Skip to content
Part 48 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Sai lokacin da na saba shiga kitchen na fito na kama aikina.

Sai kuma wurin cin abinci muka ga juna da Aunty Farha, washegari kuma dole ta shiga kitchen abin da ba ta yi a gidanta ga Madam Hajjo a gefen ta.

Ni sai na bar mata ma gidan, gidan Hafsa na shiga muka tafi gidan Khadija muka yi hirar mu sai yamma sosai na dawo na kuma shige ɗaki.

Ko da suka zauna cin abinci ban fito ba ta waya ya kira ni na fito na ci kaɗan don na ci abinci gidan Khadija.

Da safe ina shirin makaranta ya same ni a daki ya ce gobe idan Allah ya kaimu zai tafi Lagos kan harkar wasan shi na Polo kwana biyar zai yi.

Ranar farko da ya tafi daga makaranta gida na dawo Hafsa da Khadija suka shigo muka yi yammaci.

Rana ta biyu mun ziyarci Suleja garin su Hafsa muka gaishe da iyayenta sosai na ji dadin tafiyar.

Rana ta uku gidan Mami muka tafi tare da su, Mami ta yaba da samun su da na yi, don ta yaba ƙwarai da su.

Rana ta huɗu muna dakin Khadija, kayanta da ta yi order sun iso muna ta dubawa wata atamfa ta ɗauki hankalina, na daga na ce ina so Hafsa ma ta ce ta yi mata muka dauki biyun kafin in yi mata transfer Hafsa ta biya, ita ma Khadija ta dauki guda, suka ce za mu je wurin telan su in gwada ɗinkin wurin.

Washegari da muka tashi makaranta muka je da Hafsa kwana biyu kacal aka kawo ɗinkunan da suka yi matukar burge ni.

Na ajiye ta akan ita zan yi wa ya Safwan kwalliya a ranar da zai dawo.

Sauran ranakun mukan zauna ne a gidan daya daga ciki don haka ban zauna da Aunty Farha ba.

Muna waya da Raihan ita ke faɗa min Aunty Farha daru ta tada ma ya Safwan gidana ya fi na ta girma. Da abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa shi ne ya amince zai mata gyaran gida amma sai dai ta koma gidansu har a gama, har ta tafi kwananta daya ta ce ita ba za ta zauna ba shi ne ta taho gidana.

Na jinjina lamarin watau Aur̃nty Farha tafiya ba yanzu ba indai gyaran ya Safwan ne.

Tafiyar tashi da ya ce kwana biyar zai yi sai ga shi ya yi sati don da ya gama kwana biyar ɗinshi a Lagos Taraba ya ce min ya wuce.

Cewar da ya yi zai shiga Taraba sai kewar mahaifiyata da ƙannena ta kama ni, ga shi kwana biyu ba na samun wayar Maman nawa da ta mijinta.

A sati guda da ya Safwan ya yi kewar shi mai yawa ce ta ishe ni don haka ranar da zai dawo sosai na cika da zumuɗin dawowar shi, na kuma taki sa’a ranar da zai tafi

Ina ta shiri bayan girke girke da na yi hajjo kuma ta gyara ko’ina na gidan, don ta shigo kitchen ta taimaka min na ce ta bar shi ta gyara min gida, ta kuwa gyara ko’ina ƙal, ni kuma na gyara na maigidan na sanya ƙamshi mai sanyaya rai.

Wanka na yi mai kyau na sha kwalliya da doguwar rigar atamfa ta wurin Khadija

Na gama gyara kwalliyata bayan mun ƙare waya da shi ya ce ya kusa shigowa ya biya gidan Mami ne.

Na daga labulen window na zura wa get ido ba ko ƙiftawa, ba abin da nake fata in ga motar da direba ya je daukar shi ta shigo har ƙafafuwana suka gaji da tsayuwa ba alamar hakan na koma bakin gado har zan ɗauki waya in kira shi sai kuma na koma jikin window kamar jira ake in tsaya get man ya wangale get motar ta kunno kai cikin sauri na taka na fita dakin ba kowa a Main palour don Aunty Farha ma ta fita sai dai kamar na ji maganarta ina kyautata zaton ta dawo.

Turus na tsaya daf da zan karasa inda motar take ganin direba ne kaɗai ke ta bidirin fito da kaya amma ba alamun akwai ya Safwan a ciki na karasa ya gaishe ni na tambaye shi ya Safwan ya ce yana nan shigowa.

