Skip to content
Part 9 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Qofar babban falon gidan Mama Atika muka bu’de da sallama dauke da bakinmu,babu kowa falon sai qarar Tv da tashar Africa TV ce ake kallo zama mukayi nida Halima a kujera mai 2seater muka fara kallon film episode na Iyalina dashi ake haskawa tashar Africa TV ‘din muka tarar,bamu jima da zama ba Mama Atika ta shigo falon da sallama gami da fara’arta muka amsa mata ta zauna kujera mai kallon tamu.

Gaisheta muka yi ta amsa murya sake ta kalleni.

“Lale marhabin da manyan baqi,Yanzu Ina kitchen naji kamar anyi sallama shine na leqo ashema kune,amma kuka tsaya daganan kamar gidan baqonki ne Sumayyah.”

Mama Atika ta qarasa zancen fuskarta sake
Na kalli Mama Atikar na ce,

“Yanzu nake shirin shigowa sai gaki.”

“Mama Atikar ta ce,

“Ya mutanan gidan,kwanaki Khalifa yayi anguwar taku har nace ya biya yaji lafiya kwana biyu,Auntyn tasu bata turoku,to sai ya kirani waya yace dare yayi bazai samu biyawa ba,ni ‘dinma naso zuwa to hidimar yau da kullum idan baka ya kicewa saita hanaka zumuncin na.”

Na jinjina kai na ce,

“Hakane Mama,muma makaranta ta ‘boye mu bamu zuwa.”

Ta ce,

“Hakane yanzu a jikinki nawa ne.”

Na ‘dan yi murmushi.

“Wannan shekarar mukayi qualifying.”

Mama Atika ta ce,

“Allah ya taimaka ya bada sa’a.”

Na amsa da

“Amin”

“wannan fa banganeta ba.”

Tayi maganar tana nuna Halima.

Na ce
“Qawata ce,sunanta Halima,ai mun ta’ba zuwa nan da ita”

Mama Atika ta ce

“Aiko bangane taba,sai yanzu….”

Bamu qarasa zancen ba,Aunty Abida ta qaraso cikin falon ta nufi gurin Mama tana magana a shagwa’be,ko gaisuwar da muke mata bata saurara ba ta fara magana.

“Mami yunwa nake jii.”

Tsaki Mama Atika tayi ta kalleta

“Zoki daukeni ki cinye,tunda baki san hanyar kitchen ba sakarai kawai, Kuma baki ga su Sumayyah bane,har gaisheki suka yi.”

“Yi hakuri Mami ban ji bane”ta qarasa zancen tana kallonmu

Mama Atika ta ce

“Kyaji ai”

“Sannunku”Aunty Abida ta ce Mana

Muka amsa cikin ha’da baki “yawwa,Aunty

Abida ina yini”

Ta amsa da

“Lafiya lau”

Daga nan tayi gaba a girme Aunty Abida ba wani girmemin tayi da yawa ba kawai matsayinm qanwar uwa gare ni nake girmama ta,amma banda haka mai zai ja min gaidata,kawai matsayin ta gareni yaja haka
Maganar Mama Atika ta katsemin tunanina.

“Ina Rumaisa ne,ba kuzo da ita ba.”

Na ce,

“Eh amma Mama ta ce zasu so da ita da Ahmad da Khadija,nima saboda zan tafi Katsina nazo yau.”

Mama Atika ta kalleni.

“Katsina Kuma gurin wa?”

Na ce “gidan Abba Hashim (Baban Katsina”

Mama Atika ta kalleni ba tare da tace komai ba ta ce

“Allah ya kaimu lafiya”

Na amsa da “Amin” nasan Mama Atika tayi niyyar magana sai dai ganin Halima nafi tunanin ya sata yin shiru domin tunaninta bai bata Halima tasan abubuwa da dama a rayuwata ba.

Sai la’asar bayan munyi sallah muka baro gidan Mama Atika bayan munci abinci mun qoshi da dukda nace mata munci abinci sai da ta tilasta muka qara ci,Kaya masu yawa ta bamu da ku’di dan Mama Atika akwai san kyautatawa ‘yan uwanta yaranta ne dai ba su da kirki,zan iya cewa kaf dangin Mamanmu babu mai san Mama kamar Mama Atika kodan kasancewar kusan tare suka taso kuma gidansu ‘daya sai dai matsala guda Mama Atika bata zuwa gidanmu sosai bakomai na halin da muke ciki ta sani ba,ita kuma Mama bata fiye kai qorafin yanayin rayuwarta ba takan ce”Ubangiji ya kamata mu kaiwa kukanmu,shine yake son mai roqarsa amma ‘dan adam bayansa roqo,ta kance shima korafi kamar roqo ne,ita bata fatan tayi”hakan yasa bakomai ‘yan uwan Mama suka sani game da rayuwar da take ciki ba sai inhar sunzo su gani da idonsu su yi ta fa’da bata fa’damusu,dukda suma ‘din ba wani qarfi garesu ba,Mama Atika ce dai dukta fi su hutawa,ita kuma ba wani zuwa dangi take ba,wasu sunce mijin tane bai fiye bari ba.

