Skip to content
Part 43 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Rintsi idanunsa yayi zuciyarsa na dukan uku-uku muryar dady ya jiyo yana faɗin wannan ba ita ba ce” likitan ya ce “bari mu duba sauran biyun to” ajiyar zuciya Anwar yayi yana mai dafa kafaɗar Hafiz “AlhamdulilLah! Abokina ba ko ɗaya a cikin su” ajiyar numfashi ya yi ‘AlhamdulilLah!’ ya faɗa a zuciyarsa yana mai fita ɗakin da sauri yana ƙara godiya ga Allah. Sallama suka yi wa likitan suna mai yi masa godiya. Zaune suke a masauki falon Dady “ba mamaki bayan ya ajiye su ne ya ɗauki su waɗan nan da hatsarin ya rutsa da su.”

“Eh tabbas kam hakan ce ta faru, sai dai abin ya fara ba ni tsoro fa, saboda naga wankin hula na shirin kaimu dare, duk inda ake zato ba su ba labarin su, sannan kuma ‘yan-san-da sunyi iya ƙoƙarin su amma babu wani labari. Jikina ya yi matuƙar sanyi.”

Dady yayi maganar cikin damuwa. Tashi Hafiz ya yi ya je wajan tagar falon yana kallon harabar gidan ya ce. “Ni kuma Dady wani tunani ne yake yi mini yawo a cikin ƙwaƙwalwata, duk da dai banda tabbaci a kan hakan.”

“Mine ne? Komai ƙanƙantar tunani karka barshi a ranka ba mamaki faɗar zai iya kawo mana wata mafitar” dawowarsa yayi ya zauna a kan kujera cikin jan numfashi ya ce.

“Zhara suna a kusa da mu, tabbas ba wani wajan suka tafi ba.”

“Idan har ba wani wajan suka tafi ba Hafiz ai da mun gansu tunda babu inda ba mu je ba, sannan ‘yan-san-da suna ƙoƙari wajan neman na su.”

“Shi yasa na ce suna kusa Anwar, saboda binciken da ‘yan-san-da  suka yi da a ce sun bar garin nan da dole za a samu wata shedar gani da ido a tashoshin garin nan, hakan kuma duk wasu masu ababin hawa dai da suke da ƙungiyoyi mun je amma ko mai kama da su ba a gani ba. Hakan yasa nake tunanin tabbas suna garin nan kuma cikin dangi.”  dukan su suka yi shiru na ‘yan daƙiƙu kafin daga bisani Dady ya katsi shirun “maganar nan da kayi tasa mini wani zargin, duba mana karfe nawa yanzu.” kai dubansa ga agogon da ke manne a hannunsa ya yi “ƙarfe goma daidai” Hafiz ya ba Dady amsa idanunsa a kansa, komai Dady bai ce ba sai miƙewa da ya yi tsaye yana ɗaukar key ɗin mota “Dady fita za ka yi?” Anwar ya masa tambayar yana mai kafe shi da idanu, “za mu koma gidan Yayarta Fati na fi zargin suna gidan ta ko kuma dole ta san ina suka je” karɓar key ɗin Anwar yayi suka fita gaba ɗayan su.

Cikin sa’a suka samu Maigidan tare da baƙo a ƙofar gida suna magana, yana ganinsu ya yi sallama da baƙon ya zo wajan su “sannun ku da zuwa ku ne tafe da daren nan.”

“Wallahi kuwa Alhaji Usman, ai mun zo ba mu tarar da kai ba.”

“Allah sarki da yake nayi tafiya jiya na dawo da yamma, bismillah ku shigo” falonsa ya kaisu bayan sun zauna “ya kuma ƙarin haƙuri Malam Husaini kuma lokaci ya yi”

“To ka ga ni lokaci ya yi”

“Allah ya jikansa Allah yasa ya huta, Ubangiji Allah ya ba mu guzirin tarar da su alfarmar Annabi (S.A.W)”

“Amin muna godiya sosai, Allah ya ba da lada”
“Ai ranar da a ka yi rasuwa  ina gari ranar addu’a da safe tafiya ta ta so mini, na so na kira ko ta waya na ma ta aziyya  Fati take faɗa mini ai ba ka ƙasar an ta kiran wayar ku ba a same ka ba” cikin gyara zama Dady ya ce. “Tabbas anyi haka, ba komai Allah dai ya ba da lada.”

