Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Kasaitar So by Nana Haleema

A k’asa kuwa Daddy komawa yayi ya zauna tare da dafe kai dan har ga Allah lamarin zafin zuciyar Zaid ya fara bashi tsoro abu kad’an sai ya tunzura shi ya harzuk’a yayi ta huci kamar zaki, baya ragawa kowa duk wanda yayi masa sai ya mayar baya bari ko kad’an,”irin dabi’ar da ka koyawa d’an ka kenan Abubakar? Kana kallo a gaban ka yana mata irin wannan cin kashin amma ka kasa hana shi ko? Wato ga banzaye marasa amfani ya zage mu san ransa harda yunk’urin duka mu yake a gaban ka a kan idon ka” Uncle Sani ya fad’a rai a b’ace yana kallan Daddy da hannun sa yake kansa.

“Kayi hak’uri dan Allah, ina baku hak’uri a madadin sa” Daddy ya fad’a yana had’e hannayen sa alamun rok’o, dan shi kam bai san mai zaiyi ya canja halayyar Zaid ba.

Mik’ewa Uncle Sani yayi fakam-fakam yayi waje yana fito da waya alamun waya zaiyi, sai bayan ya zaga bayan gidan ne ya kalli ko ina yaga babu kowa a wajan kana ya buga wayar.

“Zagayo gani” yana fad’ar hakan ya kashe wayar yana cigaba da girgiza kai tare da kwafa.

Da sauri ta k’araso wajan tana zuwa ta kalli bayan ta kafin ta kalli Uncle Sani tace, “Ya akayi ka kira ni? Kasan fa yana nan kar ya fahimci wani abun fa” Amina ta fad’a a d’an tsorace tana kallan Uncle Sani. Gyara babbar rigar sa yayi yace, “Wai kuwa kina aikin nan yadda ya kamata kuwa? Dan ni banga wani result akan hakan ba har yanzu.”

“Ina yi wallahi kasan halin yaron kallo ma ban ishe shi ba balle ma yaci abinci na, amma yanzu na samo mafita sai dai a hankali zan gabatar da komai dan bana son uban sa ya fara zargi na.”  D’aga kai Uncle Sani yayi kafin yace, “Ki dai hanzarta mun san abin yi lokaci yana sake wucewa gwara mu gama dasu tun kafin a fara maganar auren Zaid” ya fad’a yana zura hannun sa aljihu tare da mik’awa mata leda bak’a ya cigaba da fad’in, “Ko wanne akwai yadda zakiyi amafani dashi kar a samu matsala Amina.”

Rigar ta ta d’aga ta tusa ledar kafin tace, “babu matsala kar ka damu” ta gama fad’ar hakan ta juya da sauri ta koma shi kuma ya d’auko waya ya kara a kunne yana magana kamar waya yake a haka ya dawo falon, Daddy yana zaune kansa a sunkuye sai fad’a suke masa kamar su suka haife shi suna zagin sa suna zagin Zaid shikam bai d’ago bama balle ya tanka musu. “Ku tashi mu tafi kafin waccan mara tarbiyyan yaron yazo ya kora mu da bulalai” ya fad’a yana cika hannun sa da dankali yana yin waje, hararar Daddy sukayi suma kafin su fita ko wanne ya cika aljihu da abinci.

Motar Uncle Sani aka shiga suka bar gidan kowa ransa a b’ace, “wai nikam Yaya yaushe ne burin mu zai cika? Ka duba irin dukiyar da bawan Allah nan ya tara amma muna k’okarin zama y’an kallo.” Uncle Sani yayi murmushi yace, “Ku k’yale ni dasu dukkan su a tafin hannu na suke kudai ku jira zaku gani.”

Wanda yake bayan motar ya bud’e baki zaiyi magana kawai suka ga ansha gaban motar tasu, da sauri wanda yake tokin ya taka burki suna kallan mutanen da suka zagaye su ko wanne da wuk’a a hannun sa,  biyu daga ciki y’an daban ne suka k’arasa wajan motar su Uncle Sani d’aya ya bud’e inda Driver yake yace, “Kai fito ka koma baya” ya fad’a yana zaro masa jajayen idon sa. 

