Skip to content
Part 2 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Iface-iface ke ketashi a cikin motar, Jafar da Biba addu’a ce abakin su, sunata maimaitawa.

LA’ILAHA’ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN

Suke ta nanatawa, wannan addu’ar in dai ka dogara da Allah kariƙa yinta alokacin da kake cikin bala’i Allah zai fiddaka da izininsa,,,Tunatarwa ce.

“Mun shiga ukku direba meya faru?.”

Direba ko motsi baiyi rai yayi halinshi.

Suna ganin haka suka ƙara ruɗewa.

Duka mutanen motar fitowa sukayi ganin hanya ta tsage gida biyu ya ƙara tada hankulansu sukayi cikin dajin da mugun gudu.

Gudu suke ko wai waye basuyi iyakar ƙarfinsun suna ƙara kutsawa cikin dajin.

Daji ne wanda ko daga yanayin bishiyoyinshi kaɗai sun isa su sa mutum sumewa, wani irin shu’umin daji ne wanda bishiyoyin cikinshi kansu suffar dodanni garesu, ga wata irin duhuwa dake gareshi, duwatsune manya_manya cikin dajin ga wani irin iska wanda shi kaɗai ya isa ya tabbatar maka da kuna cikin tashin hankali,masifa da bala’i.

Iska ne ke kaɗawa kamar kana cikin maƙabarta wani shuuuuw! Ga iska ya game da kukan wasu irin tsuntsaye, yana bada sauti mai firgitarwa.

Gudu suke kamar ransu zai fita, abinda basu sani ba duk gudun da suke haryanzu suna farkon dajin.

“Wayyoh zani Mutu! Kutsaya mu huta, wayyoni ƙishirwa ku taimaka mani.”

Basma ke maganar numfashin ta na fita da ƙyar.

Abokin zaman kujerarta a mota afusace ya fara magana.

“Kee amma bakida hankali kina nufin mutsaya musanya rayuwarmu ga halaka?, to in bazaki zo mu ida fita adajin nan ba wallahi nan zamu barki muyi gaba.”

Kafin ya ida rufe baki dajin ya gauraye da wata mahaukaciyar dariya.

“Kunyi kuskuren shigowa DAJIN KAI KAZO!! Ku masu taurin kai Dukkan ku babu wanda zai fita da rayuwarshi,zamu riƙa yimaku ɗauki ɗai_ɗai har sai mun ƙarar daku hahaha.”

Wata mahaukaciyar guguwace tayo kansu.

Gudu sukaci gaba dayi suna waiwayen iskar dake biyosu, tim! Daya daga cikinsu ya fadi tsayawa sukayi domin taimakonshi, Jafar ya tsaya suna kokarin isowa gareshi, suna daf da isowa gareshi iskar nan ta sureshi tayi sama dashi.

Firgicewa suka ƙara yi masu koke_koke da iface_iface nayi.

Sauƙinsu ɗaya duk gudun da suke basu rabu da juna ba.

Gudu suke har duhun magriba ya fara.

Wani wuri suka tsinci kansu mai yalwar bishiyoyi manya_manya gasu kuma dogaye abun tsoro.

“Assalamu alaikum!, jama’a ya kama tafa musan abunyi, kamata yayi musan inda muke kutsa kanmu, karfa wurin gudun ceton rayuwa mukai kanmu ga halaka.”

“Maganarka haka take, kamata yayi mubar gudun nan musamarwa kanmu mafita ga duhu ya fara.”

Biba ta fad’a tana mai ƙara dubar mutanen.

Wani saurayi mai zubin ƴan daba daga cikin fasinjojin motar ya fara magana.

“Yanzu kamata yayi mu samu inda zamu ƙwana shine kawai mafita in safiya tayi saimu nemi hanyar fita daga dajin nan.”

“Wallahi baka isa ba mu babu inda zamu kwana cikin wannan ƙazamin dajin, in kai ƙazamine toni dubarni da kyau banyi kalar da zani haɗa wurin kwanciya daku ba.” Salma ta faɗa tana aikamai da kallon wulaƙanci.

