Skip to content
Part 43 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Samira tayi ƙus! Ba baka sai kunne, kamar ruwa ya cinyeta. Tsabar kunya da yanayin tozarcin da take ciki ji take ina ma ƙasa ta tsage ta shige ciki ko ta daina amsar waɗannan manya-manyan maganganun daga bakin Rahma?
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!!

Rahma bata damu da halin da ta shiga ba ta cigaba da cewa

“Ni fa da za ki fahimce ni, ba tone-tone nace miki mu yiwa juna ba, saboda idan muka ce haka zamu yi ba zamu taɓa mantawa da baya mu fuskanci gaba ba. Kawai dai dalilin da yasa kika ji na miki wannan zancen shi ne, saboda ina so ki san da cewa na fa san halin da kike ciki, amma ni ban riƙe ki ba ko kaɗan! Kuma wallahi na yafe miki.

Amma kema ina so ki yiwa kanki adalci Samira, ki yi ma kanki karatun ta nutsu, ki tubarwa Allah. Ki daina yawon banza, ki samu ki nutsu waje ɗaya ki kame kanki. Idan kika tubarwa Allah sai ki ga ya jiƙanki, ke ma Ya kawo miki kamilin miji wanda zai riƙe ki tsakaninshi da Allah.

Ni kuma na miki alkawarin in Allah Ya yarda ni da mijina, za mu ba ki duk wani taimako da tallafi da kike bukata da izinin Allah!”

Ganin ba gurin gudu ba gurin ɓuya yasa Samira ta fashe da kuka. A fili alamun nadama da da-na sani ƙarara a tattare da ita.

Ganin haka yasa Rahma ta ja ta jikinta tana mai lallashinta da kalamai na kwantar da hankali har dai ta samu tayi shiru sai jan numfashin kuka take yi.

Tana shessheƙa da share majina take ba Rahma haƙuri.

“Kiyi hakuri don Allah, ki yafe min Rahma. Haƙiƙa na miki butulci, na zalunceki, kiyi haƙuri, sharrin shaiɗan ne da sharrin zuciya. In Allah ya yarda daga yau baza ki sake kama ni laifuka makamantan waɗannan ba. Zan nutsu, zanyi amfani da duk shawarwarin da kika bani.”

“Na yafe miki duniya da lahira ƙawata. Na san har da sharrin zuciya da shaiɗan kamar yadda kika faɗa. Shi yasa ban riƙe ki ba ko kaɗan. Kuma na ji daɗi sosai da kika tuba Samira.

Saboda na san can ƙarƙashin wannan Samirar mai sharholiya, akwai Samira wadda take kamilalliya ce kuma ta san mutuncin kanta sosai. Allah Ya yafe mana kurakuranmu gaba-ɗaya.”

“Ameen!”

Suka amsa a tare.

Rahma ta cigaba da cewa,

“Kin ga yanzu ina so nan da sati uku idan an gama bikina, ki dawo nan gaban Iyallu kiyi istibra’i, in Allah ya yarda za ta je har gida ta yiwa Mamanki bayani don ta barki ki zauna. Hakan yayi miki?”

Murya a ɗashe da kuka tace,

“Nagode Rahma. Haƙiƙa bani da abinda zan ce miki sai Allah ya saka miki da alkhairi. Allah ya bar zumuncin da ke tsakaninmu. Hakan yayi sosai, na gode.”

Saboda tsananin jin daɗin ganin yadda Samira ta bata haɗin a sauƙaƙe, abinda bata tsammaci samunsa da sauƙi kamar haka ba. Ƙara rungumeta tayi tana addu’ar Allah ya ƙara nesanta shaiɗan a tsakaninsu ya haɗa kansu fiye da yadda suke da can baya.

“Amin ya Allah Ƙawata.”
Samira ta amsa fuskarta yalwace da dariyar da sai an kula sosai za’a gane na yaƙe ne.

*****

“Ka tabbata ita ka gani?”

Ya tambaya da sauri, muryarsa na rawa, cike da ɗoki sosai yake sauraren amsar da ake bashi daga can ɓangaren. Ana ƙara tabbatar mishi tabbas ita ɗin ce.

