Skip to content
Part 9 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Ko da suka isa gida shima babu Wanda yabi takan dan’uwansa kowa zuciyarsa a wuya take.

Abinda zaici ma masu aiki ne suka kawo masa , kadan ya ci ya tashi ya fice,ràshin sanar da ita zai fita ya Kara harzuka mujaheeda ranta yayi matukar baci.

Hakan yasa tayi ta jiran dawowarsa.bai shigo gidan ba sai karfe sha daya saura na dare. Kai tsaye daki ya wuce bai saurari mujaheeda ba bai kuma damu da irin kallon da take masa ba, yayi Shirin wanka ya shiga wanka .har ya fito ya kintsa mujaheeda na tsakiyar gado rike da wayoyi ta danna wannan ta aje ta danna wannan Karo na farko kenan da yaji ransa ya Fara sosuwa agame da yadda mujaheeda ta dauki waya da matukar muhimmanci yadda bata iya minti biyar bata dauki waya ba.
Ahankali ya gama Shirin bacci ya haye gadon ya kwanta gami da janyo bargo ya rufe jikinsa sosai.

” Yaya Taufiq” mujaheeda ta Kira sunansa tana kallon bayansa. Ya amsa ba tare daya juyo ba ko ya motsa.

Tace ” ban fahimci wannan sabon lamarin ba” ” na mene ?” Ya tambaya a gajarce.
Ta jinjina Kai tace ” yaya kake magana tamkar baka fahimci abinda nake nufi ba , bayan kafi kowa fahimtar abinda nake nufi, tunda Muka dawo sai wani huci da isa kake Ka fita baka cemin komai ba, ka dawo kana cigaba da cika da batsewa don kawai Baka son nayi aiki.”

Ya gyara kwanciyar sa yace ” eh Bana son kiyi aiki bana Jin Kuma akwai Wanda ya isa na barki kiyi aiki.”

Cike da mugun mamaki tace ” Amma wannan maganar da mahaifiyata kake yi ko, itace bata isa ba to shikenan atsaya anan saboda Naga abin Naka Yana so ya wuce gona da iri, Kuma Kada Ka manta wacce kake yin maganar nan akanta mahaifiyata ce wacce ban hadata da komai ba, ba Kuma zan juri Ka dinga kokarin rainata.”

Afusace yace ” ban rainata ba , amna ina son ki sani babu yadda zaayi Ku dinga kokarin juya rsyuwata yadda kuke so ba tun kafin auren nan akesa min dokoki yanzu Kuma bayan Auren ina tsammanin na mallaki yancina sai Kuma Ku dinga kokarin nuna gszawata da kasawata kuna kokarin maidani wani sakarai, ta yaya Zan zauna mahaifiyarki ta dinga kokarin juya akalar rayuwata kema kinsan bazai yuwu ba.”

Ta yi masa kallon tsaf sannan tace ” yanzu don kawai mahaifiyata tana kokarin ciyar da rayuwata gaba shine kake ganin aibu kamfanonin nan kusan duk mallaki na ne ta yaya kake neman Ka hanani taimakon mahaifiyata bayan na kawo karfin da Zan iya taimakon ta tun rasuwar mahaifina ita ke tsaye Kan ganin ta tafiyar da komai yadda yakamata meye laifinta don kawai yanzu ta nemi taimakona , zaman me zanyi agidan ? Meye laifi don na fita nayi aiki.”

Yace ” babu laifi sai dai ràshin raayina Akan hakan, Bana son muna Jan maganar nan , bana son mu Sami matsala ,aiki dai bana so , ba Kuma Zan barki kiyi ba Donni banga abinda zaisa kiyi aiki ba.”

“Idan Kai Baka San dalilin dayasa zanyi aiki ba to ni nasan dalili Kuma dole zanyi aiki”
Cike da mamakin ràshin kunyar mujaheeda da yadda take gaya masa magana babu mutuntawa Ko girmamawa yasa ransa yayi matukar baci ya juyo afusace ya dubeta yace
” Dole sai kinyi aiki ” ta gyada Kai alamun eh ya jinjina Kai yace ” zanga Wanda zai sani na barki kiyi aikin.”

Tace ” ok zaka gsnshi kuwa”
Ya juya ya kwanta da alkawarin bazai Kara tankawa ba ,hakan yasa ta cigaba da maganganun ta Amma bai Kara tankawa ba hakan ya Kara harzuka mujaheeda Kwarai.
Washegarin ma haka suka tashi ,kamar yadda suka kwanta .haka zalika Taufiq Yana karyawa yabar gidan.

