Gabatarwa
Rubutu abu ne mai matuƙar muhimmanci a wurin kowace irin al’ummar da take rayuwa a cikin wannan duniya. Irin muhimmancin da rubutu ke da shi ne ya sa kai tsaye ake danganta shi da ilimi, domin ya dace da shi ƙwarai da gaske. Duniyar rubutun labarai na ƙasar Hausa ba ta da faɗi sosai in aka ce za a kwatantata da irin na sauran manyan ƙasashen duniya. Domin ba a fara rubutun ajami a ƙasar Hausa ba har sai da Hausawan suka cuɗanya da Larabawa. Kuma ba a fara rubutu da Hausar boko ba, har sai da Turawan mulkin mallaka suka zo. Kenan in aka yi la’akari da wannan, a iya cewa samuwar rubutu, musamman irin na Hausar boko a ƙasar Hausa bai wani jima can ba.
To sai dai kuma, da yake harshen Hausa gagarabadau ne, daga lokacin da rubutun Hausar boko ya samu zuwa yanzu an samu tarin litattafai da kuma ƙarin marubutan da ba su da adadi, kuma a kullum ƙaruwa suke yi. Wannan ya taimaka ƙwarai wajen ci gaban adabi da kuma al’adun Hausawa. A bisa wannan dalili ne na nazarci wasu litattafan ɗaya daga cikin zaƙwaƙwuran marubutan wannan zamani, wato Lubna Sufyan. A cikin wannan nazari nawa ne na hango irin kamanceceniyar salo, zubi, tsari da ma taurari da ita marubuciyar ta yi amfani da su wajen gina waɗannan labarai nata. Wannan kamanceceniya kuwa ta zo ta fannoni da da yawa, sai dai zan taɓo kaɗan ne kawai daga ciki.
Samun kamanceceniya a cikin labaran marubuta ba sabon abu bane, kuma ba aibu bane kai tsaye. Sai dai a wasu lokutan yana iya zama maimaici ne kawai na abu guda maimakon samar da wani abu sabo. A bisa wannan dalili, wannan muƙala za ta yi duba ne kawai zuwa ga kamanceceniyar ba wai aibun samuwarsu ko amfaninsu ba. Sai dai daga ƙarshe, za a samu wasu ‘yan shawarwari waɗanda za su taimaka wajen yin amfani da kamanceceniyar yadda ya kamata.
Wacece Lubna Sufyan?
Marubuciya Lubna Sufyan an haife ta ne a ƙaramar hukumar Ingawa da ke birnin Katsina. Fitacciyar marubuciyar ta fara karatun addini tun tana ƙarama kuma ta yi karatunta na Firamare ne a garin Katsina, daga baya ta koma garin Kano inda ta yi karatunta na Sakandire har ta gama. Bayan ta gama ne sai ta koma Katsina in da ta yi karatun Diploma a ɓangaren zanen taswirar gidaje. Daga baya kuma ta ci gaba da karatu a mataki na gaba, wato babbar Diploma wadda da Turanci ake kira Higher National Diploma (HND) a Kaduna.
Kamar mafi yawancin marubuta, marubuciyar ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makaranta, kuma ta kasance ɗaya daga cikin fitattun marubutan online na wannan zamani, domin abu ne mai wuya ka faɗi sunanta a duniyar marubuta da makarantan wannan zamani ba a samu wanda ya santa ba. Zuwa yanzu marubuciyar ta rubuta litattafai sama da guda goma sha ɗaya.
Har’ilayau kuma, marubuciyar ta kasance mai son girke-girke ce sosai. Kuma baya ga rubutu, marubuciyar tana yin fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa, wannan aiki na fassara ne ma ya zama sanadin yin aikinta da kamfanoni da ƙungiyoyin gwagwarmaya masu zaman kansu a lokuta daban-daban a kuma kan batutuwa iri daban-daban kamar su GiveNorthEducation, WomenInArewa, WomenInFinance da dai sauransu. Sannan kuma, marubuciyar ta sha yin aiki da makarantun Islamiyya da bloggers wajen fassara musu aiyukansu. Haka kuma ƙwararra ce wajen haɗa ɗuwatsun ƙawa na adon mata. Sannan kuma tana aikin juyar da bayanan murya zuwa rubutu (transcription). A taƙaice dai, duk in da aikin rubutu yake, to a nan marubuciyar ta fi ƙarfi.
