Skip to content
Part 12 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Ahankali iskar da ta kwasosu ta fara lafawa.

Tare da 6acewa 6at! Tamkar bata ta6a wanzuwa ba.

Hannu Jafarne ya fara motsi, idanunshi suna ƙoƙarin budewa, samun kanshi yayi da furta, “
ALHAMDULILLAHILLAZI AHYANA BA’ADA MA AMATANA, WA ILAIHINNUSHUR”

Kanshi daya ji yana barazanar tarwatsewa ya dafe yana Ambaton “INNALILLAHI WA’INNAH ILAIHI RAJIUN, ALLAHUMMA AJIRNI FIYMUSIBATI WA’AKLIFINI KHAIRAN MINHA Ya ubangiji ka kawo mana ɗauki akafitar damu daga wannan musiba.”

Dubanshi yakai inda su Basma ke kwance basu san mike faruwaba.

Abinda idanuwanshi suka hasko mashi ya sanyashi idan miƙewa daga kwanciyar da yake yayi saurin zaunawa, hannuwanshi yakai kusa da idanunshi ya murza idanun yaga kodai gizone suke mashi.

Ƙara tabbatar wa yayi ta hanyar tsinkulin kanshi yaji kodai mafarki yake, da gaskene su Rabson ne ba gizo idanuwanshi keyi mashi ba.

Wani farin ciki marar misaltuwa ya wanzu azuciyarshi baisan lokacinda ya kalli alƙibla yayi sujadar godiya ga Allah daya bayyanar masu da abokan tafiyarsu.

Motsin dayaji ne ya sanyashi saurin juyawa.

Su Basma, Jamcy da Tk ne yaga sun farka lokaci ɗaya suna dafe kansu dake masu tsananin ciwo.

Rabson ne ya fara harba ƙafarshi saman wuyan Salma, ita ma motsi ta fara alamun zata farka Kulu da Nas suma farkawa sukayi.

Rabson waige_waige yafara kamar yana naiman wani abu, su Jafar daya hango yasashi fara ja da baya yana salallami.
“INNAHUMIN SULAIMANU, LA’ILAHA ILLALLAHU_, ku kuke ganinmu bamu muke ganinkuba,wayyo namutu na lalace, shikenan gasunan sunzo mana da suffar abokan tafiyarmu, wayyoh Salma masoyiya kina ina”

Ya ƙarashe maganar yana janƙugu yana baya_baya.

“Hhh! Kai Rabi’u Rabson ɗin Kaka, munefa da gaske ba horror bane.”
Jafar ya ida maganar yana dariya.

“Mtssw! Sauna kawai, kabi ka cika ma mutane kunne ko ina kaga horrorn.”?
Salma ta faɗa tana hararar Rabson.

Wiƙi_wiƙi Jafar yayi yana rarraba ido.

Gaisawa sukayi ta yaushe rabo, bayan sun gama shan hira da taya juna jimamin rashin fitarsu wannan baƙin daji.

Shawara suka yanke ta yanzu bazasu ƙara tafiyaba gudu zasuci gaba dayi sallah da abinci kaɗai zai tsaidasu.

Matsawa sukayi wurin wani iccen gwaba suka tsinka, Jafar ne yafara rarrabama masu.

Salma gani tayi Jafar bai kawo kantaba, miƙewa tayi a fusace ta bangaje Jafar gwabar ta 6are ƙasa, taga_taga Jafar yayi zai faɗi ya tsaya, wani icce ya kama ya riƙe yana mamakin halin irin na Salma.

Salma gwaibar ta hau tsinta tana tattarawa, tatss! Kake ji Biba ta ɗauke Salma da wani irin gigitaccen mari.

“Tabbas rashin tarbiyya da rashin sanin darajar ɗan adam babban ciwo ne, ke yanzu in banda bakida wayo wanda yakasance shine jigon tafiyarmu shikike bangajewa?, ke kowa baki ɗaukarshi da mutumci kin raina kowa, sakara wadda batasan indake mata ciwo ba.”

Zafin marin da Biba taima Salma ya sanya ta zunduma mata duk wani irin zagin dayazo bakinta tana faɗar in suka koma gida saitasa anɗaure Jafar da Biba.

Haukan da Rabson yaga Salma nayi yasanyashi fashewa da dariya tareda tashi ya kamo hannunta.