“Kuturun chan kayyasa! Yau Garba kisa ne mace ke faɗawa magana, yarinya kinci arziƙin a wani hali muke da hukuncin kisa shi zai hau kanki, amma yanzu sai dai in maki bugun da ko kallon banza bazaki ƙara yi mani ba.”

Wani wawan tsalle ya daka ya isa gabanta ya fara ɗauketa da ta gwayen maruka.

Mutanen wurin sukayo kanshi suna rirriƙeshi ana bashi haƙuri.

“Ni ka mara?, wallahi sai kayi nadama sai ka ƙwammace bakazo duniya ba, ko daddy na bai taba marina ba sai kai matsiyaci talaka da kai.”

Jafar ya daka mata wata irin tsawa.
“Keee! Ya isa, yanzu a wannan halin damuke ciki haɗin kai muke buƙata bawai mu tsaya muna faɗa da juna ba, daga yanzu bazamu laminci wannan faɗace_faɗacen naku ba, ku zo muyi gaba muga in da ya dace mu yada zango.”

Sunyi ƴar tafiya mai nisa suka ga wani gida a gabansu.

Gidane wanda aka gina da katako, da alamu gidan ya daɗe a kulle saboda yanar data lullube ƙofar gidan.

Hayaniya aka farayi ta wanda zai shiga ya duba.

Rabson guy da akace ya shiga su duba karkace kai yayi yace shi in dare yayi bai gani sosai.

Cikin abokan tafiyarsu na mota mutum huɗu da suka rage Garba kisa, da wani audu gwarama, sai wani nura shila su duk abokai ne wani aiki na shiyasa suka samu zasuje su tada rikici abiyasu.
Sai mace ɗaya mandiya Ita kuma karuwa ce labari ta samu anfi samun kuɗi a abirnin Kai kazo shiyasa ta fito yawon duniya zataje Birnin kai kazo.

Jafar, Garba kisa, audu gwarama sai nura shila, su zasu shiga gidan su duba masu.

Ƙofar gidan kulle take gam, da ƙyar suka samu suka buɗeta, wata irin k’urace ta ke fitowa daga gidan dole suka ja da baya sai da ƙurar ta gama ficewa sannan Jafar yai bisimillah suka kutsa kai cikin gidan.

Duhu ne sosai gidan ko tafin hannunka baka gani, sai lokacin Jafar ya tuna da wayarshi, fiddota yayi amma abun mamaki kwata_kwata babu network gurin ko alamun shi babu.

Touchlight ya kunna, tuni haske ya gauraye wurin, wani irin gidane mai wani irin fasali, inda suke tsaye wani tangamemen falo ne mai ɗauke da gadaje uku gefe daya kuma kujerune aduk da katakai akayi su, sai wasu ɗakuna biyu dake kulle, in ka matsa bayan kujerun wurin dafa abincine shima da katakai aka ƙera wurin, amma duk yana da ƙura ta lullube kayan gidan ,idanunsu ne suka hasko masu wani hoto amma ƙura ta lullubeshi, matsawa mukayi a hankali Jafar yayi bisimillah tare da goge ƙurar,Hoton Turawane ya bayyana mata da miji da kuma ɗiyarsu, sunyi dariya aka ɗauki hoton su, sunyi matuƙar kyau.

Kansu kullewa yayi, suna ma kawunansu tambayar miya kawo turawa acikin dajin nan har sukayi gida?, lallai al amarin nan akwai ban tsoro.

Ƙofofin ɗakin suka buɗe da tagogin take haske ya bayyana duk da lokacin duhun magriba ya fara.

Sun duba ko ina amma basuga wani abu na cutarwa ba.

Ɗakunan nan biyune kaɗai basu buɗeba.

Fitowa sukayi suka umarci abokan tafiyarsu dasu shigo daga ciki.

Bayan shigarsu ne kowa ya naimi wuri ya zauna yana jimamin halin da suke ciki.

Jafar ne yayi gyaran murya ya fara magana.

“Ƴan uwana ya kamata mutashi mu gabatar da sallolin dake kanmu, nasan da wuya musamu ruwa a hanlin da muke ciki yanzu amma abinda yafi shine muyi taimama kawai zai fi mana.”