“Akan me zai fita? Motar kace ko ta uban ka?”Uncle Sani dake gaban mota ya fad’a cikin masifa, nauyi wanda yake b’angaren sa tsaye ya kaiwa Uncle Sani akayi sa’a ya same shi a baki yace, “kaima fita ka koma baya wallahi kafin na canja maka kamanni”. “A’a Mugu k’yale shi a gaban kai shiga baya, kai kuma koma baya” ya fad’a yana kallan wanda yake mazaunin mai tuk’i. Ai bai gama rufe baki ba ya fita da hanzari ya koma baya Mugu ya shiga baya suka ja motar a guje suka nufi wata hanya da babu kowa a hanyar.

Wani Estate suka ja su Uncle Sani wanda babu kowa kafin suyi parking d’in motar suce, “ku fito”. Jiki na b’ari suka fito dan su sun d’auka kidnapping d’in su akayi.

Nan suka yi tozali da rik’k’akun y’an daba har su biyar a tsaye suna zuk’ar taba suna yi musu kallo kask’anci.

“Dan Allah kuyi hak’uri kuyi mana rai kada ku cutar damu in kud’i kuke so akwai k’ani na Ambassador ne a k’asar waje duka abinda kuke so zai muku” Uncle Sani ya fad’a jikin sa na rawa sosai.

Tsaki suka ja suka kalli juna tare da murmushi d’aya daga cikin su ya bugawa Uncle tsawa yace, “Maza ku tashi ku fara rawar malam bud’a mana littafi tunda naga kun sha babbar riga”. Kallan kallo suka shiga yi a tsakanin su tsawar da aka sake yi musu ne ya saka dole suka mik’e suna bula babbar riga suna casar rawa. Dariya suke yi sosai suna kallan su dan yadda jikin su yake rawa kasan a tsorace suke, sai da suka wahalar dasu kana suka ce suyi kamun kunne, haka suka kama kunne kusan mintin su talatin da ka d’ago za’a cira maka allura dole ka koma, rana ce ta bud’e sosai dan lokacin sha biyu tayi zuwa lokacin sun galabaita sosai sai gumi suke Uncle Sani harda amai.

“Yauwa ku d’ago ku zauna” ai da sauri suka d’ago kowa jiki na rawa suka baje a wajan suna hakki.

“Daga rana irin ta yau wallahi kuka sake aibata mana mai gida sai na cirewa ko wannen ku kunne d’aya kun gane?” A galabaice Uncle Bala ya d’ago kai yace, “Mu mun isa muga me irin shigar ku ma muyi masa kallan banza balle magana.”

“Dallah malami kayi mana shiru mai gida Zaid nake nufi, na rantse da Allah kuka sake b’ata masa rai kuyi kuka da kanku dan babu abinda zai hana bamu zubar muku da jini ba yanzu ma kawai mun k’yale ne” suna gama fad’ar haka suka fad’a motar su suka ja suka bar su a washe a wajan.

Bayan fitar su Daddy ya mik’e ya hau saman Zaid a fusace ba tare da knocking ba ya bud’e k’ofar falon nasa ya shiga, warin sigari ne ya fara yiwa Daddy sallama a falon Zaid, da hannun yake kore hayakin yana sake nufar ciki ya toshe hanci da hannu d’aya. 

A zaune ya hango shi ya dafe kai da hannuyen sa duka yana kad’a k’afa, “Zaid!” Daddy ya fad’a yana k’arasawa kusa dashi.

Bai motsa daga yadda yake ba badan baiji kiran da Daddyn nasa yayi masa ba, “Zaid meye haka? daman har yanzu baka daina shan wannan abar ba?”. Sai a lokacin ya cire hannayen sa daga kansa ya kalli Daddy da idanun sa da suka koma jajaye ya lumshe su ya bud’e yace, “Eh Dad, jiya ma nasha.” “Why Zaid? Wannan shine sakayyar da zaka yiwa Maman ka?.” “Daddy sai raina ya b’aci nake sha.” ya fad’a yana mayar da idon sa ya kulle.

“Koda wasa bana so ka sake aikata abinda ka aikatawa y’an uwa na yau, yayye nane uwa d’aya uba d’aya bani da wasu a duniya sama dasu, kaima kuma baka da sama dasu komai lalalcewar su, ko babu raina su zaka numa matsayin iyayen ka dan sune jini na yake yawo a jikin su, ina son su ina kuma ji dasu kar na sake ji kayi musu rashin kunya ko wani abu na rashin kyautawa kaji ko?” Bai jira amsar saba ya juya ya fita dai bazai iya jure warin da yake tashi a falon ba.

