Skip to content
Part 16 of 25 in the Series Labarin Asiya by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Misalin karfe shidda na yamma ta shigo gidan nasu don daukar Baba su wuce gida, tun kuwa da ta shigo suka cika mata kunne da labarin sun ji hirarsu, kamar yau ne suka fara jin muryarta a gidan radio, kila ko don wannan karon hirar ta musamman ce a kan abu na musamman, kowa yabawa da sanya albarka yake yi, tare da fatan alkairi.

A haka ta shiga bangaren Hajjah.

Da Haidar ta fara cin karo, cike da murna ya makaleta yana fada mata ya kalleta a tv ana hira da ita.

Ta yi murmushi hade da shafa kansa

“Momy na ce Hajja ta kira min ke in tambaye ki ba ta kira ba.”

Ya fada fuskarsa dauke da yar damuwa.

A daidai lokacin kuma Asiya ta shiga cikin falon inda Hajja da Jamila ke zaune suna kallo.

“Dama me za ka tambaye ni? tambayar ni yanzu.”

“Menene cutar HIV, da mutane suke gudun mai ita?”

Asiya ta yi saurin kallon Hajja, ita ma Hajjar Asiyar take kallo, a hankali ta mayar da idonta kan Jamila suka hada ido.

Zuciyarta ta karye, tausayinsa ya kamata, yana dauke da cutar a jikinsa amma bai santa ba, wane hukunci zai yanke masu ne idan ya girma kuma ya fahimci yana dauke da wannan cutar ta dalilinsu.

Allah ya sani a duk cikin yaranta ta fi kaunar Haidar ga mi da tausaya masa, saboda rayuwarsa akwai kalubale a nan gaba.

Ta yi kokarin mayar da hawayenta tare da fadin”Wata cuta ce da ke kama mutane, tana da hatsari sosai.”

“Ta ya ake kamuwa da ita?” ya kuma jeho mata wata tambayar.

“Ta hanyar jinin mai cutar ya hadu da na mara ita.”

Ya zuba mata ido, da alama bai fahimta ba.

“Ana nufin a debi jinin mai cutar a karawa mara ita, ko mai cutar ya yi amfani da reza ya yanke sai mara ita ya dauka shi ma ya yanke jininsu ya hadu.” cewar Jamila tana kallonsa.

Ya jinjina kai

“To Momy menene kuma shayarwa?”

Wannan karon Hajja murmushi ta yi kafin ta ce “Ba wa yaro nono”

“Kenan masu cutar basu ba yaronsu nono sai madara? Haka na ji kin ce a cikin hirarku.” 

Jinjina kai Asiya ta yi ba tare da ta ce komai ba. 

“Momy ke ma kina da cutar ne, na ga ba ki ba Baba Nono?”

Ba Asiya kadai ba, hatta su Hajja sun yi mamakin tambayar Haidar, don haka Jamila ta yi saurin cewa “Shi Baba baya son shan Nono, tashi maza ka dakko shi wajen Aunty Amarya zasu tafi gida.”

A guje kuwa ya fita.

Asiya ta share kwallan idonta, zuciyarta ta yi mata nauyi, wani daci da kunci take ji, ina ma ciwon nan iya kansu kawai ya tsaya bai shafi yaransu ba.

Tabbas da laifinta kamar yadda Hassan ya fada, da ta rika zuwa asibiti tabbas  kila da ba ta haifi Haidar da wannan cuta ba.

“Me ye kuma abun kuka, ki share hawayenki kar yaran nan su shigo su same ki.” cewar Hajja tana kallon Asiya.

Ta shiga share hawayen nata tana fadin “Ina jin tsoron ranar da Haidar zai tuhumemu gami da cutar da ke jikinsa Hajja. Sannan ina tausayawa rayuwarsa a gaba, ya zai yi da kalubalen da ke gabansa?” 

Kafin Hajjar ta ba ta amsa aka turo kofa, Haidar din ne ya shigo tare da  Zee

“Momy dinkina fa?” Haidar ya  tambaya lokacin da yake dora mata Baba a kan cinyarta

“Kar ka damu gobe sha Allah zan kawo ma, ba sai jibi za ku tafi ba?”

Ya gyada kai alamar  eh.

“To zan kawo ma gobe sha Allah. Kuma sai ka ga yadda dinkin ya yi kyau” ta yi maganar cikin murmushi tana kallonsa. 

Ya fara tsallen murna

“Ai dai ka iya karatun sosai ko?”