Basma da Biba, Mandiya tare sukayi sallah, ƙiri_ƙiri Salma taƙiyin sallar cewa tayi ita gobe in an samu ruwa ta haɗa tayi.

Garba kisa da yaranshi kuwa sai dai shiriyar Allah, domin tabarsu kusa fiddo daga cikin aljihun wando da ashana suka hau hura hayaƙinsu.

Dare yayi nan ido ya raina fata, kowa ka kalla zakaga tsantsar tashin hankali atare dashi.

Bayan sun kakkabe ƙurar da yana kowa ya fara neman inda zai kwanta, Mandiya,Basma,Biba da Salma gado ɗaya suka kwanta, inda Salma tayita tsoki wai ita bazata haɗa jiki da su ba nan Mandiya ta taso mata kamar zasu bigi juna, sai da Garba yace duk wadda ta ƙara masu hayaniya zasu fiddata daga ɗakin sai dai ta kwana waje.

Nan Salma tayi zuciya ta sauko ƙasa ta baza ɗan figaggen gyalenta ta kwanta sama.

Bayan kowa ya kwanta wasu sunyi addu’a wasu kuma ko uho.

Cikin bacci Salma taji kamar ana lasar mata ƙafa, afirgi ce ta buɗe idanunta ta sauke su kan wata irin ƙatuwar mage baƙaƙirin bakinta wasu zara_zaran haƙora jini na ɗiga daga bakinta ga wasu irin idanu manya_manya masu ban tsoro, wata mahaukaciyar ƙara ta ƙwala da tayi sanadiyyar farkawar kowa daga bacci daya ɗauke su.

Ganin irin halittar magen ba matan kaɗai ba har mazan sai da hantar cikinsu ta kaɗa.

Garba kisane yayi ƙarfin halin shaƙe wuyan magen.

“Kuyi sauri ku buɗe mani ɗakin nan.”

Jafar ne yayi saurin buɗe ɗakin, Garba ya fita da guda magen na hannunshi a shage.

Sai dai kash! Daya san abinda zai iske a wajen bazaiyi gigin fitaba.

Kan Magen ya riƙa bugawa da ƙasa amma ko gezau batayi ba sai ma hannunshi dayaji kamar an daka mashi kaifaffar wuƙa, ihu ya ƙwala ya wurgar da magen yana duba hannun yaga ashe cizone ta sakar mashi a hannu, take jini ya hau zuba ba ƙaƙƙautawa, nufar hanyar gidan yayi zai shige, juyowar da zai yi yaga abinda ya kusa sanadiyyar tsayawar numfashin shi.

Magen nan ce ta rikiɗe ta koma wani basa muden Aljani jikinshi duk jini bakinshi wasu haƙora ne zaƙo_zaƙo irin na zombie, juyawa Garba kisa yayi da nufin komawa gidan horror ɗin yayo kanshi yana ƙoƙarin cizon Garba.

A tsorace Garba ya nufi ɗakin zai shige yana ihun su taimakeshi, ganin halin da suke ciki yasa su buɗe ɗakin, yana gabda shigewa ɗakin aljanin na kamo ƙafarshi mutanen daki hannuwan Garba suka kama domin ceton rayuwarshi, da kyar suka jawo Garba ɗakin suka maida ƙyaure suka rufe.

Nura ne ya lura Garba ba alamun numfashi a tare dashi, “kai Oga fa yabar numfashi ku duba ƙafarshi ga wani cizon nan ya ƙara samu.”

Rigar jikin shi suka keta suka ɗaure mashi ciwon, suna yi mashi firfita.

“Yau ni Rabi’u nashiga uku na lalace, wayyo kakata ƙila shikenan mutuwa ke kirana ita ta raboni da gida.”

Kowa ka kalla a ɗakin hankalinshi a tashe yake, yana tunanin makomarsu.

A hankali Garba ya buɗe adanunshi da suka yi mashi nauyi, ya sauke su ga ƙafarshi dayaga an ɗaure mashi.

Kwance wurin yayi sai dai abun mamaki ciwon ya warke sai dai wuri rauni yayi wani irin baƙi wasu jijiyoyi sun fito sun miƙe har wajen cinyarshi, kamar yadda jini ke gudana haka wannan baƙin abun ke gudana ajikin Garba kisa.