“Amin ya Allahu. Abubuwa marassa daɗi sun ta faruwa, na dawo na tarar da maiɗakin Mamacin da ita Zhara a ke yi faɗa mini abin da ya faru” kallon-kallo a ka shiga yi tsakanin Dady da su Hafiz suna masu sauki a jiyar zuciya kusan a tare. Alhaji Usman ya kalle su da mamaki “lafiya kuwa?”

“To Alhaji Usman a yanzun dai na ce lafiya saɓanin daƙiƙon da suka gabata. Saboda ko da muka zo ba mu tarar da kowa a gidan ba, mun ta yawon nema amma ba mu gansu ba, har gidan nan mun zo a ka ce ba sa nan. Yanzun ma dai mun zo ne ba dan muna da tabbacin za mu same su ba.”

“Wannan ai shashanci ne ku zo har gida kuma ta ɓoye ma ku gaskiya, ni wallahi sam ban sani ba, sannan da na dawo ba ta faɗa mini ka zo ba, kawai dai sun faɗa mini abinda ya faru, gobe ma suke shirin tafiya Jigawa wajan baffan su.”

“Ba komai kasan ɓacin rai babu abinda ba ya sawa, AlhamdulilLah dai tunda suna nan dama addu’ar da muke ta yi kenan Allah yasa suna hannun ƙwarai” miƙewa yayi tsaye yana faɗin ina zuwa” bayan fitarsa falon Anwar ya ce. “Ikon Allah Dady ka ga dai hasashen Hafiz ya zama gaskiya.”

“Wallahi kuwa ai sai mu godema Allah da ya sauƙaƙa mana lamarin.”

“Mu tafi ko?”

“Mu tafi ina?” Anwar ya masa tambayar idanunsa a kansa” fuska a haɗe ya ce “gida mana, tunda an sa ina suke ai magana ta ƙare”

“Humm duk kuka da ciwon da kayi na son ganinta fa ya tashi a banza” harararsa ya yi yana mai kama hanyar fita, “eh ai fa yanzu ka samu kanka dole ma ka samu zarafin hararata.”

“Hafiz Anwar duk ku dawo ku zauna.”

“Dady bai kamata mu zauna ba tunda hakan suka zaɓa kawai mu yi tafiyar mu, haba kwana nawa suna wahalar da zukatan mu da kuma jikin mu”

“Fushi ba na mu ba ne Hafiz, ko me suka yi suna da gaskiya, laifin na mahaifiyar ka ne ba na kowa ba, duk abinda suka yi ni banga laifin su ba. Dan haka koma ka zauna” zama ya yi fuskarsa a haɗe, duk da haushinta da yake ji sai dai zuciyarsa a ɗokanci take da son ganinta.

zaune take a kan kafet ta kife kanta jikin kujera “wai ba za ki raba kan ki da wannan ƙuncin ba ko, abincin kirki ba kya ci, ko yaushe kina ƙunshi cikin ɗaki kina ƙunci, wallahi kar ki kashi kanki abanza a kan wani ɗa namiji da ba a ce dole sai da shi ne za ki rayu ba” ɗago kanta tayi tana share hawayen da suke kwaranyowa a cikin kurmin idanunta ta ce. “Ni fa ba a kan Yaya Hafiz ba ne, kawai ina  kewar Abbana ne.”

“Humm na yarda da kewar Abban na ki, amma harda maganar Hafiz tunda an hana ki magana da shi, haifar ki fa muka yi ba za ki fi mu wayo ba. Duk abinda kikaga mun yi mutuncin ki ne muke janyo ma ki, domin banga dalilin nacewa ɗan wacce ba ta san darajar ki ba.”

