Skip to content
Part 22 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Washe gari Fareeda ta tashi lafiya ƙalau, babu wani ciwo ko ƙanƙani da take ji a jikinta.

Amma saboda ɗoki da zakwaɗin cikin jikinta da Mukhtar yake yi haka ya dinga tarairayarta, duk inda ta saka ƙafa yana biye da ita. Duk aikin da ta kamo haka yake saka hannu ya tayata suyi su gama.

Ba yadda baiyi da ita ba kan ta zauna ta huta ta ce a’a! Ita baza ta iya kwanciya ba tare da ta gyara ɗakunanta ba.

Ya ce ta barshi yayi aikin, nan ma ta ce a’a! Baza ta iya zama tana kallonshi shi kaɗai yana aiki ba.

Wannan shi ne dalilin da yasa ya saka sauƙaƙan kaya marasa nauyi ya dinga taimaka mata. A yinin wannan rana, sun sabunta soyayyarsu fiye da yadda ake zato.

Minti ɗaya biyu zai kalleta da faffaɗan murmushi a fuskarsa ya ce

“Ina son ki Fareeda.”

Idan ya faɗi haka wani irin girma kanta yake yi kamar zai fi ƙarfin gangar jikinta, zuciyarta ta cika ta tumbata da matsanancin farin ciki, har takan manta yanzu ba ita kaɗai ce da shi ba.

A yangace cike da ƙasaita take mayar mishi da martanin murmushinsa.

“Nima ina son ka Uban ƴaƴana.”

“Allah ya barmu tare”

“Ameen thumma Ameen”

Suke haɗa baki su biyun gurin amsa kyakkyawar addu’ar da yayi musu. Sai su ƙara musayar murmushi sannan su cigaba da aikin da yake gabansu.

Irin kalaman soyayyar da ya dinga faɗa mata a wannan rana, kamar lokacin da ta samu cikin farko ne, tana Amarya.

Suna bala’in mararin juna tun gishiri bai fara sauka daga kan kaza ba.

Da an ɗauki ƴan mintuna zai riƙo ta zuwa jikinsa, cikin salon soyayya yake shafa lafaffen cikinta da in banda likita ya tabbatar tana da ciki babu wanda zai ce akwai ajiyar ɗa a ciki saboda shafewarsa.

“Baki gaji ba Matata? Ba na so ku wahala ke da Babys ɗina…”

Ta zazzaro idanu a tsorace ta ce

“Babys ɗin har guda nawa Habeebee?”

“Uku mana! Wancan karon kin bani biyu rayayyu kuma lafiyayyu yanzu ba sai ki bani uku ba?”

Ya raɗa mata a kunne, har lokacin yana shafa cikinta.

“Ban yarda ba, ni dai gaskiya ban yarda ba Habeebee. Haihuwa wahala, ko ɗaya Allah ya bani Allah ya saka mishi ko mata albarka.”

Kukan shagwaɓa ta sakar mishi bayan gama maganar tana bubbuga ƙafafunta a ƙasa.

Ƙara riƙeta yayi sosai a jikinsa yana dariya yayi sama da hannayensa yana lalubeta kamar yana mata cakulkuli. Daƙyar ta iya ƙwace jikinta ta matsa gefe itama tana dariya.

Ko da ta gama abinci ta zuba na Fatima wadatacce a kula shi da kansa ya ɗauka ya miƙa mata.

Ya tarar da ita bakinnan a gaba don har lokacin bata manta maganar da ya yaɓa mata jiya ba. Kuma da safe ko sararin leƙawa ya duba yadda ta tashi baiyi ba, ta leƙa ta window fiye da sau talatin da tunanin ko ya fita ne sai taga motarsa na ajiye a tsakar gida.

Saboda wannan baƙin cikin da ƙyar ta iya buɗe baki ta gaishe shi.

Ya amsa hankalinshi kwance ba tare da ya bi ta kan ɗaure fuskar da take yi ba. Ya kai mazaunai zai zauna kenan kan ɗaya daga cikin kujerunta ta kalle shi da salon saƙa magana ta ce

“Ai na zaci ba ka lafiya ne. Tun safe nayi ta zuba idon ka shigo mu gaisa baka shigo ba, har na fara tunanin ko idan ba ranar girkin mace bane baza ka dinga leƙawa da safe kaga lafiyarta ba”

Zaman da yayi niyyar yi ne ya fasa, ya tsaya a tsaye.

