Skip to content
Part 1 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

“Wallahi ƙarya kake Habib, baka isaba ka hanani zuwa bikin ƙawata dole ne inje duk wani tsoratar dani da kake akan kar inje.”

Miƙewa yayi a fusace.

“Ke harni zaki kalla kice ina maki ƙarya, to in har kika bar gidan nan bada yawuna ba kuma duk abinda ya biyo baya kada ki kuka dani ki kuka da kanki.”

“Oho dai! Tafiya ce ko kana so ko baka so sai nayi, yardarka da rashinta kai suka dama banga wanda ya isa ya hanani tafiyar nan ba.”

“Haka kika ce? To Basma jeki zaki gani, sai kinyi nadama kuma kada ki sake ki jemani da da ko ƙofar gidan nan ne.”

“Ina zani da danka haka kawai ya takura mani, shakuruminka danka gida zani barshi.”

Ficewa yayi daga gidan zuciyar shi na matuƙar yimashi ƙuna.

Kuka take kamar ranta zai fita ga mahaifinta tsaye kanta da wayar wuta, jibgarta kawai yake babu ƙaƙƙautawa.

“Ni zaki zubda ma mutunci Salma! Ince maki kiyi hakuri amma ki kafe sai kinje bikin wata ƙawar banza, kinko san illar dake tattare da hanyar da zakubi?, to ƙara in karya ƙafafunki inga da wadanne ƙafafun zaki tafi,”

“Haba Alhaji!, kasheta kake son yi?, dan Allah karabu da ita hakanan kada kayi mata illar ka nakasa ta.”

“Ki barni in nakasata inga da wadanne ƙafafun zata bar gidan nan, wurgar da bulalar yayi ya fice daga falon.”

“Yanzu Mama ace duk yadda muke da hajara amma ace Daddy ya hana ni zuwa bikinta, kawai dan ance hanyar nada haɗari.”

“Ke fah sakara ce, yanzu so kike a gabanshi in goyi bayanki, ai dole ne kije bikin hajara kada ki damu in lokacin yayi ce ma shi zaniyi kinje biki a dangin mu.”

(Kuji abun takaici uwa daya kamata ta bada tarbiyya itake warware wadda mahaifin ya bada, Basma kinyi kuskure kina kai kanki ga halaka dakinsan mizaku iske ga tafiyar da kinyi zamanki gida muje zuwa.)

Rungume momyn ta tayi tana murna.

“Yawa momy na shiyasa nike ƙara sonki, yanzu Momy zani nunawa daddy na haƙura da tafiyar dan kada yayi zargin wani abu.”

“Yauwa ki nuna ma shi, shima nasan dan yaga ke ɗaya ya mallaka shiyasa bai so kiyi tafiyar, ga kuma abokinshi munafuki daya ce ma shi wai hanyar bata da kyau.”

Tashi Salma tayi ta nufi ɗaki.
“Momy na tafi in shirya kayana kinsan wallahi na ƙagara inga lokacin nan yayi…”

*****

“Jafar abinda zani faɗa maka kaji tsoron Allah aduk inda kake, tafiyar nan da zakayi nemo Mahaifinka daya daɗe da bacewa aka ce an ganshi achan garin, Jafar ka riƙe addu’a ka kiyaye yin sallah a duk halin daka tsinci kanka, wallahi jinike badan Mahaifinka daya bata zakaje nema ba da na hanaka tafiyar nan saboda an ce hanyar wata shu’umar hanya ce sai dai addu’a.”

Tunda ta fara maganar kan shi yake ƙasa sai yanzu ya ɗago.
“Umma addu’arki nike nema i ta ce kaɗai nike buƙata a duk inda nike Umma.”

“Jafar Allah ya tsare hanya, Allah ya kareka a duk inda kake, yanzu tashi ka fara haɗa kayanka.”

“To Umma nagode da addu’arki, insha Allah kamar yadda kika buƙata zani kasance mai ruƙo da addini da kuma addu’a…”

*****
“Yanzu Rabi’u tafiya zakayi ka barni, katai maka kada kayi rafiyar nan ance hanyar shu’umar hanya ce, kada kaje a kashe mani kai.”
Ta ida maganar hawaye na wanke mata fuska.

“Haba! Haba!! Haba!!! Kaka nifa ki daina ce mani Rabi’u, Rabson guy nike haba in cikin abokaina ne ai saiki kunyatani.”

“Nidai ina roƙonka ka janye maganar tafiyarnan Rabi’u.”

