Skip to content
Part 1 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

‘Yan mata biyu ne kyawawa da ba za su haura shekara 20 zuwa 22 ba, kansu ɗaya idan ka gan su kai tsaye ba za ka iya banbanta su da ‘yan biyu ba, suna sanye da kayan makaranta na boko, ɗayar na tafiya haɗe da ‘yan tsalle-tsalle, ɗayar kuma tafiya kawai take fuskarta ɗauke da murmushi. Mai yin tsalle-tsalle ta ce, ” Zhara yau sosai nake jina cikin farin ciki gaskiya dole ne yau na haɗa ‘yar wata ƙwarya-ƙwaryar party.”

Ta dire gaban Zhara dukan su suka tsaya kafin ta ci gaba da fadin “Ya kika ga fuskar Uncle Munir a gaban shugaban makaranta.” Zhara ta tuntsire da dariya “Wallahi Halima baki da dama, wallahi tausayi ya bani, ya yi wani tsuru-tsuru da shi ga uban gumi kamar an ciro shi daga cikin tafkin ruwa.”

“Ya ma daina baki tausayi wallahi mutum duk ya bi ya uzurawa rayuwar mu, abu na laifi da ba na laifi ba ya hau duka da zaginmu shi ya sa kawai na je na masa sharrin yana neman mata a gun shugaban makaranta, kinga gobe ai ba zai ƙara ba, ni fa so na yi ma a kore shi.” Suna mai cigaba da tafiya Zhara ta ce, “Kai Halima kora fa kin san adadin nauyin da ya ke kansa kuwa, ki dinga jin tausayi a ranki Halima sannan ai kai tsaye wannan ba zai sa a kore shi ba tunda karo na farko ne da a ka kama shi da hakan, kawai dai ki kiyaye kar a zo a gano gaskiya allura ta tono garma.”

“Hmm ni ban damu ba dan an koreshi koma miye ai shi ya janyowa kansa.” Suna tafe suna zancen har suka samu daidaita suka hau, ana zuwa unguwar su layin farko a ka sauke Zhara su ka yi sallama akan sai da yamma idan za su islamiya, tafiya kaɗan a ka ƙarasa gidan su Halima ta sauka ta biya shi kuɗi sannan ta shiga cikin gidan su tana waƙe-waƙenta, ta samu Hajiyar su tana shanya tufafin da ta gama wanki, kallonta Hajiya ta yi tana faɗin, “Allah ya shirye ki Halima naga sanda za ki yi hankali sallama wannan ba za ki yi ba sai dai ki shigo gida da waƙoƙin banza.”

Ta ɗan turo baki a shagwaɓe ta ce; “Oh Hajiyar mu shikenan daga shigowa ta kuma har an fara tarbana da faɗa ko kewata ma ba ki yi ba.” Tana sharce zane ta ce, “Rigimar taki ce zan yiwa kewa, ni dai je ki ki cire kayan makaranta ki zo ki yi sallah.” Cikin shagwaɓa ta ce,
“To amma fa yunwa nake ji Hajiyar mu, kuma dama ance ci na gaba da sallah, kar naje ina sallah ina tunanin ɗa’ami.” Hajiya ta gyaɗa kanta tana faɗin “Ni dai je ki kar ki cika min dodon kunne da surutun ki.” Ta nufi ɗakinta Hajiya ta ce, “ki saki jiki kizo kiyi sallah sannan ki ci abincin.” Ta riƙe kai aranta ta ce, ‘Idan har ba sallar nan nayi ba Hajiyarmu ba barina za ta yi ba.”

*****
Da yamma Halima ta biya ta gidan su Zhara ko da ta shiga har ta shirya ta ɗauki jakar ta da Ƙur’ani za su fito Halima ta ce, “Wai ya naji gidan shiru ne ina Mama da ‘yan biyu?”
“Kin manta na faɗa maki yau zasu tafi Kano bikin murnar dawowar Babban ɗan Daddyn Kano daga Australia.” “Oh na manta Yaya Hafiz da ya kammala karatun sa ko?”
“Shi fa.” Ta faɗa tana rufe gidan da key, ta je ta kaiwa maƙociyar su Aunty Sumayya ajiya, bayan sun fito suna tafiya a hanya Halima ta ce; “Su ‘ya’yan masu kuɗi sun ji daɗin su wallahi”
“Mu kuma ‘ya’yan talakawa fa.”
“To sai dai mu ce AlhamduliLlah kawai, ki duba kiga yanda karatun gaba da Sakandire Jami’a ya ke neman ya fi ƙarfin ɗan talaka sun rufe makarantu, da masu shekarar ƙarshe da masu shekarar farko da farawa komai ya tsaya cak! Su masu kuɗin da shugabanni masu faɗa a ji sun ja baki sunyi shiru ko a jikin su tunda su nasu ‘ya’yan sun kaisu ƙasashen waje suna shan romon ilimi ko a jikinsu.”

