Skip to content
Part 42 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Bayan kwana biyu, kamar yadda Boka/Malam ya mata umarnin komawa don karɓar abubuwan da za tayi amfani da su ta samu cikar burin rayuwarta. Ta dira a gabanshi tun da duku-dukun safiya, don tsabar ɗoki da zakwaɗi ko Lovina bata gayyata wajen rakiya ba.

Lokacin da ta isa gurin ko fitowa bai kai ga yi ba, sai da ta zauna zaman jiranshi fiye da awa ɗaya. Lokacin da ta shiga bukkar ta durƙusa a gabanshi kuwa jikinta har rawa yake yi saboda tsabar murna, babu abinda idanunta ke hange zuciyarta ke hasashe sai ganinta a gidan Salim matsayin matar aurensa.

Tuni ta gama haɗa bajet ɗin yadda rayuwarta za ta gudana, da yadda za ta dinga yin facaka da kuɗi da kayan kuɗi, da irin manyan motoci da shiga ta alfarma da za ta dinga yi tana taka wanda take so ta ci uban wanda ba ta so.

Bayan dogon tsibbace-tsibbace da zane akan ƙasa yana sharewa tsulum tandun kwalli ya bayyana a gabansa. Ya ɗauki tandun kwalli ya miƙa mata, ta sanya hannu biyu ta karɓa gaba ɗaya jikinta na kyarma

“Kamar yadda na faɗa miki rannan, wannan shi ne kwallin da za ki saka a idanunki, sannan ki tabbatar ranar da kika sanyashi kun haɗa idanu da shi Salim da kuma Rahma a lokaci guda. Kina haɗa ido da shi, to shi kenan, zance ya ƙare. Zai manta da duk wata ɗiya mace da ya taɓa sani a duniya sai ke kaɗai zai dinga gani a idanunsa yana tunawa da ke a zuciyarsa. Haka itama Rahma kuna haɗa ido da ita za ta ji gaba-ɗaya Salim ya fita a ranta, ba ta son shi ba ta ƙaunarshi. Kuma ko da zai zama su biyu kaɗai suka rage a duniya, sam babu aure a tsakaninsu.”

Matsananciyar murna ce ta cika mata ciki, ji take kamar ta tashi ta taka rawar jin daɗi.
Da kunnen basira take sauraren duk wasu bayanai da yake karanta mata tana haddacewa a ƙwaƙwalwarta.

A karo na biyu ya ƙara ɗauko wata laya baƙa ƙirin mai kauri ya miƙa mata
“Wannan kuma a bakinki za ki saka, idan kin tabbatar kun haɗa ido da shi da ita, sai ki tauna layar ki haɗiyeta. Shi kenan zance ya ƙare, yadda wannan layar ta shiga cikinki babu zancen fita, to babu wani mahaluki da zai iya karya mana wannan aiki da yardar Allah!”

Samira ta duƙufa ta dinga mishi godiya cikin murna da tsananin jindaɗi kamar ya bata aljannah. Bayan ya sallameta jiki na rawa ta fice daga bukkar ta fara tafiya a gaggauce har tana haɗawa da gudu, babban burinta ta fice daga cikin dajin ta isa titi ta samu motar da zai mayar da ita cikin Kaduna da gaggawa.

*

Ko da ta koma gida, wani babban abin takaici da baƙin ciki shi ne yadda ta shafe kwanaki uku tana jelar zuwa gidansu Rahma bata samunta. A rana ta huɗu ne Allah ya tarfa ma garinta nono ta yi sa’ar ganinsu su biyun. Bayan ta shafe yini guda cur a gidan, daman a zuciyarta ta ƙudurta a wannan ranar baza ta koma gida ba sai burinta ya cika, idan ya kama ta kwana ne ma za ta kwana.

Daman Iyallu ta ce mata Rahman ta jemakaranta ne, amma ta faɗa mata ƙarfe huɗu za ta dawo. Don haka ta miƙe ƙafa tana zaman jiransu, tsabar samun guri irinna Samira da ganin yadda Iyallu ke haba-haba da ita har wani gani-gani take yiwa masu aikin gidan, minti ɗaya biyu ta daka musu tsawa tana hantararsu kan ɗan kuskure kaɗan.

Kamar yadda Iyallu ta ce, ƙarfe huɗu da minti ashirin Samira ta ji ana buɗe gate ɗin gidan alamun za’a shigo da mota. A dabarance ta matsa jikin window tana leƙen tsakar gidan sai taga motoci biyu sun danno kai cikin gidan. Ɗaya motar ta security ce, ɗayar kuma wata latsetsiyar Benz ce tana ta ɗaukar ido da sheƙi alamun sabunta.