Marubuciyar kuma na ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar marubuta na Fikra Writers Association. Lubna Sufyan ta yi aure a shekarar 2022, kuma tana zaune ne a garin Kaduna yanzu haka tare da mijinta.
Litattafan da ta rubuta
Marubuciya Lubna Sufyan ta rubuta litattafai da dama, ga wasu daga cikinsu;
• Rayuwarmu
• Akan So
• Mijin Noble
• Tskaninmu
• Abdulƙadir
• Alƙalamin Ƙaddara
• Martabarmu
• Rai Da Ƙaddara
• Wata Bakwai
Labaran litattafan a taƙaice
A wannan muƙala, na nazarci litattafai guda huɗu ne daga cikin waɗanda ta rubuta. Ga taƙaitaccen bayani game da kowanne daga cikinsu;
Abdulƙadir
Alhaji Ahmad Bugaje yana da matan aure har guda huɗu. Matarshi ta farko ita ce Hajiya Safiyya wadda ake kira da Hajja. Ta haifi yara takwas tare da shi, su ne Muhsin, Yazid, Khadija, Mubarak, Abdulƙadir, Zahra, Nazir da kuma Zainab. Matar shi ta biyu kuma ita ce Hajiya Saratu wadda ake kira da Mama. Tana da yara biyar da Alhaji Ahmad dukkan su maza. Ahmad (wanda ake kira da Babangida), Yasir da Yazid waɗanda suka kasance ‘yan biyu, sai kuma Salim da Khalid.
Hajiya Sakina ita ce matar shi ta uku da yaransu ke kira Mami, wadda kuma ita kaɗai ce ya aura a bazawara, don shekararta ɗaya da wata uku da yin aure Allah ya yi wa mijinta rasuwa bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita. Ya kuma rasu a lokacin ya barta da cikin wata shida. Ta haifi yarinyarta mace, bayan ta yayeta ne suka haɗu da Alhaji Ahmad Bugaje. Bai aureta ba sai da ya yi mata alƙawarin riƙe mata yarinyarta. Bayan Waheedah, ta haifi yara uku da shi, su ne, Sa’adatu (wadda ake kira da Amatullah), Aminu da kuma Habib. Hajiya Halima kuwa da yaran duka ke kira Anty, ita ce mata ta huɗu kuma amarya a gidan Alhaji Ahmad, ‘yar tsohon Wazirin Kano ce da Allah ya yi wa rasuwa ya aura. A cikin matan shi ita kaɗai ce take aikin gwamnati, domin kuwa da aikinta ya aure ta. Allah ya azurta su da yara shida, saboda ta fi sauran matan shi haihuwa gab da gab, kusan abinda akan kira da kwanika ko gwarne. Yaran su ne, Nusaiba, Nabila, Kabiru, Adnan da Baraka.
Duk da wannan yawa nasu, hakan bai sa yaran kansu ya rabu ba, domin suna son junansu kuma suna girmama na gaba da su. Sannan suna da haɗin kai tare da zumunci da kuma damuwa da junansu. Domin ko ƙurjewa wani ya yi aka ce ga shi can kwance, to yanzu za ka gansu ɗuuu duk sun yo kanshi. Wannan dalili ne ya sa kusan ko’ina suka je nan da nan ake gane su. Hatta Waheedah da ba Alhaji Ahmad ya haifeta ba haka suke mata, saboda ba sa nuna mata wani bambanci, komai a tare suke yi.
Abdulƙadir tun yana da ƙarancin shekaru yake sha’awar aikin soja, kuma har ya girma yana da wannan ra’ayi. Yana da zafi sosai, kuma ba ya ɗaukar raini balle ɗaga ƙafa. Saboda takurawa ƙannensa da yake yi ne a gida ma har suka sa mishi suna ‘Commander’ a ɓoye. Yayan shi Yassar ne kaɗai yake ɗan saurarawa a duk cikin gidan saboda sun fi jituwa.
