Skip to content
Part 13 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

“Kin gansu nan?”

Ta buɗe jakarta ta ciro wasu robobin magunguna guda uku, ta ɗauko wasu kwalaben turare ƴan ƙanana guda biyu ta miƙa ma Fareeda.

Ita kuma ta karɓa jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da mamakin yadda tun bayan fasuwar zancen ƙarin auren da mijinta zaiyi ake ta nufo ta da irin waɗannan abubuwa.

Ƙuri tayi tana ƙare ma ƴan ƙananan robobi da kwalaben turaren kallo. Roba ɗaya a cikin garin maganin sak ararraɓi, amma dai bata ce ba, sai ta mayar da hankalinta kan Ramlah don jin ƙarin bayani.

“Duka biyar ɗin ki bada dubu arba’in. Wallahi Dubu hamsin ne ma amma saboda hidindimun da suke gabanki ki bayar da arba’in, sai in cika miki dubu goma. Kin wuce komai a gurina Fareeda, bazan manta lokacin da muke secondry irin kyaututtukan da kike yi mana mu ƙawayenki ba, don na cika miki kuɗin magani banyi miki komai ba.”

Da saurin gaske Fareeda ta miƙa ma Ramlah magungunan tana cewa

“Kin ganni Ramlah? Wallahi tallahi ba ni da kuɗi. Ni a yanzu da kike ganina ko dubu biyar ba na magani. Na gode da ƙaunar da kika nuna min, ki mayar ma da Hajiyar maganinta kema ki riƙe dubu goman ki. Allah yabar zumunci.”

Baki buɗe Ramlah take kallonta. Ta ɗan muskuta, zuciyarta cike da addu’ar Allah yasa kar Fareeda taƙi siyan maganin.

Daga fara harkar karɓo ma Fatima magani ba ƙananun kuɗaɗe take samu a ɓangarenta ba. Tunanin cin riba biyu a duka ɓangarorin biyu tunda duk ƙawayenta ne yasa ta kawo ma Fareeda, idan Allah yasa ta siya dubu sha biyar ne ribarta a ciki.

“Amma Fareeda kin fahimci maganganun da na gama karanta miki a matsayin sharar fage kuwa?

Wallahi kin ji na rantse da girman Allah babban burin Fatima idan aka yi aurennan ki wulaƙanta a gidannan. Daga ƙarshe baƙin ciki da takaicin yadda za ki ga tana juya mijinki ya zama ajalinki.

Magunguna take amfani da su kala-kala, wanda suka dace da waɗanda basu dace ba, ba ta jin ƙyashin kashe ko dubu nawa aka faɗa mata kuɗin magani matuƙar aka tabbatar mata da ingancinsa…”

“Uhmmm! Taje tai tayi wallahi, Ramlah ƙyaleta taje tai tayi. Ni Allah ya sani tun farkon tarayyarmu ba Fatima kaɗai ba, da zuciya ɗaya nake zaune da kowa. Ko da suka ƙullah za suyi aure ni ba na mata fatan ta wulaƙanta, Aniyar kowa ta bi shi tsakaninmu.”

Duk yadda Ramlah taso juyar da tunaninta don ta sayi maganinnan ko bashi ne bayan biki ta biya ƙin karɓa tayi. A ƙarshe dai haka suka rabu dutse a hannun riga, zuciyar Ramlah cike da takaicin buƙulun da Fareeda tayi mata, ta fice a gidan tana jan tsaki.

Bayan fitarta Fareeda ta daɗe zaune a gurin, hannayenta biyu tallabe da kunci, damuwar zuciyarta na ƙara ninikuwa.

Daga fara maganar aurennan zuwa yanzu matan da suka zo takanas ta kano har cikin gidanta da kuma waɗanda suka kira ta a waya da maganganu na ɗaga hankali baza ta iya ƙayyade yawansu ba.

Kaso biyu da rabi cikin uku na masu yi mata jaje da bata shawarwari ce mata suke yi

“Fareeda sai kin tashi tsaye, wallahi idan baki tashi tsaye ba kina ji kina gani gidan mijinki zai gagareki.”

