Skip to content
Part 16 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Alh jibrin ya jinjina Kai cike da fusata yace, ” kawai yarinya karama zata zo ma mutane da tsurfa, to matukar tace zata bankado abinda ke rufe to zata kwana aciki , Kuma hawanta kujerar manaja bazai Hana mu cigaba da yin abinda Muka sababa, yadda na ninke mahaifiyarta a Bai bai ta dauki amana da yarda ta dora min haka itama Zan tura Mata yarda da ni ko ba don Allah ba.”

Murtala yayi dariya yace ” ina goyon bayanka oga, Kuma Kada a manta acigaba da yaga min kamar yadda aka Saba amanace tsakaninmu babu Mai ji balle ya gani.”

Haka murtala ya Kara dararrashewa Yana Kara zuga Alh jibrin.

Unin ranar Sam Taufiq bai wani samu sukuni ba a office hakanan ya ke kokarin dorama Kansa fitina ta tunanin abinda baida tabbas akai.sosai yake son sanin waye mutumin da yaga mujaheeda tsaye dashi da daddare, meye tsakaninsu?

Shin ko dai tambayarta zaiyi? Amma don me zai tambayeta bayan Kiri Kiri tayi masa karya.

Har ya tashi daga office ya wuce asibiti baya wani cikin walwala.

Ya tadda jikin Àlh Yusuf lamido da sauki domin yafi Jin sauki yanzu akan dazu, Haj saratu ta gaya masa yau tuwon alkama da mujaheeda ta kawo ya uni ci, hakan kuwa yayi masa dadi.

Bai dade sosai da zuwa ba itama mujaheeda ta shigo office Kai tsaye itama daga office din take ta tashi da wuri ne saboda tana son dawowa asibitin ta Kara ganin jikin surikinta.

Haj saratu ta cigaba da Lura da yadda Taufiq yake basar da mujaheeda, itama mujaheedan zuwa lokacin ta tabbatar ma kanta da cewa akwai wani abu akasan zuciyar Taufiq to amma menene?, Domin dai aiya tunaninta babu abinda ya faru tsakaninsu. Ta cigaba da Lura da canjawar Taufiq, har zuwa lokacin da tayi sallama dasu ta kama hanyar gida can tabar Taufiq a asibitin.

Har ta Kai gida zuciyarta cike take da tunani .
Sai da ta ci abinci ta koshi sannan tayi wanka ta shirya tsaf ta fito falo ta kwanta tana danna wayarta.

Har karfe goma na dare Taufiq bai dawo ba, hakurinta ya gaza ta dakko daya wayarta ta danna ta kirashi amma har ta gama kukanta ta katse bai dauka ba.

Bata Kara Kira ba , shima bai biyo kiranta ba.
Sai karfe goma sha daya saura minti biyu Taufiq ya shigo gidan. Bayan sannu da zuwa da mujaheeda tayi masa ya amsa ba yabo ba fallasa.ido ta cigaba da binsa dashi har ya shige cikin daki, sai da ya gama wanka ya shirya ya fito falon ya zauna.

Mujaheeda ta dubeshi tace ” gafa abinci can, Kona dakko na kawo maka nan.”

Kallon tsaf yayi Mata sannan yace ” ki dakko ki kawo min , ai baki Saba yin hakan ba , ki daina masu aiki su kawo min ko.”

Ta kalleshi sosai tana Kara nazarin fuskarsa, tace ” yaya Taufiq wai meke faruwa ne, gaba daya Naga Ka canja min ne, tun daga jiya nake ganin tamkar wani abu na damunka, tamkar akwai matsala,”

Ta Kara kallonsa sosai tace, “Idan akwai wani abu ne kayi hakuri ka gaya min, domin dai ni aiya sanina banyi maka komai ba.”

Ya Watso Mata wani irin kallo yace ” Abu daya nake son ki gane ki Kuma sa aranki, duk matar da ta ci amanar aure sai Allah ya gwada Mata ishara tun a duniya kafin aje lahira, Kuma duk abinda mutum zai aikata ko a karkashin kasa ya shiga ya aikata akwai ranar da asirinsa zai tonu ranar yauma tubulal sara’ il wato ranar tonuwar dukkan asirai, don haka mutum yayi komai amma ya sani akwai ranar kin dillanci.”

