Skip to content
Part 3 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Koda na dawo gida saida na labartama Mama duk irin abinda ya faru da kawai ni tabawa hakuri tare da nunamin yadda nake tunanin halayyar wasu daga cikin ‘yan adam tafi irin yadda Aunty Asma’u ta nunamin tata halayyar

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya garemu har Ahmad kanina yasamu adaidaita sahu ta haya da akwanakin baya ya wani makwabcinmu Alhaji Yassar Makama da yake raba adaidaita sahu yazo garin da ba zaman Kanon yake ba yana Abuja da zama nan ya rabawa matasan layinmu adaidaita sahun da Allah yayi da rabon Ahmad wanda kana gama biyan ku’din adaidaita zata zama taka,bawai dan Ahmad yakai shekarun da zai iya tu’ka ba,sai dai nace Allah ne yasa zai samu ‘din Alhaji Yassar yanada alkhairi sosai dan Tahfiz din da muke zuwa shiya ginata mallakinsa ce kuma a kyauta muke zuwa danasan banda hakan karatun addinima gagararmu zaiyi,sai gashi Allah ya dubemu a lokacin ginata mu da muke makwabtansa a kyauta muke islamiyyar da kullum nayi sallah nakan masa addu’a da fatan alkhairi dukda ban ta’ba ganinshi ba amma tarun alkhairinsa ya sani hakan,nakan ji a raina inama duk wani mai ku’di ya zama kamar Alhaji Yassar ‘din,inada burin na ganshi fuska da fuska dukda bazan iya sakamasa da abunda yayi mana ba amma dai zanji dad’i ace nasan mutumin da yake mana alkhairi,da danginmu suka kasa yi mana a dalilin Alhaji Yassar na yarda ashe akwai masu ku’din da basu k’yamar talaka.

Ahmad yana samo adaidaita sahun da duk muka cika da murna da sai washe garin ranar zasu je su anso a kamfani da za’a ha’da musu ita gefen Mama ya zauna yana bamu labari da muka shimfida tabarma tsakar gida na dubi Ahmad d’in
“Wai niko Ahmad kaga Alhaji Yassar Makaman.”

Ya kalleni kallon baki da wayau ‘dinnan

“Wannan mutumin kike tsammanin za’a gani,ai ganinsa saikin cike Form Yaya.”

Nima dubensa na ‘karayi

“Allah ya kyauta saboda kallon ‘dan adam kamarni na tsaya cike form”

Mama sai yanzu tasa baki ta dubeni

“‘dan adam ne Sumayyah amma dai Allah ya bashi matsayin da bai bamu ba,kinga shiyasa saikama cike form ‘din ba lallai ka gansa ba.”

Na jinjina kai dan gaskiya Mama ta fa’da dan wa’danda basu taka ‘kafar arzikin Alhaji Yassar ‘dinba suke wuyar gani bare kuma wannan mutumin da nidai har tsayawa nake Iina yarinya kallon irin tsarin ginin gidansa,saida na girma na saba da kallon gidan na daina”

Maganar Ahmad ta katsemin tunanina.

“Ki barta Mama gani take wasa ne, managernsa ma kwananmu biyu muna zuwa sai ana biyu muka ganshi bare kuma shi,da cewa ma akayi ranar da yazo garin ya koma a jirgi an kirasa Abuja kiran gaggawa ,ai irin wa’dannan saidai ka gansu a hoto,dan koda sunso suga talakawa ba lallai su samu lokaci ba,shimafa mai ku’din bafa a hutu yake ba”

Mama tace

“Hakane Ahmad,fatanmu dai a kullum Allah ya bamu arzi’ki mai albarka dan tarin dukiyar nanma ba wani abu bane,wani lokacinma ita ke halakar da kai”

Muka jinjina kai alamun gamsuwa da maganar da Mama tayi,

Na dubi Mama

“Amma dai irin wa’dannan masu ku’din Mama zako a samesu da wata damuwa a ransu”danni tunanina a kullum yakan bani damuwa ta talakawace irinmu.

Maganar Mama ta katsemin tunanina.

“Sumayyah kenan ai ba wanda baida damuwa,saidai ta wasu ta ‘dararma ta wasu,akwai wanda damuwarsa ku’dinsa bazasu magance masa damuwar dake damun sabama,kawai dai mu cika zuciyarmu da godiyar Allah.”

