Skip to content
Part 24 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

A hankali, ta fara takawa zuwa inda yake. Idanunta kyam a kanshi ta kasa kiftawa, kamar wadda take tsoron idan ta kawar da kanta koda na dan kankanin lokacine zai bacewa ganinta.

Kallon daya kafeta dashi yasa taji gwiwoyinta suna kokarin sagewa. Da kyar ta karasa inda yake.

Babu magana babu komi, ta shige cikin kirjinshi da bata san tayi tsananin kewa ba sai a lokacin.

Shi kuwa kamar mai jira, ya sanya hannuwanshi duka biyun ya zagaye bayanta dasu.

Kanshi ya nutsa gefen wuyanta yana shakar daddadan kamshin da take yi. Tana jin yadda zuciyarshi take bugawa slow and steady, ta lumshe idanunta tana sauke numfashi a tare da bugun zuciyar tashi.

Sun jima a hakan, kafin ta fara zame jikinta a hankali, lokacin data gama tabbatar da cewa lallai shi dinne da gaske.

Ta dan matsa baya tana jefa mishi kallo mai dauke da alamun tambaya, “Yaya Abdul! Ta yaya aka yi kazo nan, kuma yaushe?”

Ya daga kafada yana dan murmushi, “zuwan kenan!”
Ta kara kallonshi, “to ai baka amsa min dayar tambayar ba, ta ya aka yi ka zo nan?”
Murmushi ya sake saki, ya karasa inda take ya kama hannunta ya sanya a nashi, “kwatance aka yi mun obviously, tunda ke kinki daga wayar taki ma balle in tambayeki”

Sai a lokacin ta juya ta kalli Zainab data coge a gefe tana kallonsu cikin murmushi. Ta jinjina kai itama tana murmushi, “oh! Waton dama dazu abinda kike yi mun da waya kenan shi yasa kika dinga dariya?”

Dariya Zainab din ta saki, “Aunty shi yace kada in fada miki. Surprise ne”

Ta kalleshi tana dan turo baki, “amma saboda Allah ka kyauta min kenan?”

“to yanzu kuma don miji yazo ganin matarshi hakan sai ya zama laifi kenan?”
Ya furta hakan yana langabar da kanshi gefe guda.

Sai ta saki murmushi kawai, “ni ban ce kayi mun laifi ba. Kawai dai naso ace ka fada min da wuri. Watakila da ban yini cikin tunani da damuwar abinda yasa ka ki kira ko dawo min da amsoshin sakonni na ba”

Bata san bakinta ya zarce da fadin hakan ba sai data ji kalmomin suna zagaye a cikin kunnenta. Sai kuma ta tabe baki kawai.
Watakila da da ne dai, da sai tace hakan bai dace ba. Amma a yanzu kam, ta riga data gama amanna da ranta, kan cewa babu gudu, babu boye-boye, babu kawar da kai. AbdulMalik mijinta ne, ta kuma amsheshi. Don haka babu wata kara da zata kara yiwa rayuwar aurensu ko shakulatin-bangaro.

He was floored to say the least. Magungunanta sun dakeshi a cikin zuciyarshi kwarai da gaske. Ya kai yatsunta baki ya bisu da sumba daya bayan daya yana kallonta da wani tausassan kallo mai nutsar da zuciya, “gani ai nazo tsaye a gabanki Kauthar. Baki da wata damuwa ko matsala matukar ina nan, ina nan din kuma, babu inda zani Kauthar. Babu inda zani!”

Bata iya mayar mishi da amsa ba sabida yadda taji bugun zuciyarta yana haurawa yana neman ya wuce misali, ga idanunta dake neman cikowa da kwalla. Ace wannan halittar gaba dayanshi, da surarshi mai kyawun nan da kyawawan halayen da ba a cika samu a wajen kowa ba, nata ne ita. kadai. Da yadda ta dinga yi mishi abubuwan data mishi, amma har a yanzu bai juya mata baya ba. Sai ma sonta da yake kara yi, ita kam me tayi data cancanci. mutum kamar AbdulMalik?

Ta kara sanya hannunta ta kame nashi kam. Suka jera ba tare da sun sake yin magana ba suka fara ninkaya cikin lungun unguwar. Zainab tana binsu a baya.

