Skip to content
Part 1 of 7 in the Series Barrister by Maryam Ibrahim

Ya Allah abinda muka fad’a daidai Allah ka k’aramana fahimta abinda muka fad’a ba daidaiba Allah ka gyaramana.
Wannan littafi labari ne me salo daban-daban labari ne me d’auke da izza mulki girman kiyayya rashin tausayi zalunci da kuma madarar soyayya.

Bismillahir Rahmanir Raheem.

*****
Wani fillin jirgin sama ne na garin Abuja wani jirgi yasauka abinda nafara gani shine wani haɗɗaɗen matashin saurayine me jini a jiki ya fara tako wa yana sauka tundaga samansa harƙasa nakare masa kyakkyawane ajin farko. Farine yana da kewayayyiyar fuska da saje idanunsa manyane yanada faffaɗan ƙirji ta ko ina ya haɗu bashida makusa.

ƴan mata suna sonshi duk in da ya shiga kowacce ƴa tana sonshi wasu ko hotone suyi da shi, sai dai muce masha Allah don BARRISTER ya haɗu ba irin wannan mazajen da kika saba gani bane, ko jin labrinsu no wanna shi na mussaman ne.

Tafiya ya keyi har ya sauka ƙasa yan jari da suka ƙaraso suka mishi ca suna tambayarsa irin nasa rorin da yasamu a England, be kulasuba yashigesu tare da faɗawa mota sabida shi irin mutanan nan ne da basa son hayaniya kuma miskiline ajin farko.

Yana shiga sojojin da ke bayansa suka rufa masa baya suka wuce…

Wani kayataccen haɗaɗden gidane hmm Masha Allah, (Da naga wannan nace anya a Nigeria aka gina sa) Gidan babba ne ya haɗu ta ko ina, tun daga bakin gate har zuwa sauran guraren, wani kayataccen gurin shakawatawane wanda aka kawata shi da kayan alato kala-kala ta gefen sa kaɗan swimming pool ne me kyau gabansa can guri ne dazaka motsa jikinka.
Duk wannan waje ne bamu shiga ciki ba horn akafara da sauri Baba me gadi ya mike y wangale katafaren gate, nan suka shigo ya yi parking a hankali yake fitowa daga cikin moton har yaƙarasa fitowa, ɗaya daga cikin sojojin nan ne yake binsa da briefcase suka shiga cikin wani karamin gate haƙiƙa nayi mamaki ashe can wajene nanne ciki inda komae ya ke swimming pool gurin motsa jiki daidai saraunsu tafiya suke har suka karasa shiga cikin fallon, Wow abinda nace kenan fallone ya ƙawatu da kayan alatu komai na cikin Fallon sky blue ne…

“Aa maraba BARRISTER na ai sai kamin waya naje airport da kaina na taho da kai.” “Aa Mom gara dai namiki surprise dan nasan za ki ce za ki je nikuma gaskiya banason kiringa wahala.”

“Ka jika airport ɗin ne idan naje zan wahala? “Yesss Mom” Hmm “Son kenan baka da dama karasa ciki ka watsa ruwa dan nasan ankwaso gajiya” “Ok Mom ya miƙe ya haura sama ɗakine guda biyu a wurin kowane yana kallon gefensa ya shiga ɗaya daga ciki abin mamaki komai na fallon Sky blue ne lalle wannan guy yana son wannan kala
yana shiga ya cire kayan jikinsa yasa na wanka yashige privency don yin wanka, shiru-shiru be fitoba saida ya ɗauki 40 minutes kafin yafito da tawul ya ɗaure a girjinsa ya iso mirror yashafa mayuka kala 4 hmm turare kan yakai kala 10 wanda yashafa masha Allah, barrister Yazid ka haɗu nace ba dole yan mata suyi hauka akansaba.

Wasu ƙananun kaya ya fitar yasa masu taushi da kyau wando jeans ne dark blue da riga Red yafito ya yi kyau.

Tafiya ya ke har ya isa bedroom “Mom… Mom na kammala shirina” “Wow son ka haɗu sosai” “Really Mom? Yess to muje kaci abinci” “Ok Dad fa” y?”Yana hanya zuwa anjima zai ƙaraso.”

