Skip to content

Sharhin littafin ‘Na Sake Ta’ na Mustapha Abbas Rijiyar Lemo

Sunnan littafi: Na Sake Ta

Marubuci: Mustapha Abbas Rijiyar Lemo

Inda aka buga littafi: Hikaya

Shekarar wallafawa: 2023

Mai sharhi: Abba Abubakar Yakubu

An gabatar da wannan sharhi da farko ne a zauren Bakandamiya Reading Club na Facebook a ranar Lahadi 30 ga watan Juni 2024, da karfe 9 zuwa 10 na dare.

Tarihin marubuci

Mustapha Abbas Rijiyar Lemo haifaffen unguwar Rijiyar Lemo ne da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano. Ya fara neman iliminsa da karatun Islamiyya, kafin daga bisani a saka shi a firamare a wata makaranta da ake kira ‘Yammata Special Primary School. A shekara ta 2004 ya shiga ƙaramar sakandire a J.S.S. Gogau, daga nan kuma sai ya kammala babbar sakandire a G.S.S. Kwachiri duk a cikin birnin Kano. Yanzu haka bayan rubutun labaran hikaya, Mustapha ɗan kasuwa ne, kuma yana sana’ar ƙawata gine-gine. Ya fara rubutun adabi ne a shekarar 2008 lokacin yana aji uku na ƙaramar sakandire da labarinsa mai taken Ƙaddarar Mutum, wanda shi ne rubutun labari mafi tsayi da ya taɓa yi kawo yanzu.  Daga nan ya rubuta wasu gajerun ƙagaggun labaran wato short stories, har guda 7, da suka haɗa da wannan ƙaramin littafin da ake rubuta wannan sharhi akansa, watau, Na Sake Ta. Sauran littattafan da marubucin ya rubuta sun haɗa da Halacci Ko Butulci?, Ranar Kuskure, Girman Alƙawari, Inuwar Sirri, Kuɗi Ko Rai da So Ko Ƙawance?

Game da littafin

Littafin ‘Na Sake Ta!’ na Mustapha Abbas Rijiyar Lemo Kano, ƙaramin littafi ne da bai wuce shafi shida ba, da kalmomin da kaɗan suka haura dubu biyu da ɗari huɗu. Gajeren labari ne wanda marubucin ya nuna cewa ya faru da gaske, sai dai ‘yan sauye-sauye na hikimar marubuci da aka yi, domin ɓatar da hankalin mai karatu daga sanin haƙiƙanin mutanen da abin ya faru da su.

Labarin wani mutum ne da aka sa wa suna Kamal, kodayake ba a kwatanta yanayinsa ko shekarunsa ba a cikin labarin, amma hasashena na manazarci ya nuna matashi ne da ba zai wuce shekaru 25 zuwa 30 ba.

Kamal talaka ne da ke neman kuɗi ido rufe, yana da mata Hajir, wacce ta kasance salihar mace ce, mai biyayyar aure, kuma sun yi aure ne na soyayya. Sai dai duk da soyayyar da ke tsakanin ma’auratan nan biyu, sai da wani tsohon saurayinta Usman, wanda ya kasance mai tashen arziƙi kuma abokin mijinta ya yi amfani da shegen son kuɗin mijinta Kamal ya raba su, ta hanyar yi masa tayin kuɗi har Naira Miliyan 5. Tayin da Kamal ya kasa ɗauke kwaɗayinsa a kai, sanin cewa ko dubu biyar ba a taɓa sawa a asusun ajiyarsa na banki ba.

Son zuciya da rashin daraja soyayyar da matarsa Hajir ke nuna masa, sun rufewa Kamal idanu har ya amince da buƙatar da Usman ya gabatar masa, duk kuwa da kasancewar hakan ya girgiza shi. Amma haɗamar son abin duniya sun rufe masa idanu har ya sallamar da aurensa da farincikin matarsa, saboda rashin samun abokin shawara nagari. Kamal ya kasance matsiyaci ne mai masifar son kuɗi, wanda har iƙirari yake yi cewa zai iya yin komai saboda kuɗi.

A ƙarshe, bayan Kamal ya samu arziƙin da yake burin yi, samun kwanciyar hankali ya gagare shi. Ya yi nadamar abin da ya aikata, musamman ganin duk aure-auren da ya yi har bakwai, amma ya kasa samun salihar mata kamar Hajir. Sakamakon irin halayen da matan da yake aura suke nuna masa, saɓanin na salihar tsohuwar matarsa. Kamar yadda ya bayyana cikin takaici da nadama.