Bai dade da fita ba Haj murjanatu ta kirata awaya da son Jin abinda ake ciki.
Mujaheeda tadan numfasa tace ” Aini mummy gaba daya gani nake kamar an canja min yaya Taufiq tun daga jiya” , Haj murjanatu tace ” kamar yaya?”

Mujaheeda tadsn gyara zamanta asaman kujera tace ” tunda Muka dawo daga gida jiya ya dauki wata isa da iko ya dora ma Kansa, duk yadda naso ya tsaya ya fahimceni ya Kuma barni nayi aikin nan yaki, asalima ya Kara tabbatar min da cewa bazai taba barina nayi aiki ba babu Kuma Wanda ya isa ya sashi yabarni.”

A kufule Haj murjanatu tace ” haka yace ?” Ta daga Kai tamkar tana ganinta tace ” haka yace, Kuma ko da ya fita dazu babu alamar zai sassauto domin ko ta Kaina bsi bi ba ya fita”
Ran Haj murjanatu ya Kara baci tace ” Yana karya ne don bai Isa ba ki kwantar da hankalinki badai kina so ba to aiki ya Zama dole ko da hakan na nufin faruwar abubuwa da dama.”

Mujaheeda tayi saurin cewa ” aah mummy bana son wannan abin ya Zama wata matsala daban,akwai hanyar da nake son bi wacce matukar na bita bata bulle damu ba to dole ayi hakuri abar maganar kawai mummy” ” ki fasa aikin bayan ranki na so” cewar Haj murjanatu, mujaheeda tace ” eh Zan hakura tunda ina son Zama lafiya dashi , Amma sai nabi hanyar da nace din idan ban dace ba shikenan sai a hakura.”

Haj murjanatu tace ” wace hanya ce zaki bi” tace ” Kada ki damu mummy Zan sanar dake sai na aiwatar Amma” ta gyada Kai tace ” shikenan sai na jiki” daganan sukayi sallama.
Haj murjanatu ta saki tsaki matsalar talaka Kenan mutum baida ko Sisi Amna ya dinga fankama da takama ta banza da wofi shiyasa harka da talaka akwai damuwa.

*******
Karfe uku da minti ashirin da biyu motar mujaheeda ta tsaya aharabar gidan Alh Yusuf lamido.

Ta Bude kofar motar ta fito sanye cikin wata hadaddiyar doguwar Riga mai matukar kyau samnu ahankali ta tunkari cikin gidan idonta nakan rumfar aje mota ràshin ganin motar surikinta ya tabbatar Mata da cewa baya gida Wanda ba haka ta so ba , Kuma ko karfe nawa zai Kai bai dawo ba ya Zama dole ta tsaya ta Jira dawowarsa domin wajensa ta zo.

Haj saratu ta tarbi surikarta sosai kamar yadda ta Saba ta wadatata Kuma da duk abinda take bukata , sai dai dabiarta da Haj saratu bata so shine na son jikin mujaheeda da aikin Tabe Taben waya .domin dai kwance take Kan doguwar kujera hankali kwance tana aikin chatting.

Sai karfe hudu da rabi da minti shida Àlh Yusuf lamido ya shigo Kai tsaye bangarensa ya wuce.

Haj saratu ta bishi da duk abinda tasan Yana da bukata a dai dai wannan lokacin.

Saida ta tabbatar ya natsa ya ci abinci yasha furarsa wacce ta Zama daya daga cikin al” adar rayuwarsa kullum sai yasha ta sau uku.
Sannan ta dubeshi tace ” mujaheeda tazo tun dazu tana nemanka” yayi saurin kallonta yace ” lafiya suke ko ita da Taufiq din ba wata matsala.”

Tace ” to ni dai bansani ba amna ina ganin da akwai matsala atsakaninsu da Naga slams ko a fuskarta amma ba wata alamar hakan.”

Yace “To Allah yasa jeki Kira min ita” ta tashi ta fice cikin kankanin lokaci mujaheeda tayi sallama acikin falon.

Cike da kulawa da murmushi yace ” zoki zauna mujaheeda.’

Ta wuce Kan kujera tayi zamanta tana Dan murmushi sannan ta gsidashi ya amsa Yana tambayar ta meyasa tazo ita kadai don motarta ya gani awaje.

Tadan gyara zamanta tace ” ni kadai nazo Abba saboda yaya Taufiq fushi yake yi dani dalilin zuwana gareka kenan.”

“Wane irin fushi meya faru?” A hankali mujaheeda ta gaya masa komai ta Kara da cewa ” to ni Abba na rasa aibun wannan abin ba karkashin wani zanyi aiki ba balle yace zaa takura masa kamfanina ne babu wani abin damuwa Amma ya dage yace babu yadda zaayi nayi aiki ba Kuma Wanda ya isa yasa yabarni,

Shiyasa nazo gunka saboda Kaine ubana Kaine Kuma nasan zaka iya gaya masa ya yarda Ko ba ya so, kwarai ina son yin aikin nan KO don na rsgema mahaifiyata aiki.”