“Momy ai to na ga ba shi ne ya mana laifin ba ko, kuma ko Allah dai ya halicce mu baya kama bawansa sa laifin wani bare kuma mu bayi. Don Allah ku fahimci ni, Dady da Yaya Hafiz ba su cancanci hakan daga gare mu ba.”

Momy za ta yi magana Mama ta katseta tana faɗin “ƙyaleta Yaya Fati rashin sanin ciwon kai ne yasa ana nuna mata gabas tana yin yamma, ƙarshen w… Shigowar Alhaji Usman yasa ta yin shiru, yana daga bakin ƙofa ya ce. “yanzu kun kyauta abin da kuka yi? Saboda Allah bawan Allah nan ya cancanci hakan daga gare ku? Kun kuwa san irin wahalar da ya sha wajan neman ku, ya zo har gidan nan ku ɓoye masa kanku.”

“Oh Allah dai yasa ba faɗa masu kayi suna gidan nan ba Alhaji?”

“To zan ɓoye masu gaskiya ne, ko irin ƙwaƙwalwar ku ce da ni. Sam ba ku kyauta ba abinda kuka yi” Mama ta sunkuyar da kanta “kayi haƙuri, kawai munyi hakan ne dan yanki duk wata alaƙa da su saboda zaman lafiyar mu, dan matuƙar ba mu fita rayuwar su ba Turai ba za ta taɓa barin mu zauna cikin salama ba wannan yasa muka ɓoye masu.”

Zama ya yi a kan kujera yana faɗin “sharrin mutum ɗaya ba zai goge alkhairin mutum biyu ba ko ma na ce alkhairai” ya nuna Yaya Fati yana faɗin “ke Fati babu adadi na sha jin kina yaba alkhairin ɗan’uwan mijin Ƙanwar ki, to saboda me za ku biye wa shirmen wacce bata isa tayi komai ba um, sannan taya za ki raba alaƙar da ta riga da ta haɗu, kina tare da jinin ƙanen sa, sannan ga cikin ɗansa jikin ‘yar ku, ai alaƙa ta riga da ta haɗu babu zance raba wa.”

“Hakan ne am… Ɗaga ma ta hannu ya yi “kinga Fati ba na son jin komai, ku tashi mu je ga su can a falo” wani irin farin ciki ta ji har ba ta san sanda ta nufi hanyar fita waje ba “ai sai ki zo ki ɗauki mayafi, in kin so ma daga can sai ki bi su tunda kare ya canye zuciyar ta ki!” Kallon Mama tayi jiki a sanyaye ta kasa ɗaga ƙafafunta daga inda take Alhaji Usman ya ɗauki hijab ɗin da ke kan kujera ya miƙa ma ta “kinga Zhara ƙyale iyayen nan na ki maza ki je ki ga mahaifin ki da mijin ki kinji ko” gyaɗa kai kawai tayi bayan tasa hijab ɗin ta fito kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.

Kanta na kifi jikin Dady ji take kamar Abbanta ne, kuka take sosai, ya kasa hanata sai ƙoƙarin haɗiye nasa kukan da yake, Hafiz ya kafeta da idanu tausayinta yake ji sosai, ji yake kamar ya rungumota jikinsa ya lallashe ta.  “Uhm! Ina mai miƙa ta’aziyata a gare ku Ubangiji Allah ya masa rahama, ya kuma ƙara mana juriya da haƙurin rashin sa da muka yi, domin rashi ne da ciwonsa ba zai taɓa barin zukatan mu ba har sai bayan ba mu” jan numfashi ya sake yi a karon farko kafin daga bisani ya ci gaba da magana “ina kuma ƙara ba ku haƙuri da abinda Turai ta yi ma ku wanda sam babu yawo na ko sani na a ciki,”

“Mu ne za mu ba ka haƙuri da har muka ɓoye ma gaskiyar inda muke, har ga Allah munyi hakan ne saboda tunanin dawowa cikin ku tamkar sake yankan tikitin ɗin wulaƙanci ne a wajan Turai, hakan yasa muka yi ƙoƙarin nisanta kanmu da ku.”

