Skip to content
Part 17 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Gabana ya ƙara ƙarfin bugawa na fara ƙoƙarin ƙwace hannuna, ya riƙe shi da kyau yana murzawa na dube shi duba na masifa don in sauke mishi kwandon bala’in ni ba yar iska ba ce, wani irin yanayi na gani a fuskarsa “Na yi ƙarfin halin cewa ka sakar min hannuna ni ba yar iska ba ce.”

Tunda kika ce min ɗan iska zan rungume ki in yamutsa ki, soyayya ce ba iskanci ba, son ki na ce ina yi kuma soyayya ta wayayyu za mu yi, ki nuna min irin son da kike min in nuna miki irin wanda nake miki.

Ita ce soyayyar zamani ba ta kauyawa irin wadda aka yi lokacin kai na cikin tukunya.

Na fizge hannuna ina hararar shi buɗe min ƙofa in fita.”

Ya karyar da murya “Ki yi haƙuri to daga ba ki so amma ba wani abu bane so ne, yadda kike babbar yarinyar nan yawa ne kina irin wannan abun.

Kin haƙura? Ya tambaye ni na yi banza da shi ya ce “Za mu kwana anan kenan.”
Sai ya ƙara maimaita”Kin haƙura?

Saboda matsuwata in bar motar na ɗaga kai ya ce “Tnx”

Sai ya miƙo hannu zai ƙara taɓa ni ko me ya tuna kuma sai ya yi saurin janyewa “Sorry baby son ki nake sha’awarki ta kama ni.”

Gabana ya ƙara yankewa ya ce ras! Jin ya ambato sha’awa, ni Bilkisu na ga ta kaina, ƙaddarar zawarci kuma yau ga inda ta kawo ni. Tun da na ga irin kallon da yake yi min tun farkon gani na da shi na san za a rina, shi ne ya fake da wani yana so na, yana dai sha’awata ga ta nan ya faɗi.

“Mu je baby.” Na ji muryarsa ashe har ya fita ya zagayo ɓangare na, ya ɓalle murfin motar sai ya kwantar da kansa jikin murfin na daga kaina karaf muka haɗa ido na yi saurin kawar da kaina “Ko sai na ɗauko ki? Ya faɗi cikin wata lallausar murya.

Ƙafata na miƙa da niyyar fita sai ya kauce ya tashi daga jikin ƙofar.
Ina bayan shi har muka shiga Office na Director na makarantar, bayan gaisuwa da yan maganganu da suka yi ya karɓi foam a hannuna ya ba shi bayan ya min yan tambayoyi ya kira wata a waya ta shigo Office ɗin cikin sauri ya ba ta umarnin ajin da za ta kai ni.

Sama muka hau aji mai ɗauke da ɗalibai da suka haura arba’in ta kai ni, na zauna kusa da wata mata da shekarunta aƙalla za su haura talatin ta tarbe ni da fara’a na gaishe ta da girmamawa ta faɗa min sunanta Haj Halima, ni ma na faɗi mata sunana.

Shigowar teacher ya sa ta fasa maganar da za ta yi min muka fuskance shi, sosai na nutsu, kuma fahimci abin da aka koyar.

Ana tashi na sauko ina tunanin ko zan gane gidan kai tsaye ko sai da lalube wannan Hajiyar ta tsaya gaba na da mota tana min tayin in shigo ta rage min hanya. Ban kai ga magana ba malamar nan da ta yi min jagora ta iso cikin sauri “Har kun tashi ne? Ta tambaye ni cikin murmushi, na daga mata kai “Yayanki bai faɗa miki idan aka tashi zan dinga miki lesson na 1hour ba? Na ce “Bai faɗa min ba.”
Ta ce “Zo mu je.”

Na juya wurin Hajiyar na yi mata bayani ta ja motarta na bi bayan malamar, wani keɓantaccen aji da shi ma aka riga aka tashi muka shiga dalla dalla ta shiga ƙara koyar da ni abin da aka yi mana na gamsu ƙwarai awa daya na cika ta sallame ni na fito.

Ina fita get din wani mutum da ke jingine jikin wata ash color ɗin motor ya taso ya nufo ni, gaishe ni ya yi har yana dan ranƙwafawa ya miƙo min wayar hannunsa “Yallaɓai Najib ne bisa layi ya ce in ba ki wayar na karɓa na kara a kunnena sai muryar Najib na ji “Ki shiga baby ya kai ki gida.”

“To na ce na miƙa mishi wayarsa inda motar take muka nufa na shiga ya ja muka bar wurin.