Aka cigaba da cewa daga can ɓangaren
“Ka manta na faɗa maka ƙawar Sauda ce ta ƙud da ƙud? Daman tun kwanaki na yi ma Sauda dabarar cewa don Allah duk ranar da Nana ta fito ta faɗa min, akwai saƙon da aka bani in bata. To ɗazu ta kira ni tana faɗa min za su haɗu a gidansu Farida, yanzu kuma ga ni a hanya ina hangensu suna tafiya zuwa kan titi don samun abin hawa, tabbas ita ce.”

Duk da rashin ƙarfin jiki da yake fama da shi na tsawon kwanaki masu yawa saboda rashin lafiyar da yayi. Da zafin nama ya yunƙura ya miƙe tsaye, taga-taga yayi kamar zai faɗi da saurin gaske ya dafe bango, har lokacin bai bar wayar ta suɓuce daga kunnensa ba.


“Alhamdulillah! Allah na gode maka. Bale wannan dama ce da na daɗe ina jira, don Allah kar kayi min wasa da ita.”

“Ba ka da matsala Kham! Kai ɗin nawa ne Amini, yanzu dai mecece mataki na gaba?”

*****

Da mamaki maɗaukaki a fuskar Ziyada ta bi shi da kallo, kamar baza ta tanka mishi ba. Sai kuma ta miƙe a gaggauce ta ƙarasa kusa da shi ganin yana daf da ficewa daga cikin falon.
“Daddyn Nauwara? Lafiya kuwa? Me yake faruwa? Ina kake haramar zuwa kai da ba lafiya ce ta wadace ka ba?”

Da saurin gaske yaja burki, a hankali ya waiga yana kallonta. Har ga Allah shi ya ma manta da wani rashin lafiya da ya kwashe tsawon kwanaki goma yana yi. Daman rashin lafiyar ta Bilkisu ce, yanzu kuwa ya samu damar ganawa da ita a sauƙaƙe, wace rashin lafiya ce kuma tayi saura a jikinshi?

Da murmushi a fuskarsa ya ƙarasa kusa da ita, zuciyarsa cike da matsanancin jin daɗin yadda a cikin kwanakin yanayin zamantakewarsu ta fara daidaituwa. Tunda ya fara rashin lafiya ta watsar da kaso sittin na haushinshi da take ji tana kula da shi daidai gwargwado.

Hannunsa na dama ya ɗaga ya ɗan shafo kumatunta, da yanayi mai baiyana jin daɗin kulawarta a gare shi ya ce.
“Ba nisa zanyi ba Umman Nauwara. Saƙo zan amsa nan bakin titi. Muhimmin saƙo ne da bazai yiwu inyi aike a karɓa min ba, dole in tafi da kaina.”

“To shi kenan! A dawo lafiya.”
Ta amsa a sanyaye tana jin wani rashin nutsuwa daga wani ɓangare da bata sani ba yana mamayarta.

Ko da ya amsa mata bata koma cikin falon ba, tana tsaye a gurin har ya fice daga cikin falon da sassarfa. Ga tsammaninta a ƙafa zai fita, amma wani ƙarin ban mamaki a gare ta sai ta jiyo shi yana tayar da mota. Idanu ta ɗan buɗe alamun girmama mamakinta, har ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare shi don tambayarshi amso saƙon yayi nisa sosai ne da har sai ya fita da mota?

‘Me ya shafe ki Ziyada? Wannan binbinin na menene kike mishi kamar wani ƙaramin yaro?’
Wani sashe na zuciyarta ya kwaɓe ta.

Da wannan dalilin yasa ta ɗan taɓe baki, a maimakon fita zuwa tsakar gida sai ta juya zuwa cikin falon ta zauna kan kujera. Har lokacin tana jin wannan rashin nutsuwar yana ƙara mamaye duk ilahirin jikinta, sannu a hankali kuma sai ta fara jin faɗuwar gaba.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”

Ta faɗa a fili da dukkan yaƙini da sallamawa ga ubangijinta. Ta ƙara da addu’ar Allah yasa ba wani mummunan abu ne yake shirin faruwa da ita ko yaranta ba.

Yaran duk basa nan, kasancewar yau asabar ce, tun safe suka wuce makarantar Hadda. Ga shi lokacin ɗora girkin rana baiyi ba balle aikin abinci ya ɗebe mata kewar zaman shirun da tunani. Kallon Tv da take yi kafin fitowar Khamis a yanzu bayan fitarsa sam ta daina fahimtar abinda ake cewa.

