Skip to content
Part 20 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Cikin nutsuwa taja da baya ta ƙara shigewa cikin kujeran da take zaune. Da wani irin salo ta ɗaga ƙafa ɗaya ta ɗora kan ɗaya, ta ɗaga hannu guda ta tallabe kumatunta. Ta ƙure shi da kallo tana wani irin narai narai da fuska kamar za ta saki kuka.

Tunani take yi

‘Saboda Allah a maganganunta ina abin ashar da fusatarwa? Shi fa Mukhtar haka yake! Idan tsiyarshi ta motsa da abin faɗa da ba na faɗa ba duk faɗa yake yi, kamar mai aljanu ne, idan ba jirgewa suka yi ba sam ba’a samun sauƙi. Ita kam gaskiya ba ta jin za ta iya biye mishi ya ɓata mata rai a wannan lokaci da take jin zuciyarta sakayau babu wata damuwa.’

Muktar dai har lokacin yana tsaye yana huci kamar wani bijimin sa.

Yana so yayi magana, amma ya san idan ya buɗe baki domin yin magana mai daɗi baza ta taɓa fitowa daga bakinshi ba, don haka ya zaɓi yin shiru yana ƙoƙarin rage ƙarfin fusatar da yayi.

Fareeda da bata san dawan garin ba a hankali ta sake kallonshi, ta mayar da idanunta kan Fatima da take zaune tsamoo kamar kazar da aka tsamo a cikin ruwan zafi. Ta ƙura ma kan kafet idanu, ko tunanin me take yi oho!

Idanunta ta dawo da su kan Mukhtar ta ƙara rage muryarta ta ce,

“Idan akwai abinda ya fusatar da kai a maganganu na Allah ya huci zuciyarka Abee”

Ta kira shi da yadda su Sayyid suke kiranshi, bata bashi damar cewa wani abu ba ta cigaba da magana.

“Idan kuma Kwana casa’in ɗin da na ƙara muku sunyi kaɗan ne to na ƙara muku wasu kwana casa’in ɗin, kaga wata shida kenan. Idan su ɗin ma sun muku kaɗan ba laifi ku ƙara wasu kwana casa’in ɗin akai, daga haka…”

Wani irin wawan damƙa da ya kai ma kafaɗarta na hagu yasa ta katse maganar da take haɗe da cewa.

“Ahhhhhhh! Wayyo Allah Hannuna… Wash za ka murƙusa ni.”

Sai ga wasu zafafan hawaye sun silalo daga idanuwanta.

A gaggauce ya sake ta haɗe da ja baya. Cikin fushi ya nuna ta da yatsarsa manuniya

“Ki kiyaye ni Fareeda. Ni ba sa’an wasanki bane, kar ki kuskura ki ce za kiyi wasa da ni ko kuma ki nemi raina min hankali. Wallahi tallahi baki isa ba, ba’a son kwanakin. Saboda Allah da Annabi ni ne kike kyauta da ni kamar wani tsohon kaya Fareeda? Ni? Ni kike ma haka?”

Yayi mata tambayoyin bakinsa na ɗan rawa-rawa.

Ya ƙara murtuke fuska yana sake ɗaga murya cikin bala’i da masifa ya cigaba da cewa,

“Ke in banda rashin hankali da ƙuruciya ina kika taɓa jin an ƙara ma miji da kishiya kwana casa’in? Na yi magana kuma kin sake ƙara mana wasu casa’in ɗin, ke gwana har da sake ƙara wasu kwana casa’in ɗin. Haba Fareeda? Ba kya so na ne? Ko kuwa kishi na ne ba kya yi?”

Yai mata tambayoyin yana zazzaro idanu waje don tsananin ɓacin rai da takaicin da ƙari kwanakin suka cusa masa.

Ita dai har lokacin hawaye take yi, Allah ya sani sosai ta ji zafin riƙon da yayi mata. Ita ba ta son irin wannan, ita ƙashinta ba irin ƙauƙau ɗinnan bane da take jure wahala. Har yanzu zafi take ji a inda ya riƙe mata.