“Kutt! In zanye fa kika ce?, Kaka ai dole in yi tafiyar nan ga inda ɗan ladi yace zani samu kuɗi amma kina maganar in zauna ai sam bazai yiwu ba, kinga bari inje in fara shin tafiya.”
Ya fice yana tafiya yana yin doro kamar wani zabo irin tafiyar gayun zamanin nan.

Binshi tayi da kallo zuciyarta na mata ƙuna saboda kinjin maganarta da jikanta yayi, ahalin yanzu shi kadai ya rage mata tun bayan rasuwar iyayenshi sanadiyyar gobara shi kadai ya tsira.

Shima gashi yanzu yana shirin kai kanshi ga halaka, dan tun tana budurwa takejin labarin dajin kai kazo, mugun daji ne wanda indai ka fita cikin shi ka auna babban arziƙi

*****
“Biba ba wai banison tafiyarki bane, Aa ina jin tsoron hanyar da zaku bi, Biba Mahaifinku ya rasu tunda Allah ya amshi abunshi ke kike sana’a kina hidima damu yanzu ace kema karatu zaki tafi, ni babbar damuwata wannan shu”umar hanya da zaku bi ta wurinta, in na tuna hankalina na matuƙar tashi Biba.”

“Mama addu’ar ki a duk inda nike ita nike buƙata, Mama inna zauna banyi karatun nan ba dami zani taimake ku nan gaba nidai kiyi mani addu’a Mama.”

“Shikenan Biba Allah ya tsareki a duk inda kike, biba ki riƙe maraicinki kada ki banzatar da rayuwarki Allah yayi maki jagora Allah ya kareman ke aduk inda kike.”

“Amin Mama.”

“Bari inje in samo rancen sayayyar da zaki ida.”

“To Mama sai kin dawo.”

….Fizge akwatin hannunta yayi, yana nuna ta da yatsa cikin tsananin bacin rai.

“Yanzu tsabar baki da mutumci in hanaki tafiyar nan amma sai kinyi?.”

Kallon shi tayi a wulaƙance.

“Tafiya sai nayi banga ɗan yarinyar daya isa ya hanani ba, kabani akwatina kafin in zabga maka rashin mutumci, dan da in fasa tafiyar nan ƙara aurena ya mutum in je bikin.”

Tsabar bacin rai idanunshi har sunyi jajur jikinshi har kyarma yake, wurga mata kayan yayi yana mai nunata da yatsa.

“Basma yau ni kike kira Ɗan yarinya?, har wata ƙawa tafini a wurinki? To bazance maki komiba kije zaki gani, sai kinyi nadamar tafiyar nan sai kinyi kuka da idanunki, sai kin yi nadama a lokacin da bata da amfani a wurinki.”

Ɗansu dake ta darza kuka amma Basma ko ajikinta bata damu da shiba ya ɗauka yayi daki dashi.

“Oho dai ni kaga tafitata.”

Tayi gaba tana wata rangwaɗa kamar budurwa, ga ɗamammun kaya ansha jikinta duk ana ganin shi ga ɗan figigin gyale.

(Ya ubangiji ka shiryi matan auren wannan zamanin, wallahi wata shigar banzar da matar aure zatayi ko budurwa baza tayi ta ba, ko ni nan nasha ganin matar auren da tayi wannan shigar samari sun ɗauka budurwa ce sukayi ta tsai da ta, Allah ka shiryemu.)

*****

“Kai Momy! Ni dai kiyi sauri lokacin tafiyar fa yayi, kada inje in iske mota ta tashi.”

“Kin ci gidanku Salma! Yaushe garin ya waye da har mota zata barki tasha.”

“Mamana har an shirya kenan?, to i ta tafiya tana buƙatar guzuri ungo nan ki ƙara riƙe wa zasuyi maki amfani, ki gaida mani su kaka da ƴan uwa sosai.”

Amsar kuɗin tayi tana godiya.

“To daddy na zasuji, zanyi missing ɗinka daddy na.”

“Nima haka Mamana, ki kula da kanki sai kin dawo byee.”

Ya faɗa yana ida shigewa ɗakinshi.

“Momy ki rakani bakin gate ko nasan yanzu idi driver ya fita.”

Suna fitowa ya nufosu yana gaidasu, amsar kayan dake hannun Salma yayi yasa a boot ɗin motar, shigewa motar tayi na ɗagama Momyn ta hannu.

Sulalawa motar ta cikin haɗaɗɗen gate ɗin gidan ta fice.

Suna fita Momy taji jikinta yayi sanyi, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, jitayi dama ta hana Salma tafiyar a lokaci ɗaya, sai dai ina bakin alƙalami ya bushe.

*****

Tsaye gaban mahaifiyar ta, cikin shiga ta kamala tasha hijabinta tana sauraren nasihar da take mata.