Cikin ajiyar zuciya Zhara ta ce, “Hakanne Halima ai ƙasar tamu ce sai addu’a, da yawa ina jin mutane suna kukan matsalar yajin aikin nan da aka shiga da yanzu sun gama sun fara fafatukar aiki bayan kammala NYSC.”

“Ki duba ko Yaya Mahmuod ya tattara duk wani buri nasa a kan karatun nan da kuma aikin gwamnati amma komai ya sauya sanadin yajin aikin dole ya koma kasuwa tare da Baba.” “Allah dai ya kyauta kawai.”
“Amin dan Alfarmar Annabi (S.A.W), ni har fargaba nake ji anya burinmu na zama lauya zai cika?” “Da yardar Allah zai cika ki dai cigaba da addu’a muna fatar sauyi ga ƙasar mu.”
“Allah ya sa.”
“Amin, kin iya hardar ki kuwa?” Zhara ta mata tambayar tana kallonta “A’a wallahi cikin sumuni uku biyu kawai na iya.”

“Tab ashe kuwa yau ke da Malam Isa mai raba ki dashi sai Allah.”
“Hahaha idan ban iya ba ko, kafin a fara biyawa sauran a kaina dama gyara ne ya mun saura rashin mutumcin nasa na yau sai dai ya yi wa wata ba dai Halima ba.”

*****
Tun bayan dawowar su Mama daga Kano Zhara ta fahimci Mama tana cikin damuwa sam bata da kuzari kamar koyaushe hakan sai ya jefata a damuwa, bayan ta ƙarasa wanke-wanke ta ɗora girkin dare kasancewar yau Alhamis babu islamiya, ɗaki ta shiga ta samu Mama tana zaune a kan kujera ta yi tagumi zama ta yi kusa da Mama ta dafa kafaɗan ta “Mama” cikin ajiyar zuciya Mama ta juyo da kallonta kan Zhara ta ce; “Na’am Maman manya har kin gama aikin ne?”
“Eh na ma ɗora tuwon “Gyara zamanta Zhara ta yi kafin ta ce; “Mama wani abu ya faru ne bayan tafiyar ku Kano?”
“Me ya sa kika mun wannan tambayar?”
“Mama naga tun bayan dawowar kike cikin damuwa da kin zauna ke kaɗai sai naga kina tunani, dan Allah Mama me ya faru ko matar Daddyn Kano ce ta maki wani abun kamar yanda ta saba?” Cikin ajiyar zuciya ta ce; “Zhara ban taɓa ɗaukar matsalar Hajiya Turai matsala ba bare har na sa ta a raina kema kin sani kuma.”

“Haka ne Mama, to faɗa min me ke damun ki?” Bata so ace ta ji ba har sai taga abinda ya turewa buzu naɗi sai dai bata da wani zaɓi da ya wuce ta faɗa mata ɗin kamar yanda Baban su ya umurce ta, dama ko bata tambaye ta ba tana da niyar kiran nata, “Zhara ba komai ne ya saka ni cikin damuwa ba ke ce Zhara” da sauri ta kalle Mama tana fito da idanu ta ce; “Ni kuma Mama?”

“Eh Zhara, lokacin da mu ka je Kano bayan gama biki da dare Mahaifin ki da Daddyn Kano sunyi magana a kanki da kuma Hafiz” Mama ta yi shiru, Zhara zuciyar ta ta dinga bugawa da ƙarfi ta shiga fargaban jin abinda ya ke bakin Mama, Mama ta numfasa kafin ta ce; “Sunyi shawara a tsakanin ku za su haɗa ki aure da Hafiz, Zhara abu biyu ne suka jefani cikin damuwa na farko ko ba kya so na tabbata mahaifin ki ba zai dubi illar auren dole ba zai ce zai maki ko da bakya so, sannan kuma ina duba matsalar mahaifiyar sa Hajiya Turai ta tsane ni na tabbata ba zata taɓa son abinda ya ke tsatsona ba, sannan.”

“Sannan me kuma? Wato ke da na ce kawai ki faɗa mata maganar tsayar mata da miji sai ki kawo wani zance can da zai sa ta bijire min ko?” Baba da tun ɗazun ya ke tsaye bakin ƙofa wanda sam basu ji shigowar sa ba ya yi maganar ransa a ɓace, ƙarasa shigowa ya yi ya zauna gefen Zhara suka sa ta a tsakiya Mama ta ce, “Kayi haƙuri Baban Zhara wallahi ba nufina kenan ba.” Ko ta kanta bai bi ba ya riƙo hannayen Zhara ya sa cikin nasa ta yi ƙasa da idanunta domin a tsorace take, ji take yi kamar ace mafarki take domin bata son abinda zai roshe mata dukan muradanta da take da su.

