Skip to content
Part 21 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Duk da matsananciyar yunwar da yake ji, ɗan kaɗan ya tsakuri abincin ya kora da ruwa. Duk ƙamshin da naman yake baɗawa ko buɗe ledar baiyi ba balle ya ɗanɗana.

Abu ɗaya da ya iya yi shi ne saka ledar naman a cikin firij, saboda kar ya canza ɗanɗano zuwa safe tunda akwai kayan haɗi a ciki.

Yana gama cin abinci ya shige cikin ɗakinsa. Hanci ya buɗe sosai ya shaki wani ƙamshi mai bala’in daɗi na turaren wuta, wanda a ɗazu sa’adda ya shiga duba Fareeda hankalinshi yayi gaba, sam bai ji ƙamshin ba.

“Hmmm! Fareeda ba dai son ƙamshi ba.”

Ya faɗa a fili sa’adda ya buɗe banɗakin nasa ya ji ƙamshin turaren wutan ya daki hancinshi.

Yana gama biyan buƙatarsa bai ɓata lokaci wajen yin shirin barci ba, ya gama komai ya canza ƙwan lantarki zuwa mai duhu ya bi lafiyar gado.

Jikinsa a saɓule, wayarsa ya janyo ya danna mata kira, nan take kamfani suka faɗa mishi wayar a kashe take. A dole ya haƙura ya kwanta ba don ransa ya so hakan ba.

Allah ya sani yau ya saka ran jin ɗumin jikinta, yayi kewarta, irin sosai ɗinnan. Sai a lokacin ma yake tunawa ashe rabonshi da ita tun dawowar da yayi ya zo mata da zancen zai auri Fatima.

Tun lokacin ta raba musu makwanci. Shi kuma duk ƙulafucinta da yake yi bai taɓa nuna mata ya damu da raba makwancin ba.

A sannu ya runtse idanunsa, yana jin yadda wani matsanancin kewa da sha’awarta ke ƙara lulluɓe shi. Zuciyarsa cike da fatan nannauyan barci yazo yayi awon gaba da shi.

Bayan tsawon lokaci yana juye-juye daƙyar ya samu barci ya ɗauke shi a wahalce.

****

Motsin da ya ji a kicin yasa shi ƙarasawa da sassarfa. Ita ya gani, tana tsaye gaban cabinet tana fasa ƙwai a cikin roba.

A firgice ta juya jin anyi ma ƙugunta wani wawan damƙa. Ganinshi yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta kwaɓe fuska, tayi narai-narai da idanunta ta ɗan tura baki gaba

“Ashe kai ne, ka tsorata ni…”

Cikin salo ya juyo da ita suna fuskantar juna. A sannu a hankali yana riƙe da ita ya dinga matsawa da fuskarsa zuwa tata, ita kuma ta dinga ja da kanta baya har sai da ta kusa kwantar da kanta kan Cabinet ɗin

“Abee ka bari mana don Allah, za ka sa inyi ɓari fa.”

Tayi maganar tana zazzaro idanu ƙirjinta na bugawa. Bata san me yasa ba sam ba ta son ya sumbace ta.

Hannayensa ya ɗaga daga ƙugunta zuwa bayanta ya tallabota dakyau, a hankali ya janyota ya matso da ita tsakiyar kicin ɗin, har lokacin yana riƙe da ita.

Murmushi ya sakar mata. Ita kuma ta ƙara daidaita yanayin fuskarta zuwa ba yabo ba fallasa.

“Jiya, na zaci zan tarar kin shirya min kyakkyawan tarba? Me yasa kika ƙi zuwa ɗaki na? Kuma nai ta ƙwanƙwasa ƙofarki kina ji na kika ƙi buɗewa”

Idanunta ta wulƙita kamar tana harara, kamar kuma tana kallon gefe da gefe.

“Abincinka, da duk wani abu da na san za ka buƙata na ajiye maka. Ɗakinka duk da ko wane lokaci a gyare yake sai da na sake ƙalƙale shi. Me kuma kake buƙata bayan waɗannan Habeebee?”

“Ke”

Ya amsa kai tsaye.

“Ke nake buƙata Fareeda! Allah ya sani ina kewarki…”

Katse shi tayi ta hanyar sakin wata irin dariya a sakalce.