Ko yayi mamaki ko yaji kyankyamin yanayin unguwar, da gidansu Adidat, AbdulMalik bai nuna komai a kan fuskarshi ba.
Tuni an ci karfin aikin da ake yi a gidan. An sanya kyaure a duka kofofin gidan. An yi foundation wanda za a zagaye gidan da katanga sai a ruguje wadda take kokarin zubewa. Shima bandakin gidan an gyareshi, an zagayeshi an sanya kyaure, an sanya slab da tiles har a jikin bango.
Data shiga gidan sai taga tsananin bambancinshi da gidan data shiga a jiya. Wani sai ya rantse yace ba haka yake ba. Lallai gyara yayi.

Bai damu da dauda da tarkacen dake zube a tsakar gidan ba, durkusa yayi har kasa yana kwasar gaisuwa wajen Adidat.

Shi da ita sai aka rasa wanda zai durkusawa wani, don kuwa itama sai ta tafi ta zube tana gaidashi.

Kauthar da dariya ta kusan hanata magana, ta rasa ko intimidating dinta ne yayi ko kuwa tsananin girmama surikine irin na al’adarsu ya janyo hakan? Ta tafi ta tadata tsaye dai tana cigaba da dariya.

Fita waje suka yi shi da Yusuf suka tafi masallaci don kuwa wasu wajajen har an fara kiran sallar magriba.

Suma su Kauthar bayan sunyi, aka dauko babbar tabarma sabuwa aka shimfide a tsakar gida. Adidat ta fara fito da abinci da aka dafa tana shiryawa.

Su Yusuf suna dawowa suka hadu duka aka zuba abincin suka fara ci.

Tuwon shinkafa ne da miyar egusi, kasan miyar yare ba dai nama ba, ta sha kifi kala-kala, nama shima kusan kala uku, ga kponmo, fadar dadin abincin ma kam bata baki ne.

Ga kuma jollop din Taliya spaghetti wadda ko kallonta Kauthar bata yi ba tunda dama can ba cimarta bace.

Sai da suka ci suka yi nak, suka kora da ruwan sanyi.

Bata yi musu ba lokacin da Adidat tace ta tashi ta bi mijinta su koma masaukinshi. Ta musu sallama suka tafi. Zainab da Yusuf da suka rakasu dauke da kayan data bada Yusuf ya sayo mata, sai da suka ga tafiyarsu a motar da yaje da ita kafin suka juya.

Tafiyar mintuna ashirin da wani abu, ta shigar dasu garin Keffi. Babu wata hira da suke yi, sai jifa-jifa idan ya tambayeta wani abu ta bashi amsa.

Wani gidan masaukin baki suka wuce. Da alama anan ya fara sauka, saboda suna fita daga motar, hannunta ya ja suka shiga ciki kai tsaye zuwa wani daki dake hawa na uku.

Daga ita har shi a gajiye suke matuka, don ma cikinsu a cike yake sosai.

Suna shiga dakin wanka kawai suka yi, ya ja su suka yi sallah, daga nan suka bi lafiyar gado.

Da Asubahi ita fara farkawa. A gefe daban-daban suka kwanta, bata san lokacin da suka gangara suka hade a tsakiyar gadon har suka zama kamar abu guda ba.

Kwance yake a rigingine, ita kuma rabin jikinta na kanshi, kafafunta sarke cikin nashi, hannunshi a tsakiyar bayanta, ita kuma kanta akan kirjinshi.

Ta samu a hankali ta zare jikinta daga nashi ta shiga bandaki. Alwala ta daura ta fita. Dakin babu haske sai wanda hasken wutar bandaki data kunna yake kaiwa, ta hasken ta sameshi zaune a gefen gado da alama ita yake jira.

Magana yake mata, sai ya kula babu Aids a kunnenta.

Ya daga hannunta yana mata sign, “yaushe kika farka?”

Wasu abubuwa take ji a cikinta suna cunkushewa da kullewa da warwarewa a lokaci guda.

Al’amuran AbdulMalik cike suke da abin mamaki da daure kai. Har lokacin bata gama dawowa daga shock din sign language daya iya ba, wanda tasan ko rantsuwa tayi to ba zata yi kaffara ba, saboda ita ya koya.

Ta daga kafada tana mayar mishi da amsar, “yanzu ba jimawa.”

Bai sake ce mata komi ba shima ya shiga bandakin shima.

Lokacin daya fito har ta fara raka’atanil fajr. Ya shimfida wani abin sallar shima ya kabbara.

Bayan ya ja su jam’in sallar Asubah din, sake komawa suka yi kwanta. Don kuwa har lokacin da sauran gajiya a jikinsu. Ba su suka farka ba sai can wajen karfe tara.