Sannu suka shiga yi mashi, baccin da basuyi ba kenan har gari ya waye.

Bayan sunyi sallah, nan suka shiga tunani abinda zasu samacikin su, kowa akayima maganar yafito su tafi naiman abinda zasu sama cikinsu sai ya noƙe yaki fitowa.

Daga ƙarshe dai Jafar da Biba suka ce su zasu fita su nemo.

Tunda suka fara tafiya basu samu komi ba ko bishiyoyin da zasu ciri ƴa’ƴan suci basu samu ba.

Ƙorama suka iske ruwa na gudana , tsayawa suka yi suka sha ruwan suka ɗibar ma sauran wanda zasu sha.

Sunyi tafiya kaɗan suka fara hango wata bishiyar kwaba a gabansu tsayawa sukayi.

“Kin ga dai tun ɗazu bamu samu komi ba duk yawo da mukasha, yanzu ni zani hau in tsinko ke kiriƙa ɗaukewa.”

Haka kuwa akayi sun ɗibi mai yawa suka nufi hanyar komawa wurin abokan tafiyarsu.

Kowa yayi murna da samun abinda zasu sa ga bakinsu banda Salma da ta ce ita tafi ƙarfin cin gwaba, babu wanda ya matsa mata taci cikinta ne inma bataci ba.

Shawara suka yanke su ƙara kwana nan in Garba ya ji sauƙi sai su cigaba da tafiyar.

Dare yayi sosai kowa ka gani yasha jinin jikinshi yana tunanin abinda zai faru.

Garba tunda lamarin nan ya faru jikinshi ke rikiɗewa yana komawa baƙi, amma bai sanar da kowa ba.

Zaune yake ya sadda kanshi ƙasa kamar mai bacci, lura abokan tafiyar sukayi kamar Garba yabar motsi, audu ne yayo kanshi da sauri dan ganin halinda yake ciki, ya isowa jikin Garba na ida rikiɗewa ya koma green da baƙi.

Duƙawa audu yayi dan ganin mike faruwa da Garba.

Shak’arda Garba yayi ma audu gwarama yasanya ƴan ɗakin fara iface_iface ganin yadda kaman nin Garba suka chanza.

Rabson guy tsabar firgici sulalewa ƙasa yayi ya sume.

Garba da yatsunshi da suka zama zaƙo_zaƙo ya dakama audu su a wuya ya wurgar dashi ya bugu da bangon ɗakin ya faɗo ƙasa ba alamun numfashi atare dashi.

Garba juyawa yayi yai kan Salma da tayi mutuwar tsaye hada fitsarin dole yai wani irin kukan kura wanda seda ilahirin dajin yayi amsa kuwwar da ’ya’yan cikin kowa suka kad’a…….

Sake kallon Salma yayi akaro na biyu tare dayi kanta a guje.

Tamkar yunwa taccen zaki haka Garba yayo kan Salma gadan_gadan, tsabar tsoro ko motsi takasayi ta rufe ido tana sauraren mutuwar data nufota.

Ganin halin da ake ciki yasa Jafar yin kabbara ya ya ɗauki wani katako yayo kan Garba kisa gadan_gadan, sai dai kafin ya iso Garba yayi nasarar shago Salma ya fara gama kanta da bango, tsabar azaba nan take ta suma.

Ya isa isowa daf da Garba yayi kabbara da ƙarfi ya ƙwaɗama Garba katakon nan a tsakiyar kan shi.

Take Garba yayi wata irin kururuwa ya faɗi ƙasa.

Salma da ana gwara mata kai da bango ta sume batare da tasan mike faruwa ba.

Biba da ke labe bayan kujera tana addu’a tana hawaye fitowa tayi jin abun ya lafa, Ganin Garba da tayi kwace ƙasa Kanshi jini na malala nan hankalinta ya ƙara tashi, abun mamaki jikin Garba lokaci ɗaya yayi wani irin fari fat! Tamkar babu jini jikinshi ko ɗigo, kallon_kallo Biba da Jafar suka hau yima juna.