“Biba kiji tsoron Allah aduk inda kike, ki zauna da mutane lafiya, ki riƙe addu’a, ita addu’a takobin muminice, Ki kasance mai riƙon amana da faɗar gaskiya aduk halin da kika tsinci kanki, Allah ya tsareki ya dawo dake lafiya Habiba ta.”

“Amin Ummana.”

Juyowa tayi ta kalli ƴan ƙannenta da suka yi jigum_jigum.

“Bakuyi mani addu’a ƙannena? Ko baku so in zani dawo inyi maku tsaraba.”

Hada baki sukayi cikin farin ciki dajin maganarta, “Allah ya kiyaye aunty Biba, sai kin dawo.”

Sallama tayi da Umma tafito jiki ba kwari tayi addu’ar fita daga gida ta hau a daidaita ta nufi tasha.

*****

“Rabi’u yanzu tafiyar nan zakayi?”

“Chan Allah ya haɗaki da Rabi’u, ni Rabson guy nike, kada ki bata mani lokaci ni tafiya zaniyi.”

“Kakus ki kula mani da Ɗan bunsuruna, dan ranar dana dawo lokacin na samo kuɗi ranar zai sha wuƙa.”

“Rabi’u kai kaɗai ka rage mani tunda mahaifanka suka yi haɗari suka mutu, yanzu kai ma tafita zakayi ka barni.”

“Haba kakus! Kuɗi fa zani samo, kuma inna tai ba daɗewa zanyi ba zani dawo.”

“Ni dai bada yawuna zakayi tafiyar nan ba, in katai komi ya faru ba ruwana tunda bakajin maganata.”

“Heeey! Chau_chau kakus, kina bata mani lokaci kinga tafiyata.”

Yafice yana waka abakinshi ba tare da addu’ar fita daga gida ba.

Binshi tayi da kallo wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, ji take aranta kamar Rabi’un ta ba zai dawo ba.

******
“Har ka fito Jafar?”

“Eh Umma lokaci nata ja.”

Nan tayi ma shi nasiha mai shiga jiki mussaman kan ruƙo da addu’a aduk halin da mutum ya shiga.

Bankwana sukayi jikinsu yayi sanyi.

Jafar ya fito ya nufi tasha.
xswHayaniya ce ke tashi acikin tashar kowa nata hada hadarshi.

Basma, Salma, Biba, Rabson guy, da Jafar duk lokaci ɗaya suka iso tashar.

Gudu_gudu suka iso gaban motar da kwandastan keta faɗi.
“Kai kazo! Kai kazo!! Saura mutum biyar mota ta cika.”

Basma, Rabson, Jafar, da Biba sunyi nasarar shigewa motar amma banda Salma data bige wata tsohuwa.

“Kai amma dai ke wace irin jakar tsohuwace?, idanunki basu gani hanya koko?.”

“Ɗiyata kiyi haƙuri.” amma abinda zani faɗa maki kada ki kuskura kiyi tafiyar” nan Ta fada tare da kamo hannun Salma.

Tatss! Ta ɗauke tsohuwar nan da mari.

“Kina ƙazamarki har zaki kamo hannu na, talaka marar amfani kawai.”

Tayi gaba tabar tsohuwar tsaye.

Abun mamaki tsohuwar dafe take da kumci amma dariya take mai ban tsoro.

Salma na isa motar ta cika, dan dama Motace mai cin mutum goma.

Sun ɗauki hanya an fara tafiya.

Salma da Rabson guy kujera daya suke zaune.

Sai Biba da jafar suna gaban kujerarsu Salma.

Sai Basma ita da wani mutum aka haɗata.

Gudu motar ke shararawa akan titin, in da mytanen motar kowa da abunda yakeyi.

Biba da Jafar Hisnul muslum ne hannunsu suna karanta azkar.

Basma earpiece ne kunnenta tana shan ƙiɗa.

Rabson da Salma charting kawai suke sha, Rabson satar kallon Salma kawai yake.

Sauran mutanen motar hirarsu suke sha.

Wani mahaukacin birki da direban yayi shiya sanya kowa kallon abunda ya haddasa faruwar haka, tuni kowa ya ruɗe wasu suka hau iface_iface wasu suka hau salati…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Bakar Tafiya 2 >>

5 thoughts on “Bakar Tafiya 1”

  1. Lallai wanan tafiyar akwai darussan a ciki mai tarin…oh basma da Salman da Rabson sune tantiran yan air su tafi ba tare da Albarka ba,
    Kar dai wanann tsohuwar fa Aljana ce lallai Salma zata gane kurenta…
    Oh babi Da Ja’afar Allah ya kare ku kune kawai na ƙwarai….

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×