Tana kallo aka buɗe gidan baya, Rahma ta fara fitowa. Wata doguwar riga ce a jikinta ta wani rantsattsen swiss lace baƙi mai adon fulawoyi gold, ta yafa gyale mai faɗi a jikinta.

Yadda tayi wani irin kyau, da wani kwarjini da tayi da cikar kamala da haiba, sai da Samira ta ji gabanta ya faɗi, ta daɗe bata ga Rahma ba, sai taga ta sauya mata sosai, ta zama wata irin babbar mace ƙasaitacciya wadda ita kanta idan za ta cire hassada ta san Rahma ta riga ta fi ƙarfinta nesa ba kusa ba.

A maimakon jikinta yayi sanyi, zuciyarta ne ta ji ta ƙara cika da tsanarta gaba-ɗaya, da gasken-gaske take so ta ga Rahma ta tagayyara, haka kawai babu gaira babu dalili.

Tana kallo shi ma Salim ɗin ya fito daga ɗaya gefen, suit ne a jikinshi waɗanda suka yi mishi matuƙar kyau nesa ba kusa ba. Ta shagala da kallonshi baki a sake sakaka har bata san lokacin da suka shiga cikin falon gidan ba. Sai da ta ji alamun buɗe ƙofa.

Da bala’in sauri kamar walƙiya ta ruga zuwa hanyar kicin, ta laɓe a gurin ta lalubo kwallinta ta rambaɗa a idanunta, cikin sauri ta dauki layar ta jefa a baki. Ta juya da hanzari ta fice zuwa falon daidai lokacin da su Rahmar suka shiga falon, tana ƙoƙarin ƙaƙaro fara’ar dole ta manna a fuskarta.

Rahma tana ganinta, ta saki jakar hannunta ta nufeta da sauri ta rungumeta cikin matsanancin murna tana mata oyoyo.

Wani irin Ƙamshi mai tsananin daɗi yayi mata marhabun a hancinta, haka nan itama ta sanya hannu ta rungume Rahmar ba don ranta ya so ba. Kishi ya cika mata rai fal.

Rahma ta tsaya tana kallonta da murna tace,
“Lallai ƙawata idonki kenan? Kiyi haƙuri, Iyallu ta faɗa min muna ta samun saɓani, kina ta zuwa ni kuma bana nan bamu samu mun haɗu ba. Afuwan! Wallahi abubuwa ne suka yi min yawa shi yasa!”

Ita dai sai murmushin yaƙe take saki saboda an ce idan ta sanya layar a baki kada tayi magana har sai ta ga haɗiye layar. Ta dinga ƙoƙarin su haɗa idanu da Rahma har Allah ya bata sa’a suka haɗa idanun, lokaci ɗaya sanyin daɗi ya dabaibaye zuciyarta.

Rahma da bata san wainar da take toyawa ba, ta ja hannunta har zuwa gaban Salim wanda yake tsaye a tsakiyar falon. Ta tsaya a gabanshi tana mishi wani irin sansanyan murmushi ta ce
“Dear, ka ga babbar ƙawata Samira da nake ta baka labari, yau dai Allah ya nufa kun haɗu!”

Ya kalleta a kaikaice, cikin sa’a shi ma sai suka haɗa idanu. Sai taga ya ɗan dakata yana kallonta, kafin ya ɗauke kanshi ya mayar ga Rahma yana maida mata da martanin murmushinta, da daddaɗar muryarshi ya ce
“hakane Baby, Allah ne bai yi haduwar tamu ba tun a baya sai yanzu!”

Ita kuwa Samira ganin sun haɗa idanu daƙyar ta samu ta taune layar nan ta haɗiye tana jin ɗacinta yana mata maƙaƙi da hamami har tsakiyar kwanya, ta cigaba da kallonsu tana zare ido cikin uƙuba.

Hirarsu suke yi suna ƙus-ƙus a tsakanin su biyun, kamar ma sun manta da ita tsaye a gefe ɗaya, kuma duk kusancin da take da su bata ji me suke cewa ba.

Ba a jima ba Salim ya juya ya ƙara kallonta, kafin ya juya yana kallon Rahma ya ce
“Baby bari in wuce. Mom tun dazu take ta kirana game da canjin wajen da za ayi dinner. Bari inje inji yadda ake ciki. Pls idan Mama ta fito ki gaishe ta.”

