Skip to content
Part 8 of 9 in the Series Nisfu Deeniy by Deejasmaah

His Visit

A cikin kwanakin kowa ya koma ga ayyukan da suke gaban shi, yayinda ‘yan Abuja suke haramar komawa don kowa ya baro ayyukan shi masu muhimmanci a can. A masu shirin tafiya har da Lele don ita ma ta kwan biyu bata lek’a office d’in ta ba, dan ma Ummu ta kan lek’a mata time-time to yanzu kam ita ma bata nan.

Duk tsayin sati biyun da suka yi bata had’u da Burhaan ba, wanda shine ya tsarawa kan shi. Sai dai a gefenta ba k’aramin rad’ad’i da kewan rashin shi take ji ba, a na gobe zasu koma ya shigo wurin Ummu. Time d’in sun k’uk’e ita da su Suleim suna tattaunawa duk rabin hirar kuma shirye-shiryen bikinsu ne, abun ka da iyayen zumud’i kamar gobe za a yi.

Sai da ta tabbatar da komai is intact kafin suka d’aga zuwa Abuja birnin tarayya, ita da Ummu dan Abbu da twins ma sun koma tuni. Shi ko ElSadeeq yayi wucewar shi Lagos akan aiki, dama shi bai fiya zaman Abujan ma rayuwar shi tafi Kaduna sai Lagos in ka gan shi Abuja toh workshops ne, symposiums ko seminars bayan nan ko sai gida wanda kafin ma yaje can taka nas ta Kano su sun zo.

Saturday da yamma suka bi evening flight bayan ta gama wa Hajjah shagwab’ar ta na sabo, su twins ne suka d’auko su daga airport zuwa gidan su dake cikin embassy. Ko da suka shiga direct d’aki ta nufa saboda gajiya don da gaske Lele langab’u ce ta bugawa a jarida, wanka tayi ta kwanta bayan ta kira Hajjah.

Few weeks later.

Zaman ta gidan su zama ne mai matuk’ar dad’i da sanyaya rai, ita ke had’a breakfast kafin su had’u duka su ci cike da soyayya kafin kowa ya wuce nashi wurin aikin. Ita d’aya suke bari don bata fita sai 11 am ko twelve ma.

Yau 10 ta fito ta nufi office saboda skincare products d’in da aka fara manufacturing na companynta, da aka kawo daga Pakistan. Sanye take da Bubu gown na wani material mai mugun taushi da tsada, bata cika son bubu ba amma in ta sanya sukan mata kyau da b’oye sirantar ta.

Office d’in ta na Abuja mai suna Yerwa’s touch babban waje ne sosai, haka kuma k’ayatacce duk inda ake zancen had’uwa toh wajen is more than that yafi na Kaduna girma da komai. But, one beautiful thing is price d’in su is flat, yanda yake a Kaduna haka yake a Abuja though akwai na VVIPs inda su wainnan su suka saka akayi creating wajen, ko da kud’in ka sai da rabonka kun san yadda hajiyoyin Abuja suke da son gwangwaje jiki hakan yasa cinikin nan har yafi na KD amma kuma tsarin d’aya ne ba bambanci sai wanda baa rasa ba.

Sanda ta isa har an gama sauke su a tsakiyar office d’inta, zama tayi inda maaikatan wurin suka fara bubbud’ewa duk da an tura mata samples a time d’in tana Kaduna ma but she’s impressed with what she saw.  Dukan su natural ne masu gyara jiki da sa taushin fata, murmushi tayi ta tabbatar mutane zasu yaba ainun da products d’in don ba ma su kenan ba akwai wasu masu zuwa daga Sudan sai na Maid wanda su suke packaging d’in shi a nan sai a kai na Kaduna. Da na Maid d’in ma suka fara har yanzu da suka fara importing burinta ma su fara had’a nasu da kansu ba wai bata iya bane Aa kawai isassun maaikatan da suka iya ne babu. Kuma a Nigerian akwai da yawa da suka iya had’a kayan but sun fi ba ma bleaching k’arfi, don haka ta barshi izuwa gaba kar tayi gaggawa.