A hankali ta ɗago fuskarta da sukai kace kace da hawaye ta ce,

“Ni ce ba ni da hankali ko Mukhtar? Ni ɗin ce dai mare hankali don na yi muku abinda kuka nema. Na gode Mukhtar, ga mai hankali nan a kusa da kai ka tattara ta ku fice min daga ɗaki. Ke kuma”

Ta mayar da idanunta kan Fatima, ta nuna ta da yatsa manuniya, cikin ɓacin rai ta cigaba da cewa,

“Ba dai Mukhtar bane? Ga ki ga shi nan! Kin dai ji da kunnenki na ƙara muku kwana casa’in kan casa’in bisa wasu casa’in ɗin ko? To don Allah ki tarkata shi ki riƙe a gurinki. Amarcin da kika ce me kukai a cikin kwanaki uku ina so kije kiyi ta sharɓan romonsa har nan da shekara guda mu ga tsiyar da za ki tsinta a cikinshi…”

“Fareeda”

Mukhtar ya katse ta da kiran sunanta a haukace cikin tsawa.

Idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ya fara kora mata kashaidi bayan ya shata rantsuwa

“Wallahi Tallahi in kika sake cewa kin bada kwanakinki ga Fatima sai nayi mugun saɓa miki anan gurin.

Ke daga yau ma na soke batun wani kyautar kwana ko me zai je ya zo a gidannan. Babu wata mace da ta isa ta ce za tayi kyauta da kwanakinta ga abokiyar zamanta.

Ni ne maigida, sai na so za’a aikata min duk irin waɗannan abubuwan a gidannan! To ba na so!! Na ce ba na so!!!”

Ya ƙarasa cikin tsawa da tartsatsi.

A fusace ya ja musu tsaki ya kaɗa kai ya shige cikin ɗakinsa na nan ɓangaren Fareeda.

Fatima ta raka shi da idanu. Zuciyarta damƙam da mamaki da tsoro. Abin har ya kai a ƙara musu irin waɗannan magagan kwanaki masu yawa ya ƙi karɓa? To saboda me? Bayan duk irin maƙudan kuɗaɗen da ta kashe gurin magungunan mata da magungunan mallaka a ina ne aka samu matsala? Lallai ya kamata ta koma baya a hankali tayi karatun ta nutsu ta gano inda ta kuskure tayi gaggawar gyarawa…’

Dogon tsakin da taji saukarsa a kunnuwanta yasa tayi gaggawar dawowa cikin hayyacinta, sai ganin Fareeda tayi ta balla mata harara da manyan idanunta ta wuce tana gaf da shigewa cikin ɗakinta.

Ita kuwa tana zaune, kamar wacce aka dasa ta a gurin, ta kasa motsawa balle har ta tashi ta fice zuwa ɓangarenta. A madadin zaman banza da tunani ma sai ta fara ƙare ma falon kallo.

Lallai dole Mukhtar ya raina mata ajawali. Ba wasu sababbin kaya Fareeda ta zuba a falon ba fa, amma saboda tun farkon sayen kayan an zuba manyan kuɗaɗe ne ba tare da ƙyashi ba an sai na gari don mayar da kuɗi gida shi yasa har yanzu kayan ƙal suke.

Ga Fareeda kamar mayya take gurin tsafta, duk iya hangenta bata hangi wani ɗan datti da za taga cikashin falon ba.

“Gaskiya da sake! Ya zama dole in shiga in fita in nemo kuɗaɗe in gyara ɗakunana.”

Tayi maganar a fili, zuciyarta cike da ƙyashin kyawun ɓangaren Fareeda.

Kwatsam sai ga Mukhtar ya fito daga ɗakinsa zuwa cikin falon kamar wanda aka jefo shi. Ganin Fatima a zaune kuma babu Farida yasa shi yin turus yana kallonta da mamaki.

“Zaman me kike yi anan?”

Sai da tayi fari da idanunta sannan ta ƙanƙance murya ta ce

“Ai na zaci ka shiga ciki ka fito mu tafi ne? Haskenah ko ka ƙi karɓar mana kwanakin da ta ƙara mana har yanzu magrib da zan fita a girki baiyi ba. Gurina ya kamata a ce…”

“Girko! Fatima na ce Girko!! Za ki ɓace min da gani ko sai na ja ki a wulaƙance na fitar da ke?”

Ai a saba’in Fatima ta fice daga falon. Zuciyarta cike da mamakin wannan irin murɗaɗɗen hali na Mukhtar!