Ambassador Abubakar Ali shine sunan Daddy asalin su y’an garin Kaduna ne kafin aiki ya dawo da ahlin su garin Kano, Ambassador su biyar ne a wajan iyayen su wanda suka jima da rasuwa, Sani shine babba, Bala, Abubakar, Saifullahi sai y’ar autar su Asma’u, ko wanne a cikin su yana da rufin asiri babu wanda za’a kalla ace masa talaka dan a cikin su babu wanda shekara zata zuwa ta wuce ba tare da sunje zirayar saudia ba, Abubakar ya fara aiki a k’ark’ashin Foreign affairs dake garin Abuja a lokacin Allah ya had’a shi da Maryam a garin, Maryam ta kasance marainiya bata san mahaifin ta ba sai a hoto ta rayu da mahaifiyar ta na wasu shekaru kafin ta bar duniya itama, tun daga lokacin take shan wahala a wajan matan uba kasancewar ta k’arama a wajan mahaifiyar su daga baya ta dawo Kano wajan Kakar ta da ta haifi Babar ta, Soyayya me tsafta ta shiga tsakanin su har ta kaisu ga aure, tun farkon auren su ta fara fuskantar wulaqanci daga dangin sa amma bata nunawa kasancewar mijin ta na santa bata damu ba.

Arzuk’in Abubakar yana ta k’aruwa kasancewar sa mai biyayya iyayen sa sun bar duniya suna saka masa albarka hakan ya saka babu wanda ya kama k’afar sa a y’an uwan sa, k’iri-k’iri y’an uwan sa suke nuna masa bak’i da hassada a fili, cikin ikon Allah arzukin Daddy na gaba nasu na dad’a k’asa a haka har cikin Zaid ya bayyana.

Bayan haihuwar Zaid sai abun nasu ya dad’a gaba dan a lokacin arzuk’in kamar a sama Daddy yake tsintar sa, duk wata sai ya aikawa da ko wannen su abinci da kayan shayi da kud’in cefane, banda mota da gida da ya bawa ko wannen su amma kullum cikin rainuwa suke.

A lokacin da Zaid ya kai shekara hud’u a duniya a lokacin aka bawa Daddy Ambassador a k’asar Cyprus suka tarkata suka koma can da zama, wannan samun matsayi da Daddy yayi ya sake tsone musu ido sai suka fara yi masa fatan mutuwa su samu gado, tun daga lokacin da aka haifi Zaid ko sau d’aya ta yi b’ari daga lokacin bata sake ba koda b’atan wata ba.

Shekaru biyar yayi a Ambassador na Cyprus kafin su dawo Nigeria a lokacin Zaid nada shekaru tara a duniya.

Tun dawowar su aka fara farautar rayuwar Zaid ana yiwa babar sa Wulaqanci kamar zasu kashe ta, duk abinda ake Zaid yana gani kuma duka yana sane da duk abinda ake yi a lokacin yayi yarinta da fahimta. 

Abdullah wato Zaid yaci sunan mahaifin Mama ne hakan ya saka take masa lak’abi da Zaid yaro ne mai zafin zuciya tun yana k’aramin sa, yana da saurin fushi abu kad’an ne yake harzuk’a masa zuciya, bashi da ya yawan magana kuma ya taso a cikin turawa wannan dalilin ya saka rashin maganar tasa yaso yayi yawa, Zaid baya san hayaniya sabida Allah ya jarabce shi da wani ciwon kai da indai ya shiga hayaniya sosai to tabbas zai tashi in kuma ciwon ya tashi kamar zai bar duniya dan sai  an saka abu an d’aure masa kan dan ji yake kamar zai tarwatse, likitoci da dama sun duba shi amma basu ga wani abu a kan na sa ba haka yasa aka hak’ura aka cigaba da rok’on Allah.

Zaid yana san iyayen sa sosai da sosai lokacin da ya fara hankali ya fara lura da irin zallar k’iyayyar da dangin mahaifin sa suke masa shida mahaifiyar sa, Zaid baya san shiga mutane yafi so ya killace kansa a wajan da babu hayaniya ko kuma ya koma d’aki yayi ta kid’a da kayan kid’an sa dan Allah ya bashi fasahar iya kid’a.