Packaging suka fara yi da ya d’auke su har azuhur ba su gama ba, duk da suna da yawa wainda ya samu kawai suka iya yi. Ware na Kaduna a kayi gefe guda sai na wadanda suka yi order suma aka aje su gefe for delivery,  aka jera wasu a wajen su sauran aka kai store, sai da ta tabbatar da komai is in place kafin ta zauna. Wayarta ta d’auko ta na booking studion da zasu yi mata commercials, amg.ingenious da shi ke mata stickers da bags tayi ma magana inda ya tura mata price list d’in shi mafi tsada da quality ta zab’a a take tayi full payment duk da ana iya yin part payment but tafi gane yin full a komai. Tsaida ranar da za a yi aikin sukayi izuwa next weekend lokacin kayan Sudan sun iso, sannan sun gama aikin stickers d’in da zaa sa wa containers don nata sun yi k’asa ba zasu isa kayan da za a kawo ba ajiyar zuciya tayi tana gyara zamanta aiki ta fara ba kama hannun yaro. Lissafin kud’in da aka kashe a kayan tayi, ta kuma lissafa wainda aka ajiye a nan da wanda akai order and the rest.

(Being a CEO is not easy ooo only real business owners suka san me yake faruwa a business world ko da lissafi aka bar mutum kawai ya ishe shi balle sauran pressures Allah ya sawa neman mu albarka, lest I forget you can contact amg.ingenious for your graphics, photography, videography na suna biki birthday shoots and even commercials ga masu business, suna yin katin aure stickers bags fliers har ma da souvenirs and everything as far as content creation is concerned. check them on IG, Facebook and tiktok on Amg.Ingenious, Amgstudios and I assure you will be impressed).

A mugun gajiye ta tashi yau hakan yasa ta tsaya akai mata massage mai shiga jiki, kafin ta samu jikin ya sake ba laifi. Gida ta nufa tana sawa cewa gobe ba zata je koina ba, ta na shiga da motar cikin gida ta ga bak’uwar mota a parke bata bi ta kan motar ba ta parka tata a inda ta saba ajiyewa. Jakarta ta d’auka tana dosar cikin gidan, bud’e k’ofar tayi da sallama tana shiga ciki karaf idanunta ya fad’a na shi.

Wani mugun kallo ya jefa mata da ya sanya ta d’auke nata idanun, gaishe shi tayi ya amsa yana yanda ya saba. Simi-simi ta wuce kitchen in da take jiyo motsi, Ummu ce a tsaye tana had’a kayan motsa baki a tray. Rungumeta tayi tana cewa ” Ummulkhair!!”, amsa ta bata da “Bintulkhair welcome home”. Sake shagwab’ewa tayi tana k’orafin gajiya cewa tayi ” Bintie and laziness, sake ni kije ki kaima Yayanku and move straight to your room and freshen up kin san zai zo instead ki dawo ki kintsa ko ni ma baki gaya min ba if not da ya gayawa Abbu I need to shove sense into your head silly girl”.

Tura baki tayi jin fad’an da Ummun take mata, ba ma ta san cewa ita d’in bata san da zuwan na shi ba. Sai dai bata tanka ba abunda ta sata ta wuce dayi kawai, trayn ta d’auka ta nufi parlor ajiyewa tayi ta a gabanshi bata ce masa uffan ba ta nufi d’akin ta kawai wankan tayi kafin ta zuro wani free skirt black da top pink. Vintage scarf pink ta d’aure kanta da shi, duk da bata yi kwalliya ba banda chapped da ta sanya amma tayi kyau ainun wani soft slipper ta sako zuwa parlor. Da sallama ta sauko k’asan, shi da Ummu ne suke magana cike da fahimta da shak’uwa.

Barka ta musu tana jin kamar ta koma inda ta fito, sai dai ba dama. Dining ta wuce cikin rasa abun yi, zama tayi kawai tana danna waya. Message ne ya shigo wayarta tayi saurin dubawa “ki dawo parlor ku gaisa” d’an tura baki tayi ta na mai jin kamar ta sa hannu aka tayi kuka, bata da buri sai na kasancewa da shi yet, had’uwar su bata da faida kallon shi na d’azu ya tabbatar mata da hakan sai dai bata iya musu ba ga kowa ma balle ga Ummu.

Taso wa tayi ta dawo parlorn ba Ummu sai shi d’aya, zama tayi a seat d’in da yafi kusa da tashi. Rasa abunyi tayi sai ta samu kanta da tambayar shi hanya, bai amsa ba bai ma kalleta ba sai wayar shi da yake latsawa cikeda isa. Sai da ta cire rai da zai yi magana kafin taji muryan shi ciki-ciki yana cewa ” don’t tell me you are thinking that I’m here for you?“. D’agowa tayi da hanzari jin kalaman shi, ita me ruwanta da zuwan shi tana son ganin shi infact da kewar shi take kwana ta tashi ta kuma yi farincikin ganinshi. Amma ko da wasa bata sa ran zai zo gidan su dominta ba, not so soon.