“Dariya kike yi…?”

“Eh to ai dole inyi dariya Habeebee! Ni da tun kafin amarya ta zo aka tattarani aka aje gefe ɗaya? Ai kaje ka ji da Amaryarka kawai, babu komai, zan baku lokaci sosai har fiye da yadda kuke buƙat…”

A bazata ya haɗe bakinsu guri ɗaya. Ya fara aika mata da wani irin zazzafan sumbata, duk yadda ta so ƙwacewa ta kasa, sai kawai ta mishi kakim shi kaɗai yake kiɗansa yake rawarsa.

Hakan bai dame shi ba. Daga bisani ma ɗaga ta yayi cak suka nufi ɗakinsa. Duk yadda take ƙoƙarin zillewa bai sauke ta ba sai da ya kaita har kan gadonsa.

Ko kafin tayi yunƙurin sauka ƙasa har ya mata rumfa ta yadda baza ta iya sauka ƙasa ba sai ya bata dama. Daman har lokacin kayan barci ne a jikinta, don haka bai sha wahala wajen zame mata da cillar da su ba.

Da wani irin zafi-zafi da rawar jiki kamar wanda ake ingiza shi yake aikata komai. Sosai jikinsa ke karɓar duk wani abu da yake yi.

Duk da a ɓangarenta babu wani armashi ko tallafi a hakan dai ba ƙaramin samun yadda yake so yayi ba.

Sai da ya gama taɓo duk wani guri da zai motsa shi yana gyarata da nufin ayi mai gaba ɗaya ba zato ba tsammani gaba ɗaya kuzarinshi ya tafi. Ya wani kwanta lakaf kamar ba shi ne yai tsaye ƙiƙam yana zakwaɗin samun biyan buƙatarsa ba.

Hannunsa yakai gurin, a tsorace ya janye hannu ya kai idanunsa jin kamar ya taɓo lagwani don sanyin da yayi.

Ya ɗago idanu a tsorace ya kalli Fareeda da take kwance da ɗaurarriyar fuska, ya sake mayar da idanu jikinshi yasa hannu ya ɗan taɓo bakinshi na rawa ya ce ma Fareeda

“Lllllla…fiya.. kuwa…? Kin ga… yadda…na zama?”

A lalace ta ɗaga idanu ta kalli inda yake nuna mata. Ganin yadda yayi lakaf kamar wanda ya gama aikata komai yana buƙatar hutawa sai ta kawar da kanta gefe ɗaya.

A bazata wani irin faɗuwar gaba ya sameta.

‘Mukhtar lafiyayye kuma jarumin namiji ne da ko bai gani ba bai taɓa ba haka kawai yake miƙewa saboda tsananin lafiya da jarumtarsa. Amma yanzu ace ya kwanta ligif tun ba’ayi komai ba? Lallai an gogu da Amarsu ta Ango mai zaƙin miya.”

Da sanyin jiki sosai ta zame ƙafafunta ta mirgina gefe ɗaya, ajiyar zuciya take saukewa a hankali kuma akai-akai.

Tunanin kwanciyar me za ta cigaba da yi tunda ba halin yin abinda yasa shi ɗaukota sai ta yunƙura za ta tashi.

Da sauri Mukhtar ya riƙota ya sake komar da ita kan gadon.

A hankali ya fara yamutsata jikinsa na rawa, ƙoƙari yake ya taɓa duk inda ya san zai tayar da kanshi da gaggawa.

A yanzu ɗin wani irin salon soyayya yake gabatar mata wanda ba shi kaɗai ba, ita kanta duk ɗaurewarta da kawar da kai sai da ya samu nasarar kunnata. Da armashi sosai ta juyo tana mayar mishi da martanin wasanninshi, sai a lokacin ita kanta tasan ta yi kewar mijinta.

Wani abin mamaki da ban tsoro ga su biyun kamar ɗazu dai haka ne ya sake faruwa. Duk yadda Goga Mukhtar ya miƙe tsaye ƙiƙam kwanciya ya sake yi lakaf sa’adda ya zo zai ratsa gonar da ta daɗe da zama halaliyarsa.

Ruƙunƙumeta yayi da ƙarfi a ƙirjinsa yai shiru, zuciyarsa na bugawa fafafat! Hankalinsa a bala’in tashe.

