Skip to content

Kalubale kam an samu, amma ba daga gida ba sai daga marubuta ‘yan’uwana – S. Reza

Hikaya ta tattauna da matashin marubuci Salisu Adam wanda aka fi sani da S. Reza. A cikin wannan tattaunawa, ya bayyana mana abubuwa da dama da suka shafi gwagwarmayar da ya sha a harkar rubutu. Ga yadda hirar tamu ta kasance:

Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarka.

Amsa: Tom! Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Salisu Adam wanda duniyar rubutu ta sani da S. Reza. Ni haifaffen garin Benue Mokordi ne, amma mahaifina ɗan jihar Jigawa ne, hakan ya sa nima na tashi a can. Na yi karatu na a Jigawa wanda yanzu haka ina zaune a Benue, wato dai na dawo gida da zama tare da Mamana da Babana.

Tambaya: A wacce shekara ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinka har ka fara rubutun?

Amsa: To ina tunanin dai na fara rubutun littafin ne a shekarar dubu biyu da goma sha takwas (2018). Abun da ya ja hankalina shi ne, a lokacim da nake Jigawa a kwai wani abokina da yake son karatun littafi, to wani lokaci idan zai karanta littafin sai ya ce dole sai na zo na zauna a gurin nima na ji, wai a kwai daɗi. To ana haka nima na ɗan fara karatun ranar da ba mu da sabo kuma sai na ce ma, bari na gwada rubuta nawa. To tun lokacin dai zan ɗan saci wani abu daga cikin abun da muka karanta din, har yana min dariya cewar ba zan iya yin irin wannan rubutun ba, domin abun ba da ka ake yi ba, yana buƙatar natsuwa da ilimin abun. To tun dai ina yin shirme har na ɗan yi ƙoƙari, daga ƙarshe dai na haƙura, to sai da na dawo gida kuma Allah ya nufa na fara.

Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Eh! Littatafai dai waɗanda na fitar izuwa yanzu za su kai guda takwas ko tara haka, banda ƙanana da kuma wanda ban fitar ba. Ga su kamar haka:

  1.  So Ne
  2. Uwata Ce Sila
  3. Addininmu
  4. Ameera Da Adam
  5. Mutum Da Aljan
  6. Gidan Arna
  7. Rayuwar Gidanmu
  8. Chakwakiyar Soyayya

Wadannan sune littattafan da na fitar izuwa yanzu.

Tambaya: Wanne littafi ka fi so a duk cikin litattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?

Amsa: Gaskiya duk ina son littattafai na, amma wanda mutane suka fi so kuma ni ma zan iya cewa shi ne littafin da ya sa aka sanni shi ne littafin Uwata Ce Sila. Gaskiya littafin ya yi farin jini fiye da yadda na yi tsammani. So amma kuma ni littafin da nake ganin zafin so shine littafin Addininmu Domin labari ne wanda ya faɗakar sosai, ko ni sanadin wannan littafin na ƙara sanin abubuwa da dama game da Addininmu da ma addinin wasu, domin sosai na yi bincike da tambayoyi da shige-shige wajen sanin addinin Musulunci da na Kirista da ma wasu addinan, to Alhamdulillahi saƙo dai na tabbatar ya isa wurin da ya dace.

Marubuci S. Reza (Salisu Adam)

Tambaya: Shin kana da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?

Amsa: Eh! Tabbas ina da uwar gida wacce har gobe ina faɗa cewar ita ce ta dafa min a lokacin da nake neman wurin fakewa. Haƙiƙa na ƙaru da ita sosai, duk da cewar ba wai ta jani jikinta ba ne, amma dai Alhamdulillah ta min abun da wasu basu Amin ba. Itace Hafsat Garkuwa, marubuciyar littafin Taufikk.

Tambaya: Wanne littafi ne ka taɓa karantawa da ya fi burge ka?

Amsa: Gaskiya suna da yawa. A kwai shi wannan littafin na Hafsat Garkuwa wato Taufikk, sai littafin Uwa Uwa Ce na Batul Mamman, sai littafin Fulani na Khadija Candy da kuma Rayuwarmu na Lubna Sufyan, da dai sauransu…

Tambaya: Shin ka taɓa shiga wata gasa? Idan e ne amsar, shin ko ka taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?