“Biba yanzu ba lokacin kuka bane musamu mafita, ni fa gani nike mu haƙura da dajin nan mu zauna cikin gidan nan kawai in Allah yayi zamu fita shi zai kawo mana ɗauki da kanshi, soboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam daya ce in annoba ta samu gari to naciki su zauna a garinsu na waje kuma kar su shigo garin.”

“Nima ina da wannan tunanin Amma yanzu abinda ya kamata mu samu abokan tafiyarmu su farfaɗo sannan muyi gaggawar rabuwa da gawar nan, kaga fa yadda ta koma, ina tunanin barinta tare damu kamar wani haɗari ne babba.”

“Maganarki haka take, yanzu bara mu fara shafa masu ruwa su farfado mujita bakunan su.”

Wurin Audu gwarama suka fara zuwa sunyi sa’a suna shafa mashi ruwa a fuska ya ja a jiyar zuciya yana mai shafa wuyanshi dake mashi tsananin zafi, shi ma dai_dai in da Garba ya yakusheshi wurin ya fara green da baƙi.

Sannu sula riƙa jero mashi yana amsawa.

Wurin Salma suka matsa ita ma tana nan kwance tamkar gawa.

Jafar dubar Biba yayi yana mata magana a hankali yadda in ba kusa kake dashi ba baza kaji mi yake fada ba.
“Biba Salma kinga mace ce bai kamata in tabata ba ke yaka mata ki fara duba inda Garba ya buga mata kai ki kiyi addu’a nasan a firgice zata tashi saboda halin firgicin da ta shiga,sannan ki shafa mata ruwa a fuska.”

A hankali ta fara buɗe idanunta ta sauke su kan Biba dake tsugune kanta.

“Nashiga ukku ni Salma! Yanzu shikenan nima horror zani zama, wayyoh daddy na danabi shawararka da yanzu ina gida zamana, yanzu gashi na kawo kai na ga halaka.”

“Aa Salma Garba bai cijeki ba, ya dai bugaki da bango yayi sanadiyyar sumanki.”

Tamkar wata ƙaramar yarinya haka Salma ta maƙale jikin Biba tana kuka.

“Addu’a zakiyi ba kuka ba Salma, a wannan halin da muke ciki addu’a kaɗai ce magani, kuka bazai amfane mu da komi ba.”
Biba ta faɗa tana ɗora hannayenta a kafaɗar Salma.

Audu lura yayi da halin da Ogansu ke ciki.

Da gudu ya rugo ya rungume Garba yana mai fashewa da wani irin kuka, “Oga shikenan katafi ka barmu cikin wannan halin, Oga ji nike dama nine na mutu na huta ba kai ba, haka muma zamuyi ta mutuwa ana kashemu ɗaya bayan ɗaya, ina nadamar yin Baƙar tafiyar nan yanzu nasan nayi bankwana da kakata.”
Kukan dayaci ƙarfinshi yasa maganarshi sarƙewa.

Jafar ya iso wurin Garba ya rabashi da gawar yana bashi haƙuri, addu’a ce kaɗai zata kawo masu mafita.

Lura sukayi da abokan tafiyarsu babu Mandiya da Nura shila da Basma.

Sun bincike ko ina amma basu gansu ba.

Ɗakin farko sukayi shawarar buɗewa ko ciki suka buya.

Sai da suka haɗa ƙarfi wurin buɗe ɗakin, Ɗakine mai yalwar faɗi ba laifi, sai dai tsananin duhun ɗakin ya hana ka ga mike ciki, motsin da suka jiyo ne ya sasu juyowa a razane, Nura shila da Basma suka gani ƙarƙashin wani bencin katako sun boye ganin su yasa suke ƙoƙarin fitowa.

Bayan fitowarsu Biba ta fara magana, “Sanin haɗarin da muke ciki yasa daga yanzu ko wani bala’i ya samu ɗan uwanmu kada wanda ya ƙara ƙoƙarin guduwa ya rabu da sauran.”