Murmushin takaici Dady ya yi kafin daga bisani ya ce. “Na roƙe ki ko ba yau ba kar ki sake yanki mini hukunci da laifin da ba ni na aikata ba, domin na shiga tashin hankali na rashin ganin ku, sannan ita Turai me ta isa ta yi, ikonta ake ba wai ita take yin ikon mu ba, dan haka ku manta da duk abinda ya faru na ma ki alƙwari In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba da yardar Allah”

“In sha Allah, Ubangiji Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar zumunci.”

“Amin ya Allah. Ku ɗauko kayan ku sai mu tafi gida.”

“Haba Alhaji gidan da a ka tozarta su saboda shi gidan ne za ka ce ta koma bayan an riga da an kwance mata zane a cikin jama’a.”

“Ke Fati me yasa ne kike son mayar da hannun a gogo baya ne, kina matsayin babba amma kina so ki mayar da kan ki babbar kwabo iyi!”

“A’a daina yi mata faɗa gaskiya ai ta faɗa, ba damuwa su shirya zuwa safe za mu tafi Kano In sha Allah, ni kaina sai na fi samun natsuwa idan har suna a kusa da ni” Mama ta kalli Dady tana faɗin “anya kuwa Yaya kawai dai a bar shi na zauna anan ɗin,”

“Idan kika ce hakan tamkar ba ki huci ba ko?” Ajiyar zuciya tayi har cikin ranta ba ta son zama kusa da Turai sai dai ba ta son musu da shi ne yasa ta amince ba dan ta so hakan ba. Bayan sun yi sallama sun koma ciki Dady sun fita waje a ka bar ta daga ita sai Hafiz, da rairafe ya ƙarasa gabanta yana mai kafeta da idanu “kin kyauta hakan da kika yi ko? Kin kuwa san irin halin da na shiga. Na tabbatar da da ana mutuwa kafin wa’adin mutum ya yi tabbas da tuni damuwa tasa na jima a kushewata,”

“Kayi haƙuri ni ma ba a son raina ne nayi hakan ba, na shiga damuwa fiye da yadda ka shiga domin abu biyu ne na rasa a tare, Abbana da kuma mijina” janyota ya yi jikin shi kusan a tare suka saukar da ajiyar zuciya”rayuwata ba za ta taɓa yin haske ba matuƙar babu ke a tare da ni Zhara, ban san wani irin so nake yi ma ki ba, sannan ba ke kaɗai ba ce ki ka yi rashin Abba ki sani wannan rashin na mu ne gaba ɗaya, mutuwar sa ta matuƙar girgiza ni, uhm! Tsakanin mu da shi kawai sai addu’a amma munyi rashi babba wanda ba za mu taɓa samun abinda zai maye mana gurbinsa ba,”

Ƙara shigewa tayi jikinsa ba tare da ta iya cewa da shi komai ba. Kiran Dady da ya shigo wayarsa yasa shi miƙewa tsaye tare da ita yana faɗin “Kinga Dady yana kira na a waya nasan zai ce mu tafi, ni kuma ban ga ji da ganin ki ba, ko za ki zo sai mu tafi masauki.” fito da idanu tayi tana faɗin “kai a’a ba zan iya ba, ka tafi Allah ya tsare, gobe ai muna tare.”

“To mine ne a ciki Dady ki ke kunya ko Anwar.”

“Ni dai ka tafi kawai gobe za mu haɗu Allah ya tsare” shafa cikinta ya yi idanunsa na a kanta “fatan dai yana lafiya” tana gyada kai ta amsa masa “lafiya lau yake” haka ya tafi suna shauƙin juna.

Da murna Khadija da Kande suka tare su, bayan sun ci abinci sunyi wanka Kande ta shigo ɗakin Zhara da yake gidan “sannun ku da hanya, Maman masu gida duk gajiyar hanya ce tasa a ke shirin baccin yamma” tashi tayi ta zauna tana murmushi “kawai dai na kwanta ne, ya aiki”

“AlhamdulilLah!”