‘Me yake faruwa ne haka?’

Tana kwance a jikinsa wani irin tashin zuciya ya fara zuwar mata bagagatan, amai take jin yi, duk da cikinta babu komai da ta ci a safiyar nan sosai amai ke taso mata.

Jin miyaun bakinta ya tsinke sosai alamun ko wane lokaci aman na iya ƙwace mata yasa ta fara ƙoƙarin ƙwace jikinta.

Mukhtar bai lura da halin da take ciki ba. Hankalinsa yayi nisa gurin tunanin inda matsalar take, sai ya ji ta fara ƙoƙarin ƙwacewa daga riƙon da yayi mata.

Jajayen idanunsa ya ɗago ya zuba mata sai yaga yunƙurin da take yi da yadda take kai hannu tana tare bakinta.

“Lafiya…?”

“Amai”

Ta amsa daƙyar sannan ta sauka a guje zuwa banɗaki.

Wani irin ƙaƙƙarfan amai ne take yi kamar za ta amayar da ƴan cikinta. Jin yunƙurin ya ƙi ƙarewa dole ya taso zuwa bayin yana jera mata sannu.

Hankalinsa ne ya ƙara tashi ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci ta galabaita. Ta gama aman kumallo yanzu kuma yunƙurin aman take yi babu abinda ke fitowa. Kuma ta kasa daina yunƙurin.

Sosai ya riƙe ta a jikinsa ganin tana ƙoƙarin zubewa ƙasa saboda rashin ƙarfin jiki. Hankalinsa a ɗugunzume. Sannu kuwa ya jera mata ya fi baki ɗari.

Bayan tsawon lokaci suna cikin banɗakin daƙyar yunƙurin da take yi ya ragu. Ruwa ya tara mai zafin gaske cikin kulawa da tarairaya ya salleta soso da sabulu.

Cikin rashin ƙarfin jiki ita kuma ta lallaɓa tayi na tsarki, duk da ruwan zafi take amfani da shi tana yi jikinta na kyarma-kyarma.

Babban tawul ya rufa mata yana riƙe da ita a gefen kafaɗarsa ya kaita gefen gado ya zaunar da ita, sannan shi ma ya faɗa wanka.

Ko kafin ya fito daga wanka ta kwanta, bayan ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta har saman kai. Wani irin rawan sanyi take yi sosai yadda ko daga waje ne ana kallon yadda take jijjiga a cikin bargo.

Ko mai be shafa ba ya zura kaya a gaggauce yana yi yana kallonta. A daidai lokacin kuma daga can falo ya ji muryar su Sayyid suna ƙwala kiran Ammee, da raunin murya mai nuni da alamun ko wane lokaci za su iya fashewa da kuka.

Da sauri ya fita falo gurinsu. Ganinshi yasa suka taho da ɗan gudu gudu suka rungume shi suna gaishe shi cikin harshen nasara.

“Ammee ba ta da lafiya. Me kuke so?”

Ya tambaye su da kulawa bayan ya amsa gausuwarsu.

“Abee, yunwa muna ji.”

Suka amsa da gwaranci a muryoyinsu.

Ganin kayan barci ne a jikinsu ya bashi tabbacin yanzu suka tashi. Sai yaja hannayensu zuwa banɗaki ya goge musu baki, yayi musu alwala. Ya shimfiɗa musu sallaya ya durƙusa a gabansu ya ce

“Kuyi sallah, idan kun idar yanzu zan kawo muku kayan break fast. Kun ji?”

Kawunansu suka ɗaga.

Sai ya wuce kicin da sauri, wani ƙwan ya sake fasawa ya soya musu, saboda wancan da Fareeda ta fasa a buɗe suka bar shi.

Ya haɗa musu tea a ƴan kofunansu ya ɗauki biredi da ƙwan da ya soya ya kai musu.

Gurin kayanta ya nufa, bayan ya ɗauki Inner wears sai ya ɗaukar mata doguwar rigar atamfa mai faɗi, ya ɗauki babban hijabi mai kauri ya koma gurinta a ɗakinsa.

Yanzu ta rage jijjigar da take yi, barci take, amma irin wahalallen barcin nan mai tafe da zazzafan zazzaɓi. Ko da ya taɓa jikinta zafi sosai.

