Skip to content
Part 1 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

Ubangiji Ya kan jarrabi bayinSa ta hanyoyi da dama. Sai dai ita Jarrabawa ga ɗan adam daga Allah, tana ɗaya daga cikin alamun soyayyar Allah gare shi. Kyakkyawar halitta, tarin dukiya, zuzzurfan ilimin addini da na zamani haɗi da duk wata ni’ima da ɗan adam ke buƙata don ya rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali Ubangiji Ya hore masa, sai dai kash! A dai-dai lokacin da ya fara morar ƙuruciyarsa katsam! ya tsinci rayuwarsa a gadon asibiti kwance ba ya iya koda motsa wata gaɓa dake jikinsa.

Tsayin watanni biyar sai dai a kwantar, a tayar, a yi masa duk wata ɗawainiya, bayan kuma a lokacin da yake da lafiya mutum ne shi mai cike da ƙarfi da tarin ƙoshin lafiyar da ke sa shi tinƙaho da izza. Yau an wayi gari fararen kyawawan idanun sa kaɗai ke iya kai kawo tsakanin abubuwan da bakinsa ba zai iya taɓa su da kansa ba sai dai kallo kawai.

A hankali ya sauke ƙwayoyin idanunsa kan mahaifinsa dake tsaye yana kallonsa da fuskar tausayi. Kallon da ke tabbatar da cewa shi kaɗai ne yake iya gane haƙiƙanin abinda rayuwarsa take buƙata, shi kaɗai ne yake iya fahimtar yaren shirunsa.
Alhaji Ahmad Mukhtar ɗaya ne daga cikin manyan attajiran da kasuwancin su ya bunƙasa har yake amsa sunan sa a faɗin ƙasar Nigeria. Ya share ƙwallar da ta taru cikin idanunsa. Shi kaɗai ne ɗan da ya haifa, shine komai nasa. Ya dubi farin ba’indiyen Likitan da ke ta ƙoƙarin auna bugun zuciyar ɗan nasa, sannan da raunin murya kuma cikin harshen turanci ya ce, “Doctor idan duk abinda na mallaka a gidan duniya zai ƙare kan nemawa Mashkur lafiya a shirye nake in bada ko nawa ne, ni dai buƙatata ya miƙe ya taka da ƙafafunsa kamar yadda yake a baya, don wa nake neman kuɗin ne? Don me na tara dukiyar?”

Ya matso daf da shi haɗi da kai hannunsa ya shafi sumar kansa a hankali zuciyarsa cike da damuwa ya ci gaba da faɗin, “Doctor ka je ka yi duk abinda ya dace na yarda da kai sosai, sannan na ɗora hope ɗina a kanka.”

Doctor Imtiaz Abdulkalam Likitan dake jagorantar kula da lafiyar Mashkur ɗaya ne daga cikin manya-manyan likitocin da katafaren asibitin Max Super Speciality Saket da ke New Delhi ta ƙasar India ya tanada musamman don ceton ran al’umma ɓangaren larura irin ta Mashkur a tsammaninsu. Cikin yanayin tausayawa da ƙwarewa irin ta aiki Doctor Imtiaz ya dubi Alhaji Ahmad dai-dai lokacin da yake ƙoƙarin kammala abinda yake yi ga majinyacinsa, cikin harshen turanci ya ce, “Babu damuwa Alhaji za mu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu don ganin yaron ka ya samu lafiya, wannan aikin mu ne.”

Ya cire abin gwajin daga kunnensa kana ya fara tafiya a hankali, “Mu je office ɗina.”
Tattaunawar ta ɗauke su tsawon lokaci. Daga can waje matarsa Zinatu na zaune tana jiran sa har lokacin da suka kammala. Alhaji Ahmad na fitowa ta yi saurin miƙewa ta tare shi fuskarta na nuna alamun son jin halin da mara lafiyan ke ciki. Ya fahimce ta don haka bayan ya ƙaraso inda suke zaune ya ce, “Alhamdulillahi! Zinatu Likita ya sanar da ni da izinin Allah za su nuna ƙwarewarsu, don ganin Mashkur ya samu lafiya in har da sauran numfashinsa a gaba.”

Hawayen idanun Zinatu suka ƙarasa saukowa kan kumatunta ta ce, “Oh! Ya Allah ka agaza mana da lafiyar yaron nan.” Alhaji Ahmad yana dube-dube ya ce da ita “Ina Suraj?”

