zai kwashi wayoyinsa Haidar ya shigo da Sallama dagowa Al’ameen yayi tare da yin murmushi yace.

“Yau dai Allah ya ƙaddara bazaka min ƙorafi ba, muje na shirya.”

Dariya Haidar yayi tare da juyowa suka fita wayar Faruq Haidar ya kira kasancewar tare sukayi zasuje wajen Nafeesa, kusan 3miss call Faruq bai ɗauka ba, da kansa Haidar ya shiga part ɗin nasu nan ma dai baya nan, haka suka shiga mota shida Al’ameen suka ɗauki hanya, sunyi nisa da tafiya Haidar yace.

“Yau dai Al’ameen zaiga Nafeesa Allah yasa ka yaba da zaɓi na.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Har kullum bazan daina faɗin wannan kalmar ba, a soyayya babu zaɓen kyau, an dai fi buƙata ka zaɓi ƴar mutunci wacce zata baka daraja da cikakkiyar kulawa a rayuwarka, sannan taga mutuncin ahalinka wacce zata kare martabar ka, mai cikakken ilimin addini koda kuwa bata da na zamani, idan ka samu wannan to Tabbas kayi kyakkyawan zaɓi komai munin fuskarta kuwa.”

Murmushi Haidar yayi yana cigaba da dreving ɗinsa yace.

“Shiyasa nake son naga zaɓinka Al’ameen domin kuwa duk macen da tayi nasarar samunka a matsayin miji to fa lallai ta ɗaga tuta.”

Still dai murmushin Al’ameen ya kuma yace.

“Zaɓi kam na riga da nayisa Haidar domin kuwa idanuna sunga matar da ta dace dani.”

Kusan sake sitiyarin motar Haidar yayi tare da furta.

” whattttttt!”

Al’ameen saurin riƙe sitiyarin yayi tare da cewa.

“Au kashe mu zakayi ne meye abin sake sitiyarin motar.?”

“To ai dole na sake Maganar taka ce ta bani mamaki kai da baka kallon mata, a ina ka gano budurwar kaga Abokina faɗa min wacece wannan wacce tayi matuƙar dace haka?”

Dariya sosai Al’ameen yayi tare da dukan kafaɗar Haidar yace.

“Tayi dace ko kuma ka tausaya mata, ko ba cewa kuke zama dani sai an saka haƙuri.”

Murmushi Haidar yayi tare da cewa.

“Ni fa ba wannan maganar ba, kawai so nake nasan wacece budurwar?”

Yayi Maganar dai-dai suna isowa ƙofar gidan su Nafeesa.

“Ban gama saita komai ba idan na gama dole zaku sani kai dai yanzu kira jarumar taka.”

“Kaga bara kaga mu koma gida dole sai ka sanar dani domin kuwa babu ruwana da ka saita ko baka saita ba.”

Yayi Maganar yana dannawa Nafeesa kira ya sanar da ita sun iso.

Murmushi kawai Al’ameen yayi tare da buɗe motar ya fito ya jingunu da jikin motar yana harɗe hanunsa a ƙirji tare da bin ƙofar gidan su Nafeesa da kallo shima Haidar fitowa yayi ya tsaya gefen Al’ameen ba’a juma ba kuwa sai ga Nafeesa ta fito, tunda ta fito idanunta akan Al’ameen suke, haka kawai take jin munguwar ƙaunarsa koda tana son kuɗin amma har zuciyarta tana jin soyayyarsa, ji take kamar ta ruga da gudu ta rungumesa, ashe ma yafi kyau a zahiri fiye da hoto, shi kuwa Al’ameen baima lura da ta fito ba domin ya saka idanunsa akan wayarsa, saurin saita kanta Nafeesa tayi tare da sakin murmushi tayi sallama.

Amsawa Haidar yayi shima yana murmushin yace.

“Barka da fitowa Duniyata, kinyi kyau fa.”

Ɗan dariya Nafeesa tace.

“Ban dai kaika kyau ba, sannu da zuwa abokinmu.”

Tayi Maganar tana duban Al’ameen, ɗago idanunsa Al’ameen yayi yana murmushi yace.

“Yauwa sannu, kece Nafeesa ko?”

Murmushi tayi tana ƙura masa idanu ta amsa da.

“Ƙwarai ni ce ya kk.”

“Ina lafiya sai dai fa jinki yafi ganinki, da alamu keɗin ruwa biyu ce.”

Wani irin tsinkewa zuciyar Nafeesa tayi tare da jin haushin maganarsa (jinki yafi ganinki to me yake nufi da hakan? Da gani wannan zaiyi izza da rainin wayo, Lallai dole sai nayi babban shiri akansa, gashi dai kamar a sace a gudu sai babu sauƙin kai) Tayi Maganar cikin zuciyarta, sai kuma ta ɗan saki murmushi tare da duban Haidar tace.

“Farin ciki na kana jin abinda yake faɗi wai jina yafi gani na, sanar dashi ban damu wani ya yabeni ba, Muddun dai kai ka yaba.”

Murmushin gefen baki Al’ameen yayi tare da cewa.

“Iya dai gaskiya ta na faɗa.”

Yayi Maganar yana buɗe motar ya shige…

<< Aminaina Ko Ita? 18Aminaina Ko Ita 20 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita? 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×