Duk da cewar da na yi ya sauke ni daga bakin get ƙi ya yi sai da ya yi horn mai gadi ya buɗe ya sulala da motar ciki har kuma bakin part ɗin Mama ya sauke ni, ya ciro ledoji guda biyu ya miƙa wa Dauda da ya taso suna gaisawa da alamar sun san juna, ya ce ya shigar min da su.
Falon Mama na fara shiga ganin lokaci ya yi nisa karfe biyu har ta gota na yi mamakin rashin ganin kowa a falon sai na wuce bedroom ɗinta na yi knocking daga ciki ta bada iznin shigowa na buɗe na shiga tana kwance bisa gadonta riƙe da littafin ahlari ta yi murmushi “An dawo Bilkisu? Na ce “E Mama sannu da gida.” Ta ce “Yawwa kin kwaso rana.”
Na ce “Akwai rana.” Ina juyawa sai na ja mata ƙofar.

Sama na haye Zainab kadai na samu a falon tana barci na wuce toilet na yo alwala duk da bak’ar yunwar da ke sakaɗar cikina na zo na kabbara Sallah, da na idar gado na haye bayan Zainab motsina ya sa ta buɗe ido sai ta yi saurin wattsakewa “Kin dawo Billy? Na ce “E. Har kin ci abinci kenan? Sai da na dubi inda kayan abincin ke ajiye sai na girgiza kai “To me ya sa ? Na yi shiru ta yi yar dariya “Au Fulatancin ne ya motsa? Ta sauka gadon ta fara zuba abincin “To bismillah bafulatana.”
Na sauka na zauna na fara ci.

Ihsan ta shigo da ledojin nan da direba ya ba Dauda ta ce in ji Dauda ta miƙo min, da na karɓa sai na ajiye Zainab ta dube ni da alamar tambaya kan fuskarta na ja iska ta hanci “Wai Najib ne ya bayar a kawo min.” Ta ce “To ki buɗe mana.” Na ce “Ke ki buɗe mana.” Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta janyo ledojin ta farko chocolate ne kala kala da biscuit masu tsada da youghout sai drinks.
Ta biyun kuma dangin su Apple ne su Strawberry.
Ta zuba wani Youghout ta kai baki sai ta lumshe ido “Ina son youghout din nan, idan na ce miki so ina nufin so sosai nake masa.
Sau daya Baba ya taɓa sawo mana shi kullum ina da burin in ƙara shan shi sai jiya Allah ya ara min dama ya Najib ya same ni sai na tsara shi na lissafa mishi irin abubuwan da ya kamata ya riƙa sawo miki na ce ka ga yadda jikin nan nata yake lukwi lukwi duk inda ta fito kasan tana jin daɗi sai da irin waɗannan, ya ce haka ne.”
Na yi murmushin jin zancen ta a raina ina faɗin wane daɗi na ji a al’amarin rayuwata? Kawai halitta ta ce haka Ubangiji ya yi ni, lokaci ɗaya ne nasan na lalace na komaɗe a gidan Malam da bala’in kishiya ya taso ni.
Na miƙe don na kammala na koma kan gadonta ta ce “Wallahi ki koma gadonki kar ki haɗa ni da Ya Najib, ko sai na ɗora ki? Ta nufo ni da wani Youghout din da ta tsiyaya “Kin bar ni da kayan daɗi sha ke ma ki ji daɗin.” Na miƙa hannu na karɓa daɗin kuwa ba kaɗan ba, ban ankara ba sai cup ɗin ta kuwa yi ta min dariya.

Muna nan har Khadijah ta shigo ban fita ba sai da na yi La’asar shi ma Maman su Ahmad ce ta kira ni a waya wai in zo in yi mata kunun aya,
na bar Zainab na tafi.

Tana zaune a falonta ta ce in wuce kitchen ta ajiye komai.
Na wuce cike da mamakin ta to in ban iya ba fa?
Sai da na gyara ayar na wanke ta da kyau sai na ɓare dabinon na cire ƙwallayen na zuba, kwakwar na fasa na yayyanka ta ƙanana na zuba citta da ɗan kanumfari na janyo blander na markaɗa kafin na tace da ruwa mai sanyi,, sugar kaɗan na zuba na sanya flavour sai na fasa madara peak na juye a jug guda biyu babba da ƙarami na sanya a fridge sai na fito.
Tana zaune inda na bar ta ta ce “Har kin me? Na ce “Na gama.” Ta ce “To dan kawo min in ɗanɗana.
Na koma na dauko mata ƙaramin jug din da cup na kawo mata.

Tana kurɓa ta dube ni “Kai ya yi daɗi, ashe haka kika iya? Dole Baban su Ahmad ya sha akwai saura? Na ce “Akwai a blue jug din nan babba.”

Ta ce “To je da wannan, Najib ma ya leƙo yana neman ki na ce kina kitchen kunun aya za ki yi min.”
Na amsa na yi mata godiya na fita.