Duk inda zaman shiru yayi yawa dole tunanika marasa ma’ana su lulluɓe zuciya. Irin haka ce ta kasance ga Ziyada, aɗan zamannan da tayi bayan fitar Khamis babu irin mummunar saƙar da zuciyarta bata yi mata ba. Domin kore shaiɗan da mummunan tunani, sai ta janyo wayarta ta kunna karatun Alƙur’ani, wayar na riƙe a hannunta ta miƙe tsam ta shige cikin ɗakinta, kwanciya tayi a kan gadonta tana bin karatun da murya ƙasa-ƙasa, har zuwa lokacin da wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita.

A firgice ta farka bakinta ɗauke da salati mai ƙarfi saboda wani mummunar mafarki da tayi, ko bayan da ta fahimci mafarki ne, ta ɗauki tsawon daƙiƙu ƙirjinta na bugawa fat! fat! fat!!! don tsananin tsorata da abinda ta gani a cikin mafarkin. Daki-daki mafarkin ya dawo a cikin idanunta kamar a lokacin komai yake faruwa.
‘Mannirah ce ta gani kwance cikin jini, kayan jikinta a yayyage, jini yana bin ƙafafunta, da ta kalli fuskarta kuwa wani kakkauran miyau mai yauƙi fari kar ke dalala a bakinta. Kamar dai wacce tasha guba…’

Lokaci ɗaya ɓangaren kanta na dama ya ɗauki ciwo mai tsanani kamar ana buga mata guduma, ta daɗe a zaune idanunta a lumshe tana jan duk wasu addu’o’i da suka zo cikin zuciyarta. Hannunta tallabe da ɓangaren kanta da yake mata matsanancin ciwo. Ta ɗauki tsawon lokaci a haka kafin daƙyar ta iya buɗe idanu ta sauke kan agogo, ƙarfe goma sha biyu da minti arba’in da ɗaya.

Tunawa da girkin abincin rana da bata ɗora ba yasa ta miƙe a hankali, tana jin yadda kanta yake cigaba da bugawa gaf! gaf!!. Cije gefen bakinta tayi, ko da ta kalli madubi sai taga idanunta har sun kumbura.

Ɗankwalin kanta da ya fara zamewa saboda barci ta sake ɗaurawa tamau ko za ta ji dama-dama da yadda kan ke buga mata. Ta kama hanyar ficewa daga ɗakin tana tafiya a hankali. Fitowarta falo yayi daidai da shigowar motar Khamis cikin gidan.

A karo na biyu ta sake kallon agogon falon, awa biyu da minti hamsin da fitarsa karɓo saƙo a bakin titi sai yanzu ya dawo. Bata zurfafa ma kanta tunanin dalilin daɗewarsa ba ta cigaba da tafiya sannu a hankali don zuwa kicin, domin ta sama ma yara abinda za su ci. Ƙarfe ɗaya da rabi ake tashin ƙananun yara, duk abinda za ta girka ya zama dole tayi mai sauƙi saboda suna dawowa bayan
“Mummy sannu da gida” abinda suke tambaya na gaba abinci ne. Shi yasa duk yadda za tayi in dai ba da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba tana ƙoƙarin kammala girki kafin su dawo gida…

Kiciɓus! Aka ce mugun gamo. Juwa mai bala’in ƙarfi ne ya kusa kifa ta da ƙasa tayi saurin riƙe ƙofar kicin ɗin saboda wani mummunan gani da idanunta suka yi.

Ko kafin ta dawo hayyacinta, har Khamis ya shige cikin falon ba tare da damuwa da irin firgicin da ta shiga ba, kamar ma bai ga tsayuwarta a gurin ba. Riƙe a hannayensa ya ɗakko ta kamar ƙaramar yarinya, Ƙatuwar budurwa ce fara tas kamar a taɓa ta jini ya ɓullo. Duk da hijabin jikinta ya rufe fuskarta ana ganin santala-santalan hannayenta farare tas da suka sha zanen jan lalle.

Minti biyar ta ɗauka riƙe da ƙofar tana ganin duniyar na juya mata kafin komai ya koma dai-dai a idanunta. Sai kuma take ga kamar ba mace taga Khamis ya wuce riƙe da ita ba, da wannan dalilin yasa da saurin gaske ta bishi cikin falon domin share ma kanta tantama.

Ba shi a cikin falon, amma ga ƙofar ɗakinsa nan tana hange a buɗe. Don haka ta nufi cikin ɗakin da sauri, tana isa bakin ƙofar shi kuma yana fitowa. Ƙiris ya rage suyi gware da kawunansu yayi saurin kauce mata yana bin ta da kallon tuhuma, sai yake ga kamar wani abu ne ya biyo ta.