“Fatima Zhara na sani ke ɗin yarinyar kirki ce mai biyayya ba zaki taɓa bani kunya ba, Yayana ya nemi haɗa ki aure da babban ɗansa Hafiz domin ƙara ƙarfafa zumuncin mu ni kuma ba zan iya ce masa A’a ba, anan take na amince masa, dan haka ina roƙon ki da kada ki ba Babanki kunya da ya ke da matuƙar yarda a kanki.” Ya zuba mata idanu yana kallonta gumi ne ya ke tsattsafo mata cikin jikinta har ga Allah babu zancen aure a tsarin ta wannan lokacin dai, babban burinta ta yi hardar alƙur’ani da wasu littafai, sannan ta zama lauya domin ƙwato haƙƙin ‘yan’uwanta mata bayan wannan sannan ta yi aure, amma ba zata iya ɓata yardar da Babanta yake da ita a kanta ba, cikin sanyin murya ta ce, “Tunda har ka amince Baba nima banda wani zaɓi da ya wuce naka zaɓin.”

Cikin farin ciki ya ce; “Allah ya yi maki Albarka Mamana, na sani ke yarinya ce mai biyayya ba za ki taɓa ba Babanki kunya ba.”

Kallonsa ta yi da murmushi a fuskarta ta ce, “Amin Baba.” Mama dai kallo kawai ta bisu da shi ta sani Zhara ta amsa ne kawai dan ba zata iya musa masa ba, addu’a kawai za ta mata dan bata isa ta yi komai ba, amma tana ji mata tsoron zama da Hajiya Turai.

*****
Bayan magarib Zhara ta je gidan su Halima ta samu tana zaune a kan darduma idanunta a rufe tana karatun ƙur’ani Hajiya na lazumi, gaban Hajiya ta ƙarasa ta gaishe ta cikin ladabi cikin fara’a Hajiya ta amsa mata gaisuwar tana tambayar ta mutan gidan “Suna lafiya, Mama ta ce na gaishe ki.”

“Ina amsawa, kwana biyu ai haɗuwa ta yi wahala Insha Allah zan shiga gidan naku gobe ko jibi.”
“Allah ya nuna mana.” Halima ta ƙarasa kai aya ta juyo tana faɗin “kin san Allah karatun nan nake amma gaba ɗaya zuciyata tana wajanki.”
“Tunanin me ki ke a kaina to”
“Oho ni kawai dai tunanin ki nake.” Riƙo hannunta Zhara ta yi ta tashi suka shiga ɗakin Halima zama sukayi a kan katifa Zhara ta ɗora kanta jikin Halima ta sa kuka mai ƙarfi wanda tunda dama tun ɗazun ya ke ciyo ta tana dannewa dan bata son ko kaɗan ta nunawa Mama damuwar ta bare har itama ta damu, cikin tashin hankali Halima ta ce; “me ne ne Zhara baki da lafiya ne ko wani ne ya mutu?” Zhara ta kasa cewa da ita komai sai kukan da take, Halima itama ta sa kuka Hajiya ta shigo tana faɗin “Subhanalillah kai me ya faru kuke kuka haka?”
Cikin kuka Zhara ta ce; “Nima ban sani ba kawai Zhara ce ta zo tana kuka” tsaki Hajiya ta yi kafin ta ce; “Shi ne kuma dan shashanci maimakon ki lallashe ta ta faɗa maki abinda ke damunta sai kema ki fara kukan?” Zama tayi kusa da Zhara tana lallashin ta “‘Ya ta Zhara yi shiru ki daina kuka ki faɗa min abinda ya ke damun ki.”
Cikin kuka ta faɗa ma Hajiya komai, ihun kuka Halima ta sa Hajiya ta kai mata duka tana faɗin, “Bana son shashanci Halima za ki min shiru ko sai na ɓaɓɓallaki?” Gefe ta koma tana ci gaba da kukan ta sai dai ta rage sautin murya, cikin tausayi ta ce, “Kinyi albarka Zhara da har ba kiyi tunanin bijirewa mahaifin ki ba, Insha Allah Tunda har ki ka yi biyayya zaki ga sakamako mai kyau za kuma kiyi farin ciki, ki daina wannan kukan ki ƙara ƙarfafa zuciyarki kiyi ta addu’a a kan Allah ya sa hakan ya zama Alkhairi ga rayuwar ki, nima zan taya ki da addu’a insha Allah” Sosai ta lallashe ta da nasiha har ta yi shiru, ta fita ta barsu su biyu,