Amsa: Gaskiya bana shiga gasa, a kwai dai gasa da aka taɓa yi a cikin ƙungiyar mu ne kuma na zo na ɗaya. Amma kwanan nan na shiga wata gasa da aka saka a group ɗin marubuta dake WhatsApp, gasar ta gwarazan hikayata ne da suka bada tukuici ga marubuta sai aka saka gasa. Wannan shi ne karo na farko da na shiga kuma tun a zagayen farko aka yi ɓarin makauniya da labarin nawa. Wanda duk wanda ke cikin ƙungiyar mu ta marubuta yasan naji zafin abun, har ake ce min saboda bana shiga gasa ne ya sa karon farko abun zai dame ni, gaskiya na ji zafi sosai, hakan ya sa yanzu na ɗaura ɗamarar shiga gasa ko wacce iri ce muddin babu zubar da mutunci. Maganar nasara kuma Alhamdulillah kullum cikin samunta muke yi, kuma muna fatan fiye da hakan.

Tambaya: Idan za ka yi rubutu, shin ka kan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye kake farawa?

Amsa: A’a nakan ɗauki lokaci ina tsare-tsare, dan wani lokaci ma sai na yi nisa a gina labarina a cikin kaina sai kuma na wargaje shi na sake sabon kamu har dai na tabbatar na samu abun da nake so kafin na ɗora alƙalamina.

Tambaya: Wacce hanya ka ke bi wajen samun jigon labarinka?

Amsa: Gaskiya ina bin hanyoyi da dama, ka ga wani lokaci na kan ɗauki wani ɓangare daga cikin littafin da na yi a baya sai na faɗaɗa shi, ko kuma na kalli wata matsala a zahiri sai na yi rubuta a kai, wani lokaci ma a cikin wani littafin zan samo nawa jigon, kuma ba tare da ya yi shige da littafin da na karanta ba, musamman littafan magabata.

Tambaya: Ya kake yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Ka kan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?

Amsa: Eh to wani lokaci nakan yi ƙoƙarin ganin na shigar da abun cikin shi littafin da nake rubutawa ɗin, idan har abun ba zai yi tsayi ba, wani lokaci kuma ina ajiye labarin ne har sai na gama wanda nake yi domin bana son haɗa aiki biyu gaskiya.

Tambaya: Ka kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kana bincike kafin ka fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ka tsawon wani lokaci kafin ka kammala rubutun littafin?

Amsa: Gaskiya abun da ya fi ɗaukar lokacina shi ne bincike da rubutu, yanzu zan iya yin wata biyu ko ɗaya ina yin bincike, dan wani lokaci ma ni kaina sai nake mamakin ko na fasa yin rubutun ne. Lokaci da zan fara rubutu kuwa tashin farko na kan yi da yawa domin kasan lokacin ina marmarin abun kafin na zo na fara tsaki. To zan dage na tara sosai, sai na tabbatar na kusa kammala littafi kafin na fara posting. Ina jin littafi ɗaya ne kawai lokacin da nake yin sa kuma nake posting ɗinsa shi ne littafin Uwata Ce Sila. Amma baya shi duk sai na kusa nake fara posting.

Tambaya: Wacce hanya ka ke bi wajen fitar da halayen taurarinka tare da basu sunan da ya dace da su?

Amsa: Babban aikin kenan. Da farko idan zan ba wa jarumai suna da kuma irin halinsa, to sai na tsaya na kalli a salin shi mai sunan, domin gaskiya ko ta suna ina iya isar da sako. So ina ƙoƙarin ganin na samu sunan da zai dace da mai halin.

Tambaya: Shin ko ka taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarka a cikin rubutunka?

Amsa: Eh na taɓa yi, amma ban fitar da littafin ba, in sha Allah zan fitar da shi da yardar Allah.

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka taɓa rubutawa?