Waheedah tana da sanyin rai da sauƙin hali, ga haƙuri da ladabi da biyayya. Wannan yasa kowa ke sonta. Tana da wata ƙawa da ke maƙwabtaka da su mai suna Nuriyya. Duk da cewa gidan su Nuriyya talakawa ne, hakan bai sa Waheedah ta ƙyamace ta ba. Shaƙuwar da suka yi ne ma ya sa har ɗinki da sauran abubuwa na yau da kullum akan yi musu tare. Domin har ce musu ake yi ‘yan biyu. Babban abin da ya raba su shi ne, Nuriyya tana da son abin duniya.
Yau da gobe, duk da baƙin hali irin na Abdulƙadir da takura da dukan da yake yi wa yaran gidan da zarar sun yi laifi ko wani ɗan kuskure bai hana zuciyar Waheedah kamuwa da ƙaunarsa ba. Wannan kuwa ya faru ne tun tana da ƙarancin shekaru. Sai dai ta ɓoye soyayyar a zuciyarta domin da fari ita kanta bata san cewa abinda take ji a ranta sunan shi so ba saboda ƙarancin shekaru. Shi kuwa Abdulƙadir sam ba shi da burin auren mace irin Waheedah, wannan yasa ko sau ɗaya bai taɓa kawota a ranshi ba. Amma bayan ya zo bikin ƙannensa, a wannan lokaci sai ya ji zuciyarsa ta fara bugawa Nuriyya, domin tana da siffa irin ta macen da yake so, sai dai ya ƙi bayyana mata saboda a lokacin yana tsaka da karɓar horo a makarantar Sojoji ta NDA da ke Kaduna, kuma ya ƙudurce a ranshi cewa sai ya kammala tukunna ko da zai sa ranshi a wani al’amari da ya shafi aure.
A gefe kuma, Yazid ya kamu da son Waheedah sosai, sai dai shi ma bai faɗa mata ba saboda yana tunanin ta yi yarinya da yawa. Ita kuma Nuriyya, ta samu wani saurayi mai suna Anas wanda yake sonta tsakaninsa da Allah, sai dai ita kuma bata son shi, tana dai kula shi ne kawai saboda yana kashe mata kuɗi. A ƙarshe dai Mahaifinta ya aura mata shi duk da bata so ba. Hakan ya sa Abdulƙadir ya ji ba daɗi sosai.
Da Yassar ya gane cewa Yazid na son Waheedah, sai ya yi marmaza ya sanar mishi da cewa ai suna soyayya da Abdulƙadir. Shi kuma saboda ba zai iya haɗa soyayya da ƙaninsa ba sai ya ja baya, a ƙarshe ma ya yi nesa da garin. Abdulƙadir kuwa, da dai ya ji cewa ai Waheedah tana son shi, sai ya nemi ji daga bakin ta. Ko da ya samu tabbaci, sai nan take ya samu mahaifinsa da maganar aure.
Kowa na gidan sai da ya jinjina maganar auren, amma hakanan aka yi tunda sun nuna suna so. Bayan an yi auren da wasu ‘yan shekaru ne Nuriyya ta kaso nata auren ta fito, ta kuma zo ta aure wa babbar ƙawarta miji, wato Waheedah.
Akan So
Fu’ad Arabi shi ne ɗa na huɗu daga cikin ‘ya’ya bakwai da Alhaji Salman Arabi da Hajiya Aisha suka mallaka. Fu’ad ya fita daban da sauran ‘yan gidansu. Domin ya kasance mai son kai, taƙama da kuma nuna isa. Bugu da ƙari baya kallon kowa da gashi bayan iyayensa da ‘yan uwansa sai kuma babban abokinsa wato Lukman. Tun tasowarshi ba shi da aiki sai buga wasan ƙwallon ƙafa. Ya sha ƙin zuwa makaranta akan wasan ƙwallo. Tun suna duka da faɗa har suka gaji suka soma ba shi goyon baya. Lokacin da ya shiga aji shida a Sakandire ne ya samu ɗaukaka zuwa ƙasar Europe.