Wajen wani lilo na shaƙatawa na hangi Najib da Zainab suna zaune na yi kamar ban gan su ba zan yi tafiyata Zainab ta ƙwala min kira na waiwaya sai na juya zuwa inda suke, tunda na doso yake kallona har na isa inda suke gabaɗaya na daburce kusa da Zainab na tsaya sai ta janyo ni na zauna kusa da ita “Tunda ba ta ba ni kunun da aka ce min tana yi ba na roƙa karɓo min Zainab.”

Na yi saurin miƙa mata ya ce Zainab ta kawo mishi cup ta tashi ta tafi kamar in fasa kuka bari na da ta yi da shi.

Ya matso kusa da ni magana yake min cikin kwantar da murya na sunkuyar da kaina ina sauraren shi har Zainab ta dawo ta miƙa mishi ya tsiyaya ya sha ya ce “Wow! Na lura dai ita komai ta iya ki roƙe ta ta rinƙa yi min girki.”

Baki ta kama “Ka ji ya ya Najib kai da masoyiyarka, kun fi kusa ni a wa? Bari ma ka gani in kama kaina.

Ta miƙe don barin wurin na kama mata riga ya ce “Kin gani? Ƙarar da na kawo miki bayan guduna da take yi ba ta yi min magana, sai ka ce zamanin kakanninmu don ko iyayenmu na san ba su yi haka ba.”

Ta ce “Sai a hankali ya Najib za ta saba da kai.”
Ya ce “Ku je sai anjima zan zo zance.”
Muka wuce tana dariyar shi.

Sai da muka fara zama falon Mama muka yi sallah da cin abinci na tashi na hau sama gadon Zainab na haye na yi kwanciyata ban jima ba sai ga ta waya suke da Najib ɗinta sai da ta gama ta dube ni “Ki tashi ki shirya ya Najib ya kusa zuwa zance.”

Wani irin kallo na yi mata “Wane irin shiri kuma? Kwalliya mana da yammata ke yi idan an zo wurin su.” Na kifa rub da ciki na yi mata banza turo ƙofar da aka yi bai sa na motsa ba ƙamshin turarensa da na ji ya sa na gane kowaye.

Da mamaki cikin maganarta ta ce “Kai ya Najib ni ina ce daga get za ka tsaya ka aiko a kira ta?
Ya ce “Duk cikin gidan nan sai in rasa wurin zance sai na je get? To a dakin nan ma za mu yi ki fita ki bamu wuri.”

Gabana ya ce dam! Na shiga gwalo ido daga kwance, sai na kama addu’a Allah ya tsare ni daga duk sharrin wannan bawa. Sam barka sai na ji ta ce “A’a ya Najib mu fa barci za mu yi, ku dai dan fita daga ƙofarmu, zan ma dauko maku kujerun zama.” Ya ce “To ta tashi mu je.” Ganin ban motsa ba ta ce “Ka je ya Najib zan kawo ma ita.”

Sai da ta ga ya fita ta ce “To tashi ya tafi.” Na tashi zaune “Wai me kike yi haka Bilkisu? Ya Najib na bala’in sonki ki yi mishi fari ki wanke shi kin tsaya wani sinne sinne soyayyar nan kin yi ta bare ki ce ko sabon shiga ce, ki tashi ki ɗan yi kwalliya yadda za ki ƙara tafiya da hankalin sa.”

Na dan buɗe ido”Ke ni ba kwalliyar da zan yi na janyo dogon hijab ɗin da na yi sallah na saka a raina ina faɗin ya zan yi daga gidanku na zo cin arziki, amma da hakanan ne tunda na gane manufar shi a kaina fata fata zan mishi na sanya silifas ta zo daidai kunnena ta rage murya “Bayan harkar mota da yake yana da wurin saida waya da ya karbu sosai ki tsaya mu ci arziki kina mana bakin ciki.”

Dariya ta kwace min jin zancen ta na karshe muka fita yana tsaye ya dogare hannayensa a karfen benen jin motsi ya waiwayo hasken da ke wurin ba mai yawa ba ne zantuka ya fara min cikin kwantar da murya har Zainab ta dawo ɗauke da kujerun ta ajiye ta wuce daki tana faɗin “Dole yar ku ta farko ku sanya mata Zainab wannan taraliya da nake sha.

Ya juya ya dube ta tana shigewa ya juyo wurina wata leda da na lura da ita tun fitowata ya miƙo min “Ki duba kaya ne gobe after 4 za mu fita ki sha Ice cream in kai ki ki sayi irin kayan kwalliyar da kike amfani da su don kar ki canza ki samu canjin fata, ya rage murya.

“Tunda nake ban taɓa jin hannun mace mai laushi irin naki ba.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 16Mutum Da Kaddararsa 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×