Wannan karon shi ya rigata tashi, don kuwa har yayi wanka ya gama shiryawa tana kwance.
Sai daya gama da zai sauka kasa samo musu abinda zasu ci sannan ne ya tasheta.

Kafin ya koma dakin itama har tayi wanka ta shirya cikin Abaya ruwan madara da gyalenta. Ta dan yi mata yawa amma data sanya belt din rigar ta daureta, sai ta fito mata das a jiki. Tayi mata wani irin kyau mai daukar hankali.

Tana fesa turare data gani cikin jakar da Yusuf ya hada mata, ya tura kofar dakin ya shiga. Ta dan dakata tana kallonshi, casual shiga yayi, pants ne a jikinshi ruwan toka mai aljihuna a jiki kamar na sojawa, da sai ya sanya long sleeve shirt mai v-neck. Wani irin kyau yayi mata wanda da kyar ta iya dauke idanunta daga kanshi don kada yace tana mishi kallon kurilla. Amma daga yanayin dan murmushin da taga yana yi, tasan ya ma riga daya ramfota.

Dakin ya shiga, ya ja karamin coffee table zuwa tsakiyar dakin yana baza ledojin daya shiga dasu.

Take away ya fara fitarwa da robobin lemuka, bayan ya gama shiryasu ya juya yana kallonta, “abubuwan da suke dasu anan ba lallai mu iya cinsu ba shi yasa na je wani wajen”

Ta gyada kai cikin nuna alamun fahimta.

Kujera taja ta zauna yayinda yake zuba musu masa da farfesun kayan ciki a cikin disposable bowls.

A nutse suke cin abincin babu wata hira dake gudana sai jifa-jifa.

A lokacin ta fara bashi labarin tsarin da take yi a cikin ranta game dasu Adidat da iyalanta. So take yi kafin ta tafi ta samar musu gida a unguwa ta rufin asiri ba irin wadda suke ciki ba, kullum cikin tsoron abinda zai je ya zo, tana kuma so ko babu komi ta samarwa Adidat din sana’ar yi da zata dinga juyawa, tana kuma so ta mayar da Zainab makaranta da Yusuf.

Yana saurarenta har suka gama cin abincin bai ce komi ba sai data gama sannan. Ya kalleta yana murmushi, “way ahead of you baby, yanzu haka mun gama magana da wanda zai samar musu gida, he’s on it already.”

Ta rasa me zata ce mishi, ta rasa me zata ce. Sai kawai ta tashi ta je inda yake tsaye yana daura agogo a hannunshi, ta rungumeshi.

Tace “Mata gode Yaya Abdul, Allah Ya biyaka da mafificin alkhairi!”

A karon farko kuma na rayuwar aurensu, da tayi initiating wani abu. Ta tashi tsaye akan yatsun kafarta ta kai bakinta kan nashi in a peck, cikin abinda bai fi rabin sakan ba. Wai a tunaninta wannan ne kadai zai iya nuna mishi irin farin ciki da tayi da jin kalamanshi, don bata jin kalaman nata zasu isa.

A hankali tayi kokarin janyewa. A lokacin shi kuma ya maidata jikinshi da karfi, ya kamo bayan wuyanta ya kara hade bakunansu. Dagawar da bakinta yayi wajen fitar da dan sautin razanar da hakan ya haddasa mata, yayi nasarar nutsa harshenshi cikin nata, ya kamo ya fara gudanar mata da wasu irin abubuwan da suka sa kwalwarta ta fara neman tarwatsewa.

Tana cewa bata taba jin kwatankwacin abinda taji ba lokacin daya taba sumbatarta a gidanshi dinnan, ashe wancan lokacin ba komi taji ba akan wannan.

Kissing dinta yayi thoroughly, babu inda harshenshi bai shiga ya tabo ba a bakinta. Zuwa lokacin daya saketa, mintoci masu yawa ne suka wuce, sai da yaji numfashinta yana kokarin barin jikinta.

Ya riketa ganin kafafunta suna kokarin kadata, kallonta yake da wannan murmushin yana lasar. baki kamar wanda ya gama shan ice cream, “yumm!”
Sai taji kamar kasa ta tsage ta shige saboda kunya…

*****

Kwanansu hudu a garin, kullum da safe zai kaita gidansu Adidat inda zata wuni wajen ganin dangi da kara zantawa da Adidat din, shi kuma ya tafi wani wajen ko shi kadai ko tare da Yusuf, sai dare zai koma su ci abincin dare a can kafin kuma ya dauketa su koma masaukinsu.