Mu duka muka kalli Mama muka ce

“Alhamdulillah” haka muka cigaba da firarmu.

Ahmad da yake aji uku a secondary hakan yasa Abbanmu ya daina zuwa kasuwa ya koma jan adaidaita sahu ka’in da na’in dan dama zuwa kasuwar anayine kawai badan ana samun wani abuba.

A lokacin abubuwa suka fara sauyawa a rayuwarmu a lokacin na shiga aji biyar a secondary muna ‘ko’karin zana jarabawar Qualifying a lokacin Mama ta haifi ‘yarta mace da akasa mata suna Aisha muna ce mata Humaira da sunan ya kasance na Mamarsu Abbanmu.

Kasancewar haihuwar Maman da sallah ne hakan yasa ‘yan uwan Abbanmu suka zazzo harma wa’danda ba Gwarzo suke da zama ba dalilin zuwan sallar da suke,da muma a baya muna zuwan saboda ‘kananun maganganu yasa tun ina primary rabonmu da zuwa da ‘karamar sallar saidai Abba yaje,mu kuma da Babba muje mu da Mamanmu.

Tun ana gobe suna ‘kannen Mama su biyu Aunty Jamila da Aunty Asiya da yaransu da kowacce tazo da wanda suka take goyo suka fara zuwa dan ma gidan namu baida girma hakan yasa biyu ne suka zo a ‘yan uwan Mama,da indai hidimar Mama ta tashi suna yi mata Kara hakan yasa ba laifi inason ‘yan uwan Mama da rashin wadata yasa nasan basuyi mana abubuwa,amma dukda hakan da Mama ta haihu sunzo mata da kaya da yawa da wanda zata yi fitar suna dana girkawa

Ranar suna dangin Abba da Mama sun ha’du da dangin Abba ba yabo ba fallasa suke amsa gaisuwar da muke musu ‘kawata Halima da tazo tun safe muka shiga ‘daki da ita da sai ‘karfe biyu muka fara ‘ko’karin yin wanka bayan angama aike aikenmu da harda Haliman ake aiken namu.

Baban Katsina da yazo da matarsa da ‘ya’yansa da tun ina yarinya rabon dana gansa sai dai sunansa da muke ji a gwarzo shi Abba yazo ya kiramu mu gaisa da ko minti biyar basuyi ba a gidanmu suka fito zasu tafi damu lokacin muna ‘dakinmu muna shirin fitar suna nida ‘kannena haka muka biyo bayan Abba har zuwa waje inda Baban Katsinan yayi parking ‘din motarsa hakanan naji banaso na gansa saboda tunowa da nayi a dangin Abba ba wani wanda muke da matsayi a gurinsa ga wannan kuma da duk ya fisu ku’di dan inaji ana maganar irin ku’dinsa a Gwarzo idan munje hakan yasa naji zullumin ganinshi domin nasan ba zamu samu wani kallon arzi’ki a gurinsa saboda nasan yadda masu ku’di suka ‘ki jinin su ga talaka, da wannan tunanin muka ‘karasa inda motar tasu take Abba yayi sallama Baban Katsinan da ‘kafarshi take waje daga cikin motar ya fito da ‘kansa ya kalli Abba yana amsa sallamar,ina ganin Baban Katsinan na ganeshi dan koda bansanshi ba yana kama da Abba sosai zan iya ganesa
Gaishesa mu kayi ya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa matarsa da take bayan motar ta le’ko muka gaisa da itama na ganeta ‘ya’yansa ma duk mungaisa da wanda yake jan motarsa da nafi tsammanin ‘dansane dukda ba wata kama yake da Baban Katsinan ba naji yana cewa.