To don Allah ita ya suke so tayi da rayuwarta? A matsayinta na marainiya babu uwa ba uba ta tashi tsaye taje ina? Ita ba kuɗi take da shi ba, kuma ko tana da kuɗin tana roƙon kar Allah ya nuna mata ranar da za taje gurin wani ko wata don neman taimako akan Mijinta.

Tana neman taimako ne a gurin Allah kaɗai, kuma tana da tabbacin shi zai kareta daga duk wani sharri ko bita da ƙulli da zai sameta, ba ma akan al’amarin auren Mukhtar ba, aduk wasu lamura na rayuwarta a duniya.

Idan ta ce maganar da Ramlah ta faɗa mata kan Fatima bai tsaya a zuciyarta ba tayi ƙarya. Amma babu komai, ita dai tana ta cigaba da addu’a har a gama rugu-rugun bikinnan kar Allah yasa imaninta ya raunana kan ɗa namiji.

Ɗa namijin da bashi da tabbas, tun zamanin kakanninmu da iyayenmu har yau maza sun kasa mallakuwa. Ko a tarihi da labarun hikaya bata taɓa jin wata shahararriyar mace da ta samu nasarar mallake ɗa namiji ya mallaku mata har abada ba.

To me zai kaita ta kashe ƴan kuɗaɗenta sannan ta ɓata lokacinta a banza? Ba dai Mukhtar bane? Tana ta ƙara dagewa da Addu’a Allah ya cire mata damuwa da al’amarinsa a ranta.

Za tayi masa biyayya, za ta bi umarninsa kamar yadda addini ya umarta. Amma idan ya aje ta gefe Wallahi ita ma za ta aje shi ne, idan ya zaɓi Fatima ya ce ita Fareeda zai wulaƙanta za ta rabu da shi, rabuwa ta har abada.

Ta rasa uwa da uba a duniya tayi haƙuri ballantana wani ɗa namiji? Miji goma ba uba goma bane, za ta cigaba da zama ne kawai idan ya riƙe ta da darajarta. Allah bai wulaƙantata ba babu wani mahaluki da ya isa ya wulaƙanta ta.

Fatima kuwa in dai Mukhtar ne ga ta ga shi nan, Allah ya basu sa’a.

*****

“Mukhtar wai don Allah da gaske kake wannan maganar?”

Abokinsa Ibrahim ya tambayeshi, da fuskarsa mai ɗauke da matsananciyar mamaki.

“Au! wai kai baka yarda ba? Wallahi da gaske nake yi.”

Ya rantse don ƙara tabbatar masa da gaskiyar maganar ƙarin aurensa, ya cigaba da cewa

“Yanzu haka ma na kai komai da ake buƙata, saura kwana takwas ɗaurin aure. Kaga tunda bazawara ce babu wani amfanin ɓata lokaci…”

“Amma gaskiya ka bani mamaki, anya kuwa wannan busasshiyar haka ta barka? Kai da kake da mace kamar Fareeda wani kuskure ko rashin rabo ne zai kai ka ga auro Fatima? Matar da a fuska kawai za ka gane duk bula ce, idan bata girma maka ba ba na jin kai za ka girme mata.

Ni a ture ma zancen Fatima Aminiyar Fareeda ce, tunda aurenku ba haramun bane duk mai hankali bazai tsaya ja’inja ba.

Amma don Allah me ya shiga cikin hankalinka? Kai da na sanka mutum mai bala’in tsantsenin bazawara? A cikin ƙungiyar abokanmu kowa ya sanka kan wannan aƙidar ta cewa baza ka iya mu’amala da wacce wani namijin ya rigaka mu’amala da ita ba, ko da kuwa sakin wawa ce.

Sai ga shi ba ma sakin wawa za ka kwaso ba wacce ta haife ƴaƴaye rututu, ina wani abin sha’awa ko burgewa a tattare da ita don Allah?

Ko ka manta falsafarka da kake cewa duk wanda zai ƙara aure ya tabbatar wacce zai auro ta fi matarsa ta gida da abu uku.

Tafi ta kyau

Tafi ta asali

Tafi ta ƙuruciya.

A cikin abu ukunnan wannene Fatima ta fi Fareeda?

