A makalar da ta gabata mun yi bayani ne akan yadda ake amfani da haruffan Hausa. A yau za mu dora kan wurare da ake hadewa da kuma rabe kalmomi a rubutun Hausa.
(A) HAƊEWA
Akwai wuraren da doka ta ba damar haɗa kalma a rubutun Hausa. Babbar manufar kula da
haɗa kalma a mahallin da ya dace ita ce, don a tabbatar da ma’anar da ake nufin rubutawa ba ta canza ba. Ya kamata mai rubutu ya kula cewa, akwai wasu abubuwa da doka ta tanada na a rubuta su a haɗe, irin waɗannan sun haɗa da:
1. Kalmomin Jama’u:- Kalmomin jama’u su ne kalmomi waɗanda yawanci mutane suke rubuta su a rarrabe maimakon a haɗe kamar yadda dokar rubutun Hausa ta tanada. Irin waɗannan kalmomi su ne:
Kuskure Daidai
ko wa kowa
ko me kome
ko ina ko’ina
ko wace kowace
ko yaushe koyaushe
ko wanne kowanne
d.s.
2. Mafayyata:- Su ne kalmomi waɗanda ke fayyace abu a cikin jimla ko magana. Ana rubuta kalmomi mafayyata a haɗe ba a rabe ba. Misalan kalomomi mafayyata su ne:
Kuskure Daidai
wa ni wani
wa ta wata
waɗan su waɗansu
wan can wancan
wa su wasu
wan can wancan
waɗan can waɗancan
wac can waccan
d.s.
3. Wakilin Suna:- Wakilin Suna Kalmomi ne da suke maye gurbin sunaye a inda ba a son a yi amfani da suna kai tsaye, ko kuma don gudun maimaita suna a cikin jimla ko zance. Misalan wakilan suna da ake haɗa su a wajen rubutu su ne:
Kuskure Daidai
mi ni mini
ma ka maka
ma sa masa
ma su masu
ma ta mata
ma ka maka
d.s.
4. Doguwar Mallaka:- A wajen masana nahuwan Hausa, doguwar mallaka takan kasance tilo ko jam’u, namiji ko mace. Kuma ta ƙunshi abubuwa guda biyu wato manunin jinsin abin da aka mallaka da wakilin suna. Idan aka zo rubuta su, tare ake rubuta su wuri ɗaya ba a rarrabe su. Ga misalai
Kuskure Daidai
na wa nawa
na su nasu
ta mu tamu
ta wa tawa
na ki naki
na shi nashi
d.s
5. Manunin Lokaci Sabau:- Kalmomi ne da ke nuna cewa an saba aikata wani abu. Ma’ana abu ne da ake saba aikatawa. Kuma kalmar na ƙunshe da wakilin suna da kuma manunin lokaci saban. Don haka ana rubuta su a haɗe maimakon a rubuta su daban daban. Ga misalai.
Kuskure Daidai
na kan nakan
ta kan takan
ku kan kukan
su kan sukan
mu kan mukan
a kan akan
ki kan kikan
ya kan yakan
ka kan kakan
d.s.
Baya ga waɗannan wurare da aka kawo, akwai wasu wuraren da dokar rubutun Hausa ta amince a haɗe kalmomi. Ya kamata mai rubutu ya san dokokin haɗe kalmomin. Dalili kuwa shi ne, tun asalin rubutu da haɗe kalmomin aka fara. Daga baya ne aka gano raba kalma da sakin layi da sauran ƙa’idojin rubutu.
(B) RABEWA
Ya kamata mai rubutu ya kula cewa, akwai wasu abubuwa
da doka ta tanada a rubuta su a rabe, irin waɗannan sun haɗa da:
1. Kalmomin Dirka:- Kalmomi ne ‘yan ƙanana waɗanda suke taimakawa jimloli su dire sosai. Kalmomi dirka a Hausa su ne: ‘ne’ da ‘ce’ da ‘ke nan’.
A Hausa, ba a liƙa wa kalmomin dirka kowace irin kalma walau a gaba ko a baya, don haka a ƙa’idar rubutun Hausa raba su ake ba a haɗe su. Ga misalan kalmomin dirka da yadda ya kamata a rubuta su.
Kuskure Daidai
nine ni ne
kece ke ce
sune su ne
kenan ke nan
menene mene ne
mecece mece ce
shine shi ne
sune su ne
d.s
2. Manunin Lokaci Shuɗaɗɗe:- Su ne kalmomin da suke nuna cewa an aikata wani abu. Ma’ana an riga an yi abin. Irin waɗannan kalmomi sun ƙunshi lamiri; suna da kuma kalmar aiki. Amma wasu mutane suna haɗe su a lokacin rubutu, wanda yin hakan kuskure ne, domin a ƙa’idar rubutun Hausa
ana raba su ne. Ga misalan kalmomin da yadda ake rubuta su.
Kuskure Daidai
nayi na yi
yayi ya yi
kasha ka sha
tazo ta zo
mukayi muka yi
sunce sun ce
kince kin ce
anyi an yi
d.s
3. Manunin Lokaci Mai Zuwa:- Su ne kalmomin da suke nuna cewa za a aikata wani aiki. Ma’ana ba a haɗe su da kalmomin da suka gabace su ko kuma suka zo bayansu. Amma duk da haka, akwai mutanen da ke amfani da kalmonin manuni lokacin mai zuwa a haɗe da na gaba da su ko na baya da su. Ga yadda ake rubuta kalmomin kamar haka:
Kuskure Daidai
zanzo zan zo
zakayi za ka yi
zaije zai je
zakubani za ku ba ni
za’ayi za a yi
aje a je
mayi ma yi
nazo na zo
zataci za ta ci
4. Wasalin ‘a’ Da Aikatau:- Wasalin ‘a’ kan zo kafin aikatau a jimla. Yakan zo kafin aikatau mai gaɓa ɗaya ko mai gaba biyu ko mai gaɓa fiye da biyu. Don haka, yakan rikitar da mai rubutu, domin a ƙai’dar rubutun Hausa ba a haɗe wasalin da kalmar aiki, sai dai kash da dama masu rubutu kan haɗe wasalin da kalmar aiki wanda hakan ya saɓa, kuma yakan rikita mai karatu tare da
jirkita ma’ama. Ga misalan kalmomin:
• Wasalin ‘a’ Da Aikatau Mai Gaɓa Ɗaya
Kuskure Daidai
ayi a yi
azo a zo
aƙi a ƙi
aba a ba
ace a ce
asa a sa
d.s
• Wasalin ‘a’ Da Aikatau Mai Gaɓoɓi Biyu Ko Fiye
Kuskure Daidai
arubuce a rubuce
abuɗe a buɗe
arufe a rufe
adafa a dafa
ashare a share
atsaya a tsaya
d.s
Baya ga waɗannan wurare da aka kawo, akwai wasu wuraren da ƙa’idar rubutun Hausa ta amince a raba kalmomi. Ya kamata mai rubutu ya san dokokin raba kalmomin.