“Ziya? Lafiya kuwa…?”

“Kamar mace naga ka shigo da ita riƙe a hannayenka?”

Ta katse shi da tambayar bakinta na ɗan rawa-rawa.

Sai a lokacin ya fahimci dalilin rashin nutsuwarta. Kasancewarsa mutum da bai saba ɓoye-ɓoye ba, da sanyin murya ya amsa mata kai tsaye ba wani kwana-kwana
“Ba kama bace, mace ce.”

Kafin ta sake cewa wani abu ya kama hannunta zuwa cikin ɗakin, kyakkyawar budurwar da ya shiga da ita ce kwance akan gado. Ya cire mata hijabin jikinta, buɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa da yake jikin yarinyar bai hana bayyana cikar halittar jikinta ba. Hular kanta da ya ɗan zame ya bayyana yalwataccen baƙin gashin kanta da ya sauka har kafaɗunta, duk da barci take yi cikin nutsuwa, idanun Ziyada basu gaza gano asirtaccen kyawun da yarinyar take da shi ba.

Daƙyar ta iya ɗauke ganinta daga kan yarinyar ta mayar kan Khamis, ta buɗe baki za tayi magana ya finciki hannunta da sauri suka fice daga cikin ɗakin.

Bai sake ta ba sai da suka isa tsakiyar falo, ya zaunar da ita kan kujera mazaunin mutum uku, shi ma ya zauna a gefenta.

A karo na biyu ta sake buɗe baki za tayi magana ya sake katse ta ta hanyar ɗora mata yatsarsa manuniya kan laɓɓan bakinta.

“Shshhhhhh! Kar ki ce komai don Allah! Ki saurare ni da kunnen basira. Ita wannan yarinyar da kika gani, sunanta Nana Bilkisu…”
Sannu a hankali da baiwar iya magana da Allah ya huwace masa ya kora mata cikakken bayanin wacece Bilkisu? Inda ya fara haɗuwa da ita, matsananciyar soyayyarta da ya kamu da ita farat ɗaya, matakan da ya bi tun daga farko har zuwa yanzu da yake bata labari, bai ɓoye mata komai ba har sanadiyyar ciwon da yayi na kwanaki goma cif saboda fargabar rasa Nana Bilkisu ne…

Zuciyarta bugawa take yi, zafi take mata kamar ana zuba mata tafasasshen ruwa. Amma da yake Allah yayi ta da baiwar cin ribar zance bata yi yunƙurin katse shi ba har sai da shi a karan kansa ya dasa aya a maganganunsa.

Ta daɗe cikin shiru tana kallonsa, kanta a kulle, ta ma rasa tunanin da ya kamata tayi a daidai wannan lokacin.

‘Khamis! Bazai taɓa canjawa ba!!!’
Magana daga wani ɓangare na zuciyarta.

Maganar da ya zama kamar allurar da aka tsira mata don dawo da ita cikin hayyaci da nutsuwarta. Muskutawa tayi, ta ɗan gyara zama, a dabarance ta matsa kaɗan daga kusa da shi.

“Yanzu da ka ɗakko musu yarinya ba tare da saninsu ba, me kake niyyar yi?”
Ta jefa mishi tambayar a nutse, daɗai babu wani ƙunci ko damuwa danƙare da zuciyarta.

Kallonta yake yi, kamar bazai ce komai ba. Sai kuma ya buɗe baki a sanyaye ya ce
“Umman Nauwara… Na fahimci iyayen yarinyar nan baza su bani aurenta cikin sauƙi ba…”

“Ni ma na fahimta.”

Ta katse shi da sauri domin so take ta ji magaryar tuƙewa a zancensa.

“Ni kuma Allah ya gani ina bala’in son ta…”

A fakaice ta lumshe idanu saboda wani suka da ƙirjinta yayi da jin kalmar son wata mace daban ba ita ba daga bakin Daddyn Nauwara. Ba yau ne ta fara jin shi yana furta kalmar ina son ki ga karabitin ƴanmatansa ba, amma kalmar ta yau ta sha ban-ban da waɗancan.

Wannan kalmar daga ƙarƙashin zuciyarsa ta fito, da dukkan gaskiyarsa yake faɗa mata, shi yasa kalmar ta buge ta ba kaɗan ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 42Lokaci 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×