Ka manta…”

“Ka ga don Allah saurara Ibrahim, tunano tsofaffin maganganun da nake yi a baya tun kafin in waye da rayuwar duniya ya isa haka.”

Ya katse abokin fuskarsa na bayyana matsanancin ɓacin rai. Cikin zafin zuciya ya cigaba da cewa

“A ɓangaren zaɓin abokiyar rayuwa ni nake da ƴancin yin haka ba wani ba. Kuma duk waɗannan maganganun da kake yi a baya ne na furta su, a yanzu ina kan wani mataki ne na nemawa kaina mafita da hanyar ɓullewa cikin salama ba tare da baƙin ciki ya kashe ni tun lokacina baiyi ba.

Fatima dai ita ce zaɓina, ita nayi ra’ayin aure a matsayin mata ta biyu.  Idan kuma akwai wanda yake da iko da rayuwata sai ya canza min ko kuma a hana ni ƙara aure gaba ɗaya.”

Daga haka bai sake cewa komai ba ya shige ɗaya daga cikin ɗakuna uku da ke cikin ginin yana sake duba irin gyaran da ma’aikan sukai masa.

Lokaci bayan lokaci shi kaɗai yake jan tsaki. Ya rasa dalilin da yasa duk wanda ya ji labarin zai ƙara aure da kuma wacce zai aura sai ayi ta kushe lamarin, bakin mutane bai taɓa furta alkhairi kan lamarin.

Da yawan mutane nuna masa suke lallai ya tafka kuskure a gurin zaɓinsa. To ina ruwan jama’a da ra’ayinsa?

A wannan lamari shi ne mai ruwa da tsaki, kuma ga wacce yake ga tayi daidai da irin ra’ayinsa. Me yasa mutane baza suyi koyi da Hadithin nan da yake cewa a faɗi alkhairi ko ayi shiru ba?

Bai san Ibrahim ya fice daga gidan ba sai da ya fito daga cikin ɗakin. Ko da ya leƙa ƙofar gida bai tarar da motarsa a gurin ba.

Ko a jikinsa ya sake jan tsaki tare da komawa cikin gida bayan ya janyo ƙofar apartment ɗin da aka gama gyara ya kulle. Gyaran yayi kyau sosai da sosai, angama komai.

Sai dai duk tattalin arzikinsa ya kusa shigewa a wannan gyaran, maƙudan kuɗaɗe ya saki sosai aka gyara gurin don kawai ya faranta zuciyar Fatima.

Tunda ta bashi tabbacin kayan gado da kujeru masu bala’in tsada za ta siya ta zuba a ɓangarenta, shi yasa yayi gyaran da baza ta taɓa ji a ranta tayi asarar kashe kuɗinta ba.

Da sallama a bakinsa ya shiga ɗakin Fareeda.

A hankali ta ɗaga kanta daga kan wayar da take dannawa ta kalle shi tana amsa sallamarsa.

Cikin ɗakin ya shigo, ya nemi guri kan katifarta ya zauna, idanunshi a kanta. Cikin kwanaki goma sha huɗu da ɓullar maganar auren ta yi wani sanyi gaba ɗaya kamar ba ita ba, sam ba ta da karsashi.

Har wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar rama tayi a fuska, hancinta ya ƙara tsawo. Amma fa ko ya ƙi Allah ya san tana cikin nutsuwarta.

Babu abinda ta fasa masa na dangane da hidimar gidan, sai dai gaba ɗaya ta janye jikinta daga gare shi. Kuma babu wani ɓacin rai a fuskarta balle ya ce haukar kishi ke damunta.

Jingine shi tayi a gefe ɗaya, magana idan ba dole ba bata cika son yana shiga tsakaninsu ba, ko ɗakinsa ta daina zuwa, shi kuma ko sau ɗaya bai taɓa yi mata ƙorafi kan haka ba.

Ya zuba mata idanu ne yaga iya gudun ruwanta. Aure ne dai, bazai fasa ba.

“Biki saura kwana takwas”

Ya karya shirun da ke tsakaninsu da faɗin haka.

“Allah yasa muna da rabon gani.”

Tayi maganar cikin rashin damuwa.