Murmushi tayi confidently tace ” why would i think so?”, tab’e baki yayi yana cewa ” I know how shallow minded you can be gwara da kika rufawa kan ki asiri because that’ll be the last thing I’ll do”. Fad’ad’a murmushin ta tayi bata ce masa uffan ba sai dai deep inside she’s burning, sai dai baza ta tab’a nunawa ba ji tayi ya sake yanko mata wata maganar “I know kina nan kina godiyawa Allah ko? burin ki ya kusa cika ko?”.

Da mamaki ta kalle shi cos ta san shi ba gwanin magana bane but ji yanda yake zubo su kamar wanda aka rubutawa, tana son frustrated tone d’in shi don ta lura ya kan sa shi magana. In da Burhaan zai gane toh da yin shiru gabanta sai ya fiye mai don ita ba abunda take so kamar taji muryan da yake rowarta, tace “Alhamdulillah, ai mu kullum cikin godewa Allah muke hakan ne ma ya sanya yake k’ara mana “.

Tsuke fuskar shi ya yi yana maida kan shi ga waya, ita ma nata ta d’auka tana latsawa cikeda yanga. “Ki rufawa kanki asiri kar ki sake ki yarda ayi auren nan, don zakiyi nadama tabbas”, ya furta a hankali yanda ba mai ji sai ita ” idan gidanka wuta ne then I’m ready to walk into hell to be with you”. Ta bashi amsa cikeda tabbatarwa, kallonta yayi tsaf yana jin zafin kalmarta ga kunne da zuciyar shi wai ita wata kalar macece mara zuciya?.

Don’t say I didn’t warn you, and mark you this should be the last time da zaki k’ara cewa kina so na don I won’t take it likely with you”, he said it with bitterness shi ba gwanin nuna weakness d’in shi bane bai son magana haka bai son damuwa but Nadeefah tana sa shi magana mai tsawo. Amsar ta ta bashi mamaki ” Ko ban sonka zan zauna da kai in maka biyayya, ko ba komai umurnin iyayena na martaba da na ubangiji balle ma ba zan iya maka alk’awari ba Ya Islaam don abune mai wuya a gareni”. Had’e hak’waran shi yayi gritting hard yace ” your problem, not mine “. Ya furta yana mik’ewa, kitchen ya lek’a yana shaidawa Ummu zai fita a dawo lafiya tayi masa, ta kitchen d’in ya fita don bai son ganinta.

Fitar shi ya sanya Ummu fitowa zuwa parlorn, zama tayi gefenta tana cewa ” Bintie ki natsu wallahi in ba haka ba zan sab’a miki akan Burhaan, yaro mai hankali ya sauke abunda yake yi yazo wajenki amma kina son ki wasa da damarki ko?, toh tun wuri ki gyara don ba zan d’auki wannan shirmen ba”. Rolling idanunta tayi jin fad’an da ake mata akan Islaam, she’s sure Ummu bata san halin shi bane amma ba zata tab’a bari ta sanin ba.

Kafin tayi maganar tace “and mark you, har ya tafi ke zaki dinga gyara mai d’aki and kula da abunda zai ci if you like keep misbehaving zan gyara miki zaman ki”. A hankali tace ” I’m so sorry Ummulkhair, zan gyara in shaa Allah ” better tace tana komawa inda ta fito. Tagumi tayi tana cewa ” Ya rabb you are seeing”.

Tunda ya fita bai shigo ba sai around 9 pm, ba koina yaje ba yawo yai tayi a cikin abj kawai. Duk abunda zai had’a shi da ita ba so yake yi ba, bai san tana garin ba da babu abunda zai kawo shi gidan ba da hotel zai kama. Amma yanzu lokaci ya k’ure, yayi tsaki yafi cikin carbi haka nan ya dawo don ya gaji ga shi gobe yana da sammako.

Sanda ya shigo a zaune part d’in Abbu ya nufa don ya san a can sukeyin dinner, ana d’in ya a parlor kallo sukeyi ana yi ana hira. Da sallama ya shiga suka amsa masa dukan su, gefen Abbu ya zauna daga k’asa “Our physio”. Ya furta cike da soyayya murmushi yayi masa yana cewa ” mun same ku lafiya?, ya aikin?”.