Dinning area suka nufa yanda aka jera kayan abinci ya fi kala 10 wani abincin ma sai dai a ta6a kaɗan a bar sauran dayake shi Yazid bawani me son cin abinci bane kaɗan yaci ya miƙe “Mom Bari naje na kwanta nasamu hutu” “Ok a fito lafiya.”

“Wata mashiyar budurwa ce wanda ashekaru bazata haura 22 years ba, cike da shagwa6a tace “Mommy Yazid ya dawo yau na ji labari don Allah kitaimakeni mommy kisa abbana ya aura minshi in ban auri yazid ba komai zai iya faruwa zan iya kashe…”

“Karkisoma na miki alk’awari in dai barrister Yazid ne sai kinmallakeshi koda kuɗina gwalagwalaina zinarina zai ƙare sai kin mallakeshi keɗin ta Yazid ce.”

“Shiyasa nakeson ki Mom har hankalina ya kwanta Mom anjima zanje shagon gyaran jiki da makeup da saloon inaso naje naga farincikina Yazid yaƙara kyau ya ƙara girma kinsan tun ina 17 years ya tafi” “Ok Doughter” “Zanje super market na za6a kaya me kyau” “OK kiɗauki card ki je Kiyi anfani da duk abinda kikeso” “No mommy akwai kuɗi a gurina.”

“Aa daughter ki ajiye na ki kiyi anfani da nawa” “Ok mommy na gode” “Amma daughter kinada da kayan sunfi kala 30 baki ta6a sawaba kuma naji kince za ki je super market sayen kaya? “Yesss mommy kin san komai na yazid na mussaman ne” “ok” “Bari na shirya na fita”….Adawo lafiya” cewan mommy…

*****

“Ke Nadiya kina shigamin ido kin rainani kinsan duk wani iskanci da rashin mutunci da kkyi a tafin hanuna Kk sbd kinsamu dama toni barrister yazid ba tsararkibane dan haka kima kanki kafin na dau mataki Akanki”

ya huce ya barta a hurin

“ka mallam dakata karga inasonka kace zakamin rashin mutunci toni Nadiya nafi karfin amin rashin mutunci kuma saina gaya ma daddy irin abinda kk min.”

“alright je ki fada sai na tattakeki na karya kasusuwanki”

“saide ka yi ma wani amma bani ba.”

mamakine yakamashi irin rashin kunyar da Nadiya keyi masa

Itakuma tunani take ko ya aure bazata bari ya rainata ya mata hulakanciba

Kai Nadiya meyasa ma kk tsaya kike bashi amsa ai kamata yayi ki kyalesa inya gama surutunsa kimasa shiru tunda yanzu damuwanki shine ya amince ya aureki inde ya aureki shikenan koma menene saiki masa..
Hmm kuma fa hakane cikin wani irin mayaudariyar taku ta isa garesa

“Yaya yazid kayi hakuri”
muje ko?

Mamakine ya kamashi tunda yake da Nadiya bata ta6a masa abu tace yayi ba amma saiya basar ok nahakura ya huce fuuu tabi bayansa atare suka isa.

Wata mashiyar yarinyace wacce a shekaru baza ta haura 16 years ba zataje islamiya tana tafiya ahankali kamar wacce kwai yaface mata aciki.

Tana tafe tana tunani yanxu a ina zan samu kudin daza aewa mahafiyata jinya yan uwanta duk sunki taimakamin yazanyi da rayuwa ta.