A cikin dan lokacin aka samarwa su Adidat gida mai fadi kuma mai matsakaicin kyau a saman unguwar su Uncle Aminu.

Tunda shi AbdulMalik ya sayi gidan da kudinshi, ya kuma damkawa Kauthar a matsayin nata halak-malak, ta hanashi sayen kayan gida saboda a cewarta hidimar zata yi yawa. Shi kuwa budar bakinshi yace mata, ‘don wa yake neman kudin idan ba ita?’
Tace duk da haka.

Aka samo kayan daki masu kyau da quality aka sanya a gidan. Aka warewa Yusuf bamgarenshi can bayan gidan, shima AbdulFatah aka hada mishi nashi wajen.

Tuni an fara kokarin samawa Zainab makarantar da zata cigaba, wadda Kauthar din tayi alkawarin daukar nauyin karatun har ta kammala. Shima kuma Yusuf ta biya mishi kudin makarantar har ma ya fara zuwa a cikin satin.

Kamar kuma yadda tayi alkawari, ta dauki kudade masu kauri ta ba Adidat na tayi jari, shima AbdulFatah din haka ta dauki kwatankwacin abinda ta ba Adidat din ta bashi.
Fadar irin godiyar da suka yi kuwa ma bata bakine. A rana guda suka hada kayansu suka yi sallama da mutanen unguwarsu suka koma sabon gidansu.

AbdulMalik kwananshi hudu ya juya ya tafi. Ita kuma sai data yi sati guda cur kafin tayi haramar tafiya.

Ta ga kara wajen dangi kwarai da gaske. Aka dinga mata aiken abubuwa iri-iri na tsaraba har ta rasa ya zata yi dasu. Haka itama ta bi dangi ta dinga musu hidima da kyauta kamar me.

Haka ranar da zata tafi, gidannan haka ya yini a cike da yan’uwan Adidat da suka je mata bankwana.

Karfe biyu designated direban da AbdulMalik ya ware mata yaje gidan. Ta fito cikin zugar su Adidat suna mata Allah kiyaye. Adidat da su Zainab har da kukansu, ita kanta dakiya kawai take yi bata yi kukan ba. Don kuwa yan kwanakin da suka yi ta saba dasu sosai. Da ba don makaranta bama da tare da Zainab zata tafi ta dan yi mata kwana biyu, Adidat ta hana da cewa makaranta, bugu da kari kuma tasan Babansu ba zai bari ba.

Suna daga mata hannu haka direba ya ja motar suka tafi. Airport ya kaita inda jirgin karfe hudu na yamma yake jiranta.

Suna zuwa aka gama komi, jiran mintuna sha biyar kadai tayi kafin jirgin nasu ya daga.

Saukarsu a Lagos da misalin karfe hudu na yamma, hannunta rike da karamar jaka ta matafiya ta fito daga airport din tana duba wajen masu jiran baki ko zata hangi direban da AbdulMalik yace zai tura mata.

Karaf idanunta suka hade cikin nashi, bata san lokacin data ja tunga ta tsaya ba kyam a waje guda.

Ta rasa ko menene game da AbdulMalik da idan ta kwana biyu bata ganshi ba yake rikidewa ya canza mata kamanni gabadaya. Yadda take ji a ranta a lokacin, kamar ba kwanaki uku ne kacal tayi bata ganshi ba ido da ido, tunda dai kullum suna waya, suna musayar sako, watarana ma video call suke yi.

Takawa ta fara yi zuwa inda yake, inda shima ya fara tahowa wajenta, nan suka hade a tsakiyar wajen.

Harara take jefa mishi cikin wasa da tsokana da shagwaba, “kai Yaya! Shine kace ba zaka samu damar zuwa ka daukeni da kanka ba ko?”

Yayi dan murmushi, “tsokanarki kawai nake yi Kauthar, amma ai kin san babu ta yadda za ayi in kasa zuwa tararki yar Matata.”

Baki ta turo gaba tana shirin fara mishi mita ya katse mata hanzari ta hanyar kamo hannunta ya dan jinginata da jikinshi, “naji, nayi laifi shikenan? Kin hakura ko?”
Murmushi ta saki a tausashe tana kara lafewa a jikinshi tana jinjina kai.

Ya sumbaci goshinta a tausashe, “da kyau my Princess. Welcome back home.”
Ya kama hannunta zuwa wajen inda ya ajiye motarshi. Shiga suka yi ya ja su zuwa gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 23Kauthar 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×