Asiya ta katse shi

Ya kalli Jamila “Na iya sosai ko Aunty, dazu da kika rika min tambayoyi da asuba kin ci gyarana?”

Ta girgiza kai “Ko sau daya ban ci gyaranka ba. In sha Allah nasara taka ce yarona.”

Ya kuma yin wani tsallen ya kwasa da gudu don kaiwa Addah albishir.

“Zee anya kuwa? .” Asiya ta fada hade da kallon Zee

Su Hajja suka tuntsire da dariya

“Me ta yi?” Jamila ta yi tambayar hade da janyo Zee jikinta har lokacin dariya take yi

“Ba ki ga ta  ganni ba, amma kallon arziki ma ta ki yi min.”

Suka kuma yin dariya a tare.

“To aikin san dai halin ta. Sa ce ba ka dariya sai ta baci”

Tabe baki Asiya ta yi ba tare da tace komai ba. 

Hirar tasu yau duk a kan batun gasar Haidar ne, dukkansu suna da confidence a kansa saboda ya yi ma abun shiri da taimakon malamansa da kuma mutanen gida da ke tsaya masa ta ko wane bangare. 

Musamman Hassan baya wasa a bangaren komai na Haidar. 

Duk wani abu da ya shafi Haidar to baya daukarsa da wasa. 

Magunguna, abincinsa, karatunsa, shi ya sa ko wane lokaci Haidar yake cikin kuzari ko yawan zazzabi ba ya yi. 

Sashen Addah ta biya don yi mata sallama, a lokacin  Haidar na ta gwada yadda zai yi a wurin musabaka, Addah na murmushi lokacin da ta ke jin sautin muryar jikan nata cakwai a cikin kunnenta tamkar yaron larabawa. 

Asiya ma farin ciki ya cikata, tana rokon Allah ya ba yaron nata nasara, lallai za ta yi masa wata kyauta ta musamman, ba shi kadai ba, sai ta yi wa addini wata hidima domin nuna godiyarta ga Allah. 

Yau kam duk yaran gidan ne suka yi mata rakiya, har zuwa lokacin da ta samu keke. 

Ta mika hannu hade da daukar Baba da ke hannun Haidar, lokaci daya kuma ta shafa kansa. 

“Zan kawo ma kayanka gobe in wuni muna hira.” cikin murmushi take maganar yayin da take jin wani tausayinsa a can kasan zuciyarta. 

Shi ma murmushi kawai yake da ke nuna tsantsar farin cikinsa. 

Da yake yau aikin safe gare ta, gida ta bar Baba, ko bacci bai tashi ba, Hassan ne ya shirya shi da zai wuce kasuwa ya aje shi a gidansu wajen Addah shi kuma ya wuce kasuwa. 

Misalin karfe daya na rana ta shigo gidan, a lokacin Haidar na masallaci ita ma alwalla ta yi don gabatar da sallahr azhar. 

Tana jin ihun murnarsa bayan da yaga dinkin shaddar da zai sanya a gobe, tsalle kawai yake yi yana murna su Hajja na taya shi. 

Farar shadda ce kal, dinkin babbar riga, ga farin takalmi farar hula da agogo fari. 

Asiya na sallame sallah ta kalli har ya sanya kayan sosai ya yi kyau a cikinsu. 

Murmushi hade da kallonsa kawai take ganin yadda kamanninsa yau suka fita sak da na mahaifinsa. 

Addu’a ta shafa hade da dakko waya suna mishi hotuna har da video, ita daman Jamila tun da ya shigo yana tsallen murna take mishi video har zuwa lokacin da sanya kayan. 

Sun yi hotuna sosai kamar ranar sallah. 

Sannan suka zauna cin abinci. 

A lokacin  tattauna maganar bikin Jamila suke yi, wanda yake ta matsowa,  yayin da Haidar ya sagale hannu ya kurawa Asiya ido a lokacin da take cewa,  “Ai wannan biki zamu girgije Hajjah, musamman ni uwar amarya gagara tsiwar anguna.” 

Rai bace ta juyo gami da dubansa  a lokacin da ta kai karshen maganarta

“Tashi ka fita can wajen yara, ka kura min ido kamar za ka cinyeni, komai nake fada kana daukewa a kanka.” 

Jiki a sabule yayin da idonsa ya cika da kwalla ya nufi kofar fita. 

“Zonan yarona.” Jamila ta fada, don kuwa sam ba ta son ta ga ran Haidar a bace. 

Maimakon ya zo, hannu ya sanya hade da share hawayen da ke bin fuskarsa. 