Wayar hannunta ta ajiye a gefenta, ta kalle shi cikin idanu, sai da taja addu’ar ya hayyu ya ƙayyumu kafin tayi ƙarfin halin cewa

“Ina neman alfarmar don Allah ka barni in koma wancan apartment ɗin da aka gama gyarawa…”

“Amma dai wasa kike ko?”

Ya katse ta da tambayar, yana aika mata da wani irin kallo mai kama da na lallai ba ki da hankali.

“Wasa dai? Uhmmm! Me zaisa inyi maka wasa a daidai wannan gaɓar? Da gaske nake yi. Idan ka bani dama zan koma wancan apartment ɗin in bar ma amarya wannan, ya ishe ta, tunda ba ta da ƴaƴa.

Idan baka manta ba wancan part ɗin ɗakuna uku ne, nan ɗin kuma biyu ne. Kuma wancan shi ne a farkon gida, nan kuma a baya.

A matsayina ta uwargidanka kuma uwar ƴaƴanka can ɗin ne ya dace da ni ba Amarya ba…”

“Fareeda. In dai ba tashin hankali kike nema da ni a tsakar ranar nan ba ki bar wannan maganar. Nan ɗin dai shi ne naki, can na gyara da sunan Fatee ne, ita za ta shiga ciki. Idan kina so zan iya sakawa ayi miki fentin nan ɗin, shi ma ya koma kamar sabo.

Amma can na Amarya ne, ita kanta ta sani, har na faɗa mata yanayin ginin domin siyo labulayen da zai isa. Ki bar ma wannan maganar.”

Bai sake bata damar cewa komai ba ya fice daga ɗakin.

Ta bi bayanshi da kallo, zuciyarta na wani irin tafarfasa, a hankali ta lumshe idanunta tana maimaita.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Lahaula walaa ƙuwwata illah billah.”

Su tayi ta maimaitawa tana ji ɓacin ranta na raguwa da kaɗan kaɗan, sai ta zame ta jingina da jikin gado, ba’a ɗauki lokaci sosai ba nannauyan barci ya kwasheta.

*****

“Hmmm! Fatima kenan, sai muka na samu labari a bakin Ummee wai za kiyi aure.”

Wani mugun kallo ta juya ta aika ma Ummee, wacce duk cikin yaran nata ita ce mai bala’in surutu kamar aku.

Daƙyar ta iya ƙaƙalo dariyar yaƙe ta mannawa fuskarta, ta kalli Yar mijin nata a ɗarare, da alamun rashin gaskiya ta fara kalaman kare kanta.

“Kiyi haƙuri Yaya, wallahi daman ina shirin zuwa in faɗa miki da kaina… kawai dai…”

“A’a! riƙe kawai dai ɗinki. Ina fatan baki manta wasiyyar marigayi ba?”

Ƙiƙƙifta idanu ta fara yi, da alamun ta manta wane wasiyya ne tsohon mijinta uban ƴaƴanta ya bar mata? A yanzu Mukhtar da soyayyarsa ce kawai a zahirinta da baɗini, ta daɗe da manta duk wasu abubuwa da suka shuɗe. Gaba da abinda za ta haifar kawai take hange.

“Uhmm! ƳarAdam butulu. To bari in tuna miki, a gabanki da mu ƴan’uwan mijinki kafin rasuwarsa ya ce idan za kiyi aure in karɓi ƴaƴansa.”

Wani ƙatoton ajiyar zuciya ta sauke a fili, wani murmushin farin ciki ya bayyana a fuskarta. Dama ina za ta iya kayan ƴaƴa ita da take burin yin ƙara’i na sosai a fannin soyayya.

Ta buɗe baki za ta tambayi a haɗo kayan ƴaƴan ne Yar mijin ta faɗi maganar da yasa ta ɗauke wuta na wucin gadi.

“To kinga tunda aure za kiyi, baza mu taɓa barinki da dukiyar marayun ƴaƴanmu a hannunki ba. Duk abinda kika san na Yaya ne ya siya a gidannan ki tattaro su guri ɗaya, daman already Mujittaba ya gama haɗo duk wasu takardun kadarorin da Yaya ya mallaka.