A lokacin Daddy ya sake samun Ambassador of Finland suka sake tafiya k’asar, a can Zaid ya cigaba da makaranta zuwa lokacin ya shiga University inda yake karatun b’angaren zane-zane dan tun yara k’arami in ya iya zane sosoi, ta b’angaren tahfiz ma a can yayi karatun sa sabida akwai brach d’in wata makaranta da k’asar Dubai suka kawo ta k’asar a ciki ya sauke alkur’ani ya littafai da dama, shekara hud’u ya kammala karantun sa a lokacin shekarun sa ashirin cif a duniya a lokacin kuma suka sake dawowa Nigeria. 

Zaid Allah ya bashi baiwar Fahimtar yanayin mutum tun kafin yayi magana hakan ya saka da yaga mara gaskiya a ido yake gane shi, ko a Finland y’an sandan can sukan neme shi in suna san kama marasa gaskiya, bayan dawowar Daddy ya gina masa kafaran kanfani mai suna ZAID DESIGN COMPANY kyau da tsari aka zuba ma’aikata, ana aiki kuma mai kyau dan da an zana takalmi an fitar turawa sakin kud’i suke yi su siyi design d’in. 

A shekarar Mama ta had’u da wani irin ciwo da aka rasa meye iya bincike anyi amma ba’a gano wanne irin ciwo bane shine yayi sanadin da ya kaita har lahira babu irin maganin da ba’a yi ba amma Allah baiyi zata rayu ba, a lokacin dangin Daddy kamar su zuba ruwa a k’asa sha sabida farin ciki dan sun tsani Maryam gani suke kamar ita take cinye komai na dukiyar sa, wannan farin ciki da suka nuna k’arara ya sake jefa zuciyar Zaid cikin tsanar su me muni, Mama Asma’u ita kad’ai ce me zuciya mai kyau a ciki su ita kad’ai ce take san Zaid tsakani da Allah tun lokacin mahaifiyar sa take kuma kaunar yayan ta badan dukiyar sa ba.

Bayan rasuwar Mama Daddy ya sake barin k’asar aka sake bashi wani matsayin suka tafi shida Zaid dan bazai iya barin sa shi kad’ai ga ganin irin halin kiyayyar da ake nuna masa aka bar Company a hannun abokin Zaid wanda suka yi karatu tare, rayuwar Zaid ta shiga kunci na rashin mahaifiyar sa a kusa dashi ya sake zama wani shiru-shiru zafin zuciyar sa har ya ninka na baya, fara’a kuwa kamar ba’a halicce ta a fuskar sa ba.

Shekara biyar suka samu a k’asar suka sake dawowa Nigeria a lokacin ne Uncle Sani ya bud’e wuta sai Daddy yayi aure ya kawo masa Amina yace ya aura, babu yadda ya iya tunda shine matsayin uba a wajan sa akayi bincike akan Amina komai dai-dai sannan akayi auren a lokacin Zaid ya koma Finland k’aro karatu, Komawar Zaid a lokacin suka had’u da wata baturi me suna Rahana ta soshi sosai shima ya so ta daga baya ta yaudare shi har ta kai shi ga sanin ta tun daga lokacin ya tsane ta tun daga kanta kuma bai sake gigin yin wata budurwa ba dan a ganin sa dukkanin su halin su d’aya. 

Ranar da ya dawo ranar ya fara ganin rashin gaskiya a lamarin Amina inda ya same ta dumu-dumu tana zuba masa garin magani a abinci, da yayi bincike ya gano yarinyar su Uncle Sani ce tun daga lokacin ya tsane ta itama ko abincin ta bai taɓa ci ba haka ya saka aka yi masa wani d’an small cafe a saman sa yana dafa coffe da tea a duk lokacin da yaso kasancewar abinci bai wani dame shi ba.

Babu mai hawar masa sama sai me gyara masa d’aki shima kuma namiji ya aminta dashi shiyasa ya bar shi kuma ba’a gidan yake da zama ba, silar had’uwa Zaid dasu Wizzy akwai ranar da motar sa ta lalace a k’ofar nassarawa da daddare yana tafiya a k’asa aka kwace masa waya a akan idon su Wizzy akayi suka kamo wanda ya kwace ya kawo masa da kansa kuma ya bashi hak’uri, tun daga lokacin in yazo wucewa ya kan kalli inda suke ya gansu su uku a killace babu ruwan su da mutane shi kuma yana san rayuwar zama waje d’aya hakan ya saka suka zama abokan sa, yana yi musu alkhairi sosai dan babu wanda bai san gidan su a cikin su yana zuwa ya har wajan iyayen dukkanin su in hakan ta kama.