Ta numfasa, “Ya ɗan fita, yanzun nan zai dawo.” Rufe bakinta ke da wuya kuwa Suraj ɗin ya shigo. Alhaji ya yi musu bayanin wasu daga cikin abubuwan da suka tattauna da Likita a taƙaice, sannan ya ɗora da faɗin, “Sai ku shirya ku bi jirgin yamma ku koma gida ni ina nan sai abinda Allah Ya yi.”

Zinatu ta dube shi sosai, duk ya faɗa saboda larurar ɗansa, “Alhaji dama ka bari ni na zauna da shi, kai sai ka koma ka kula da harkokinka?” Ya yi murmushi cike da jin daɗin yadda take nuna kulawa ga tilon ɗansa duk da ba ita ta haife shi ba ya ce, “Zamana a nan ba zai dakatar da komai ba cikin harkokina, ku je kawai Zinatu na gode da kulawarki, hankalina ne ba zai taɓa kwanciya ba ko da na koma Nigeria kin ji?” Ta jinjina kai alamar ta gamsu.

Nigeria

A katafaren falon Zinatu da ke gidan Alhaji Ahmad su biyu ne zaune suna fuskantar juna
“Mene ne abinyi yanzu Suraj?” Zinatu ta tambaya tana duban fuskarsa.

Suraj ya gumtsi iska cikin bakinsa ya fesar, shima dubanta yake tamkar me shirin gano wani abu a kan fuskar tata, ga dukkan alamu kuma ba shi da amsar tambayarta.
Zinatu ta numfasa kana a karo na biyu ta ce, “Sam wannan dabarar ba ta yi ba, na tabbata ko dukiyar da Alhaji ya mallaka za ta ƙare kaf ba zai fasa neman lafiyar Mashkur ba, hakan na nufin asara za ta ci gaba da shafar mu marar iyaka, dama me muke yiwa? Kuɗi kuma gashi yana ta kaiwa kafurawan banzan can suna karɓewa bayan kuma Mashkur ba zai taɓa samun lafiya ba matuƙar ba mu muka je muka warware abinda mu ka yi masa ba.”

Suraj dai har yanzu bai ce da ita komai ba. Ta gyara zama tare da miƙa hannu ta ɗauko jakarta da ke gefe ta buɗe ta fiddo wayarta, ta fara laluben lambar da take son kira, bugu ɗaya lambar ta shiga ta kara jikin kunnenta.

“Kana ina ne Habib? Maza kazo mun ƙaraso gida.” Abinda ta faɗa kenan ta datse kiran sannan ta yi cilli da wayar gefenta kan kujera.

Mintuna goma suna zaman kurame Habib ya shigo falon idanunsa a kan fuskokinsu su duka biyun, ya ƙaraso daf da su ya miƙawa Suraj hannu suka gaisa sannan ya samu guri gefensa ya zauna. Zinatu ta dube shi a tsanake, yana cikin walwala abunsa bisa ga dukkan alamu bai tsinkayi babbar matsalar da ke tunkararsu ba.

“Mutanen ƙasar India, ina fatan kun sauka lafiya?”

“Fine Habibi, fatan mun same ka lafiya kai ma?” Zinatu ta faɗa cikin ƙarfin hali tana dubansa. Ya juya ga Suraj da har yanzu ba shi da bakin magana, “Yaya dai Bro, me ke going ne?”

Maimakon ya bashi amsa sai Zinatun ce ta amshe, “Akwai matsala a tafiyar nan Habibi mun kashe maciji ba mu sare kansa ba.”

Habib ya dube ta da tarin mamaki a fuskarsa, “Me ya faru Sister? Yi min bayani mana.”
“Game da ɓarnar kuɗin da Alhaji ya ke yi kan neman lafiyar Mashkur, abin ya yi yawa, banda asibitocinmu na gida Nigeria, asibitoci daban-daban da ke ƙasashen ƙetare a ƙiyasi ya kashe kuɗi a ƙalla naira miliyan sittin a cikin ƙasa da watanni uku, yanzu haka asibitin Max Super Speciality a can ƙasar India sun buƙaci wasu maƙudan kuma na tabbata dole zai ba su, ya kamata mu san abin yi tun kafin Alhaji ya yi wa dukiyar nan mummunar illa muna ji muna gani bayan kuma muna da tabbaci kan Mashkur ba zai taɓa warkewa ba.”

Habib ya yi shiru yana duban ƙasa, shi kansa ya jima da wannan tunanin a zuciyarsa kawai dai sun riga shi furtawa ne, wa ya kai shi jin ƙyashin irin kuɗin da Alhajin yake kashewa kan neman lafiyar wanda ba zai taɓa samun lafiya ba sai dai mutuwarsa?

Kudi Ko Rai 2 >>

5 thoughts on “Kudi Ko Rai 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×