‘Na gane babu abinda ya kai matar ƙwarai irin Hajir wuyar samu a wannan zamanin, kuɗi ba sa iya samar da ita, kai yanzu na gane ma ba komai ne kuɗi ke iya saye ba.’

Labarin ‘Na Sake Ta’ ya tuna min da wani fim ɗin turanci da na kalla, mai suna ‘Indecent Proposal’ inda shi ma wani attajiri ya yi wa wani mutum, talaka kuma malamin makaranta, tayin maƙudan kuɗaɗe don ya bashi dama ya kwanta da matarsa, wacce suke cikin tsananin soyayya da juna, amma talauci ya zama musu ƙarfen ƙafa. Don haka suka yanke shawarar su karɓi tayin da aka yi musu, duk da ba haka ransu ya so ba. Matakin da daga baya ya zama sanadiyyar lalacewar aurensu, da samun kansu cikin wani mawuyacin hali.

Jigo

Kamar yadda na yi bayani a baya, jigon wannan labari shi ne illar fifita kuɗi a kan farincikin rayuwa. A taƙaice dai za a iya cewa, ‘Kwaɗayi Mabuɗin Wahala’. Mun ga yadda son zuciya ya sa Kamal sadaukar da soyayyar da ke tsakaninsa da matarsa Hajir, saboda kuɗi, a ƙarshe kuma ya kasa samun farinciki da jindaɗin da yake hasashen samu. Saboda yadda ya kasa zaman aure da duk mata bakwan da ya aura, waɗanda ya aure su cikin dukiya da walwala. Alhalin ita Hajir da ta aure shi ne saboda soyayya, ta kawar da kai daga talaucin da yake ciki, ta guji duk manemanta da suke da arziƙi, saboda shi. Amma a ƙarshe, mutumin da ta guji aurensa ta bi soyayya, shi ne ya biya mijin da ta aura, shi kuma ya sake masa ita ya aura.

Darussan dake cikin labarin

  • Illar biyewa son zuciya: Mun ga yadda kwaɗayi da son abin duniya ya jefa Kamal  cikin danasani, inda ta kai ga ya yi nadamar cin amanar da ya yi wa matarsa Hajir.
  • Illar rashin samun abokin shawara nagari: Mun lura da yadda Mansur abokin Kamal ya riƙa zuga shi da angiza shi ya ɗauki mataki kan buƙatar da Usman ya gabatar masa, ba tare da ya ba shi shawarar abin da ya dace ba. Amma a fakaice yana nuna masa ya karɓi kuɗin ya fi masa zaman soyayya da Hajir cikin talauci.
  • Illar talauci: Idan talauci ya haɗu da son zuciya, ana samun babbar matsala. Saboda yadda idanun mutum ke rufewa ya riƙa aikata abin da idan da ya yi haƙuri kuma ya yi aiki da hankali ba zai aikata abin da daga baya zai yi danasani ba. Mun ga yadda talauci ya angiza Kamal ya cefanar da soyayyarsa, saboda hangen daular da zai samu daga kuɗaɗen da aka bashi, amma duk da haka sai da ya yi nadamar abin da ya aikata.
  • Kuɗi na iya sayen soyayyar da ba ta ginu a kan tushe mai ƙarfi ba. Abin takaici ne yadda Kamal ya yi watsi da soyayyar da Hajir ta nuna masa da sadaukarwarta gareshi, yadda ta fifita son da take yi masa, ta aure shi duk da talaucin da yake ciki, ta ƙi auren Usman duk da arziƙinsa. Amma saboda tasirin kuɗi da nacin da Usman ya nuna ko ta halin ƙaƙa sai ya auri Hajir. A ƙarshe kuɗinsa ya yi masa rana, don ya sayi soyayyarta daga wajen mijinta, wanda ta ƙi aurensa saboda ƙaunar da take masa.

