Skip to content
Part 60 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ranar da ta tafi ina kwance a ɗaki da rana Mashkur na gaba na yana barci, wayata riƙe a hannuna ina duba status. Na Khadija da na duba ta ɗora wasu kaya sun yi matukar tafiya da ni take na zaɓi wadanda suka yi min na tambaye ta kudinsu.

Ashe tana kusa Stickers ta turo min ta shegantaka sai ta biyo ta da cewa Mai jego har an gama wankan ne za a koma Office? Na ce E.

Dandanan sai ga kiranta dariya take ta yi tana ƙarawa na ce Ni dai don Allah nawa kuɗin su ta sanya kudin kowanne a jikinsa a maimakon hudu da na zaba ta zabar min wasu hudun ta ce su ma za su yi min kyau amma in bayar da kuɗin shida. Tabbas akwai tsada sai dai sun ci kudin su riga da wando ne huɗu masu skirt ma huɗu ta ce ki aiko mai aikinki ta karba miki na ce “A’a ƙyale wannan mai aikin mai aikin Aunty Farha dai, ki dai ba Laraba ta kawo min. Ta ce “Laraba ta je kasuwa.” Ta kawo min idan ta dawo idan na ji shiru kuma za ki ji kira.

Muka ajiye waya na rufe ido ina kallon hoton salon da Aunty Farha ke ma ya Safwan idan na fita ba shi abinci wanda bai taba yarda ya ci sai na zuba mishi ya yin da ni kuma Inna Jamila ta sanya ni yawo da rufa.

Ina nan kwance sallamar su Khadija na ji na fito falona na same su, leda ta miƙo min mai dauke da kayan da muka yi magana na ce ina Laraban? Ta ce “Shiga kawai na yi gidan Hafsa na ce mu zo wurin ki Hafsa ta karbi Mashkur na tambayi Nanarta ta ce tana gida, ta ce “Wai da gaske kin karɓi girkin ne? Na ce “Ban karɓa ba amma ai ni ke ma ogan tun tafiyar Mai aikin Mami? Wani kallo Khadija ta yi min.

“Akan me ita matar ta shi fa? Na taɓe baki Ni ya kalallame ya ce in riƙa mishi.” Suka dubi juna Hafsa ta ce “Ikon Allah idan ba ka mutu ba za ka ga abu, dama ana haka gaskiya ki canza taku Bilkisu, ya za a yi ya mayar da ke kamar wata shashasha ta kwana da miji ki yi musu girki? Amma fa ki yi haƙuri ba zuga ki nake ki bijire wa mijinki ba mu ma nan duk muna da mazajen kowacce da ƙalubalen da take fuskanta a ta ta rayuwar auren.

Amma dai wannan ita ma ta fito ta yi ki yi shi kenan idan ma ba za a bari ki yi arba’in ɗin ba.
Khadija da ta rafsa tagumi ta ce “Allah ji nake har zuciyata na tafasa wannan wane irin rashin yanci ne ita ce mai yanci ta ƙi yin girki ta kwana da miji mai jego da shiga kitchen ta yi ƙwafa ku raba kawai ta yi na ta ki yi naki shi kenan. Ni kin ga ma budurwa ce a waje ba ma a aure ta ta shigo ba amma ta zama kamar kishiyata kuma hakanan nake hakuri ya za ka yi lamarin nan na maza. Duk suka gama zantukan su ina sauraren su na kuma dauki shawarwarin su tsaf.

Duk da ni ban ɗauka a ya Safwan sakarai ya ɗauke ni shi ya sa ya sa ni girki Farha na zaune. Yana mutunta ni ya mutunta nawa, ban nemi komai na rasa ba bai musguna min, mata nawa suka samu rabin abin da na samu a wannan zamani sai kuma in duba mazan da na aura a baya wanne na samu yadda na samu a yanzu sai nake gani idan ban bi umarnin ya Safwan ba kamar na zama butulu meye a cikin girkin da zai ci. Amma dai zan gwada ce mishi mu raba ta yi in yi.

Sun tafi ba jimawa ya Safwan ya shigo na tashi zaune daga bisa kujera ya dauki Mashkur “Yaya dai ko kewar Maman kika fara? Na yi ɗan murmushi sai na ce “Uhmm. Ya ce “Uhumm yi maganarki.” Na ce “Dama na ce ka raba mana girkin ni zan yi ranar nawa amma na bar kwanana sai na yi arba’in.”