Shi kaɗai ya tsaya a tsakiyar falon yana ta safa da marwa. Zuciyarsa sai wani irin tuƙuƙi take yi na ɓacin ran maganganun da Fareeda tayi mishi waɗanda ƙarara suke nuna mishi bata damu da shi da lamuransa ba.

Lallai zai nuna mata bata isa ba, son da yake mata ba shi zai ba ta lasisin da za ta fara wasarere da al’amarinshi ba.

Kuma zai tabbatar mata har yanzu yana nan a zazzafan Mukhtar ɗinnan da ta sani, auren Fatima da ya ƙaro bai sa yayi laushi ba.

A fusace yaje ƙofar ɗakinta ya murɗa hannun ƙofar domin suyi duk wacce za suyi sai ya tarar da kofar a rufe.

Dogon tsaki yaja, ya shafa aljihunsa yaji makullin motarsa na ciki don haka ya fice daga falon. Motarsa ya hau ya fice daga gidan ba tare da ya koma ɓangaren Fatima da take tsaye jikin window tana kallon harabar gidan ta ɓangaren Fareeda ba, a zuciyarta take lissafin mintunan da ya ɗauka bayan fitarta, tare da shan alwashin ko ana ha maza ha mata sai ta rama wannan abu a ranar girkin Fareeda.

Ko da ya fita daga gida kai tsaye unguwar dosa ya nufa gidan mahaifiyarsa. Bai tarar da ita a falo ba, sai ya zauna kan kujera yasa hannaye biyu ya tallabe ƙeyarsa, ya ƙura ma guri ɗaya ido cikin zuzzurfan tunani.

“Lafiya? Tunanin me kake yi haka ina ta sallama baka ji ba?”

Hajiya ta tambaye shi da kulawa.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. A hankali ya ɗan zame zuwa ƙasa ya fara gaisheta a ladabce.

“Ya Fareeda da mazajena? Allah yasa dai lafiya suke?”

Ta tambayeshi bayan ta amsa gaisuwarsa.

“Lafiyarsu ƙalau Hajiya…”

“To tunanin me kake yi?”

“Babu komai”

Ya amsa a kasalance.

Ƙure shi tayi da kallo tana ganin yadda ya ɗab faɗa a idanunta. Shi kam ko irin kumarinnan na angwanci baiyi ba.

Tsakanin ɗa da uwa sai Allah. Karo na farko da taji tausayinsa ya ɗan ratsa ta tun bayan da ya fara rugu-rugun neman aurensa.

Nasiha mai ratsa jiki ta fara yi masa a tausashe, cikin hikima irinta manya da balagar iya magana. A fakaice tana ƙara nunar mishi da muhimmancin adalci a cikin iyali. Da kuma hanyoyin da zai bi wajen gujewa zama munafuki a tsakanin matan nashi guda biyu.

Sosai ya samu nutsuwa, shi da yaje gidan zuciyarsa danƙare da ƙunci sai ga shi ya samu nutsuwa da walwala.

A masallacin ƙofar gidan yayi sallar magriba da isha’i, sannan yayi mata sallama ya kama hanyar komawa gida.

A Taraba suya ya tsaya ya sayi kaza, guda ɗaya daban sai kuma ya sayi rabi itama aka naɗe ta daban. Exotic ya siya babba da ƙarami ya shige cikin motarsa ya bar gurin.

Ko da ya isa gida, kai tsaye ɓangaren Fatima ya nufa. Da ledojin biyu riƙe a hannayensa. Sallama yayi ya shige cikin falon, fuskarsa yalwace da fara’a.

Tana zaune akan kujera tayi kwalliya daidai gwargwado. Jikinta sanye da kayan barci, wayarta ce riƙe a hannunta tana dannawa.

Ganin fuskarsa a sake yasa ta cewa

“Oyoyo Hasken zuciyar Fatimah”

“Amarya ƴar shagali, amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Hutawa ake yi ne?”

Yayi maganar da salon tsokana yana ƴar dariya. Ya nemi guri a gefen ƙafafunta ya zauna.

Da sauri ta janye ƙafafun ta saukar zuwa ƙasa, da murmushi a fuskarta ta ce

“Amare dai suna can inda suke! Mu kam maneji muke yi…”

“Maneji? Me yasa kika ce haka?”

Ya tambayeta da mamaki.