Cikin daure Kai da rashin sanin inda maganganun sa suka sa gaba, mujaheeda tace ” ban gane inda maganganun Ka suka dosa ba me kake nufi, maganar wace amana kake.”

Taufiq yace ” na dai gaya Miki ki kiyaye domin ranar da duk tunanina ya tabbata ranar zaki yi matukar mamakina,” Yana Gama fadin hakan ya Mike ya shige daki yayi kwanciyarsa zuciyarsa da ransa na suya tsabar damuwa.

Ayayinda ya bar mujaheeda cikin matsananciyar damuwa, mamaki da daure Kai, shin me Taufiq yske kokarin nuna Mata ta rasa gane inda maganganunsa suka Sanya gaba , me yake nufi.nan mujaheeda ta cigaba da Zama tana tunanin abinda Taufiq yake nufi.

******
“Wai ba zaki fito ki dauki tallan shinkafar ba , sai kin Gama ikon naki da kinibibi, kin.kuma sani sarai idan abincina yayi kwantai sai kinyi mamakin irin hukuncin da Zan yanke akanki”.
Cewar Ande Dije da take tsaye kan katuwar robar abincin, Hajara ta dubi muhseena da take kokarin Sanya hijabi tace ” kiyi hakuri wata rana sai labari kije ki daukar Mata tallan Allah ya bada saa ya Kuma tsare ki gabanki da bayanki”, cikin dabara muhseena ta sa hannu ta goge hawayenta domin bata son Hajara ta gani.

Da fara’arta ta juyo tana cewa ” Amin Inna nagode da addua” tsawar da Ande Dije ta cigaba da yi yasa muhseena tayi gaggawar fitowa, Kai tsaye ta nufi wajen robar abincin ta dauka ta dora akanta.

Ande Dije ta daka Mata harara tace ” kin Gama mulkin naki, muguwa saboda kina son abincina yayi kwantai Shi yasa kika ki fitowa ki dauka da wuri, kina sane komai bashi na karba ,nayi abincin tunda uwarki ta Zama Mai bakar kafa ta hana dana ya Sami arzikinsa sai wahala kawai da take bashi.”

Kwata kwata muhseena ta gaji da Jin wadannan maganganun ta Kuma gaji da Jin aibatawa da Ande Dije ke yima mahaifiyarta kullum.

Don haka da sauri ta fice hawaye ta fita daga idanunta , Wanda zubar da hawayen ya Zama wani bangare na rayuwarta domin kullum sai ta zubar dasu.

Can tsohuwar kasuwa muhseena ta tafi inda ta Saba Zama,ta zauna bayan ta aje kayan abincin. Hannu biyu tasa ta zuba tagumi tana kallon sauran Yara marasa gata irinta masu talla.

Duk duniya babu abinda ta ke so sama da karatu mafarkinta kenan arayuwa Amma tasan mafarkinta bazai taba Zama gaskiya ba domin bata da wannan gatan.

Acan gidan kuwa Ande Dije ke Kai gauro ta Kai Mari atsakar gida ta na ajema Hajara magana.hajara ta gaban wuta.

Tana iza wutar faten da take dafawa.amna ita kadai tasan abinda take ji azuciyarta ko yaya Ande Dije ta Watso Mata magana takan ji tamkar numfashinta zai dauke.

“Babu wata nadama da zanyi aduniya sama da nadamar zamowarki suukata, domin dai Baki taba Zama alheri gareni ko ga Dana ba, Shi yasa ummaru yake bami tausayi domin dai baiyi sa’ar Mata ba.”

Hajara na tsuguna gaban wuta zafin da zuciyarta take tafi zafin wutar dake gabanta .
Shin wai haka rayuwarta da ta yarta zasu Kare? Me yasa Ande Dije bata sassauta Mata? Meye laifinta a kaddarar data faru bayan Allah shine ya tsara komai yadda ya so ya Kuma ga dama.

Ande Dije ta Kara gyara zamanta abakin kofar dakinta ta cigaba da maganganunta ” Ga mummunan tarihi, ga bakin hali, ga farar kafa , ga mummunan tarihi da kika aje ai dole a tausayama ummaru.’

Hawaye sosai Hajara ta Fara yi a hankali ta Mike zata shiga daki, taku biyu tayi taji kafafuwanta sun cije, ganinta ya yaye cikin kankanin lokaci ta sulale kasa ta Fadi sumammiya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 15Nima Matarsa Ce 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×