Dalilin da ya sa Jamilar ta shi kenan  ta isa wajensa gami da daga shi da kyar ta goya shi a bayanta tana zagaye falon da shi. 

Hakan ya sa ya tuntsire da dariya, ba shi kadai ba ma hatta Asiya da Hajja sai da suka yi dariya. 

“Ai Haidar ma ba shi da dabi’ar kallon mutane idan suna magana yau ne dai kuma, shi da ko zama ma ba ya yi idan ya ga baki.” 

Hajja ta yi maganar tana kallon inda Jamila ke ta tsalle da Haidar a baya suna dariya 

Sai da ta tabbatar ya saki jikinsa sannan ta sauke shi, tana sauke shi kuwa ya yi waje a guje yana dariya. 

Asiya ta sauke wayar da take masu video ita ma tana dariya. 

Misalin biyar ta fito falon da niyyar tafiya gida saboda za ta yi girki. 

kwance yake a main palour  inda ya dora Alqur’ani hizif goma a kan fuskarsa, daidai kunnensa kuma wayar Addah ce da yake yin recording din karatunsa. 

A hankali yake sauraro yana kuma bi. 

Asiya ta dauke Alqur’anin saman fuskar nasa tana murmushi. 

A hankali ya bude ido ya kalle ta, daga bisani kuma ya lumshe.

Ganin bai yi magana ba ya sa  ta dauke wayar da ke gefen kunnensa, hade da tsayar da karatun. Bai motsa ba, illa dai kara bude idonsa da ya yi yana kallon ta. 

“Kana fushi da ni  ko?” 

Kai ya girgiza alamar a’a

“To ya ka yi cool haka?”

 Ta tambaya hankalinta a kansa. 

“Ba komai.” ya ba ta amsa kamar baya son yin maganar. 

“Idan ba komai to…” ta yi maganar hade mika masa hannunta alamun su gaisa. 

Ya yi siririn murmushi hade da mika mata hannunsa bayan ya tashi zaune, suka zubawa juna ido suna murmushi. 

Daidai lokacin Jamila ta fito “Wow! Wallahi kun yi kyau ku tsaya a haka in yi maku hoto.” 

Hotunan kuwa ta daukesu, sannan Asiya ta zare hannunta. 

“Momy shi kenan ba za ki dawo gobe ba ki ga tafiyarmu ba.” 

Ya yi maganar daidai ta kai bakin kofa,, hakan ya sa ta dakata hade da dawowa ta zauna a kan hannun kujerar da yake kai. 

“Na so ganin tafiyarku Haidar amma ina da aikin safe, sai dai Babanka da su Adda duk zasu kasance da kai, ni kuma zan yi ta yi ma addu’a, sannan alkawarin da na yi ma idan ka yi na daya yana nan, har ma da surprise gifts” 

Ya yi murmushi “Na gode, ki yi min addu’a to. Malam ya ce Allah yana amsar addu’ar iyaye a kan yaransu.” 

“kullum ina yi ma sai dai kari Haidar.” 

Ya kwantar da kansa a barin jikinta. 

“Yarona fa duk ya yi sanyi tun bai je filin musabakar ba.” cewar Jamila tana murmushi. 

“Wallahi kuwa kin dai gani, irin ɗokin da yake yanzu duk babu, ya yi wani la’ asar gabadaya, kar ya je ya kasa yin komai.” 

Asiya ta fada hade shafa kansa. 

“Haba Momy zan yi kokari sosai fa, Malaminmu ya ce idan na yi na daya zai siya min keke babba na zuwa makaranta.” 

Murmushi suka yi kafin Asiya ta ce

“Ka natsu ka ji, gabanka ya daina faduwa,, in sha Allah za ka yi nasara.” 

“Ba za ka rakani ba yau?” ta yi maganar a lokacin da take ta shi daga kusa da shi. 

Murmushi kawai ya yi ba tare da ya tashi ba. 

Ita ma murmushin ta yi hade da shafa kansa “Wish you all the best my son.” 

Jamila ce ta yi mata rakiya har sai da ta samu Napep sannan ta dawo. 

******

Tana isa gida kitchen ta shiga, ba ta karasa abincin ba sai bayan sallahr magriba. 

Shi ya sa  tana idarwa toilet ta fada hade da watsa ruwa hade da dauro alwallar sallahr magriba. 

Ganin Baba  yana rikicin yunwa dole ta tsaya  ba shi abinci sannan ta mike da niyyar kabbara sallah. 