Dole su Alhaji Salman suka ƙyale Fu’ad ya tafi. Da ƙyar ya dawo ya zana jarabawar WAEC kaɗai.
A can ya nemi gurbin karatu saboda aikinsa na wasan ƙwallon ƙafar ya sa zaman shi ya koma can.
Fu’ad da Safiyya sun yi aure ne ba tare da amincewar iyayensu ba, domin ana gab da ɗaura wa Safiyya aure ta bi Fu’ad suka je wani wurin aka ɗaura musu aure. Sai dai rashin samun albarka daga iyayen nasu ya sa auren bai yi ƙarko ba.
Safiyya ita ce yarinya ta biyu cikin ‘yaya uku kacal da Malam Audu da Zainabu suka mallaka a duniya. Safiyya na da ‘ya guda ɗaya jal, wata yarinya me ɗankaren wayo tare da saurin shiga rai da ake kira da suna Nana wacce ke fama da cutar daji. Likitoci sun bayyana cewa, domin Nana ta rayu sai an yi mata dashe (transplant). Idan ba a samu wanda ya yi daidai da ita ba, za ta iya rasa ranta cikin watanni shida ko ƙasa da haka. Mutun na farko da ake sa ran ko nashi zai zo daidai da nata shi ne mahaifinta, wato Fu’ad Arabi wanda aka fi sani da ‘Moh’ wanda bai ma san da ita ba.
Shi kuwa Fu’ad tun asali baya son haihuwa, domin har zuwa ya yi aka yi masa aikin da ya kashe masa ƙwayoyin haihuwarsa gaba ɗaya don kada ma ya haihu. Samun cikin Nana da Safiyya ta yi ne ma yasa ya saketa kuma ya rabu da ‘yan uwanshi ya koma Turai da zama har na tsawon shekaru goma sha ɗaya. Nana na son ganin mahaifinta kafin ta rasu, a gefe kuma masoyanta na fata babanta ya zama dai dai da abinda likitoci ke so domin ta tsira da rayuwarta. To amma ita Safiyya tana ganin wannan abu ba mai yiwuwa bane, domin ta san halin Fu’ad da yadda yake da son rai. Kuma maganar da ya yi mata na ƙarshe kafin ya bar ƙasar ita ce; “I don’t do happily ever after. Daga ranar da kika yarda da soyayyata ya kamata ki san ban yi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba. Ban yi kama da wanda zai yi asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Ina da su Haneef, ina da su Fa’iza. A duk lokacin da na ji marmarin ganin yara zan je gidansu in ga nasu.”
Dr. Jana ita ce likitar da ke kula da Nana. Auren soyayya suka yi da mijinta Jabir. Suna matuƙar son junansu, kuma sun aminta da juna sosai. Sannan Allah ya azurta su da zuri’a. To sai dai kuma, aikin da Jana ke yi na neman zama matsala a tsakaninsu, wanda hakan ya sa Jabir ya fara tunanin ƙara aure. Aina abokiyar aikin Jabir ce, domin waje guda suke aiki. Tana burge Jabir sosai saboda kamun kai, hankali da kuma nutsuwarta.
Nuriyya matashiya ce mai kamun kai da riƙon addini, sai dai ta yi rashin samun nagartacciyar uwa. Domin kuwa, ita kullum ƙoƙari take yi ta sa ta a hanyar baɗala. Ta kamu da son wani bawan Allah mai suna Farhan wanda ya taimaka mata a rayuwa sakamakon mummunan halin da ta tsinci kanta a ciki. A dai dai lokacin da ya yi yunƙurin aurenta, a dai dai wannan lokaci ne kuma mahaifinsa ya turje akan shi ɗansa ba zai auri mace irin Nuriyya ba, ya kuma ba shi zaɓi ko su ahalinsa ko Nuriyyar. Wannan dalili ne yasa Farhan bin mahaifinsa suka bar ƙasar. Bayan tafiyar su ne Nuriyya ta haɗu da Nawaf, wanda ya maye mata gurbin Farhan ta fannoni da dama har suka yi aure. Allah ya jarabci Nawaf da shaye-shaye da kuma baƙin kishi na nunawa a kasuwa. Ita kuma Nuriyya duk da irin son da take yi wa Nawaf, ta kasa cire Farhan daga zuciyarta.