A hankali ya ɗaga ta ya saka mata kaya, ya sa mata hijabin ya sake kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo.

******

“Barr. Ka taimaka min, don girman Allah ka taimaka min. Wallahi tallahi ina cikin wani matsanancin hali ne da idan ban samu kuɗaɗen ayau ɗinnan ba rayuwata za ta ƙara shiga cikin garari…”

“Hajiya Fatima wai saurin me kike yi ne? Idan kinyi haƙuri, wata huɗu ya rage su sake biyan kuɗin hayar nan. Da yau da nan da wata huɗu ai kaman gobe ne in dai muna raye…”

Jin da tayi yana neman yi mata yawo da hankali alhali yana da ikon taimaka mata kawai sai ta sakar mishi kuka. Shi kaɗai ne hope ɗinta na ƙarshe da take tunanin za ta iya samun rancen kuɗi a gurinshi kafin ƙarshen shekara a biya kuɗin hayar shagon da take da kaso a ciki.

Dubu ɗari biyu da hamsin ake biya duk shekara, to ita a rabon gadon da aka yi duk sa’adda aka biya kuɗin tana da dubu saba’in da biyar a ciki.

Wani abun armashi shi ne, masu biyan kuɗin hayar shagon idan sun tashi biya suna bada na shekara biyu ne. A lissafi tana da dubu ɗari da hamsin kenan.

Yanzu saura wata huɗu kenan a biya kuɗin. Jiya da daddare ta yanke shawarar kiran lauyan da yake tsaye akan kadarorin ƴaƴan mijinta ta roƙe shi ya taimaka ya bata kasonta tun kafin lokacin biyan kuɗin yayi.

Shi ne yake ta mata yawo da hankali, sai yayi kamar zai taimaka mata sai ya zille, ga ɗari biyar ɗin da ta ci bashi a wayarta kuɗin na tafiya a iska babu biyan buƙata.

Jin kukanta ya ɗan karya mishi zuciya, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa

“Tsaya, tsaya, saurara Hajiya Fatima. Ai abin duk bai kai na kuka ba. Kin dai san yanzu lokaci ya canza gwamnati ta hana aikin da babu riba ko?”

“Eh!

Ta amsa da rawar murya.

“Zan taimaka miki, amma bisa sharaɗi ɗaya idan kin amince. Kuɗinki na shekara biyu dubu ɗari da hamsin ne, idan kin amince zan cire dubu talatin, yanzu in baki ɗari da ashirin ni kuma idan sun biya in riƙe ɗari da hamsin ɗin. Kin amince?”

Shiru tayi cikin tunani, ya za ta yi? Ba ta da wani hanyar samun kuɗi da ya wuce wannan. A baya al’mubazzaranci kawai tai tayi da kuɗaɗe ba tare da tunanin irin wannan lokacin zai iya zuwa ba.

“Na amince”

Ta amsa a raunane.

Ko minti biyar ba’ayi ba da yake yana acc ɗinta taji wayarta yayi ƙaran shigowar saƙo, tana dubawa taga ɗari da ashirin ɗin ne ya turo mata.

Tsananin farin ciki yasa  ita kaɗai ta fara ƙyalƙyala dariya, kamar wata sabuwar kamu. Tana wannan dariyar taji kamar ana ƙwanƙwasa mata ƙofar falo.

Ajiye wayar tayi a kusa da ita ta ƙara saurarawa da kyau, sai taji tabbas ƙwanƙwasawar ake yi. Agogon fuskar wayar ta kallah taga ƙarfe takwas da minti arba’in da bakwai na safe.

Hijabi ne a jikinta, sai ƙarfe takwas ta samu sararin gabatar da sallar asubah tun da ta idar shi ne bata cire ba ta zauna kiran lauya.

Har za ta fita sai tayi tunanin idan ba Mukhtar ba wa zai ƙwanƙwasa mata ƙofa da safennan? Hijabin ta cire ta aje a gefen gado, ta cire zanin da ta ɗora kan rigar barcin jikinta tayi sallah ta ajiye.

Ta sake kallon rigar barcin jikinta, shara shara take ana ganin komai na jikinta. Murmushi ta saki ta nufi ƙofar falon ta buɗe tana ta wani gantsare – gantsare.