A daidai lokacin kuma wayarta ta yi kara “Sweet sister” ta gani hakan ya sa ta yi saurin dagawa don Jamila ce

“Aunty ki yi sauri ki zo yanzu” cikin wata irin murya Jamila ta yi maganar. 

Gaban Asiya ya fadi, saboda ta san koma menene tabbas babba ne. 

Allah dai ya sa ba jikin Hajja ne ya tashi ba, don tana da low B.P.

Dama tun dazu ta lura kamar ba ta jin dadin jikinta, ta yi shiru ne dai ba ta tambayi Hajjahn ba. 

Ta so ta yi sallahr amma ba ta da natsuwar yin ta, saboda yadda kiran Jamilar ya daga mata hankali. Hakan ya sa ta dauki Baba da ya fara bacci ta goya, ta yi waje jiki a mace. 

Tun da mai napep din ya aje ta gabanta ya tsananta faduwa Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un kawai take ambata a hankali, tana shiga harabar gidan ta ga motar Hassan hakan ya sa ta kara jin koma dai menene serious ne.

Ba kowa a tsakar gidan idan ka dauke yaran da suke a baranda zaune suna  kallon Asiyar da wani yanayi a kan fuskarsu wanda ta kasa fassarawa.

Kaf! Mutanen gidan suna bangaren Hajja,, hakan ya sa tana tura kofar ta gansu jugum-jugum yayin da wasu ke ta share hawaye, sai gabanta ya kuma tsananta faduwa kamar ana fisgarta haka ta rika tsallake mutane zuwa asalin falon Hajja

A guje Jamila ta fada kanta hade da fashewa da kuka mai tsanani tana fadin “Sai hakuri Aunty,, mun yi rashi, mutuwa mai daci hade da taba zuciya.”

Jikin Asiya ya dau rawa, cikin rawar murya take tambayar waye ya rasu “Ba dai Hajjahta ba ko? Waye ya rasun fada min don Allah. “

“Aliyu ne Allah ya yi wa rasuwa. “

“Wane Aliyun? ” Asiya ta tambaya cikin rashin fahimta

“Haidar ne.” Cikin kuka Jamila ta karasa maganar.

“Haidar! Wane Haidar din?  Haidar nawa?”

“Sai hakuri, lokaci ya riga ya yi, addu’a za ki yi mishi”

Asiya sama-sama take jin wannan magana, ba ta ma gane mai maganar ba saboda yadda idonta ke gani bishi-bishi.

A hankali kuma ta daina gane komai daga nan kuma sai ta ji shiru ta daina gani komai da muryar kowa.

Lokacin da ta farko kwance ta gan ta a kan cinyar Aunty Muna jikinta jike da ruwa, wannan ya tabbatar mata da suma ta yi. 

A hankali ta rika bin mutanen dakin da kallo, kafin daga bisani kwakwalwarta ta rika dawo mata da maganganun da ta ji.

“Haidar ya rasu?” ta fada a hankali, kafin ta furta kalmar Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un a hankali

Hawaye suka shiga ambaliya a fuskarta yayin da Aunty Muna ke ta ba ta hakuri

“Aunty Haidar ya rasu fa, ko cikakkiyar awa biyu ba mu yi da rabuwa ba, kuma lafiya kalau na bar shi.”

“Ikon Allah ya fi gaban haka Asiya” Aunty Amarya ta fada.

Asiya ta daga kanta tana kallon Aunty amarya.

“Aunty Haidar fa! Haidar fa Aunty!” lokaci daya ta kuma fashewa da kuka. 

“Sai hak’uri Asiya, ki yi hakuri ki yi masa Addu’a, mutuwa ba sai da ciwo ba.” cewar Aunty Amarya da ta taso zuwa inda Asiya ke kwance tana kuka mai ban tausayi. 

“Kai Aunty, kai Aunty, Innalillahi Wa’inna Ilaihir raji’un”  cewar Asiya cikin kuka. 

“Ashe dazu kallon karshe yake min ban sani ba, na kore shi, dana san yana min kallon karshe ne dana bar shi ya ci gaba da kallona. Ashe ganin karshe na yi masa dazu. Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un. Aunty Yarona. Yarona mai kwazo Aunty.”

“Sai hakuri Asiya, yi hakuri…” haka mutanen falon ke ta maimaitawa, wadanda ko ganesu Asiya ba ta yi. 

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un” 

kalmar da ta rika maimaitawa kenan a yayin da numfashinta ke sama yana kasa.

Hakuri kawai ake ba ta masu addu’a kuma na yi mata.