Tana tafe a haka har ta karaso gidan su aminiyan nata wato Aisha assalamu alaikum wa alaikin salaam cewan maman Aisha Aisha dake zaune tana kokarin goge saman takalminta ta dago kae taga Zahra tayi mata sanyayen murmurshi aa Zahra har kin shirya eh aisha na kammala to muhuce kibarta mana nasa mata abinci taci saiku huce cewan maman Aisha aa umma nagode na kwashi a gida ko kinkwashi ki kara umma cikina zai fashe kinjiki nasan bakya son cin abinci annan ne aa umma bahaka bane to ya yane hmm tayi murmushi ta tsuguna ta dau kwanun abincin tafara ci kadan taci tace ta kwashi dama ita ba irin mutanine masu san cin abinci sosae ba kuma gsky asalima a gida bawani cin abinci tayi ba garin kwakene wanda tasiya da kudin da abba yabata shekaran jiya naira dari 300 saitayi dabara tasiya garin kwake na 200 sugan 70 kulikulin 30 Allah sarki baiwar Allah shitake jikawa taci safe rana da dare wata rana in tazo gidan su Aisha umman Aisha ce take bata abinci da kyar take ci duk da mahaifiyar Aisha bawata me karfi bace amma tafisu rufin asari tasan rayuuwar Zahra da mahaifiyar sukeyi kuma yarinyan tana da tarbiya iya gwargwado ga girma ma Manya Allah kasa mudace tana zaune akan karamin kujeran da take zaune ta tsinkayo muryan Aisha tana cewa kinsan malam Hassan yanxu saiyace zai mana bulalan latti kuma kinsan bulalanshi da zafi ni wallahi tsoranshi nakeji sosai kinsan ni banason bulala tayi sauri mikewa tana me cewa umma sai mundawo adawo lfy to kitsaya mana muhuce a tare matsoraciya daga jin mgn bulala ta mike ta sauri hmm Aisha kenan aikin fini tsoro haka kkce ko to zamu gani in antare mu latti zaki yi raurau da ido malam kayi hakuri umma nikan na tafi ai dasauri Zahra tabiyota suka jera suna tafiya a hanya Aisha sai tsokanan Zahra take wai me tsoron a ta6a mata jiki da bula la
Suna tafe suna hira suna tsokanan juna har suka shiga makaran ta Allah ya taimakesu saura minti biyar afara tare latti suka shigo direct class suka huce
Suna isa Zahra ta dauko alkur aninta tafara karan tawa da zazzakan muryan ta me dadi n sauraro sunkai minti tallatin saiga malamin dayake musu karatun al qur, ani yakaraso duka class suka mike suka gaishesa ya basu kafin yace su zauna haka kuwa akayi bayan Sun zauna ya ce subiya karatun su na jiya da ya musu kari kowa yatashi ya biya nasa saura zahra itama tabiya kuma duk tafisu iyawa yaji matukar dadin karatun yarin yan ya dauko sabon dari 200 yabata taki kar6a da kyar takar6a sanda ya6a kafin
Takar6a ya musu kari ya fita daga class din malamin fikhu ya shigo shima minti 40 kamar yadda kowani malami yake yi a a haka har aka tashesu kowa ya koma gida.

Bangaren su barrister yazid shagali ake Gudanarw sosai.

Barrister yazid muna barka da dawowa abinda aka karanta Allah yabada ikon tonight aiki dashi ka sance daya daga cikin lawyoyi masu gsky da amana masu kare hakkin mutani duk inda kk karike gaskiya da mana duk wanda yarike wannan abu biyu baya ta6a faduwa.

Kayi adalci karkabi bayan karya koda za a kashe kane aikin barrister yanada walaha yana da kalubale hakika duwaan yayi aikin barrister tsakaninsa da Allah yanada nashi babban rabo ranar tashin alkiyama.

Kasani cewa in kabi dokakin aikin barrister tun anan duniya bazaka ta6a wafintaba anyi barristertoci dayawa wanda suka rasa aikinsu adalilin gsky inaso kazama daya daga cikinsu.

Ngd barrister.

kowa sanda ya tafa ma barrister Abdurrahman.

Nayi alkawarin fara aikina da gsky da amana dakuma adalci bazan bama mahaifina kunya ba tun bankai haka ba yakeda burin yaga nazama barrister duk shi babban sojana amma yaza6a nazama barrister dakuma mahaifiyata gdy nakeyi muku da taimakonku yau nazama cikaken barrister ina alfahari daku.

Nadiya yane ta tataso da sauri zuwa inda mom take.

Hakika mom nayi farin cikin ganin yazid a yau yadda yake farin da murnar cikan burinku nazaman yazid a matsayin barrister.

Jiyowa mom tayi takale Nadiya

Ngd sosai Nadiya da nuna farin cikin ki akan yazid.

Barrister 2 >>

2 thoughts on “Barrister 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×