Yau ta kama Asabar ranar da Yaya Samir zaizo tun asubar fari na gama shirina wanda inayi ina tunanin makomata idan naje gidan Baban Katsina ya rayuwata zata kasance.
Mama ce ta kalleni da na fara hawaye jin Yaya Samir ya fa’dawa Abba ya tawo yana hanya,hakan yasa Abba ya fita waje,da tun zamansa gidan yau fa’da da Nasiha yakemin kamar wadda za’ayiwa aure ko na tafi kenan bazan dawo gidanmu ba.

“Sumayyaha kukan mai kikeyi kamar wata yarinya ya kamata ki samawa kanki lafiya,ko ni da aka tura boarding tun daga JS1 ban ta’ba kuka haka ba,bare ke ‘din da girmanki kuma cikin ‘yan uwanki zaki tafi.”

Maganar da Mama tayi ta katsemin tunanin da nake da nasan dauriya kawai tayi amma dai kowa yasan ba rayuwar ‘yanci zanyi ba gwara ace ma rayuwar boarding ‘din, kamar bazan magana ba na dai daure nace
“Mama ina tsoron mai zaije ya dawo bayan zuwana kina ganin dangi Abba babu mai sonmu.”

Ta dafani.

“Haba Sumayyah ki tuna Allah a ko da yaushe yana tare dake kuma shine yake qaddara komai duk yadda akaso cutar dake ki tuna Allah baya zalinci kuma zai miki sakayya a gurin Mai qoqarin zalintarki fatana dai dake duk wuya kada ki ta’ba tunanin zalintar wanda ya zalinceki ki sakawa mai zalunci da alkhairi a koda yaushe,sai kiga alkhairi da albarka ya lullu’be ki,zan riqa miki addu’a insha Allah babu abinda zai faru dake koma ya faru ki qaddara a ranki qaddarar ki ce.”

Na share hawaye na,na ‘dagama Mama kai tare da ce wa.

“Mama kinason ki kwantarmin da hankali bayan ke naki ba kwance yake ba ,kawai kina daurewa ne.”

Mama ta riqe hannuna.

“Karki ce haka,Habiba hankalina a kwance yake saboda inada Allah,kuma ma komai zasu miki karki manta kansu zasu yiwa,kuma ba zasu canza ki ba ‘yar uwar su ce ke dole,idan Kuma sun hana wasu su fa’da ba bazssu hana wasu fa’di ba,Kuma komai sukayi na munana miki karki manta haka Allah ya qaddaro miki.”

Kai na ‘dagawa Mama,bankai ga cewa komai ba naji sallamar su Halima da Batul amsa musu mukayi da murmushi cike da fuskata Mama suka gaisar daganan suka maida kallonsu gareni na hararesu.

“Malama hararar mai kike mana”fa’din Batul tana itama hararata.

Na ce” kunfi kowa sani,yanzu ace sai yanzu da ina gaf da tafiya zaku zomin sallama”
Tsaki Batul tayi.

“Dama kika samu muka zo.”

Na ce”ai nasan ko baki zo ba Halima zata zo.

“Kin manta Kalima ce zata zo ba Halima ba,ai ni yanzu da Halima munfi tip da taya,tunda gashi zaki gudu ki bar Halima”fa’din Batul da ta bini da muguwar harara.

Mama ta fara magana

“Kai Batul da Sumayyah sababbu kun fara fa kenan,ni ku tashi ku barmin ‘daki”

Halima da sai yanzu tasa baki ta ce

“Wallahi Mama korasu.”

Batul ta ce

“Ai harda ke”

Haka muka koma ‘dakinmu muka zube saman tabarma muka cigaba da fira da yimin nasiha ko waccensu da idea ‘din da zata kawomin kuma kowacce shawararta abar dubawa ce bayan sun game min nasihar na kallesu.

“Gaskiya nagode sosai,na kuma qara godewa Allah da ya ha’dani da qawaye kamarku,ko ba’a fa’da ba nasan nasan zanyi rashin masoya.”

Murmushi Halima tayi

Batul ta goge hawayenta

“Sumayyah ban ta’ba ha’duwa da qawar da nake jinta raina ba sama da ke,sai kuma Halima,kin CANCANTA da mu yi miki komai bama nasiha ba”

Halima ta dafani.

“Sumayyah  kin cancanta da komai garemu ke qawa ce”

Na goge hawayena da nima suka tararmin
“NA CANCANTA!NA CANCANTA!haka kowa ke fa’da amman har yau na kasa fahimtar hakan”

Halima ta ce


“Dama ke ba zaki fahimta ba,amma ke qawace,ta kwarai ,baki ta’ba yin wani abu na rashin dai-dai gabanmu ba saima idan mukayi mu ki nuna mana bai kamata ba,mu shaidane a bayanki akwai uwa ta gari Mama ta miki tarbiyyar daba wanda bazai so ki da ita ba,muddin yasan kansa.”