Amsa: Idan ka ce wahala na sha fa. Littafin Addininmu da littafin Gidan Arna. Shi littafin Addininmu a kwai wani page da nake bayani akan yadda Kiristoci suke yin bikin binne gawa, to a lokacin da nake yin rubutun abun da bincike na ya bani shi ne wannan rawa da shan giyar da kaɗe-kaɗen duk addini ne, ashe kuma abun al’ada ce, to ko ni da na zo wurin sai da na ƙara tambaya aka tabbatar min cewar addininsu ne yazo a haka. To kawai ni kuma na barshi a haka. Ai kuwa bayan na yi posting sai ga tashin hankali daga gefe da gefe, wallahi ban taɓa tunanin ana bin wannan littafin haka ba sai lokacin, kuma fa har da Kiristoci masu jin Hausa, su suna bina ta laluma cewar ba addininsu ba ne al’ada ce, wasu kuwa zagi da cin mutunci, a taƙaice dai sai da na tsaya da posting ɗinsa har komai ya ɗan lafa. Sannan ta ɓangaren addinin Musulunci ma an samu haka wajan rabuwar ƙungiyoyi wai mai yasa na yi amfani da sunan fitattun munate. Wasu su ce hakan bai dace ba, wasu su ce ya yi, ni kuwa nasan dalilina na yin haka. Haka na toshe kunnena. Shi kuma littafin Gidan Arna, sai da na kusa kammala littafin sai kawai aka sace min waya, ban taɓa yin littafi mai yawansa ba, da kuma fuskoki daban-daban, amma na wayi gari babu sai page ɗin farko, wallahi sai da nayi kuka, na dawo kamar mara lafiya, a lokacin wata marubuciya ƙawata take cemin ka ga amfanin yin typing da posting a haɗe ko. Kai Allah sai da na kusa yin ƙaramar hauka, babu wanda zai gane irin abun da na ji sai marubuci wanda irin haka ya taɓa faruwa da shi, kai ko page ɗaya ne ya ɓata ya ake ji bare wajen page 97 kuma duk page ɗaya ina yin amfani da kalmomi dubu huɗu ko biyar. Gaskiya na ji haushi, amma daga baya na sake yin wani amma bai yi yawan wanc ba gaskiya, wannan duka kamar page 70 ne kawai.

Tambaya: Wanne irin ƙalubale ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ka bi har ka tsallake ƙalubalen?

Amsa: Umm! In ji mai ciwon baki. Ai maganar ƙalubale kam an samu da yawa ma kuwa. Amma ban samu daga gida ba sai daga marubuta ‘yan’uwana. Ƙalubalen da yawa amma bari na baku wani da ya faru kwanan nan ina ga ma sai kun yi dariya. A kwai wata marubuciya ba sai na kama sunanta ba, idan ta ga wannan hirar za ta tuna, ko din dama ba ta manta ba. Ƙungiyarmu ɗaya da ita, to sai na fitar da sunan littafin da zan yi na tura ƙungiyarmu, sai kawai ta ce wai ai wannan sunan ta ne sunan littafin kuma dole sai na sauya wannan sunan domin nasa sunanta da sunan babanta a matsayin sunan littafi. Na ce mata nifa littafi harma na gama rubutun sa, ta ce lallai fa sai na sauya domin wai ita matar aure ce kar na kashe mata aure. Na ce ta yaya zan kashe miki aure. Wai mutane za su yi tunanin akwai wani abu a tsakaninmu kuma gashi ƙungiyarmu ɗaya. A takaice dai ba ƙaramin rikici aka yi ba har shuwagabannin ƙungiya suka shiga na ce wallahi ba zan sauya suna ba. Da yake ta riga ni fara rubutu kuma ta riga ni shiga ƙungiyar sai ake ta ba ni laifi. Ni dai na ce babu wanda ya isa domin ni wallahi lokacin da nake neman sunan littafin na manta ma da wata mai irin wannan sunan. A taƙaice dai sai ta je ta haɗa kai da wasu ƙawayenta marubuta wai su ci min mutunci idan ban sauya suna ba. Sai wata daga cikin su wacce wallahi kafin abun ina ganinta da mutunci tai min magana wai na sake sunan littafin ko su yi littafi a kaina na zubar min da mutunci su nunawa duniya cewa ni ɗan iska ne, na ce mata duk abinda za su yi su je su yi wallahi ba zan sauya ba. Idan ka ji irin zagi da cin mutuncin da suka min akan dole sai na sauya, har wata abokiyar rubutuna mai suna Chamsiya D Amadu ‘yar ƙasar Niger ta ce wallahi na ɗau mataki akai, na ce ta barsu, iya abun da za su iya kenan zagi, shi kuma zagi mai tarbiyya baya yinsa, idan an masa ma shiru yake yi. Daga ƙarshe dai ban san me ya hana su fitar da littafin ɓatancin ba. Ni kuwa na rubuta littafi na fitar kuma na samu alkairi sosai a kan sa, duk da cewar labarin bai yi tsayi ba.

Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da ka rubuta wanne ka fi so, kuma me ya sa?

Amsa: Muhammad na cikin littafin Addininmu, saboda ya yi koyi da halin mai sunan wato Annabi Muhammad (S.A.W) wajen yafiya irin wanda ba kowa zai iya ba, sosai nake kwaɗayin wannan halin nasa.

Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin ka taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Sosai wani lokaci sai ka yi nisa a rubuta kanka ya ƙulle ko kuma ka ji rubutun ya fita a kanka. Ni dai hanyar da nake bi idan haka ya faru kawai na kan tsaya da rubutun ne na samu natsuwa, idan kuma kaina kullewa ya yi shi ma nakan tsaya bayan na samu natsuwa sai na ƙara yin bincike.