Abin lura

Mustapha Abbas Rijiyar Lemo, marubucin wannan labari na ‘Na Sake Ta’, na daga cikin matasan marubuta na onlayin da suke ƙoƙarin fitar da rubuce-rubuce masu ma’ana da kuma tsafta. Ko a salon yadda ya rubuta labarin za ka fahimci ya san abin da yake yi, musamman wajen kiyaye ƙa’idojin rubutu, da zubin labari mai jan hankalin mai karatu. Sai dai duk da haka, an ce mutum tara yake bai cika goma ba. Duk da kasancewar ya rubuta wasu littattafai da gajerun labarai sun kai 10, a nazarin da na yi wa labarin ‘Na Sake Ta’, na lura da wasu ‘yan kurakurai na tuntuɓen rubutu, kamar yadda ake gani a mafi akasarin littattafan onlayin, akwai matsalar rashin kiyaye ƙa’idojin rubutu a wasu wurare. Amma ba zan yi magana a kan kowanne kuskure na ƙa’idar rubutu da idona ya gani ba, saboda wani darasi ne mai zaman kansa. Sai dai ina fatan marubutan mu za su ƙara neman sani kan ƙa’idojin rubutu wajen haɗawa da raba kalmomi. Kuma a riƙa bai wa wasu da aka san suna da ilimi a ɓangaren su riƙa dubawa, suna ba da shawarwari.

Na lura da yadda aka samu kuskuren rubutu a wasu wuraren, kamar misali, a sakin layi na farkon labarin an rubuta ‘dai-dai’, a maimakon ‘daidai’, wato an sa karanɗori a inda bai dace ba. Haka kuma an rubuta ‘ɗan kasuwa’, a maimakon ‘ɗankasuwa’.

A wasu wuraren an yi amfani da sunayen wasu abubuwa da turanci a maimakon a ambaci sunayensu na Hausa ko kuma yadda ake kwatanta su. Misali, an rubuta ‘Taxi’ maimakon ‘Tasi’, an kuma  rubuta ‘Juice’ a maimakon ‘tataccen ruwan ‘ya’yan itatuwa’. An sa kofin ‘glass’ maimakon ‘gilashi’.

Sannan an rubuta ‘Katsam!’ a maimakon ‘Kwatsam!’

Na lura, marubucin bai yi wa labarin tsarin babi-babi ko kashi-kashi ba, kamar dai yadda akasarin marubutan onlayin suke suke rubutu, inda suke zuba shi kawai ratata. Sai dai shi a nashi salon ya ɗan sha bamban da wasu, domin ya yi amfani da tsarin sanya lokacin da wasu abubuwa ke faruwa a cikin labarin. Ko kuma ya sanya take kan wasu gaɓoɓi na labarin, kamar yadda a farko ya buɗe da ‘Asabar 7:30 pm’ (a maimakon a sa 7:30 na maraice). A wani wajen kuma ya sanya kanu, kamar ‘Ta Faru Ta Ƙare’, bayan sakin layi da basu wuce shida ba kuma sai ya sake sa, ‘Sauyi’. Haka dai labarin ya riƙa tafiya.

Arashi

Na lura a maimakon a sa wa littafin sunan, ‘Soyayyata Da Kuɗi’ ko ‘Na Yi Biyu Babu’ da makamantansu, marubucin ya zaɓi ya sa sunan ‘Na Sake Ta!’ don ya ja hankalin mai karatu, yadda zai damu ya san mene ne dalilin da ya sa aka yi sakin, wanda shi ma wani ɓangare ne na labarin.

Ya yi amfani da adon harshe da ya ban sha’awa, a inda yake bayyana cewa, ‘Sai da na tattaro dukkan jarumtata kafin na iya miƙawa Hajir mummunan saƙon da na shafe tsawon dare ina tunanin ta yadda zan fara rubuta shi kamar baƙon marubuci a fagen rubuta ƙagaggen labari.’

Shawara

Yana da kyau marubuta su riƙa mayar da hankali ga rubutun da suke yi, kuma su daina gaggawar sai sun fitar da labari a lokacin da suke son fitarwa, yadda za su samu zarafin yin gyare-gyare da sake canza wasu abubuwa, wanda a baya tunaninsu bai kai wurin ba.

Sannan su sani, yin rubutu mai inganci yana da muhimmanci, saboda ba ka san hannun wanda zai shiga ba, ko idanun wanda zai karanta ba. Kiyaye ƙa’idoji da dabarun yin rubutu mai jan hankali, kamar kwalliya ce ga rubutu, domin abin da wani yake kallo kenan kafin ya buɗe littafi ya karanta.

A karshe

Ina mai jinjinawa marubucin wannan labari game da tunaninsa, da ƙoƙarinsa na isar da saƙon hannunka mai sanda ga masu karatu.

Allah Ya ƙara basira da ɗaukaka. Amin

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page