Zaid yana yawan zuwa gidan Mama Asma’u su gaisa sosai dan yana santa dan ya fahimci ita ba dukiyar su take so ba su take so, Mummy Aisha itace kad’ai yayar Mamar sa wacce ya sani kuma take kulawa dashi, tana zaune a garin Abuja itama yana yawan zuwa su gaisa dan ita yake yiwa kallan mahaifiya a gare shi.

Zaid Namiji ne me zubin k’arfafa ko ina na jikin sa a murd’e yake kana ganin sa kaga wanda yake yawan d’aga k’arfe, bashi da fara’a ko kad’an fuskar sa da zubin sa kamar jarumin indian film d’in nan John abraham, farin ciki ko bak’in ciki baya saka shi dariya sai kai sa’a shine zaka ga yayi murmushin gefen baki shima kuma sai dai in Mama da Daddy aka yiwa addu’a amma kafin kaga haqoran sa a waje ana jimawa sosai, zaman sa dasu Wizzy ya saka ake masa kallan d’an iska d’an shaye-shaye in da abinda ya tsana a duniya bai wuce wannan kalmomin ba baya iya yafe su ko kad’an dan sanin Rahana da yayi bai saka ya cigaba da neman mata ba dalilin da ya saka ya tsani kalmar d’an iska, ko wayee ka kira shi da haka baya saurara maka nan take zuciyar sa take harzuk’a yayi maka hukunci ko ya saka yaran sa suyi maka, Zaid abokin sa d’aya takk a duniya shine Hameed wanda companyn sa yake a hannun sa bayan shi bashi da wani aboki a duniya.

Uncle bala, Uncle Sani da Uncle Saifullahi a yanzu basu da burin da ya wuce kashe Zaid shine babban burin su da sun gama dashi su dawo kan Daddy in ya mutu su kuma su mallaki komai nasa wannan dalilin ya saka suka shigo da Amina cikin rayuwar sa, aikin suke amma babu nasara kuma duk da haka Daddy bai fasa kyautata musu ba amma su burin su suga bayan sa duka kud’in su a wajan malamai suke k’arewa wajan karb’o magani.

Zaid duka ya karance su kuma shima yana dagewa wajan taya Daddyn sa da addu’a kuma shima ya kan karb’o maganin tsari wanda aka samo shi daga alkur’ani mai girma a wajan wani malami dake kusa da gidan su Wizzy, kasancewar Daddy ya kasance mai taimakom talakawa koda yaushe gidan sa a cike yake da mabuk’ata addu’ar da suke masa ita take dad’a bashi kariya daga sharrin su Uncle Sani, wannan ya dalilin ya k’arawa Zaid tsanar iyayen nasa ko kad’an baya kaunar ganin su shiyasa koda wasa baya ziyartar ko wanne a cikin su kuma baya sakewa da d’an kowa a cikin su indai ba yaran Mama Asma’u ba, yana raga musu ne ma sabida da Daddy yana nuna masa b’acin ran sa akan hakan, har lokacin kuma Daddy ya kasa gane manufar su a kan sa sabida shi tsakani da Allah yake zaune dasu shi kuma Zaid bai sanar dashi ba sabida gudun shigar sa wani hali dan sosai yana kaunar mahaifin sa.

Had’uwar Zaid da Ibteey ba k’aramin b’atawa Zaid ran yayi ba, ta zagi Maman sa sannan tace masa d’an iska ta kira shi da d’an shaye-shaye mai lalata yaran mutane, wannan kalamai nata suka dasa masa tsanar ta lokaci d’aya gashi sam shi bai iya tsanar abu ba dan in yace bayayi kawai yayi, ba’a tab’a jifan sa da irin kalman ba shiyasa ya d’auki alwashin koya mata hankali yadda ko nan gaba akace ta yiwa wani abinda tayi masa baza tayi ba dan a kanta yake tunanin fara lalata yaran mutane kamar yadda ta fad’a. 

<< Kasaitar So 2Kasaitar So 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.