Suna haɗa idanu ta sakar mishi lallausan murmushi, da wani irin salon rangwaɗa ta gantsare sannan ta duƙa a gabanshi kamar za tayi ruku’u, ƴan mamunanta suka fito sosai ta gaban rigarta ta ƙale mishi idanu ɗaya haɗe da cewa

“Haskenah! Barka da asubah hasken zuciyar Fatima. Ina fatan ka tashi cikin aminci da ƙoshin lafiya?”

Ƴaƴansa da ke tsaye gefensa yayi saurin mayar da su baya haɗe da cewa

“Miye haka kike yi? Dallah ki miƙe tsaye bakya ganina tare da yara ne?”

Ya ƙarasa maganar haɗe da ɗaure fuska tamau.

A saɓule ta miƙe tsaye tana tura baki.

“Fareeda ba ta da lafiya. Za mu tafi asibiti yanzu…”

“Allah ya sauwaƙe”

Ta katse shi tare da mayar da ƙofar falon za ta rufe.

Hannunshi ɗaya yasa ya danne ƙofar

“Za mu bar yara a hannunki ne…”

“Yara kuma?”

Tayi mishi tambayar tana yamutsa fuska. Allah ya sani ta tsani wahalar ƴaƴa, nata ƴaƴan ma ƙannenta ke ɗawainiya da su, shi yasa babu wani shaƙuwa mai girma tsakaninta da yaran har aka raba su.

Ganin wani mugun kallo da ya aika mata yasa tayi saurin cewa

“Shi kenan! Ba damuwa. Kai kuzo mu shiga ciki”

Ta miƙa hannu da nufin janyo Shahid da tun ɗazu take kallon yadda yake leƙota daga bayan Uban.

Aikuwa a tsorace yaron ya fashe da ihun kuka yana ƙamƙame ƙafafun uban. Sayyid ganin ɗan’uwanshi na kuka shi ma ya fashe da kuka yana rirriƙe ɗan’uwansa.

“Daman ba kiyi niyyar riƙe su ba.”

Yayi ƙwafa, sannan yaja hannun ƴaƴansa a fusace suka bar gurin.

Cikin rashin damuwa ta mayar da ƙofar ta kulle.

“Ai kam dai banyi niyya ba. Haka kawai ina zaƙin amarcina na samu an raba ni da nawa yaran za ka fara haɗa ni da wata wahalar? Bazan ɗauka ba. Ba ni na ɗora mata ciwo ba don haka ko za ta mutu taji da ƴaƴanta.”

Taja dogon tsaki sannan ta shige cikin ɗakinta.

Wayarta ta ɗauka ta duba lafiyar kuɗinta tana sakin murmushi. Nan gefen gado ta zauna ta fara kasafta yadda za ta bi da kuɗin daki-daki gurin magance matsalolin da take ganin su suka sa Mukhtar yake mata gani-gani.

Mintuna goma tsakani taji ficewar motar Mukhtar. Cikin gyatsine ta ce

“A gayas, Umma ta gaida Assha.”

*****

Ko da suka isa asibiti babu ɓata lokaci aka bata gado saboda yadda ta galabaita sosai. Bayan duk wasu gwaje-gwaje, Likita ya tabbatar musu tana da ƙaramin ciki na wata biyu, sai kuma tyohoid ɗan kaɗan a jikinta.

Saboda tsananin murnar jin tana da ciki bakin Mukhtar ya ƙi rufuwa. Sai rungume su Shahid yake yi kamar wasu manyan yara yana basu labarin Ammee za ta haifa musu ƙani. Suna so?

Ɗaga kai suka yi suna dariya ganin yadda yake dariya amma ba don sun fahimci abinda yake nufi ba.

Su da suka bar gida tun safe ba’a sallamesu sai da yamma liƙis. Ruwa leda biyu aka ƙara mata, kuma likita ya ce a barta ta huta ta hanyar samun wadataccen barci cikin nutsuwa.

Ita kuma Fatima wannan yinin asibiti da suka yi abin yayi mata daidai. Akwai wani yaro a maƙwaftansu da ta sani kafinta ne, tun safen ta kira shi yaje gidanta.

Ko da ta nuna mishi kujeru da shimfiɗar gadonta tana tambayarshi nawa za ta kashe gurin gyara su zama lafiyayyu? Domin kujerun har yadinsu take so a canza.