“Abba Abdallah Ina Sumayyan taka”

Abba yayi murmushi ya nuna ni

“Gata nan Samir”

Shima murmushi yayi wanda aka kira Samir yana kallona

“Abba tayi girma,kamar ba ita bace nasanta tun ana goyonta ba”

Abba ya sake yin murmushi yace “kasan girman ba wuya”

Kallon sa nayi da nima ni yake kallo a lokacin ido muka ha’da yayimin murmushi nima na maidamasa da murmushi nawa yake ha’de da mamakin Samir ‘din da naji yace
“Tunma ana goyona yasanni”

“Abba ajinta nawa yanzu”naji Samir ya sake jifan Abba da tanbaya
Abban yace masa

“Ta zana qualifying wannan shekarar”

Kai wannan akwai tanbaya na bawa kaina wannan amsar a cikin zuciyata dani duk tanbayata wani lokacin idan yaro na yiwa babba tanbaya haushin mai tanbayar nakeji amsar Samir ta katsemin tunanina da naji yace

“Allah ya bada sa’a”

Addu’a kawai muka musu

“Allah ya kiyaye hanya”

Muka baro gurin muka baro Abba da Ahmad da Sadik dan tanbayar Samir ta fara damuna kodan rashin sanin da bamuyi musu bane bansaba da suba yasa naji hakan
“Oho”

Muna k’o’karin karasa shiga cikin gidannanmu na tuna Khadija zata siyomin ruwa pure water na bawa Halima da taci abinci ba ruwansha ruwan gidan namu saboda hidimar suna duk ya ‘baci a ‘kofar gida muka tsaya Khadijan da nasan Khadijan idan ban tsaya na ansa ba tana iya ba wani

Naji muryar Aunty Luba ‘kanwar Abbanmu tana cewa

“Kinsan me Fati wallahi Yaya Hashim yayimin daidai daya tafi,to zaman mai mutum zaiyi a rasa mai za’a girka gidan suna sai danbu ka’dai shima kona shinkafarnan na zamani bai samu ba,sunan ana zaune a binni,yara sai sunzo Gwarzo su cika mutane da iyayi”

Muryar Aunty Maimuna naji ta dora da cewa

“To mai zaki gani, bayan yana tare da mai ‘kashin tsiya,anyi anyi ya rabu da ita ya’ki,ni kinga ma mu koma ciki muyi musu sallama,mu tafi gidan Asma’u mu kwana acan dan naga kamar Asma’un ba zata zo ba dan nan dai banga gurin kwana ba”

Aunty Mabaruka da sai yanzu naji muryarta itama naji tana cewa

“Ke aini yau nakejin labari ashe Yaya Hashim ya sama masa aiki a Katsina tuntuni yace ya za’ba ko aiki ko Hauwa’un yace wai ya za’bi matarsa ku jifa?”

Dawowar Khadija tare da mi’komin sa’kon yasa ba muji amsar da zasu bawa Aunty Mabarukar ba da sallamar mu ta sa suyin shiru da bakin su,a raina ina ayyana rashin mutuncin dangin Abba har yakai haka ace Baban Katsina da shine Yaya Hashim ya hana Abba aiki saboda Mamanmu,har sunfiso su gansa a irin rayuwarmu haka saboda ya nuna bazai rabu da Abba ba kuma har ake Kiran Mama damai ‘kashin tsiya hawaye na goge da suka zubomin,da muna shiga ‘dakinmu da ‘kanne Mama ke ciki da Halima da Batul wadda bayan fitarmu tazo muka tararda cin mutuncin da ‘kannen Abba sukayiwa Mama da ‘yan uwanta,da gama rigimar kenan muka shigo,Allah sarki Mama da banda ‘kaddarar aure nasan ba zata auri Abba ba ake yiwa wula’kanci kuka nayi sosai jin labarin da Rumaisa ma takeyi hakama Khadija,dama taron masu ku’dima ana tashi da ‘kananun maganganu bare wannan da kamar dole akayiwa ‘yan uwan Abba gurin zuwa sai Yamma lis Aunt Asma’u ta zo gidan suna da lokacin tuni su Batul da Halima sun tafi harna dawo rakasu, banma ganta ba muna ‘daki da ‘yan uwan Mama muka ji muna tattauna rashin mutuncin irin na ‘yan uwan Abba,da abun biyar a cikin matan ba wanda ya kawo masa,mukaji anacewa tazo da ba da’dewa naji ana cewa harta fito da nasan yanzu ‘yan uwanta zasu ‘buya gidanta kwa’dayi da su ‘dinma ba susan basu tsira a gurinta ba.

<< Na Cancanta 2Na Cancanta 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×