Kowa yayi na’am da wannan shawarar

Ɗayan ɗakin suka buɗe, buɗewarshi tayi dai_dai da bugawar zuciyoyinsu kallon_kallo suka fara yima juna, wannan ɗakin yasha banban da saura, saboda shi wani abun mamaki babu duhu acikinshi, kayan wasane na yara birjik aciki, su kansu kayan wasan in ka kallesu sau ɗaya bazaka ƙara ba saboda abin tsore, daga ɗiyar robar da aka cirema hannu ɗaya tana hawayen jini sai wadda ta cire kanta ta riƙe a hannu tana murmushi haƙoranta duk jini, wadda tafi masifar tada masu hankali wata ɗiyar babyce girmanta ya kai na jariri, zaune take jikinta jar riga ce hanta gashi ya baje ta ko ina baka ganin ko fuskarta, ga wasu irin wuƙaƙe a hannunta duk jini ya bata su, kallo ɗaya zakayi mata ka ɗauke kanka.

Wani yawu Rabson guy ya haɗiye ji kakw ƙut! Da yayi sanadiyyar juyowar abokan tafiyarshi, sun naimi Mandiya lungu da saƙo sun rasa, motsi suka jiyo bayan ƙyaure, ƙin leƙawa sukayi kowa jininshi kan akai fa saboda tsoron dake ɗawainiya dasu.

Jafar ne yayi ƙarfin halin yawo ƙyauren, tsaye take tayi labo bayan ƙyauren jin an jawo ƙyaure yasa ta fara junduma ihu, “wayyoni Mandiyar uwar daba yau nakawo kai na ga halaka, Magaji kin cuce ni da kika bani shawarar zuwa garin Kaika zo! Ashe ajali ke kirana a wannan BAƘAR TAFIYAR, nashiga ukku na balbalce.”

“Buɗe idonki ki gani mune fa abokan tafiyarki.”

Jafar ya faɗa yana mai bata hanyar wucewa.

Idanu ta buɗe danjin muryar abokin tafiyarsu.

Shawara suka yanke suyima gawar Garba sallah su binneta.

Ruwan da ya rage masu suka yi alwallar dasu, sun gama sallar sun fara gina zasu binneshi wani baƙin hayaƙi ya bayyana ya ja gawar Garba suka bace a tare.

Nan fa suka ɗiba aguje suka koma gidan suka rufe masu kuka nayi masu addu’a nayi.

Basma kuka take tana sambato ita kaɗai, “Allah sarki masoyina kuma mijina habibina, dana bi shawararka da yanzu ina gida amma haka na nace dole sai naje bikin Hajara, Allah ya isa tsakanina dake Hajara ke kikai ta turani ina ma habib rashin mutumci, yanzu gashi nan na baro ɗana mijina yana fUshi dani nasan mutuwa zaniyi.”

Babu wanda ya rarrasheta koya bata hakuri domin kowa ta kanshi yake.

Nan suka faɗama sauran abokan tafiyarsu shawarar da suka yanke ta barin wannan gidan su ƙara gaba, amma ba haka ya kamata suyi ba, kamata yayi su zauna suga yadda zata kasance.

Wasu sunyi na’am wasu kuma sun bada shawarar abar gidan, sun yanke shawarar zasu bar gidan in gari ya waye.

Duhun dare ya fara kowa hankalinshi ya ƙara dugunzuma, kingin Gwaibar da ta rage masu suka raba suka fara sha, Salma tun kafin azo kanta ta warci biyu ta faraci.

Dare yayi sosai dajin babu abinda kakeji sai kukan tsuntsaye da wani irin iska mai bada wani firgitaccen sauti in ya haɗu da kukan tsuntsaye.

Mandiya, Basma, Biba da Salma yau gado ɗaya suka haye ba zancen nuna ƙyama yau Salma.

Mazan suma wuri ɗaya suka dunkule.

Bacci ma in kaga kana yin shi to baka shiga wani bala’in ba kokoma sai dai in bacci barawo ya sace ka.

Duka ɗakin kowa manne yake da ɗan uwanshi,idosu biyu sun kasa bacci gudun abinda zai biyo baya.

A hankali tagogin ɗakin (Window) suka fara buɗewa da kansu, jikake kit!_kit! Taga ta bude da kanta, karar da sukaji ce ta maido hankalinsu ga abinda ke faruwa.