Alhamdulillah Son ya fad’a ya na dafa kafad’ar shi, kallon Ummu yayi yana mata barka da gida cewa tayi ” ka dad’e baka dawo ba daga barin je in dawo”.

D’an murmushi yayi yace ” na zaga garin ne ” gyad’a kai tayi tana cewa ” toh ga abincinka can yana jiranka Bintie, serve him”. Toh suka furta kusan a tare, su twins ne suka gaishe shi ya amsa cikin sakewar fuska harda tambayarsu aiki. Ganin basu da niyyar tashi ne ya sa Ummu sake jaddada musu, Lele ce ta fara tashi tana gyara hijab d’in jikinta. Dining d’in suka nufa sai da ya zauna ta d’auko trayn da aka shirya mai abinci specially bubbud’ewa tayi tana mai tambayar what to serve.

Yatsina yayi yana had’a tea da kanshi, sai da ya ajiye a gabanshi kafin cikin sauke murya yace “ I don’t need you around me, I’ll serve myself”. Ji tayi kamar ta ajiye amma sanin abunda zai biyo baya if she tries that yasa bata biye ba, plate ta d’auko ta fara serving d’in shi Macaroni soup with shredded beef anyi garnishing da ugwu kad’an.

Kab’e hannunta yayi kafin yayi serving kan shi da kan shi, tab’e baki tayi ta zauna a kujerar k’arshe kawai. Yana ci yana tsaki ita dai ko a jikinta don she’s admiring yanda yake cin abinci cikeda aji da kuma yanga, yana yi yana clenching jaw d’in shi kamar anyi masa dole.

Sai da ya gama kafin ya ture komai gefe, yana barin dining d’in. Had’a komai tayi tsaf kafin ta biyo bayanshi da tray d’in, ko zama ba tayi ba ta nufi part d’in su bayan tayi musu sai da safe.

Zuwan shi Abuja tamkar wani kaya ne aka aza mata a kai, banda kula da abinci da makwanci. Ga masifar wulak’ancin shi musamman ma idan su kad’ai ne, haka zai zage yayi ta gaya mata maganganu masu zafi da ciwo ko a jikinshi. Gashi bai dawowa gida da wuri, da ma wani NPS workshop yazo na 2 weeks.

Shirin dawowa Kaduna ta fara sakamakon k’aratowar bikin Nana Saraki, duka-duka 4 weeks ya rage gashi ita zatai mata gyaran jiki da turare ga kuma sauran hada-hada. Sanda ta shaidawa Ummu sai cewa tayi wai ta jira Burhaan su tafi tare, idanu ta gwalalo tana kallon Ummun.

Cewa tayi ” Meye kika tsare ni da ido ne wai?”, girgiza kai tayi kawai she don’t know why take d’aukar maganar shi har tsakar ka. Ummu bata da fad’a but akan Burhaan duk tabi ta tsangwameta, a d’an shagwab’e tana mai tura baki tace ” but Ummulkhair..!”

Kasa k’arasawa tayi tana mai kallon k’asa, d’an k’wafa tayi kafin tace ” but what?, ina lura da take-takenki a kan maganar nan toh wallahi ki sani wannan abune da ba zai tab’a yiwuwa ba dole ki sama kan ki salama and mind you, kar ki sake Abbunku ya lura da halinda kike san sa kanki a kan wannan maganar cos he wont take it lightly with you …” Hawaye ne ya zubo mata daga ido, itama fa tana son kayanta but halin shi ne take gujewa wanda ta san Ummu bata san dasu ba.

Amma bata da hanyar da zata iya mata bayani har ta fuskance ta, share idanu tayi tana cewa ” ok Ummu” tare da juyawa da nufin barin d’akin gwuiwa a sanyaye. Yanayinda ya karyar da zuciyar Ummu God knows she’s only doing her part as a mother and a wife, a matsayinta na uwa dole ne ta horar da d’iyarta akan bin mahaifanta. And as a wife dole tayi ma mijinta biyayya, and that’s what she’s doing sai dai ba zata iya zuba idanu ta bar ta da damuwa ba don haka ta janyo ta ta rungume.

Jinta jikin Ummun ne ya sanyata jin kukan ya taho mata gabad’aya ba wai na damuwa da komai ba, sai na rashin madafa da take dashi for now. Ko d’aya bata k’aunar keb’ewarta dashi saboda yanda yake jifanta da muggan kalamai don ma bata tab’a nuna mai suna damunta ba gudun kar ya san lagonta, but Allah ya sani tana azabtuwa ba k’arami ba.