Kasancewar yaron yana da tsoron Allah kuma akwai zaman amana kai tsaye ya ce mata in dai za ta ji shawararshi ta canza kujerun kawai, saboda ruɓaɓɓun katakai ne aka lulluɓe su da katifa da yadi.

“Aunty Fatima ko kin gyara waɗannan sake ɓallewa za suyi. Amma idan za’a sami dubu tamanin a hannunki akwai wasu lafiyayyun kujeru a ƙasa da sai a kwashe waɗannan a kawo miki waɗancan.”

Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina shawarar da ya bata. Ta marairaice sosai tana kallon yaron mai suna Khalipha ta ce

“Wannan harka taimaka min za kayi Khalipha. Ka ga waɗannan ruɓaɓɓun kujerun wallahi a dubu tamanin da biyar suke a hannuna. Asabe Dillaliya cutata tayi, Allah zai min sakayya tsakanina da ita. Ka taimaka don girman Allah in baka cikon dubu hamsin ka kwashe wannan ka kawo min waɗancan…”

“Ina.. Ai hamsin baza ta yi ba Aunty Fati.”

Taja yaja dai daƙyar ya karɓi dubu saba’in. Ta bashi dubu biyar kuɗin wasu sabbin shimfiɗun gado da zai kawo mata. Sai dubu biyar kuɗin motar da za’a kwaso kayan.

Yana fita bai ci awa biyu ba sai ga sababbin kujeru masu kyau daidai gwargwado ya kawo mata.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka kwashe tsoffin kujerun da shimfiɗun gadon aka zuba mata sababbi. Sai ga guri ya fara fitowa tsaf.

Bakin Fatima har kunne saboda tsananin farin ciki da jin daɗi, ita kaɗai sai safa da marwa take yi tsakanin uwarɗaki da falo tana ƙyalƙyala dariya. Idan ta gaji da zurga-zurgar sai ta daka tsalle ta haye kan kujera tana sauke ajiyar zuciya, kujeru daƙauƙau, duk tsallen da tai tayi a kansu ko motsi basu yi ba.

“Saura labulaye.”

Ta faɗa a fili tana kallon yadda ko kusa kalar kujerun basu shiga da labulayen ba.

Cikin ɗaki ta shige da sauri ta ɗauko wayarta, lambar wata tsohuwar ƙawarta Jamila da take aure kusa da kasuwar barci ta lalubo ta danna mata kira.

Sun taɓa magana da Jamilar ta tabbatar mata ana samun labulai masu kyau kuma cikin sauƙi a gwanjo, waɗanda idan ba ke kika faɗi cewa gwanjo bane za’a rantse da Allah sababbi ne.

Bayan gaisuwa Jamilar ta tabbatar mata in dai da kuɗi a ƙasa to akwai kaya. Nan take ta ɗauki hotunan kalar kujerun ta tura mata, ta tura mata kuɗi dubu ashirin.

Itama nan Jamilar bata ɓata cikakkun awa uku ba sai gata niƙi-niƙi da labulai. Kuma babu ƙarya sunyi kyau, sunyi kalar kujerunta. Sai dai a yamutse suke sosai.

Dubu biyu ta ba Jamilar da take kamar mayya gurin son kuɗi jikinta na rawa ta koma gida ta goge labulayen tas ta sake kawo mata.

Kafin ta bar gidan sai da ta taimaka suka maƙala labulayen. Sai ga guri ya sake fitowa gwanin ban kyau, ɗakin Amarya ya fito shar!

Saboda tsananin Murna ita kaɗai sai wani hura hanci take yi tana jin kanta a sama. Duk da ɗakin Fareeda ya fi nata kyau amma itama baza a raina mata ba.

“Hmmm! Wai dan ma babu kafet, dining table, da kayan kallo kenan. Ai wallahi da ɗakina sai ya yaga ma nata a kyau! Amma babu damuwa kan tafe kan isa dai.”

Ta faɗa a fili tana sake hango yadda tsarin falon Fareeda yake a idanuwanta. Sai kuma taja tsaki, lokaci ɗaya ƙunci ya mamaye farin cikin da take yi tunano har yanzu fa Fareeda ta kere mata.