Alƙalamin Ƙaddara
Mahaifin Tasneem mai suna Muftahu wanda aka fi sani da Abba, wani mutumin kirki ne talaka mai neman na kanshi domin ganin ya rufa wa kanshi da ahalinsa asiri. Amma matarsa Bara’atu wacce ake kira da Ummi irin matan nan ne da basu da godiyar Allah. Duk abinda ya kawo bata godewa, kuma sai ta fita ta je inda take so ba tare da ta tambaye shi ba, yaran kuwa bata kula d su yadda ya kamata. Kullum cikin maula take tare da kiran babu. Bisa wannan dalili ne har ƙaddara ta kai Tasneem wani gida a matsayin ‘yar aiki har yaron gidan ya yi mata fyaɗe. Wannan ne ya jawo silar da ta fara biye-biyen maza domin ta kula da ƙannenta.
Hankalin Tasneem ya yi matuƙar tashi sakamakon asirinta da ya tonu tun a daren ta na farko da auren Rafiq. Domin kuwa Ya gano cewa bata zo gidan shi da budurcinta ba Wannan yasa ta shiga tashin hankalin da har zuwa ƙarshen littafi na biyu bata fita daga cikin shi ba.
Alhaji Mustafa Shettima wanda tsohon lauya ne, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa ya kasance yana iya yin komai don ganin ya cimma burikansa na siyasa. Ciki kuwa har da yi ‘yarsa auren dole ta hanyar roƙonta da ta auri wanda bata taɓa gani ba, ita kuma ta amince saboda biyayyarta, duk kuwa da cewa tana da wanda take so wato Muneeb.
A gefe kuma ga Altaaf da matarsa Majida waɗanda ke neman haihuwa ruwa a jallo amma basu samu ba. Kwatsam! Sai Altaaf ya gano cewa yana da yara ‘yan biyu a wani ƙauye waɗanda Nuwaira ta haifa ba tare da ya sani ba bayan ya mata fyaɗe shekaru da dama da suka wuce.
Ashfaq, wanda mutuwar mahaifansa da ta ‘yan uwanshi har guda biyu tare da ɓacewar ƙanin shi ɗaya suka sa shi neman kuɗi ido rufe domin kauce wa ƙaddarar talauci kuma na kwance yana jinyar raunin harbin da aka yi mishi da bindiga sakamakon harƙallar miyagun ƙwayoyi da ta haɗa shi da wasu. Ga kuma ƙaninsa watau Tariq wanda shi kuma yake fama da jarabar shan kayan maye wadda ya kasa dainawa, duk kuwa da cewa har gidan nahaukata ya taɓa zuwa a dalilin hakan.
Rafiq na cikin tashin hankali na sanin cewa matar da ya aura ta san wasu mazan a waje, sai kuma wani sabon tashin hankalin ya faɗo mishi, domin kuwa baya iya tuƙi sai dai a tuƙa shi, duk kuwa da cewa yana iya tuno lokacin da yake tuƙin da kanshi. A gefe kuma ƙanwar shi da aka yi wa auren dole ta kira shi tana neman ya zo ya ɗauke ta sakamakon azabar da take sha a gidan mijin ya ishe ta. A daidai lokacin da ya gano cewa hatsarin mota ne da ya yi ya sa ya manta rayuwarsa ta baya, a daidai wannan lokacin ne kuma ya gano cewa wannan hatsarin ne ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa da ‘yarsa waɗanda ya kasa tuno ko da sunan su balle rayuwar da suka gudanar a tare.
Rayuwarmu
Rayuwarmu labari ne akan wani babban ahali da ya ƙunshi mutane da dama a cikinsa. Ko da yake kusan kowa da ke cikin ahalin mutumin kirki ne, hakan ba ya nufin babu saniyar ware a cikinsu, kuma hakan ba ya nufin ba za su fuskanci ƙalubale ba a rayuwarsu.