Akan idanun Samira ba kunya ko kara Rahma tayi kasa-kasa da murya tana wani karairaya da firirita,
“Tun yanzu za ka tafi Husband? Ba za ka tsaya ka ci abinda nace zan haɗa maka ba na musamman?”

“Kiyi haƙuri, idan zai kai gobe kiyi ki ajiye min tunda zan zo goben da safe. Idan kuma kina ganin zai lalace to kawai ki bari sai goben kiyi min.”

Tayi wani murmushi mai haɗe da fari tana rangaji duk cikin salon jan hankali. Kamar wata mutum-mutumi, haka Samira ta tsaya tana kallonsu har Rahma ta bi bayan Salim da nufin yi mishi rakiya.

Suna ɓace ma ganinta tayi amfani da wannan damar ta ruga kicin, ta buɗe firij ta ɗauki lemun Fanta ta buɗe gorar ta kafa kai tana sha a haukace ko Allah zai sa ɗacin bakinta ya ragu.

Tana juyawa suka haɗa ido da Rahma, wadda tayi tsaye hannu naɗe a ƙirji tana kallonta da fuska ɗauke da lallausan murmushi. Ƙirjinta ne ya buga daram! Gaɓoɓinta suka fara sanyi, domin har yanzu babu wani alamu da ta gani a tattare da su mai nuna za su rabu da juna balle a kai ga zancen daina batun aurensu har a gangaro ga maida auren kanta.

‘To ko dai ba yanzu asirin zai fara aiki a kansu bane?’
Ta tambayi kanta cike da wasi-wasi da kiɗima a zuciyarta. Sai kuma ta tuna ai Malamin ya ce aikin da yayi mata sha yanzu magani yanzu ne.

Da takun ƙasaita Rahma ta taka har zuwa inda take tsaye ta kama hannunta suka koma falo, kan kujera mai ɗaukar mutum biyu suka zauna. A karo na biyu Rahma ta kama hannunta ta ɗora mata cheque ɗin kudi, kamar wata wawuya haka ta bi Rahma da kallo mai cike da alamun tambaya, ta kasa buɗe baki ta ce uffan!.

Murmushi Rahma tayi
“Mijina ne yace in baki, a matsayinki ta babbar ƙawata ki yi hidimar bikinmu da su”

Kamar wacce aka sheƙa ma ruwan sanyi, jiki a sanyaye Samira ta duba takardar da kyau, sai ta zaro ido a kiɗime ganin naira na gugan naira miliyan ɗaya a rubuce! Bakinta na rawa ta ƙwato magana daga bakinta
“Kai! Waɗannan maƙudan kuɗaɗe haka?”

Rahma tayi ƴar dariya ta ce,
“Wannan ai ba komai bane a wajen dear. Shi yasa a karo na ƙarshe zan baki shawara Samira, ki haƙura da duk wasu mugayen ƙudirirrikan da ke ranki a kanmu, ki bada kai bori ya hau. Domin tuni mun daɗe da wuce saninki.”

A gigice ta ɗaga kai tana kallon Rahma fuskarta ɗauke da mamaki, tsoro, alamun tambaya.

A karo na biyu Rahmar ta saki siririyar dariya ta cigaba da cewa,
“Kin yi mamaki ko? Haba Samira! Wannan ai ba wani abin mamaki bane, don kuwa duk wani hali da kike ciki da duk wasu maganganu da abubuwa da kike yi a bayan idona, ina nan zaune a gida ake zuwa a feɗe min su har da recording, don haka ki daina mamaki”

Ganin yadda Samirar tayi wuki-wuki tana zare idanu ne yasa Rahmar ta dan sake sakin dariya wadda ta ƙara fitar mata da kwarjininta, muryarta a tausashe ba alamun ɓacin rai ko kaɗan ta cigaba da cewa
“Kar ki damu, wallahi ko da wasa ni ban riƙe ki a zuciyata ba. Duk da cewa dai daga farko na kasa yardarwa kaina cewa wai ke babbar ƙawata kece zaki iya yi min wannan abin. A maimakon abin farinciki da taya murna ya sameni ki tayani, a’ah, sai ma kike neman hanyar salwantar min da farin cikin da na samu.

Duk da cewa dai dama ba haka kika so ganina ba tun farko, so kika yi in ma fiki lalacewa, in zama magajiyar karuwai, yar shaye-shaye ko? To kuma sai Allah Ya so ni da rahmarshi, tunda dama can ke kanki kin sani tun farko wannan ƙazantaccen harkar ba ya cikin tsarin rayuwata. Ke kika tursasani, kika yi amfani da halin rauni da na shiga kika tunkuɗani ramin halaka, a maimakon ki taimaka min tunda a wancan lokacin abinda za ki taimaka min ba komai bane daga cikin abubuwan da kika mallaka.”