Get ɗin da aka ƙara buɗewa ya sa na kai idona can shi ne bisa dokinsa cikin kayan wasa sai na gane inda ya biya bayan gidan Mami da yake ta ce min ga shi nan.

Na ƙura ma inda yake ido direba ya miƙo min key ya kuma yi min sallama ya taka don barin gidan.

Sai da ya gama magana da su ya nufi inda yake ɗaure dokin na bi shi a baya har ya daure shi ya juyo yana kallona, ganin ni ma kallon na shi nake ya yi min murmushi kaɗan ya miƙo min hannunsa na kama sai ya ɗora min hular su ta wasa a kaina ya janyo ni ina mishi barka da zuwa muka shiga ciki, bai zauna a falo ba wurin shi ya shige na tsaya na tsiyaya kunun aya da na yi na bi shi da shi dab da shi na zauna jikinmu na gogar na juna ya karbi cup ɗin ya ce “Na sha? Da in fara gano Farha.

Na yi kamar ban ji me ya ce ba ya dora cup ɗin baki sai da ya shanye ya dire “Ya kike Mamina ya baby? Na yi mishi wani kallo sai na narke a jikinsa, abin da ban taɓa yi ba sai dai shi ya yi, jin na ƙanƙame shi, ya ɗago ni muka dubi juna ya ƙanƙantar da idonsa “Da ganin wannan kallon da ake min da matsar da ake min na san abin da kike so, zan yi kuma wallahi.”

Ya faɗi cikin wata murya da za ka fahimci ya fara samun canji.

Na rufe idona da karfi don kunya da maganar ta sa ta ba ni.

Daga haka rungume ni ya yi ya tashi da ni a hannayensa har ni har cikina.

A gadonsa ya sauke ni shi ma ɗin a kamen yake soyayyarsa mai tsayawa a rai ya gwada min ya rasa jam’in sallar magrib don har sai da aka idar ya hakura ya janye tun kafin abu ya yi nisa nake cewa ya bari ya ci abinci,ya ce in bar abincin nan mu yi abin da ya fi abincin muhimmanci.

Tare muka yi wanka na bi shi muka yi sallar magrib da na ce mu je ya ci abinci ya ce zai gano Aunty Farha, don haka da muka fito tare ni na nufi wurin abincin shi ya tafi wurin ta.

Na fara zuba mishi abincin, ina zaune tashe da abinci ya Safwan bai fito ba sai kallon agogo nake kishi ya yi matuƙar tokare ni kamar in tashi in yi tafiyata sai zuciyata mai gaya min gaskiya ta taushe ni da hakan shi ne kishin ita ma Allah kaɗai ya san yadda ta ji da ya dawo muka shige sai yanzu ya leƙa ta.

Na daure, ya yi minti ashirin kafin ya fito ban tunanin za ta fito ba sai ga ta tare da shi muka ci har ita muna kammalawa na kira Hajjo ta kwashe komai, ban zauna ba dakina na wuce na fara shirin kwanciya don a gajiye nake kwanciyar nake so.

Ban tunanin zan gan shi a lokacin ba sai dai ina tuɓe riga na fara cire ɗankunne ya shigo, zama ya yi na gama shirina muka tafi wurin shi.

Da safe yana wanka ina zaune tsakiyar gadonsa kiran Abu ya shigo yayar Aminu bayan mun gaisa ta ce tana so ta zo wurina ta kawo Amir don kullum yanzu yana damun su da maganar mamansa.

Na rufe ido na buɗe na ce ta ba ni Amir ɗin, tana ba shi tambaya ta ya fara yaushe zan zo ya gan ni yana so ya gan ni.

Ji na yi kamar in yi hawaye na rarrashe shi na ce ina nan zuwa na tambaye shi abin da yake so ya ce keke ya fara gaya min an sai ma Usaini, (Yaron yayan Aminu sa’an shi). Na ce to zan turo kuɗi a saya mishi sai da na rarrashe shi sosai na ce ya ba Abu wayar Muryar Maman Aminu na ji muka gaisa sai ta ba Abun na ce ta turo acc no zan sanya kudi ta sai wa Amir keke da ma duk abin da yake so ta dauki dubu biyar ta ba Mama dubu biyar ta yi murna sosai tana ta zuba godiya sai na ce amma su bar zuwan nan ni zan zo idan Zainab ta haihu.