Idan ana sallah ba a magana, don  Hajja tana uwar daki   ta suma ba iyaka, ga ciwonta ya tashi, kokarin tafiya da ita asibiti ma ake yi, sai dai kuma kowa hankalinsa baya jikinsa.

“An riga an gama shirya shi, zamu fita da shi a yi masa sallah a kai shi gidansa na gaskiya, ku yi masa addu’a ba kuka ba, Haidar yaron kirki ne, mai hakuri ga ilmi, lallai da ya yi tsawon rai za a yi shahararren malami, in sha Allah yana da masauki mai kyau.”

Tana jin muryar ta san malamin makarantar Islamiyar su Haidar ne, shi ya sa  ta yi saurin mikewa tana fadin “Ina son in gan shi na karshe don Allah kafin a fita da shi.”

“Bismillah” malamin ya fada.

Aunty Muna ce ta riketa zuwa dakin da aka shirya Haidar din. 

Tsaye Asiya ta yi tana kallon Haidar nade cikin farin likafani.

Idan an fada mata bayan tafiyarta Haidar zai rasu za ta ce karya ne, lallai bawa ba a bakin komai yake ba. Dazu yake wasanshi amma yanzu sai yadda aka yi da shi.

A hankali ta duka hade da tallofashi ta rumgume a jikinta, hawaye masu dumi suka gangaro mata.

A fili take magana cikin raunanniyar murya.

“Aliyu na san kana ji na, kawai dai ba za ka iya magana ba ne, na sha fada maka ina sonka, yanzu ma zan kara maimaitawa ina sonka Haidar”

A hankali ta yi amfani da hannunta daya wajen share hawayen da ke bin fuskarta.

“Ina alfahari da haihuwarka Aliyu, a matsayina na mahaifiyarka na yafe maka duk wani laifi da ka yi min, bare ma ni ba ka taba min komai ba. Ina yi ma addu’a Allah ya haskaka makwancinka.” ta kuma kai hannu hade da sharce hawayenta.

“Aliyu na san ka tafi da burika da yawa a zuciyarka ma fi girma shi ne batun musabakarku na gobe, da ina da iko dana cika maka wannan burin. Amma alkawarin dana yi ma na siya ma digital qur’an da Qur’ani hizif sittin mai pieces zan cika ma shi, zan saya in bayar sadaka. Addu’ar da ka bukata dazu a wajena zan yi ma, ba zan daina ba har kasa ta rufe idanuna Haidar.”

Ta kuma share hawayenta a karo na uku, ba ita kadai ba, hatta  Hassan, Aunty Muna, malaman Haidar na Islamiya sharce hawaye suke yi.

“Halinka na gari ya bi ka Haidar, halinka na gari ya bi ka Aliyu, Allah ya gafarta maka… “Haka ta ci gaba da fada yayin da sautin kukanta ya tsananta.

Hassan ma kuka yake yi ba zai iya tabuka komai ba, Aunty Munan ce dai jiki a mace ta janye ta.

kuka take yi sosai hade da sambatu.

“Allah kai ka ba ni Aliyu, ka kuma karbe abun ka, Allah ka sanya min hakuri da juriya. Allah ka sanyaya min zuciyata, Allah ka gafartawa Aliyu, ni dai na yafe masa wallahi. Ya Allah don ni kada ka azabtar da bawanka, Allah ka son ina son shi Allah. Allah ina son yarona, Allah ka sanya min hak’uri da juriya Allah. Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un. Aliyu! Aliyu!! “

Duka dakin Asiya ta kashe masu jiki,  kuka kawai ake yi ba mai iya ba ta hakuri.

Haka aka fita da gawar Aliyu wajen karfe takwas na dare aka kai shi makwancinshi na karshe.

A lokacin  tuni aka fita da Hajja zuwa asibiti yayin da mutuwar Aliyu ta karade yan’uwa da abokan arziki

Alhaji Abdallah ma wanshekare ya dakk o hanya zuwa gida, Aunty Zee ma haka ta biyo hanya bayan ta kwana ba bacci sai kuka.

Su Kubrah ma da Mukhtar sun iso.

Abokan aikin Asiya kullum  suna hanya wajen jajanta mata, haka yan Islamiyar su Haidar suka yi gayya zuwa gaisuwa.

Da Asiya ta gansu sai mutuwar ta dawo mata sabuwa, ta wuni kuka kamar ranar aka yi mutuwar.

<< Labarin Asiya 15Labarin Asiya 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×