Tayi shiru tana sauke numfashi, ɗan murmushi ta saki wanda bai kai zuci ba tunawa da abinda ya wuce, ta ci gaba da cewa,
“Abinda yasa kika ga duk ban damu da waɗannan abubuwan ba, saboda ta dalilin hakan ne na hadu da Salim. Wanda shi ne silar shiryuwata, kuma shi ya tsamoni daga halin halaka da sanadiyyarki na jefa kaina. Shi da kanshi Allah ya saka masa tausayina a zuciyarsa, yayi nadamar karɓar budurcina da yayi, ya kuma nemi yafiyata na yafe mishi.

Da wannan dalilin yasa ya roƙe ni alfarmar inyi mishi alƙawarin kame mishi kaina har ya gama abinda yake yi a ƙasar waje idan ya dawo zai aureni. Ni kuwa duk da ban gama yarda da hakan ba, na kame kaina daga sake aikata zina.

Dama saboda me muke bin mazan? Ba don mu samu kuɗi bane? To Salim ya ɗauke min duk wata hidima tawa da ta mahaifiyata. Kuma yana dawowa nan gida Najeriya, ya neme ni da cewar alƙawarinmu na nan. Bayan matakai da ya bi daki-daki na inganta rayuwata daga ƙarshe ya nemi a sanya mana ranar aure. To a ganinki zan butulcewa ni’imar da Allah Yayi min ne in ƙi yin aure?”
Ta watsawa Samira tambayar tana kallon tsakiyar idanunta.

Samira dai ba baka sai kunne, gaba-daya kunya ta hanata ko kwakkwaran motsi, sai zare idanu take yi tana share zufa. Hankalinta a bala’in tashe.

Rahma ta cigaba da cewa
“Shi yasa nayi mamaki sosai da aka ce min kina bin bokaye da yan tsibbu don ki hanani yin aure. Abinda nasan da ke ce a wannan matsayin, wallahi Allah kila ma sai na fiki jin daɗi, saboda ni da zuciya ɗaya nake tare da ke.

Shi yasa don in ƙara tabbatar da cewa lallai da gaske ne ba kya so na da alheri, na ajiye gashina da farcena a banɗakina, kuma sai ga shi kin zo kin ɗauka za ki kai a miki kwalli da zaki yi tozali da shi don ki rabani da Salim.”

Ai da jin haka sai Samira ta ɗora hannu biyu a ka, hankalinta ya kai ƙololuwa gurin tashi. Bata taɓa tunanin asirinta zai tonu cikin sauƙi haka ba. Tunani take yi, ta yaya aka yi har aka haihu a ragaya? Ta yaya har Rahma zata san irin wainar da take toyawa bayan duk waɗanda take bi amintattunta ne?

Kamar Rahma ta fahimci tulin tambayoyin da ke zuciyarta, ta ɗan yi murmushi ta ce
“Na san ai zuwa yanzu baki manta da Lovina ƙawar yawonki ta gidan boka ba ko?”

Shikenan! Ta faru ta ƙare an yiwa mai zani ɗaya sata.
‘Lovina ta cuceni!’
Samira ta furta hakan a cikin ranta.

Rahma ta cigaba da magana a tausashe
“Na ga alamun kin gane ta da kyau! To ita ɗin da kike gani, nan da kike zaune nan ta sameni har gida ta zayyane min abinda ke faruwa. Naira dubu ɗari uku ta nema kafin ta bani labarin, ni kuwa da yake na wuce nan sai na cike mata kuɗaɗen zuwa dubu ɗari biyar.”

Samira ta ciji yatsa, ta rasa abinda zata yi kawai sai ta ɓuge da naɗe tabarmar kunya da hauka.
“Wato dama Lovina yaudarata kawai take yi ba wani abu ba? Lallai wallahi yau sai dai ayi ko ni ko ita! Don wallahi ba zan taɓa yarda da wannan cin amanar ba! Na rantse da Allah idona idonta sai na jinyata ta…”

Rahma tayi saurin katseta ta hanyar ɗaga mata hannu
“Kin ga dakata! Har akwai wani cin amana wanda yafi wanda kika yi min ne Samira?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 41Lokaci 43 >>

1 thought on “Lokaci 42”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×