A daidai lokacin da rayuwa ke yi wa su Dawud daɗi duk da ƙarancin wadatar arziƙi da ta same su, kwatsam sai gashi wata mata ta yi wa rayuwarsu dirar mikiya ta hanyar ƙwallafa ranta akan mahaifinsu wato Auwal. A dalilin wannan mata ne suka tsinci kansu a cikin tashin hankalin da ko a mafarki basu taɓa tsammanin shiga cikin irinsa ba. Hakan ya sa Dawud ɗaukar nauyin da bai shirya ba a kafaɗar shi wadda ita ma neman wanda za ta jingina da shi take yi.
Labeeb jarumin fim ne wanda ya yi shura. Baya ga wannan, ya fito daga gidan kuɗi ta yadda ba za ka taɓa tunanin yana da damuwa ba a rayuwarsa. Sai dai kash, ya faɗa cikin rayuwar shaye-shaye da neman mata. Kwatsam kuma sai ƙaddarar rayuwa haɗa shi da Mamdud wanda ya ɗauka a matsayin aboki kuma ɗan uwanshi. Abinda bai sani ba shi ne, zuciyar Mamdud a koda yaushe ƙuna take yi bisa ganin yadda komai ke zuwa mishi da sauƙi sakamakon kuɗi da kuma baiwar shura da Allah ya yi mishi. Abin da Mamdud bai fahimta ba shi ne, duk iya farincikin da Labeeb ke bayyanawa a fili, damuwar da ke cikin rayuwarshi ta fi wannan. Rikici da turka-turkar da ke tsakaninsu ba ta fito fili ba sai da ƙaddara ta haɗa su son mace ɗaya.
Kamanceceniyar da ke tsakanin labaran
Ire-iren kamanceceniyar da ke tsakanin waɗannan labarai suna da yawa, akwai manya sannan kuma akwai ƙanana. Ga jerangiyar wasu manya daga cikinsu;
Manyan kamanceceniya
1. Soyayyar ‘yanuwantaka a tsakanin taurari maza da mata – marubuciyar takan kawo irin wannan soyayya a tsakanin taurari sosai ta yadda mai karatu zai dinga jin kamar gaske ne ba labari ba. Misali shi ne irin soyayyar da ke tsakanin Raafiq da ƙannenshi (Alƙalamin Ƙaddara), Tasneem da ƙannenta (Alƙalamin Ƙaddara), Faq da ‘yan’uwanshi (Alƙalamin Ƙaddara), Fu’ad da ‘yan’uwanshi (Akan So), Abdulƙadir da ‘yan’uwanshi (Abdulƙadir), Labeeb da ‘yan’uwanshi (Rayuwarmu), sai kuma Dawud da ‘yan’uwanshi (Rayuwarmu).
2. Kula da sallah sosai daga taurari – marubuciyar ta bayyana wannan ɓangaren sosai a cikin litattafan. Daga cikin taurarin da aka bayyana suna da irin wannan halin akwai Fu’ad da Safiyya (Akan So), Abdulƙadir da Waheedah (Abdulƙadir), Labeeb da Ummi (Rayuwarmu), sai kuma Rafiq (Alƙalamin Ƙaddara).
3. Samuwar ‘yan mata masu mutunci waɗanda mummunar ƙaddara ke faɗa wa – a wannan ɓangaren ma marubuciyar ta sako su a cikin dukkan waɗannan litattafan. Ga su kamar haka; Fadila da Nuwaira (Alƙalamin Ƙaddara), Yumna da Tasneem (Rayuwarmu), Sofi (Akan So) da Waheedah (Abdulƙadir).
4. Tarin kuɗi ga taurari maza da kuma talauci ga taurari mata – wannan ma wani abu ne da marubuciyar ta yi amfani da su a cikin dukkan litattafai huɗun da na nazarta. Taurari maza da suka fito a matsayin masu tarin dukiya suna haɗa da Abdulƙadir (Abdulƙadir), Altaaf Tafida (Alƙalamin Ƙaddara), Fu’ad (Akan So), El Labeeb (Rayuwarmu) da kuma Rafiq (Alƙalamin Ƙaddara). Mata kuma da aka bayyana sun fito daga gidan talauci su ne kamar haka; Sofi (Akan So), Yumna (Rayuwarmu), Nuriyya (Abdulƙadir) da kuma Nuwaira (Alƙalamin Ƙaddara).