Kallona ya yi da kyau “Wani abu ya faru ne?

Na girgiza kai “Ba komai na ga dai ita ɗin ma matar gida ce tana zaune ina mata girki. Ita kike ma wa? Ya tambaya yana kallona “To ai za ta kallan shashasha tana zaune ina mata girki tana kwana da miji.”

Shiru ya yi kamar ba zai ce komai ba sai ya ce “Daga yau na yafe miki girkin Bilkisu. Yadda take da cikakken iko ke ma kina da shi zan kawo ki dafa ki ci abin ki kamar yadda take yi.

Amma ni ina ce na ajiye mata biyu zan samu inda zan ji sanyi? Daga babu na hakura zan koma gidan Mamina in riƙa cin abinci. Farha kuma zan fadi miki maganar da ban son in yi maganar wata da wata, girkinta bai min ba, ni kuma an yi ni wanda bai yarda ya ci abin da bai mishi kyau a fuska ba ko a ɗanɗano da na same ta a ita ma ba ta cikin matan da ba su damu ba don mazan su sun ci girkin su sai nake ci gidan Mami da na same ki kuma ina cin naki.

Amma daga kina ganin ke danne ki nake ina ɗaga ta na haƙura da cin naki, ki yi wanka ki min kwalliya ya ishe ni.

Turus na yi jin wannan dogon magana kamar in ba shi haƙuri in ce zan yi sai dai na yi shiru ya cigaba da wasa da Mashkur karshe ya mike da shi a kafadarsa ya fice dakin.

Ya bar ni cikin nazari da saƙe-saƙe, na dai yanke zan cigaba da yin.

Da wuri na yi wanka na yi ma Mashkur sai na goya shi na shiga kitchen. Ko nan nasan na yi kewar Inna Jamila Allah dai ya taimake ni har na gama tashin shi daya.

Na koma daki na kira Ruƙayya Babangida abokiyar karatuna na tambaye ta kan karatun na mu ta ce har yau ba a yin komai, tun komawa hutu na ji daɗi don Ni ya zo min a daidai tun hutun sabuwar Shekara da aka yi har yau karatun ya ki daidaita

Sai da na yi sallar Isha’i ina addu’a ya Safwan ya shigo bai zauna ba Mashkur ya ɗauka ya fita da shi na miƙe na cire hijab ɗin na koma gaban mirror na yi kwalliya na gyara gashina na sanya turaruka sannan na ba za kayan ina tunanin wadda zan sanya ƙarshe na hakura da wasu riga da wando masu laushi kalarsu Sky blue na sanya suka lafe da fatar jikina sun toni diri mai jan hankali da rabbi gwanin tsara halitta ya ba ni.

Dogon hannu rigar gare ta sai daga wuya tana da kwala da samar rigar yake a bude saman kirjina a waje.

Dan gyale na daura a kaina na zura takalmi na juya gaban mirror sai da na ga kamar ba ni ba ina Aunty Farha me ƙaryar shigar turawa?

Na fito falon suna zaune kamar kullum Mashkur na kafadarsa yana jijjiga shi Aunty Farha na gefen shi kallo ɗaya ya yi min ya kauda kai ya sauko Mashkur “Zo ki ba shi nono kuka yake.”

Na isa gaban shi na miƙa hannu na karɓe shi kujerar da ke kallon wadda suke zaune na zauna na ɗora ƙafa daya kan daya na ciro nono na sanya mishi ya ɗan tsotsa na canza mishi sai na miƙe na kai mishi shi na wuce kitchen na yi ta karakainar shirya mishi komai da na gama na ce na gama ya taso yana zama na zauna na zuba mishi wayarsa ya cigaba da dannawa.

Muna zaune mun yi minti ya yi sha biyar ya mike ya ce min sai da safe har ya ƙule ma ganina ina kallon bayan shi.

Cikin sanyin jiki na tattara komai na mayar kitchen na wuce daki dama aunty Farha tunda muka hau dinning ta ɓace.

Na kwanta cikin damuwa da tunani iri-iri.
Da asuba ya shigo duba Mashkur don ka’ida ne sai ya shigo ya gan shi ina kan sallaya na gaishe shi ya matsa inda yake kwance yana barci ya dauke shi “Yau zan koma makaranta.”