Hajiya na fita Halima ta matso tana faɗin “Yanzu shikenan burin mu na muyi karatu tare mu zama lauyoyi muyi aikin nemawa mata ‘yanci a tare duk ya roshe?”
Cikin muryar kuka ta ce, “Nima tunanin da yafi komai ɗaga min hankali kenan, ga hardata ma tsayawa zata yi.”
“Ba komai Zhara mu yi ta addu’a Insha Allah burinmu zai cika na tabbata zai barki kiyi karatu tanda ai shima wayayyen mutum ne mai ilimi ya san amfanin ilimi dole zai barki na tabbatar da hakan, ki ma ji daɗin ki kin samu damar karatun ki a ƙasar da wannan maganar ta samu ƙwarin gwuiwa domin ita ba auren take ji ba muradanta ne ba zata so ta rasa su ba, “Na kuma san za ki so shi duk da rabona da shi tun muna yara na tabbata yanzu ya zama ɗan gayu ya ƙara kyau da girma.” Cewar Halima. Zhara ta ce,
“Humm nima dai ai ba zan iya kawo shi a yanzu ba dan na jima ban gan shi ba, tun dai muna yaran, ban sani ba ko zan so shi ko shi ma zai so ni, zamu yi wa juna ko kuma A’a?”
“Insha Allah ma za ku yi wa juna Zharana ai son kowa ƙin wanda ya rasa ce.” D1

0]ukan wasa ta kai mata su kayi dariya a tare, Hajiya da take ƙofar ɗaki tana jinsu tayi murmushi aranta tana jinjina ƙauna irin ta su, su yi kuka tare suyi dariya tare komai nasu iri ɗaya ne, tana ma su addu’a Allah ya sa zumuncin su ya ɗora har ‘ya’yansu

***
Yau tun safe Baba yaje ya yi cefane ya kawo za ayi wa su Hafiz girki zai zo tare da abokin sa, suka zage ita da Halima su ka shiga kitchen suna girki, hakan ya sa Mama farin ciki ganin ‘yarta bata cikin damuwa, fargabarta ɗaya mahaifiyar Hafiz, Zhara ciki take da tunanin ya za taga Hafiz, shin zuciyoyin su za su karɓi juna ko kuma dai dukan su biyayya za su yi wa iyayen su? Ko da goma ta yi sun gama girki sun gyara gidan su kayi wanka su ka shirya cikin riga da siket na a tamfa kayan iri ɗaya hatta ɗinkin iri ɗaya su ka yi su ka fito kamar ‘yan biyu, suna zaune suna firar yanda za su ganshi haɗaɗɗi ne kamar yanda su ke hasasu shi ko kuma akasin hakan, suka jiyo tsayuwar mota jim kaɗan su ka jiyo ‘yan biyu Hassan da Hussain sun shigo suna ihun ga Yaya Hafiz nan ya zo.

Zhara ta riƙe hannun Halima da ƙarfi har sai da hannunta ya yi ƙara, “Kai za ki ɓallani.” “Halima a tsorace nake, ban san me ya sa na ke jin faɗowar gaba ba.”
“Kinga ki ƙarfafa zuciyar ki kar ki zama matsoraciya, faɗuwar gaban ba komai bane dan wannan ne karo na farko da za ki tsaya da wuni taɗi.” Komawa ta yi ta kwanta tare da rufe idanunta, zuciyar ta na ta saƙe-saƙe iri-iri ba tare da ta iya cewa da Halima komai ba.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.7 / 5. Rating: 49

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Kuskuren Waye? 2 >>

43 thoughts on “Kuskuren Waye? 1”

  1. Nazifi Ahmad Chikawa

    Kai Masha Allah basira iya basira
    Muna biye da ke a wannan kasaitaccen labarin domin jin yadda zata Kaya

  2. Wai! Laipin dadi qarewa. Gsky banso ace anan Zan tsaya da karatun wannan labarin ba, har naji na qagara inga cigaban shi. Ba shakka an Zuba hikima da fasaha Sosai a ciki.

  3. Ma sha Allah, ina matuƙar yaba miki da jinjina miki yake fasihiyar marubuciya, Allah ya ƙaro dubun basira, muna biye dake a cikin wannan haɗaɗɗiyar labarin naki dan kuwa labari ta tsaru, fatan alkairi nake miki kullu’yaumul

  4. Dadin dake makale da labarin na daban ne amma baza muyi mamaki domin kedin gwanache achikin gwanaye Allah kara basira

  5. Wow! A gai da Indo Aisha, gwana marubuciya mai tarin hikimomi.
    Fatan Allah Ya kara basira da jajircewa Ameen 👏

    Fatan alheri ‘yar uwa 👍

  6. Maryam Tata Muhammad

    Masha Allah. Ina kyautatawa littafin zaton yin ma’ana har zuwa karshe, domin ba karyar arziki ba ta manyan gidaje tun a farko. Allah Ya dafa!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×