“Haba Sweet Salma ta Rabson na Kaka da Busurulle!, miye nasa ke bakida hankali da kuma wayo, ya kamata fa kisan yanzu tare kike da mijinki, kisan abinda zaki faɗama mutane kowa da kika gani yanada rana fa.”
Ya ida maganar yana dariya.

“Ba’a sani, inka ƙara kirana da matarka saina samu dutse na rotsa maka kai dashi, mtssw aikin banza kawai.”
Ta ƙarashe maganar tanajan dogon tsoki.

Kowa banza yayi da ita suka haushan gwaibar su.

Biba dasun haɗa ido da Jafar saisu sakarma juna zazzafan murmushi ta sadda kai ƙasa.

“Abokai kamar yadda na faɗa maku yanzu bazamu sake tafiyaba, gudu kawai zamu riƙayi daga sallah sai cin abinci zamu riƙa tsayawa.”

Oga Rabson wandonshi inna tayani cirewa ya nannaɗe suka fara gudu ba kama hannun yaro.

Gudu suke irin gudun da ake kira gudun yada ƙanin wani, yunwar cikinsu ita ta tsaida gudun da suke, tsayawa sukai suna maida numfashi.

“Wayyoh Momy, Daddy ina bataliyar sojojin da nike mafarkin ka turo afiddani adajin nan.”?

“Hhh! Shegiya ƙarya, ko gidan wane baban ne zakiga wata bataliyar sojoji, nabi bataliya da gudu, bataliyo.”
Ya tuntsure da dariya.

Jikin Basma a hankali yake komawa green da baƙi tana canza kala.

Nan suka tsaya suna hutawa.

Motsi sukaji alamun tafiyar mutane Nufo inda suke.

Zumbur suka miƙe tare da cibrewa wuri ɗaya suna jiran bayyanar abinda ke tunkarosu.

Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu yasa su ƙara dunƙulewa wuri ɗaya.

Garba kisa, Nura shila, Audu gwarama da Mandiyane suka nufosu da wasu irin wuƙaƙe a hannunsu.

Cikin Salma wani irin sauti yabada ƙuu.

Ganin wannan bala’i yasanya su Jafar da Biba fara ƙwararo addu’a.

Wani wawan tsalle sukayi tare da rabuwa suka yimasu Rabson ƙawanya.

Harshe suka riƙa fiddowa tare dayin wata kuwwa marar daɗin saurare.

Tuni Rabson ya maƙalƙale jikin Jafar ya fara kuka yana sabbatu.
Tsawar da Jafar ya Ƙwatsama Rabson ya ɗora da faɗar;
“Yanzu lokacin yaƙine domin a ceci rayuwa, tabbas yanzu lokacine da kowa zaiyi takanshi kuma zaiyi ƙoƙarin ceton rayuwarshi domin in Allah ya ƙaddara musamu ko mutum ɗayane ya kai labari.”

Bashakka jin wannan maganar jikinsu yayi sanyi sun sadaƙar zasuyi faɗa su mutu ko suyi rai.

Garba Jafar ya warto da nufin ya luma mashi wuƙar hannunshi, kokawa suka hauyi da Jafar bakinshi ɗauke da addu’a.

Nura Rabson ya jawo, Rabson naganin haka ya jawo ƙafar Salma suka tai tare.

Rabson baisan yanada ƙarfi ba sai yau dayaga mutuwa tsirara, yaga ya dage yana kaima Nura naushi ta kowane 6angare.

Kulu da Nas tare Audu ya fizgosu, Kulu itace mai ƙoƙarin ceton rayuwarta tasa ƙafa tana kaima Audu duka ta ko ina.

Su Jamcy da Tk su biyun sun bada himma suna zabga kabbara suna ƙoƙarin ceton rayuwarsu.

Bashakka wannan yaƙin na ceton rayuwa yazo da abun mamaki, domin duk da su Garba sunjima kowa ciwo da makaman hannunsu amma haka suka dage.

Wata ƙaƙƙarfar guguwa dasu Rabson sukaji ita ta sanyasu zubewa ƙasa, mahaukaciyar ƙara Rabson ya ƙwala ya dafe hannunshi da Garba yayi sanadiyyar gutulema Rabson ƙaramin yatsan hannunshi.
“Nashiga ukku sun maidani gundul sun guntule mani yatsa, wayyoh Kaka wayyo Salma masoyiya, Wayyoh ni Rabi’u nakoma Rabson gundul na busurulle.”

Wannan guguwar ta kwashe su Garba kisa tayi sama dasu…….

<< Bakar Tafiya 11Bakar Tafiya 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×