Na ce mishi “Ba za ki koma ba ki karbi girkinki kin ƙi sai makaranta?

Na marairaice bai ce min komai ba ya tafi da Mashkur a kafadarsa.

Ban fita ba sai da na sheƙa kwalliya ta daukar magana na dake a falo da zai fita ya gan ni anan ya ce ina Mashkur na ce yana barci ya wuce zuwa kofata ban bi shi ba sai da muka zauna da Aunty Farha da ta fito bayan fitowar sa.

Da na shiga ya kwantar da shi ya miƙo hannu zai taɓa ni kome ya tuna sai ya janye ya tambaye ni yaushe zan yi arba’in ɗin da na ce na ce saura kwana tara kai ya jinjina ya ajiye min kudi ya fita.

Sauran kwanakin da suka biyo baya hakan ce ta yi ta faruwa da daddare zan matse in tsuke girki ne dai tun daga sau biyu na bari don na gane da gaske yake ba zai ci ba yana dai mutuntani ya je ya zauna ganin idon Aunty Farha,

A kwana na biyun na samu kiran Mami ina gyara kayan Mashkur ta ce “Ke ma kin bi sahun waccan ɗin ne ba a yi ma miji abin da zai ci? Na ce “A’a Mami. Ta ce kuma shi ne yake zuwa nan yana cinye mana abinci? Na yi shiru.

Ranar da ta yi maganar da zai shigo da abincin shi ya shigo ya zauna tsakiyar falo na sha kwalliyata da riga da skirt da suka matse ni dam ina zaune ina kallon shi Aunty Farha ta fito wai sai ta je ta zauna za ta sa hannu ya ce “Ɗan saurara min Malama tashi ki ban waje.”

Ta mike kuwa ba ta zauna ba ta yi daki.

Idan zai fita in sheƙa kwalliya ta alfarma na kuma dage da gyara kaina shi ya sa na ƙi karɓar girkin.

Aunty Farha ta shiga wani yanayi duk da kokarin dannewa da take ta hanyar yin fara’ar da ta saba wani lokacin fara’ar ta kan ƙi bata haɗin kai ta zama yaƙe.

Ranar da na yi arba’in tun safe na yi ma Khadija da Hafsah magana suka turo min masu aikin su suka hadu da Hajjo suka fara gyaran gidan dayan wurin nawa na yi niyyar komawa Ni kuma na shiga na ya Safwan na fara gyara don gyaran duk na ƙyuya ake mishi sai ya yi mata fata-fata take gyaran.

Kan ka ce me gidan ya dauki wani irin ƙamshi ban kuma daddara ba ranar na shiga kitchen da nufin zan ba shi haƙuri don ni dai ban ji zan iya dauriyar miji bai cin abincina ba.

Farha da ta fita daga turaka ta koma ɗakinta tunda ta ji Bilkisu a falon shi tana gyarawa ta kuma san jiranta take ta fito tuna yau za ta kwana da Safwan ya kulle mata zuciya ta fita ta koma na ta ta hau gadon ta ji komai ma ya kwance mata ta tashi zaune ta shiga wanka tana fitowa kamshi mai matukar dadi ya rika shigowa ta window ta da ta daga ta saki labulan wayarta ta shiga ringing ta isa ta dauka ƙanwarta ce diyar Auntynta kayan da za su sanya ranar birthday din diyar ƙanwar ta ta ta faɗa mata kudin da za ta turo na ta da na Afnan.

Cikin shaƙaƙƙar murya ta ce za ta sanya.

Ta cillar da wayar bisa gado ta koma ta zauna tuna abin da ya yi saura a asusunta na ajiya idan ta kwashe za ta yi ma kanta ƙarƙaf Safwan ya ƙi mata daɗin kai tun yin auren shi kudaden da yake ba ta kamar bai san zafin su ba yanzu ya bari komai sai mai muhimmanci yake mata. Sai ta tuna maganar da wata yar’uwarta da ta zo gidan Auntyn ta ji Farha tana complain ta faɗa mata “Kar fa ki ga laifinsa Farha, yanzu ba da ba ne yanzu ya yi aure yasan dadin mace ta yi maka hidima don ta faranta maka amma don Allah ke me kike ma miji na faranta wa? Sai dai fa shi ya yi miki in kin bibiya ya samu wadda ta san kanta ya ba ta ta gode ta zauna ta shirya mishi girki ta tasa shi sai ya ci ba ke ba da ke dai a ba ki kudi k…. Auntyn su da ke zaune ta tsaida Yar’uwar ta hanyar cewa ya isa ganin Farha ta fara kumbura.