“Ina matar gidan ne tunda muka zo ba mu ganta ba” Mama da ta idar da lazumi ta ma ta tambayar, cikin jimami ta faɗa masu abinda ya faru. “SubhanalilLah! Abu bai yi daɗi ba, Allah ya kyauta” bayan fitar Kande Zhara ta kalli Mama tana faɗin “kinga zumunci irin na Dady ko, shi yasa a lokacin nake ta son ke da Momy fati ku fahimci n, kar a ƙi faɗa masu gaskiya”

“Koma dai miye ya riga da ya faru sai dai a guji gaba kuma.”

Bayan kwana biyu da dawowar su Zhara ta koma gidanta, yayinda Mama ta ci gaba da zama tare da Khadija a gidan Dady. Da dare tana kwance jikin shi suna kallon arewa24 hannunsa cikin na ta yana murzawa “Yaya Hafiz”

“Um mine ne?”
“Kayi haƙuri ka dawo da Halima ɗakinta.”

“Za ta dawo amma ba yanzu ba.”
“Me yasa?” Ta masa tambayar tana mai tashi zaune idanunsa  a kanta ya ce. “Na fi so sai ta natsu ta fahimci rayuwa sannan.”

“Humm ni dai kayi haƙuri don Allah komai ya wuce, sati ɗaya fa, na tabbatar da yanzu ta gane kuskurenta, kuma na sha ganin kiranta amma ba ka ɗagawa don Allah kayi haƙuri komai ya wuce don Allah” shiru ya mata ta masa cakulkuli ya riƙi hannayenta yana dariya “ke ko, shi kenan na ji za ta dawo.”

“To yaushe?”

“Ba daɗewa In sha Allah” sumbatarsa tayi a baki “na gode Sweet Babyna”

“Albishirin ki”

“Goro fari ƙal”

“Ina hanyar dawowa muka yi waya da Dady suna hanya tare da Momy ya dawo da ita.”

Rungume shi tayi “kai gaskiya na ji daɗi sosai, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba”
“Amin. Banda bakin yi ma ku godiya ke da Mama na tabbatar da ƙoƙarin ki da na Mama ne yasa Dady ya amince Momy ta dawo”

“Ka daina godiya domin mahaifiyata ce ba zan taɓa farin ciki ba matuƙar ba ta tare da mu” haɗe fuskokinsu yayi yana goga hancinsa jikin na ta “ina son ki irin son da baki ba zai iya furta wa ba” Murmushi tayi “hakan nake jin ka a raina ko ma na ce fiye”
“Na yarda da kina jin kamar  hakan ɗin dai amma ba zan yarda da ya fi ba. Zo mu je ɗaki ki ji.”

*****

Mama ta shiga ɗakin Momy dan yi ma ta sallama kasancewar yau za ta tare gidan ta da Hafiz ya saya ma ta a jan bulo ta tarar da ta idar da sallah tana cire hijab “Hajiya Turai za mu tafi gida.”

“Humm kin rantsa dai a dole dai sai kin yi kitson wance duk da  ba a da gashin wance, to sawa ya dawo da ke Kano hakan ba zai burgini ba har sai idan kin sa ya aure ki mun zama kishiyoyi sannan ne zan tabbatar da kin isa kin tinɓatsa!” Dariya Mama tayi tana faɗin “me hali da ba ya taɓa barin halinsa sai mai tsananin rabo, to Allah ya kyauta sai kisa himma kiyi ta yin haushin na ki ke kaɗai.” har ta kai ƙofa ta juyo tana kallonta “kina ji ba ina so na ba ki shawara ki lallaɓa sauran igiyoyin auren biyu da suka rage kar ki je garin janye-janyen ki ki janyo tsinkewar sauran, dan wannan karon ba zan sa ya dawo dake ba, dan kin san a yanzun ma alfarma ta ce kika ci” har ta fita Momy ta kasa ko da motsi bare har ta samu zarafin mayar ma ta da amsar maganarta. Zama tayi diɓis a kan gado “Alhaji ka cuce ni! Haka kawai ka janyo mini raini a wajan wulaƙantaciya matar nan.!”