Cikin sauyi a muryarta na rashin jin dadi ta ce To.

Muka yi sallama ya Safwan da na gani tsaye jikin mirror yana goge jikinsa na yi mamakin san da ya fito ban ji ba.

Ya gama shirin muka fita zuwa gidan Mami da ya ce har Aunty Farha ya gayyata ta ce akwai inda za ta.

Cikin matukar mamaki isar mu gidan Mami mahaifiyata na samu da kannena na shiga murna wadda daga Mamin har ya Safwan ɗin ban tunanin sun taba ganina cikin ta ba na ce ya aka yi haka ta ce mijinki ya je ya kwaso mu, na ce to wayoyinsu fa da ba na samu? Ta ce suna kwanciyar zafi aka shiga aka kwashe na ce Subhanallah Allah shi kyauta. Ta ce Amin. Ki yi wa mijinki godiya sosai ya je ya sayi filin jikin gidanmu za a buda gidanmu a yi mana sabon gini.

Na ce “To Mama. daga nan kuma za su wuce Kaduna daga nan sai Malumfashi na ce hakan ya yi.

Na wuni da su muna ta hira ana yin sallar la’asar ya Safwan da yana ajiye ni gaishe su kawai ya yi ya bar gidan ya shigo ya ce in tashi mu tafi na bata rai na ce ya bari sai dare Mamana ta ce “Kul! Tashi maza ku tafi ina laifin shi? Na ce to kannena su tashi mu tafi ta ce a’a don me? Mami ta ce “Ki bar ta ta tafi da su.”
Ta ce “To ta je da matan. Su ɗin muka tafi da su Jamila da Fiddausi, Fiddausin ita ce babba ta zama budurwa don ta kare Sakandire Mamana ta ce aure za su yi mata na ce su bar ta ta fara karatu zan yi mata komai na hidimar karatun ko tana cikin karatun ta samu miji sai a yi.

A Main palour muka zauna da su har Aunty Farha ta dawo gidan ita ke da girki ina ji tana fadi ma Hajjo yadda za ta haɗa girkin Hajjo ta shige kitchen ita kuma ta kara kishingiɗa tana latsa wayarta ni kuma na mike tsam na ja kannena muka shige wurina.

Ba mu fito ba har dare ina da wani Cake shi na ba su muka haɗa da lemo niyyata ni da fitowa sai Allah ya kaimu sai ga shi ya shigo ya ce mu fito mu ci abinci yaran suka ce sun koshi ni ma da na ce na koshin ya ce bai son zama da yunwa dole ni na bi shi na yi mishi godiyar alherin shi ga mahaifiyata muka fita Madam Farha an sha kwalliya cikin wata kyakkyawar riga da ta yi kamar yar tsana a cikinta.

Hajjo ta ƙwala wa kira ta zo ta yi saving na shi ya ce ta je kawai zai zuba da kanshi sai dai ci daya ya bata rai ya ce wane irin abinci ne wannan?

Ta ce ba ita ta yi ba. Tsaki kawai ya yi ya miƙe ya shige wurin shi.

Washegari da wuri na yi shirin makaranta muka fita da yaran muka bi direba don ina ganin kamar yau ma ba zai fita da wuri ba sai dai tun kafin mu isa gidan Mami ya kira ni ina ina? Na ce na tafi makaranta. Ya ce yaran fa? Na ce na fita da su zan ajiye su gidan Mami sai na dawo. Ya ce me ya sa ban jira shi ba? Na ce zan makara ya ce na ci abinci na ce E nan kuwa ban ci komai ba.

Na biya na sauke su sai da muka fito lacture muka je muka ci abinci da Hafsah.

Na samu kiran shi ya ce idan na tashi in wuce kawai zai zo da yaran idan zai dawo na ce To.

Na dawo a gajiye Hajjo ta same ni a falona bakar leda ta zo ta ajiye gabana kafin ta koma nesa ta zauna a ƙasa.

Na ce “Me aka samu? Ta yi fara’a “Abin biki ne, taro ya tashi lafiya Haj, dazu kanena ya zo mahaifiyata ta ce a yi miki godiya.” Na ce “Ba komai, Allah ya sanya alheri.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 47Mutum Da Kaddararsa 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×