*****

“Amma dai kin tabbatar yanzu bakya jin ciwon komai?”

Ya tambayeta cikin kulawa a hanyarsu ta komawa gida. Hannunsa ɗaya na kan sikiyari yana tuƙi, ɗayan hannun kuma na riƙe da nata yana ɗan murzawa a hankali.

Kafin ta amsa sai da tayi murmushi, zuciyarta cike da jin daɗin wani kulawa ta musamman da ya ƙara ninka ma wanda yake mata a baya da jin zancen tana da juna biyu.

“Alhamdulillah! Ba na jin ciwon komai Habeebee. Na ji sauƙi sosai.”

“Madallah! Haka nake son ji. Bari mu biya in muku takeaway, yadda baki da lafiyar nan bai kamata da mun je gida ki shiga kicin ba…”

“A’a! Don Allah ka barshi. Akwai ragowar abincin jiya babu abinda yayi. Kuma na ga ka aje nama a firij sai in haɗa in ɗunɗuma, zai ishe mu a wadace. Amarya ce dai ina roƙon alfarma ka ce mata tayi girkinta na dare, gobe da rana idan na dafa sabo sai in bata.”

“Ba damuwa, Allah ya ƙara miki lafiya.”

“Ameen”

Su Sayyid suka haɗa baki gurin amsa addu’ar! A tare iyayen suka saki murmushi.

Suna isa gida bayan ya taimaka mata zuwa ɓangarenta kai tsaye ya fice zuwa gurin Fatima.

Ko da ya shiga falon ko kusa hankalinshi bai kai kan gagarumin canjin da aka samu a kayan ɗakin ba.

“Kin ji mu shiru ko? Jikin nata ne sai a hankali…”

“Allah sarki! Sannunku da dawowa.”

Ta faɗa da wani irin yanayi da ƙarara yake nuna mishi rashin damuwarta kan ciwon Fareeda.

Sai yayi turus a tsaye ya dafa hannun kujera yana kallonta, ta ci kwalliya sosai cikin wata doguwar riga ƴar kanti.

“Muje ki duba jikinta ko…?”

“Kwance take ranga-ranga ne? Ina kallonku ta window fa da ƙafafunta ta shige ɓangarenta. Tunda jikin ba tsanani yayi ba ko zuwa sati mai zuwa ne idan bata warke ba sai in leƙa ta.”

Saboda tsananin takaici da baƙin ciki, tsawon minti biyu yana kallon ƙasa. Ya ma kasa kallonta, ya kasa buɗe baki yayi magana. Idan ya buɗe baki a yadda yake jin zuciyarsa lallai zai iya ɗuɗɗura mata ashar.

Sai kawai ya kaɗa kai ya juya zai fice daga cikin ɗakin.

“Haskenah, baka ga na yi canjin kayan ɗaki bane?”

Ta faɗa ganin yana gaf da ficewa ba tare da ya yaba ƙoƙarin da tayi gurin kashe maƙudan kuɗaɗe a gyaran ɗakin ba.

A ɗaiɗaice ya kalleta yana taɓe baki, ta wani tsuke cikin kayan da ya ƙara bayyana ramarta a fili tunda babu ciko. Ya kalli falon nata a wulaƙance, ya sake taɓe baki don ya cusa mata haushi.

“Ummm na gani. Ba laifi. Duk da haka dai da kaɗan kwaɗo ya ɗara gaya. Ni dai har yanzu ko kusa banga royal chairs da gadajen da aka yi ƙaryar za’a cika min ɗakuna da su ba.”

Ya fice yana jin sauƙi-sauƙin takaicin maganar da ta yaɓa masa kan ciwon Fareeda. Ko babu komai dai ya ɗan rama.

*****

A wannan dare, haka dai aka sake maimaita abin yau da safe. Sai bayan gama zafafan wasanni a tsakaninsu da ya yi yunƙurin shiga gonarsa sai ta kwanta likif, izuwa yanzu lamarin ya daina ba shi mamaki. Sai dai tsoro.

Ita kuwa Fareeda kawar da damuwar komai tayi tasha barcinta hankali kwance. Shi kuwa yana rungume da ita a ƙirjinsa yana karanta wasiƙar jaki.

<< Rabon A Yi 20Rabon A Yi 22 >>

1 thought on “Rabon A Yi 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×