“Shhhhhh, my baby don’t cry ok?, na san isn’t easy koyawa kanka son wanda baka shirya ba amma ki daure shi so gina shi akeyi ba haka nan take yad’o ba the most rarest and cutest is love at first sight, ki ma gode Allah akwai son ‘yanuwantaka a tsakaninku ku bawa junanku dama let love grow in your hearts first I’m sure you can’t let go of yourselves that’s why nake son ku dinga samun lone time ku biyu ko don ku fara gina shak’uwa a tsakaninku understand me kin ji baby”.

Lumshe idanu ta sake yi tana mai jin wani sanyi a ranta, nothing in this world can matches motherly love. Ji dai yanda ta kwantar mata da hankali da just few words d’in ta, shafa kanta tayi tana cewa ” is okay in bakya son bin shi, ki bi flight then”. Girgiza kai tayi tana cewa “issokay Ummulkhair your wish is my command”.

Murmushin jin dad’i tayi tana cewa ” Allah ya miki albarka Qurratu ayniy”, sake rungumeta tayi tana mai jin wani sukuni a zuciyarta. Sun dad’e a hakan kafin ta zareta daga jikinta, zama sukayi tana sake tausarta da bata some tips na zaman rayuwa.

A take ta gyare tana mai jin hope d’in ta yana dawowa, kai ba zata sare ba duk wuya duk runtsi sai ta kai gaci. ( Allah ya taimaka to)

Bata sake tada maganar ba sai hak’uri ta bawa Nanar akan ta fara zuwa wurin staffs d’in ta in ta dawo sai ta k’arasa mata, da k’yar ta hak’ura bayan dogon mitan da ta gama mata. Ummu da kanta ta shaidawa Abbu tafiyar tasu, sosai yayi murna kamar an bashi kyautar hajji ko ita Ummun mamakin yanda suke son had’in Burhaan da Lele take yi. Murmushi tayi jin yana kiran shi akan idan ya dawo ya shigo, To ya furta kawai.

Suna zaune a wurin sai gashi ya shigo falon a natse da sallamar shi, kallonshi tayi tana mai yabawa da haiba da kwarjinin shi. Tabbas Lele ta mori miji don duk inda namiji yake Islaam ya kai har da k’ari. A gabansu ya zauna yana gaishe su, amsawa sukayi dukan su da kulawa har da tambayarshi aiki. Alhamdulillah yace yana mai sauke kan shi k’asa.

Abbu ne yayi gyaran murya yana cewa “Yaushe za ku kammala ne Babana?”, a hankali yace ” saturday in shaa Allah zan koma Sunday in Allah ya kaimu”. Murmushi yayi yace ” Masha Allah, Allah ya taimaka,,,,,ammm k’anwarka zata bika in zaka koma hope babu takura dai?”.

Ji yayi kamar an doka masa guduma a tsakar ka, a rasa da wanda zaa had’a shi a hanya from Abj to KD sai Nadeefah. Wai sai sun ga ya fad’i ne kafin zasu bar shi ya sarara ne? Lumshe idanu yayi yana mai adduar samun natsuwa a zuciyar shi. Bud’e idanun yayi yana kallon su, take kunya ta kama shi ganin shi suka tsurawa ido.

Murmushi ya k’ak’alo da k’yar yana cewa ” wani irin takura Abbu? Allah ya kaimu ranar lafiya” Ameen ya rabbi suka furta harda sa mai albarka. Mik’ewa yayi da niyar wucewa Ummu tace masa ” barin sa ta kawo maka abincinka” Tohn da bai masa wahalar furtawa ita ya furta yana nufar k’ofa.

Jefa kanshi yayi a kan sofa sanda ya shiga d’akin, ji yayi dama yayi flight yabi da zai zo da babu wanda zai mak’ala masa ita. Tsaki yayi yana mai jin Abujan ta ishe shi gabad’aya, maida idon shi yayi ya rufe. A wannan halin ya fara jiyo k’amshin fitinannen turarenta da a zaman shi a gidan ya haddace shi tsaf, kafin ya jiyo muryarta tana masa sallama.

A zuciyar shi ya amsa sallamar amma a fili ko motsawa bai yi ba balle ta sa rai zai bud’e idon shi, ajiye abincin tayi a tunanin ta ko bacci yake yi. Sai da ta kai k’ofa ne ta jiyo muryar shi da ya sanya mata waigawa da d’an mamaki. “Ba za ki bi Ni ba ne…?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nisfu Deeniy 7Nisfu Deeniy 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×