“Maneji mana Haskenah! Wace irin amarya ce har yanzu Ango bai biya bashin kazar ta na amarci da yayi alƙawarin biya ba?”

Ta faɗi maganar a wasan dare tana ƙara buɗe hancinta sosai tana sake shaƙar ƙamshin gasasshiyar kazar da take ji tun bayan shigowarsa.

Dariya ya ƙyalƙyale da ita, a zuciyarsa yake yaba girman rainin wayau irin nata. Wato duk kwanaki ukun da yayi a ɗakinta bata san tayi ƙorafin kaza ba sai yanzu da ta ji ƙanshin ya taho da kaza.

Har da yayi niyyar mutsuke fuska ya hanata kazar yaga in tana da yadda za tayi da shi. Sai kuma ya tuna girman hakki da ɗazunnan Hajiya ta gama tunasar da shi, ledar da aka ƙunshe rabin kaza da ƙaramin lemun exotic ɗin ya miƙa mata.

“To ki kwantar da hankalinki. In dai kaza ce tasa kike ganinki a amaryar maneji ga ta na kawo miki, kici ki more, ke kaɗai ba tare da Ango ya miki giɓi ba.”

“Hmmm! To na gode.”

Ta faɗa da fuska ba yabo ba fallasa. Ledar da ya bata ta karɓa ta kalla dakyau, sai kuma ta kalli ɗayar ledar da take ajiye a gefensa taga ai naɗin ya fi girma.

Ba tare da wani tunanin ya kamata taje kicin ta ɗauko faranti ba ko kuma ta bari ya fita kawai sai ta warware naɗin kazar tun a nan gabansa.

Kallo ɗaya tayi ma naman ta gane rabin kaza ce. A raunane ta ɗaga idanu ta kalle shi

“Haskenah? Kana nufin a matsayina na amarya ban ci arzikin da za ka sayo min gudar kaza ba sai rabi?”

“Ikon Allah”

Ya faɗa da mamaki, bai bata damar cewa komau ba ya cigaba da cewa.

“Haba Fatima, ki dinga jin tsoron Allah mana. Fisabilillahi tunda dai kazar nan ba addini bace ya kamata ki karɓi abinda ya samu. Kuma in ba neman tayar da zaune tsaye ba duk kwanaki ukun da nayi anan baki tuna da wata kaza ba sai yanzu da kika ji ƙamshin na shigo da kaza?”

Shiru tayi mishi, ta duƙar da kanta zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Duk yadda kazar nan take ta tururi da nasha-nashan mai ga uban kayan haɗin da aka zuba wajen gasuwarta ji tayi sam bata burgeta ba.

Saboda Allah da Annabi ita da Fareeda wacece ta cancanci gudar kaza? Da ganin waccan babban ledar kaza guda ce ko kuma ɗaya da rabi, sai ita ne saboda ya raina ajinta zai kawo mata rabi?

Ganin yadda take ta cika tana batsewa yasa shi ɗaukar ɗaya ledar ya miƙe tsaye tsam! So take ta ɓata mishi rai a darennan shi kuwa gaskiya bai shirya ma hakan ba.

Nasihar Hajiya yayi tasiri ƙwarai a zuciyarsa. Tunda ya tara mata biyu to dole sai ya ninninka haƙurin da yake da shi.

“Allah ya huci zuciyarki Fatima. Kiyi haƙuri, ki daure ki ci rabin kazar. Gani nayi ke kaɗai ce anan shi yasa na siyo miki rabin kaza.

Ita kuma Fareeda ga ta, ga yara, ga kuma ni da zan kwana a gurinta. Kuma ma dai gurin sayen kazar nan wallahi ko kusa ban tuna da kina bi na bashin kazar amarci ba, amma ki ci rabin, ki yi haƙuri ki sake biyo ni bashin rabin. In Allah ya yarda in girki ya zagayo kanki zan biya wannan bashin.

Sai da safe.”

“Hmm! Ba komai, Allah ya tashe mu lafiya.”

Ta amsa a cuccushe.

Har ya nufi ƙofar fita daga falon sai kuma ya koma ciki. Nasihar mahaifiyarsa ya tuna, ɗazu ta jaddada mishi lallai haƙƙi ne da ya rataya a wuyanshi in dai yana da yadda zaiyi yayi ƙoƙarin saka ko wace mace a cikin su biyu cikin farin ciki.