Alh Yusuf lamido ya gyara zamansa yayi murmushi yace ” ki kwantar da hankalinki in don wannan ne damuwarki ta kare na gaya Miki Zan tsaya Miki Akan komai matukar zaki samu farinciki ” tayi murmushi sosai tace ” Nagode Abba Allah ya Kara girma nagode sosai” ya ce ” Kada ki damu,yanzu ki tashi ki tafi gida ni Zan Kira Taufiq zamuyi magana da Shi” ta amsa da toh sannan ta Kara masa godiya daga bisani tayi masa sallama ta fito.

Bata zauna ba sallama kawai tayi da Haj saratu ta kama hanyar gida , zuciyarta na cike da farinciki tana Kuma karama Allah godiya daya hadata da suriki irin Alh Yusuf lamido Wanda yake yi Mata so dai dai da irin son da uba yake ma yarsa.

Tana fita Alh Yusuf ya daga ways ya Kira Taufiq ya bashi umarnin yazo ya sameshi yanzu agida, Taufiq ya tabbatar masa yana hanya.yanzu zai Iso gidan.

Cikin kankanin lokaci Taufiq ya iso gidan ,ko kadan Bai kawo dalilin mujaheeda yasa Abbansa ya Kira Shi ba.

Lokacin daya shiga falon tare da Haj saratu ya tadda mahaifinsa da alama magana suke tattaunawa wacce ba tayima Haj saratu dadi ba don yadda ta hade rai.

Asanyaye ya zauna akasan kafet Yana gaida mahaifansa. Haj saratu ta dubeshi tace ” Akwai abinci na kawo maka Ka ci ne don dai nasan ba daga gida kake ba, wata kila kana can kana yawo da yunwa.”

Ya girgiza Kai yace ” Kada ki damu umma, ba daga gida nake ba amma na ci abinci Bani da yunwa”. Ta koma ta gyara zamanta ta rasa dalilin da yasa takema Taufiq kallon tausayi.

“Abbah gani’ Taufiq ya fada Àlh Yusuf lamido ya muskuta Yana kallonsa yace ” Taufiq me ya faru tsakaninka da matarka.”

Yayi saurin kallonsa yace ” Kai mujaheeda tana da matsala,kiranka tayi Abbah.”

Cike da mamaki Haj saratu ta dubeshi tace ” Au ba da izininka Bama kenan ta zo gidan” ya juya Yana kallon mahaifiyarsa yace “zuwa gidan tayi ni ban Sani ba.”

Haj saratu ta saki salati tace ” lalle yarinyar nan da sauran gyara alamarinta , yanzu tasa kafa ta fita daga gidan mijinta ba tare da izinin mijinta ba.”

Alh Yusuf lamido ya jinjina Kai yace ” eh wannan bata kyauta ba Kuma zanyi Mata magana Zan ganar da ita tayi kuskure, Amma kafin nan.”

Ta waiwayo ya dubi Taufiq yace.” me yasa Baka son matarka tayi aikin kamfani.”

Taufiq ya saki ajiyar zuciya yace ” Abbah tun farko ni ba namiji bane me son matarsa tayi aiki, saboda akwai matsaloli kwance acikin aikin mace duk da ba duka bane aka Zama daya Amma azahiri INA ganin irin rayuwar da Mata suke yi awajen aiki, ràshin kamun Kai cudanya da Maza da sauransu duk namiji me so da kishin iyalinsa Bana tsammanin zai iya barin matarsa tayi aiki shi yasa Bana so tayi aiki, bugu da Kari Kuma babu abinda mujaheeda ta nema ta rasa da zaace dole sai tayi aiki.”

Ya aje numfashi ba tare da kowa ya katse Shi ba ya cigaba da cewa” kawai abinda na fahimta shine mahaifiyar mujaheeda tana son ta shiga cikin rayuwar aurena ya Zama itace me tsara min abinda zanyi Wanda Kuma ni bazan lamunci haka ba.”

Haj saratu ta ce” ina fa haka zai yuwu dole fa Haj murjanatu ta fita a sha” anin auren yaran nan ,Kuma gaskiya ne abinda Taufiq ya fada mujaheeda bata da wani dalili na yin aiki me take nema tana cikin gata kawai dai don fitinar tsiya da ràshin son Zaman lafiya aikin me don Allah.”

Alh Yusuf lamido ya numfasa ya Fara magana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 8Nima Matarsa Ce 10 >>

1 thought on “Nima Matarsa Ce 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×