5. Kashe taurari – Marubuciyar ta kashe taurari da yawa a cikin waɗannan labarai guda huɗu. Taurarin da ta kashe sun haɗa da; Ummi (Rayuwarmu), Sameera da ‘yarta (Alƙalamin Ƙaddara), Nana (Akan So), Sajda da Arif (Rayuwarmu), Abba (Alƙalamin Ƙaddara).
6. Kawo hoton naƙuda – marubuciyar ta kasance mai ba wa allurar mata muhimmanci sosai a cikin labaranta, musamman abinda ya shafi naƙuda. Ta kan kawo bayanin yadda wahalar naƙuda take da kuma irin halin da mata masu naƙudar ke shiga ta yadda mai karatu zai ji tamkar a gabansa abin ke faruwa. Ta bayyana hakan ya faru a da taurari kamar haka; Ateefa (Rayuwarmu); Waheedah (Abdulƙadir) Ummi (Rayuwarmu).
7. Gagarumar Sadaukarwa – Wannan ma wani ɓangare ne da marubuciyar ta yi amfani da shi sosai a cikin labaran. Misali; Lukman ya sadaukar da jaririyar da aka haifa masa ga Fu’ad (Akan So), Da kuma yadda Yazid ya haƙura da soyayyar Waheedah saboda ƙaninsa yana tunanin ƙaninsa na so (Abdulƙadir), Yadda Aslam ya yarda ya auri Nuwaira, wadda yayansa Altaf ya yi wa fyaɗe (Alƙalamin Ƙaddara) sai kuma yadda Labeeb ya sadaukar wa Mamdud da ɗansa (Rayuwarmu).
8. Salon tafiyar kura – gaba ɗaya labaran nan guda huɗu ta yi amfani da salon tafiyar kura ne wajen rubuta su. Ma’ana, daga tsakiya take ɗaukar labarin ta tafi sannan daga baya ta zo ta warware farkonsa kafin kuma ta ci gaba suwa ƙarshe.
9. Kawo wani ilimi da ya shafi likitanci – a cikin litattafai biyu daga cikin huɗun nan marubuciyar ta yi amfani da wasu manyan matsaloli na ɓangaren likitanci masu kama da juna. A cikin littafin Rayuwarmu ta yi amfani da P.C.O.S (Polycystic Ovary Syndrome) wato matsalar da ka iya sa wa mutum ya kasa samun haihuwa. Kamar yadda a cikin littafin Akan So kuma ta yi amfani da Vesectomy, wato fiɗar da ake yi wa maza ta yadda ƙwayoyin halittarsa ba za su iya samar da ɗa ba ko da ya sadu da mace.
10. Taurari likitoci – a yayin da muke magana game da abinda ya shafi lafiya, marubuciyar ta yi amfani da taurari likitoci sosai a cikin labaran. Misali, Dawud (Rayuwarmu), Jana (Akan So) Fawzan (Alƙalamin Ƙaddara).
11. Yawan ahali: a cikin dukkan labaran ta bayyana taurarin a matsayin waɗanda suka fito daga cikin babban ahali mai mutane da yawa. Kuma dukkan taurarin suna son ahalin nasu sosai. Ko me ya faru duka suke ɗunguma su tafi.
12. Abota ta ban mamaki a tsakanin taurari maza – misali; Altaaf da Wadata (Alƙalamin Ƙaddara) Labeeb da Mamdud (Rayuwarmu) Fu’ad da Lukman (Akan So) sai Yasir da Abdulƙadir (Abdulƙadir)
Ƙananan kamanceceniya
Kamar yadda na faɗa, ƙananan kamanceceniyar da ke tsakanin waɗannan labaran. Ga wasu daga cikinsu kamar haka;
1. Yawan ambaton turare – duk labaran tana ba wa tuarare muhimmanci, musammaan ta hanyar nuna soyayyar taurarin labaran ga turaruka, har ma collections take nuna suna da shi.