Ledar hannunsa ya ajiye kan hannun kujera ya karasa kusa da ita ya durƙusa a gabanta.

Hannayensa biyu ya ɗora kan gwuiyawunta yana kallon fuskarta, ɗan girgiza kai yayi, sai ya sakar mata lallausan murmushi.

Ya tausasa murya sosai kamar saurayi a gaban budurwar da yake mutuwar so ya ce

“Haba Fatina, Haba Fatin Haskenta. Haba Amaryata ƴar shagali na. So kike in tafi can in kasa barci saboda barinki da nayi cikin ƙunci? Don Allah ki ɗan yi min murmushi mana ko na tafi da hoton kyakkyawar fuskarki a zuciyata.”

Tun kafin ya rufe baki ta sakar mishi faffaɗan murmushi kamar bakinta zai yage.

Ledar naman hannunta ya karɓa ya ajiye a gefe, ya miƙar da ita tsaye, a slow motion da salo irinna indiyawa ya janyota jikinsa ya rungume. Wani abu da tun ranar farko da ta shigo gidan bai sake bari ya shiga tsakaninsu ba.

Luf tayi a ƙirjinsa tana jin wani irin sanyin daɗi da nutsuwa yana kwarara a zuciyarta. Tana son Mukhtar, Allah ya sani tana son shi. Duk irin ɓacin ran da ya cusa mata a cikin kwanakinnan ƴan waɗannan kalaman da rungumar nan duk sun share wani fushi da take yi da shi. Lallai da gaskiyar bahaushe da ya ce

“So hana ganin laifi.”

Tsawon wasu daƙiƙu yana rungume da ita sannan ya sake yi mata sallama. Ya sumbaceta a laɓɓa ta mayar mishi da martani cikin rawar jiki.

Ya ɗauki ledarsa ya fice suka rabu tana farin ciki, bayan ta raka shi har bakin ƙofar falonta.

Yana fita ta kulle ƙofar, kamar ƴar tsuntsuwa ta fara daka tsalle a tsakiyar falon tana ɗebo shoki tana watsawa, zuciyarta cike da farin cikin irin rabuwar da suka yi ita da Haskenta Mukhtar a wannan dare.

Ko da yaje ɓangaren Fareeda, wani abin mamaki sai ya tarar da ƙwayayen lantarkin falon duk a kashe, sai wani mai duhu guda ɗaya da ta bari a kunne.

Kan teburin cin abinci ya hanga idanunsa. Sai yaga sabbin kuloli masu bala’in kyau da tsada ajiye akan teburin. Da saurin gaske ya ƙarasa gurin, ledar hannunsa ya ajiye a gefe ya buɗe babban kular abincin.

Farar shinkafa ce da aka dafa ta tayi wara wara da koren wake da karas, yana buɗe kular miyar ƙamshin soyayyar miyar stew ya daki hancinshi. A gefe guda kuma ga yankakken kabeji nan da albasa a cikin wani ɗan madaidaicin kwanon tangaras mai murfi.

Muƙut ya haɗiye miyau. Duk yunwar da yake ji bai tsaya cin abinci ba ya nufi ɗakinsa, a tunaninsa zai tarar da ita a ciki ta yi ƙayataccen kwalliyar barci tana jiran dawowarsa, sai yaga wayam.

Ga dai gadonshi nan lafe da sabon zanin gadon da bai taɓa ganinshi ba. Amma ya duba ko ina ba ta a cikin ɗakinshi.

Da sassarfa ya fita zuwa ɗakinta, wani abu da ya bashi mamaki kuma ya kashe mishi jiki shi ne ƙofar ɗakin Fareeda kulle yake gam da makulli.

A hankali ya fara ƙwanƙwasawa, amma har ya kwashe mintuna uku yana ƙwanƙwasawa ko motsinta bai ji ba balle ya saka ran za ta buɗe mishi.

Hakanan ba don ransa ya so ba yaja sanyayar ƙafafunsa ya koma wurin teburin cin abincin, zuciyarsa cike da tunanin ko me yasa Fareeda ta kulle ɗakinta? Shi har ga Allah ya ma manta a yadda suka rabu da ita ɗazu…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 19Rabon A Yi 21 >>

1 thought on “Rabon A Yi 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×