Za’a raba gado in Allah ya yarda gobe da yamma, za’a fitar miki da tumunin takaba a baki abinki. Su kuma yara za’a cigaba da juya musu dukiyarsu har zuwa sadda za su mallaki hankalin kansu. Na barki lafiya.”

Ko bayan ficewarta Fatima ta daɗe zaune a gurin kamar mutum mutumi, ita yanzu idan aka raba gado aka ƙwace kason ƴaƴanta a hannunta ya za tayi da batun kayan ɗaki na garari?

*****

Daf da kiran sallar magrib Mukhtar da Fareeda suka karɓi baƙuncin Hajiyarmu. Da ƴan rakiyarta Shaheed da Sayyid (Ƴan biyun Fareeda), da ƙanwar Mukhtar Zubaida wacce har lokacin bata koma gidan mijinta a lagos ba.

“Ko bakuyi murnar ganinmu bane mu koma?”

Hajiyarmu ta faɗa ganin yadda suka ƙame guri ɗaya fuskokinsu cike da mamakin wannan ziyara ta bazata.

A tare suka ƙarasa da sassarfa suna yi mata sannu da zuwa.

Zubaida da yake akwai shaƙuwa sosai a tsakaninta da Fareeda hannu ta bata suka kashe suna musayar murmushi.

Ƴan biyu da gudu suka ruƙunƙume mahaifiyarsu, kowa na ƙoƙarin bata labari da hausarsu da bai gama fita ba.

Daƙyar Mukhtar ya janye su ita kuma ta fara jelar kawo ma Hajiya ruwa da abinci, cikin mintuna ƙalilan ta haɗa ma Hajiya kayan tarbar baƙi a mutunce.

“Mummyn Twince, akwai wata matsala ce?”

Hajiyarmu ta tambayi Fareeda cikin kulawa, tana kallon yadda ta rame a fuska ba kamar zuwanta gurinta satin da ya wuce ba.

“Wallahi ba komai, me kika gani Hajiya?”

Mukhtar yayi saurin amsawa kamar shi ne Fareeda.

Wani mugun kallo ta watsa mishi, ba shiri ya sunkuyar da kai yana ba ta haƙuri.

“Daman zuwan takanas don kai nayi ta. An gama gyaran wancan ɓangaren ko? To tunda dai ɗakunanshi uku ne nan kuma biyu gobe in Allah ya kaimu Fareeda ki kira ƴan’uwanki su taya ki tattare kaya ki koma can.

Nan ki bar ma Amarya. Nan da kwanaki uku za’a dawo da su Alhassan, a cikin ɗakuna ukun sai a ware musu ɗaya a shirya musu kayayyakinsu. Ka riƙe ɗaki ɗaya, itama ta riƙe ɗaya.

Nan ɗakuna biyu, falo, bayi, kicin sun isa amarya ko ƴar gidan uban wanene. Ina fatan ka ji abinda na ce?”

“Na ji Hajiya. Haka za’ayi in Allah ya yarda.”

Ya amsa daƙyar kamar mai ciwo a maƙogwaro.

“Madallah! Zubaida tashi mu tafi…”

“Ayya mana Hajiyarmu wayyo, tunda kika shigo fa ko ruwa baki sha ba, don Allah ki bari ku gama cin abinci sai ku tafi.”

Fareeda ta katse ta da ƴar damuwar rashin zamansu Hajiyar a fuskarta.

Amma fa zuciyarta Rai fes sunan wata zani. Haƙiƙa da gaske ne duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. Ita ta fara mishi zancen komawarta can ɓangaren, ya ce bazai yiwu ba, sai ga shi cikin sauƙi wacce za ta bashi umarni ba tare da ya musa ba ta zo ta yanke hukunci, kuma ba tare da ta kira Hajiyar ta faɗa mata ga yadda suka yi ba. Allah mai girma.

Mukhtar dai tunda ya duƙar da kanshi ƙasa har su Hajiyarmu suka fice ganin sabon gini bai iya ɗaga kanshi ba. Daga can kuwa sallama suka yi ma Fareeda direban Hajiya yaja suka bar gidan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 12Rabon A Yi 14 >>

1 thought on “Rabon A YI 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×