Dirowa sukayi daga gadon suka cibre wuri ɗaya jikinsu na kyarma, duk wannan halin da suke ciki addu’a ce bakin Biba sabanin su Salma da suka fara kuka.

Ƙofofin na ida buɗewa wani farin hayaƙi ya fara shigowa yana dunƙulewa wuri ɗaya.

Yana gama haɗewa wuri ɗaya wata irin halitta Mai suffar kare ta bayyan, jikinta ko ina hannuwa ne idonta guda ɗaya ne a tsakiyar goshi, ga bakinta wagege da haƙora masu matuƙar tsini.

Dariya halittar ta kece da ita wadda ta haddasa ma ɗakin girgiza.

“Kunyi kuskure bil adama masu taurin kai da gadara, yau kwananku ya ƙare, a sannu zaku baƙunci lahira.”

Jafar yayi ƙarfin halin fara magana.
“Ƙarya kike yake wannan la’anannar halitta, ke baki isa ki kashemu ba sai dai in kwanan mu ya ƙare ubangiji ya rabuta zamu mutu yau, amma badai ke ba.”

“Hahaha! Gaskiya wannan bil adam jarumtarka ta burgeni, amma kayi kuskuren faɗa da ƴar tsito ƙaramar aljanu kuma shaiɗaniyar cikinsu, yanzu zani shanye jinin jikinka inyi gunduwa_gunduwa da naman jikinka.”

Tana rufe baki tayo kan Jafar da mugun nufi a cikin zuciyarta.

Abun mamaki kafin ta ida isa wurinshi sanadiyyar addu’ar da yake ya bace ma ganinta nan ta hau dube_dube amma babu shi babu alamunshi.

Ganin haka ya sanya ta wawuro ƙafar Basma, ihu ta hauyi itama ta jawo ƙafar Rabson guy, shima ci gaba da ihu yayi “wayyoh kakata wayyoh ɗan bunsuruna yau nayi bankwana daku, mutuwata ta iso.” cikin zafin nama shima ya damƙo ƙafar Salma, ita ma bata tsaya bata lokaci ba ta jawo ƙafar Audu, Nura shi ya riƙo hannun yana ƙokarin cetonsu.

Ganin halin da ake ciki ya sanya Jafar shammatar Aljanar yayi tsalle ya bankata ɗaki ya mai do ƙyaure ya rufe.

Gidan suka buɗe kowa yayi ta kanshi.

Gudu suke wanda su kansu in akace zasu iya yin shi bazasu yarda ba.

Gudu ne gudun yada ƙanin wani kowa ta kanshi yake.

duk gudun da suke a haɗe suke ɗayan su bai yarda ya rabu da ɗan uwanshi ba.

Gudu kawai suke amma basu san inda suke nufa ba, har sai da asuba tayi sannan suka zube suna mai da wani wahalallen numfashi.

Wata azababbiyar ƙishirwa ce ta taso masu, sanadiyyar gudun da suka sha, shawara suka yanke in safiya ta idayi sunemi ruwan sha.

Safiya nayi suka ƙara nausawa cikin dajin naiman ruwan.

A hankali jikin Audu gwarama yanata komawa green da baƙi, amma babu wanda yasanar halin dayake ciki.

Wani irin ruwa ne mai mugun fadi da yalwa gashi wucewa yake da mugun guda, suka iske a gabansu.

Nura har gudu yake ya isa ga ruwan ya sha saboda ƙishin daya addabeshi.

“Aa Nura kada ka sha ruwan nan ban yarda dashi ba.” Jafar ya faɗa yana ƙoƙarin tsaida Nura.

“Ya zaka hanani in sha bayan kasan babu abinda muke buƙata yanzu kamar ruwa.” ida gangarawa yayi cikin ruwan ya duƙa ya kam fato da hannuwanshi zai kai baki.

Wasu dogayen hannuwa ne suka bayyana suka, suka yo kanshi ganin zai fita daga ruwan hannuna nan suka fizgoshi suka nutsar dashi cikin ruwan yayi gaba dashi.

Tsabar tashin hankali su Jafar ƙara nausawa cikin jejin suka yi da azababben gudu…

<< Bakar Tafiya 1Bakar Tafiya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×