2. Taurarin da ke auren matan da ba cikakku ba ko wani abu makamancin hakan – misali; Rafiq da Tasneem (Alƙalamin Ƙaddara, Labeeb da Zulfa (Rayuwarmu) sai kuma Aslam da Nuwaira (Alƙalamin Ƙaddara).
3. Samuwar matan kirki waɗanda ke auren mazajen da ba na kirki ba – misali Labeeb da Ateefa (Rayuwarmu), Altaaf da Majida (Alƙalamin Ƙaddara), Fu’ad da Sofi (Akan So) da kuma Abdulƙadir da Waheedah (Abdulƙadir).
4. Samuwar yayye maza masu tsananin son ƙanninsu mata da kishin su – misali; Labeeb da Zainab (Rayuwarmu) Haneef da Fa’iza (Akan so) Altaaf da ƙanwarshi (Alƙalamin Ƙaddara) Raafiq da ƙanwarshi (Alƙalamin Ƙaddara).
5. Mata masu sauƙin kai da haƙuri a zamantakewar aure – Jana (Akan So) Waheedah (Abdulƙadir) Ummi (Rayuwarmu) da Majida (Alƙalamin Ƙaddara).
6. Samun iyaye mata masu nagartar hali – Ummi (Rayuwarmu), Momma (Akan So) da kuma Nuri (Alƙalamin Ƙaddara).
7. Shan ruwa – a ƙalla tana ambaton ruwa sau hamsin a cikin kowane labari.
8. Yawan zuwa yin takeaway a waje – kusan a kowane littafi sai da ta faɗi an je shagon siyayya an yi take away ko an siyo kayan ciye-ciye a ƙalla sau goma. A cikin littafin Rayuwarmu kawai ta bayyana an yo take away sau goma sha biyu.
9. Iya rawa a tsakanin jarumai – misali Labeeb (Rayuwarmu) da Altaaf Tafida (Alƙalamin Ƙaddara).
10. Kawo rayuwar ma’aurata da matsalolinsu – wannan wani abu ne da ta yi a cikin duk litattafan.
11. Akwai kuma taurari masu takewa jarumai baya da suke komawa su zama kamar ‘yan’uwa – misali; Mamdud (Rayuwarmu), Yasir (Abdulƙadir), Wadata (Alƙalamin Ƙaddara) da kuma Lukman (Akan So).
12. Mata jarababbu masu masifa – Nuriyya (Abdulƙadir) Hajiya Beeba (Rayuwarmu).
Shawarwari
Kamar yadda na faɗa a baya, manufar wannan muƙalar kawai shi ne ta zaƙulo kamanceceniyar da ke cikin labaran, kuma an yi hakan cikin nasara. To, shawarata ga marubuciyar waɗannan litattafai da ma sauran marubuta bai wuce game da abubuwa guda biyu. Na farko dai samun kamanceceniya ba laifi ba ne matuƙar an yi amfani da su ta hanyar da ta dace. Domin samuwar irin hakan na daga cikin abubuwan da ke kama wasu masu karatu, sannan yana daga cikin hanyoyin da ke bambance salon rubutunsa da na sauran marubuta. To amma in aka yi amfani da su kuma ta hanyar d na ta dace ba, zai iya zama tamkar maimaita abu guda kawai ake yi a cikin labarai masu yawa maimakon kawo sabon abu wanda shi ne ke nuna fasaha da zalaƙar marubuci.
Abu na biyu kuma shi ne; kome kyawu da nagartar abu irin wannan da marubuci zai dinga maimaita shi a cikin labaransa wata rana za su gunduri masu karatu. Yana kuma iya sa wa su daina karanta littafin marubucin, domin za su ga tamkar yana ƙoƙarin cusa musu wani abu ne da ƙarfi da yaji shi ya sa yake yawan maimaita su. Kenan kauce wa yawan maimaita abubuwan a inda ya kamata shi ne ya fi.