Zhara tana zaune falo tana dannar waya Halima da Hafiz suka fito ɗakin shi suna dariya, kallo ɗaya ta yi masu ta kawar da kanta, zama ya yi kusa da ita “ya dai Madam, sannu da hutawa.”

“Yawwa sannu da fitowa, an tashi lafiya”  ta gaishe shi cikin murmushi, “lafiya lau” idanunta a kan Halima da ta zauna gefen shi “Halima an tashi lafiya, ya gajiyar hanya”
“Lafiya lau” ta amsa ma ta fuska ba yabo ba fallasa. “Zan fita  a kwai abubuwan da nake so na kammala yau saboda gobe da sassafe In sha Allah za mu bar nan zuwa Lagos, jirgin dare za mu bi zuwa India, dan haka ki shirya cikin lokaci.”

“An gama Sweet Babyna, amma ina so na shiga na yi Mama da Momy sallama.”

“Ki dai je wajan Maman” komai ba ta ce da shi ba, dan ta riga ta fahimci baya so tana shiga wajan Momy tunda dai taƙi sakin komai ya wuce ko ranar da suka je gaishe ta da ɓacin rai suka bar gidan.  Suka raka shi mota sai bayan fitar shi suka dawo ciki. “Zhara” har ta kai ƙofa ta juyo tana amsawa “na san ko ki faɗa ko kar ki faɗa kina jin farin ciki a ranki kina jin kinyi nasara a kaina ba, to bari murnar karen ki ya kama zaki Humm” tayi ƙwafa.

“Humm farin ciki kuma, eh to ina farin ciki saboda kasancewar na isa da mijina duk abinda na ce shi yake yi, domin ba dan ni ba da har yanzu kina gida, wannan ma abin farin ciki ne gaskiya sai hamdala ga Ubangiji.”

“Kiyi lokacin ki ne, lokaci mai juyawa ne, kar ki yi fatan ya dawo kaina domin lamarin ba zai yi kyau ba, tafiya dai ce ko ga ki ga hanya za ki gani ne.”

“Na ga alkhairi, Allah kuma  ya ba ki sa’a, ki dai kiyaye halshin ki domin shi ne ke kaimu ga yin da-na-sani” daga hakan ba ta ce da ita komai ba ta yi shigewarta ɗaki.

Zama tayi gefen kujera idanunta suna ciko da hawaye ya zanyi ko nayi ƙoƙarin hana kaina kishin Zhara ba zan iya ba, saboda Allah ina adalci anan din a ce dole sai anyi tafiya da ita ni kuma ko oho saboda kawai babansa ɗan’uwan Babanta ne a dole sai an nuna mini wariyar launin fata. Ai koma miye su ne ba sa so a zauna lafiya.”

*AlhamdulilLah! AlhamdulilLah!! AlhamdulilLah!!! Dukan godiya ta tabbata ga Ubangiji da ya nufe ni da kammala littafin KUSKUREN WAYE? KUSKUREN da yake ciki Ubangiji Allah ya yafe mana, abinda muka faɗa daidai Allah ya datar da mu alfarmar Annabi (S.A.W).  Tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) da iyalan gidan sa gaba ke ɗaya.*

*Ina miƙa Godiya ta ga Bakandamiya Allah ya saka ma ku da mafificin alkhairin sa ya kuma ƙara ɗaukaka. Ina godiya ga masoya da suka juri bibiyar labarin har zuwa kammala shi, Allah ya bar ƙauna.*

*Mu haɗu da ku a sabon littafi na mai suna Fargar Jaji, da kuma Mahaukaci ne ko Aljani?*

Kuna tare da A’isha Abdullahi Yabo. Fulani

<< Kuskuren Waye? 42

3 thoughts on “Kuskuren Waye? 43”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×