Marubuci S. Reza (Salisu Adam)

Tambaya: Mene ne abin da ka fi so game da rubutu?

Amsa: Ina so na ga ina rubutu a lokacin da abun ya zo min, wani lokaci ko aiki nake idan abun ya zo min sai in tsaya kawai na samu wuri na fara rubuta kayana.

Tambaya: Me ka kan yi a duk lokacin da kake da sarari?

Amsa: Eh idan a lokacin ina da typing to nakan yi ƙoƙarin yin rubutun, idan kuwa bana da rubutu to nakan ɗan bibiyi aiyukana na baya, ko na duba aiyukan wasu, ko na fara binciken littafin da zan fara.

Tambaya: Wace karin magana ka ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: Ana cewa ‘Daga baya kenan wai an harbi jaki daga nesa’, sai ya ce idan an isa a matso kusa mana. Ina son wannan karin maganar tun lokacin da aka min ita.

Tambaya: Shin ya ya bambancin rubutun fim da na littafi yake a wurinka?

Amsa: Shi littafi fa kai za ka tsara kayanka kai ɗaya, kuma a lokacin da kake so, shi kuma Fim wani lokaci kuna da yawa, wani lokaci kuma za’a dameka da cewar ana buƙatar rubutu za’a fara aiki, ko kuma a ce ga abun da ake so ka samar, to ka ga a banbancin a fili yake, nima ina ɗan taɓa rubutun Fim.

Tambaya: A naka ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?

Amsa: Ai yanzu zamani ya sauya, dafa kamar yadda Ado Gidan Dabino ya faɗa a hirar da aka yi da shi da Hadiza Gabon ya ce, “Da sai ka yi rubutu ka kai wurin dubawa sama da wata shida ko biyar har ma shekara. To yanzu fa, wasu a minti talatin sun yi page ɗaya kuma sun sake. Gaskiya rubutun online ya fi sauki yanzu a gurina Ni S Reza.

Tambaya: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?

Amsa: Idan mutum ya kama kansa zai samu girma ne kamar Malami da ɗalibansa, domin yanzu Alhamdulillah marubuta suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ba da gudummawa sosai a yanayin rayuwar da muka tsinci kanmu, na ga marubuta suna ta rubuce-rubuce akan yadda za’a samu ɗauki kuma al’umma suna amfan har suna fatan alkairi.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da kake rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Eh ina rubutu tun kafin azumi kuma na yi sanarwa a Facebook ɗina da WhatsApp status da group ɗina, amma ban faɗi sunan littafin ba sabo da tsaro, kuma ina sa ran ko bayan salla babba ko dai bayan azumi, saboda irin haka yasa ban sanar da komai a kan sa ba. Amma in sha Allah labarin zai zo da salo na ban mamaki mai rikitarwa da yardar Allah.

Tambaya: Wane ne tauraronka a cikin marubuta?

Amsa: Lubna Sufyan, Khadija Candy, Hafsat Garkuwa

Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da saƙo?

Amsa: shi fim kallo ake, shi kuma littafi karantawa ake, so ina ga kamar amsar a fili take.

Tambaya: Wacce irin shawara za ka iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?

Amsa: Shawarata gare su ita ce Wallahi mutum ya rubuta alkairi, kuma ya kama mutumcin kansa, sannan mutum ya tabbatar da ya yi bincike kafin fara rubutu, domin rashin yin zai iya sa mutum a cikin tashin hankali Allah ya kiyaye.

Tambaya: Mene ne burinka a harkar rubutu?

Amsa: Burina a kullum Allah ya tsare ni da rubuta abinda ba zai amfani al’umma ba, Allah ya shiga tsakanina da duk wani mugu ko mai nemana da sharri, ya sa na cika da imani na amfanar da al’umma da basirar da yayi min.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ka iya cewa game da Hikaya?

Amsa: Ma sha Allah, wannan kafa ta Hikaya Allah ya ƙara ɗaukaka ku, ya tabbatar da himmar ku, sosai muna moruwa da wannan kafa, kuma in sha Allah zamu ƙara zagewa wajen ɗora littattafai dukda cewar yanzu ma a kwai littafi na guda ɗaya a ciki, in sha Allah zan dage na ɗora sauran. Ina muku fatan alheri. S Reza

An yi wannan hira da Salis Adam ne a ne a ranar 21 ga watan Maris, 2024.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page