Yadda Bilkisu ke yawo cikin shigar matsattsun kaya ta riƙa mata gilmi a ido wani zafi kirjinta yake ta bugi katifa da hannunta ba za ta iya zama tana kallon wannan takaicin da zai kusa a jalinta ba, ashe da ciki ne ya sa ta bar ta ta ci karen ta ba babbaka.

Miƙewa ta yi ta soma haɗa kayanta tana shawarar ta yi tafiyar ta ko ko ta bari ya dawo da kyar ta haƙura ta bari ya dawo sanin ta tafi gidan Auntyn ta sai ta yi da gaske kafin ta samu ya bi ta kanta.

Da muka gama gyaran gidan wanka na yi na sheka ado na dawo falon da yanzu Aunty Farha ta rage zama a cikin shi sai dai ta bar gidan ko ta shige wurin ta.

Cikin mamaki sai ga ya Safwan abin da ba ya yi dawowa da rana anan falon ya tsaya ya dauki Mashkur na ce “Ga abinci can ya Safwan.”

Kallona kawai ya yi maimakon ya amsa min sai ce mun ya yi “Amma aikin daga yanzu zai fara ba sai dare ba ko? Na yi murmushi “Har yanzu aikin Aunty Farha ne sai dare nawa zai fara.” Zai yi magana Aunty Farha ta fito janye da akwati ta dube shi ta ce tana son magana da shi ya ce To.

Ta juya ya bi ta sun dade har na fara tafasa sai ga shi ya fito kamar ran shi ya ɓaci ita ma ta fito riƙe da wani akwatin wurina ya shige na matsa inda take tsaye ta ce “Zan tafi Nana.

Tafiya kuma da ranar nan.” Ta ce “E zan wuce.”
Ta koma ta cigaba da kwaso kayanta da ban san san da ta shigo da su ba.

Isya ta kira ya kwashe mata har zuwa mota sai da ta tashi motar na koma ciki.

Kwance na same shi ɗaiɗai bisa gadona na ce Saboda Allah Aunty Farha za ta tafi ko kai ba za ka faɗa min ba. Kallona ya yi kamar ba zai tanka ba sai na ji ya ce “Ni ma dawowa ta yanzu ta ce za ta tafi.”

“Dama an gama gyaran?

“An gama. Kayan da za a zuba mata ne ba su zo ba na ce ta bari har su zo ta ce za ta koma gida.”

Na jinjina kai ya ce “To yanzu dai aikin naki ya fara ko?

Na yi dariya na ƙi magana “Miƙa ma waccan matar Mashkur sai ki zo.”

Na ce “Ni fa na tashi dakin nan.

Ya ce “To bari sai dare sai mu koma can.

Na fita na nufi dakin na Hajjo tun kafin in karasa na ji muryar ta cikin hargowa tana faɗin “Wallahi tun wuri ki fita idona ki baro wannan matsiyacin gidan, uwar me yake ba ki da nake ta fama da ke ki baro gidan kin ƙi?

Na murɗa handle ɗin na shiga da sallama ta yi wata uwar zabura da har ta ba ni mamaki sai ta cire wayar tana faɗin “A’a Baban masu gida ne. Na ce “Ke da wa Hajjo kike ta faɗa?

Ta kama yar dariya “Ni da yara ne Haj, kin san yaran yanzu.

Na ce “Haka ne. Na ji ki shiru ko gajiya ce ba ki gyara kitchen ba? Don hakanan na ji ban aminta da ba ta yarona ba.

“Haba wace gajiya Haj? Yanzu zan fito.
Na fita na ja mata ƙofar.

Na koma wurin ya Safwan na matsa zan kwantar mishi da mashkur gaban shi ya ce “Sanya shi gadon shi ki zo. Na matsa na kwantar da shi ya taso ya kama hannayena zuwa gadon.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 59Mutun Da Kaddararsa 61 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×