Nayi murmushi na ce

“Kuma bayanki akwai iyaye na gari kamar Mama na na gode Allah dana kasance na samu qawaye na gari wadanda su kayi dacen uwaye na gari”

Dariya mu kayi da dariyar tamu tayi dai-dai da sallamar Abba da kuma baqon murya wadda nasan ta ya Samir ce,da mintina ba su fi biyu ba naji Abba ya fito tsakar gidan yana cewa

“Ina Sumayyan  ne?”

Na jiyo muryar Mama tana cewa

“Tana ‘dakinsu Batul da Halima ne suka so”
Sallamar Abban naji ‘dakinmu muka amsa masa su Batul suka gaishesa ya amsa da fara’arta ya qara da cewa

“Wato anzo rakiya,Allah yasa qawartaku karta mantaku idan taje Katsina?”

Na ce cikin muryar tausayi

“Kai Abba karkamin addu’ar haka”

Yayi dariya ya ce

“Ba addu’a bace,kunsan mene”

Duk muka girgiza kai

Ya ce”haka Mama da Mama Atika suka yi da

suka je boarding suka dawo hutu”

Na ce”Mama” da qarfina

Abba ya ce

“Yi hakuri,tashi kuje ku gaisa da Samir,karki ha’damin tanbotse da Mamanku,ke ‘diyar Mama”

Gaba ‘daya muka yj dariya muka miqe inasan Abbanmu saboda yadda yake mu’amala damu tamkar abokansa,danma baida lokaci sosai a gida,amma hakan baisa mun raina sa ba,haka muka miqe ba wai dan naso gaisuwar ba da sallama muka shiga ‘dakin Mama da shi ka’dai muka samu ‘dakin yana zaune saman Carpet ‘din sallah ya ki shigi’da da jikin bango da gorar faro kusa da shi yana danna waya babu laifi Yaya Samir yana da kyawunsa iya nasa Kuma ya iya kwalliya gaisuwar da naji su Halima sun fara masa ya dawo dani tunanin dana tafi ba tare da gama ba nayi saurin bin gaisuwar da sukeyi muka qarasa tare cikin murmushi ya amsa mana
Yana kallan su Halima dani kaina ya ce.

“Habiba ban gane su ba”

Na ce

“Kawaye nane,tare muke Day dasu”

Na nuna Halima na ce masa “wannan Halima”na nuna Batul na ce”wannan Batul”

Yayi murmushi ya kalleni

“Idan kika barni,ku fa ‘yan uku ne,ashe qawaye ne,Allah ya raya ku musha biki”

Nayi murmushi kawai a raina na amsa da Amin

Kallonmu da Yaya Samir keyi ya sani saurin miqewa na ce

“Yaya bari muje”

Ya kalleni ina tafiya fa zamuyi yanzunnan”

Na ce”to ‘dakinmu zamuje”

Muna shiga ‘dakinmu nayi saurin cewa

“Kai Yaya Samir ba dai kallo ba,kunga yadda yake kallonmu”

Batul ta kalleni sheqe qe

“Kinji yarinya da rainin wayau,kice dai Yana kallanki shiyasa ma muka miqe zamu baku guri ke Kuma kika biyo mu”

Halima ta ce

“Fa’damata dai,ashe shiyasa taqi Yaya Hakim da Malam Hamid ashe zumunci za’a ha’da”

Batul tasa dariya ta ce

“Sosai kuwa,mu dai Allah yasa kar ana wanna tafiyar muji labarin ‘daurin aure babu gayyata”

Tsaki nayi na ce

“Ku fa da’dina da ku yarinta.”

Batul tasa dariya ta ce

Au banda ke,ko da ke ba sabanba anyi saurayi Mai mota”

Duk muka yi dariya,rayuwarmu da qawayena tana burgeni idan muna hira bazaka bamu qananun shekaru ba

Haka cikin mintina da Basu fi goma da zuwan Yaya Samir ba muka fito tafiya gaba ‘daya gidanmu dasu Rumaisa suka qi zuwa Tahfiz saboda tafiyata da qawayena suka rakomu har wajen motar Yaya Samir muna kukan rabuwa da ba musan ranar sake ha’duwa ba danma ina da number ‘dinsu a kaina sai dai babu batun yin wayar tunda bani da waya Mama Rumaisa ,Ahmad, Khalil hawaye suke zubarwa da nima hakane gurina ana saka kayana a boot Yaya Samir ya shiga motar nima na shiga gidan gaba yaja motar da addu’o’in iyayena da ‘yan uwana dasu Batul muka bar kofar gidanmu da ni dai tunda nake ban ta’ba zuwa guri na kwana ba,fuskata na rufe cikin hijabi ina hawaye ganin muna qoqari ficewa unguwarmu.

<< Na Cancanta 8Na Cancanta 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×