“Amma dai kin san Fareeda ba ta da lafiya?”

Yayi mata tambayar idanunshi na cikin nata.

“Haka ka ce min dai.”

Ta amsa bayan ta kawar da idanunta daga gare shi.

Da mamaki sosai a fuskarsa ya ce

“Haka na ce miki? Ƙarya nayi kenan?”

Shiru tayi bata amsa ba, sai ƙara tamke fuska da tayi tana hararar inda take kallo.

Shirunta shi ya fara fusata shi, da ɓacin rai ya kira sunanta.

“Fatima?”

“Na’am”

Ta amsa a ɗaiɗaice bayan ta taɓe baki.

“Wai me kike nema da ni ne tun jiya a gidannan?”

Yayi mata tambayar cikin tsawa-tsawa.

Runtse idanu tayi tana ƙoƙarin danne ɓacin ranta. Ta buɗe idanun bayan ta kalato hawaye ƙarfi da yaji ta kalle shi a raunane, da rawar murya ta ce

“Kayi haƙuri Haskenah! Allah ya huci zuciyarka. Ni ba nufi na in ɓata maka rai ba.”

Kaɗa kai kawai yayi ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da baƙin ciki. Ƙoƙarin watsar da tunanin komai yayi gaf da zai shiga ɓangaren Fareeda don kar ta karanci damuwa a fuskarsa itama ta shiga damuwa.

Cikin walwala da farin ciki suka ci abinci su da ƴaƴansu. Kamar a film, haka sukai ta ba juna da salon ƙauna har suka ƙoshi. Shi da yaran suka tattara farantan abincin zuwa kicin ita kuma tana zaune kan kujera a falo tana hutawa.

Ko da Magrib tayi sun rabu ne cikin farin ciki. Ita da yaran sai bye bye suke mishi kamar wanda zaiyi tafiya. Duk da bata furta ba, yana hango kewa mai girma a cikin idanunta.

Har ya fita sai ya dawo, kai tsaye inda take ya ƙarasa yaɗan riƙo ta kaɗan saboda idanun yaran ya ce.

“Ko in zauna sai zuwa anjima? sai in bata uzurin baki da lafiya…”

Da sauri ta katse shi da cewar

“A’a! Haba dai! Abinda bazan so ayi min ba bazan taɓa ba da damar ayi ma wata ba. Je ka Habeebee, Allah ya bamu alkhairi. Bayan ma kamar anjima ne kwanaki biyun za suzo su wuce…”

“Ai zan ma dinga shigowa duba lafiyarki da ta yara.”

“To babu damuwa! Sai da safe.”

Ta sakar mishi murmushi ta riƙe hannunshi cikin nata ta raka shi har ƙofar falon.

Fuskarta ya riƙe cikin hannayensa ya sumbace a laɓɓa. Ya shafo cikinta, ya tsugunar da fuskarsa saitin cikin ya sumbaceta, ya riƙo hannunta na dama ya sumbaceta.

Ya sake mata sallama ya nufi ɓangaren Fatima zuciyarsa tumbatse da kewar Fareeda da komai nata. A kasalance yake yafiya, yana yi yana tsayawa sai ya waiga ya kalli Fareeda da har lokacin take tsaye tana kallonsa, fuskarta da murmushi, hannunta ɗaya a sama alamar bye.

Duk wannan abu da yake faruwa kan idanun Fatima da tun da ya rage sha biyar a kira Magrib take ta safa da marwa tsakanin window da tsakar falon.

Ta sha kwalliya sosai kamar wacce take shirin zuwa dinner. Leƙe take yi taga ta ina Mukhtar ɗin zai fito, kuma da wani yanayi zai fito, farin ciki ko akasin haka?

Idan ta gaji da tsayuwa a window sai taja dogon tsaki, ta sake kallon agogo zuciyarta cike da matsanancin baƙin ciki da ɓacin rai.

A fili take surutan cewa

“Tun yanzu shegiyar nan za ta fara gwada min bariki ta hanyar mini ƙwangen lokacin barin miji ya dawo gurina? Wallahi sai na ci ubanta, zan nuna mata bata isa ba. Wato za ta nuna min ta fi ni sanin daɗin miji ko? Ni rannan ai ba haka na mata ba, tun la’asar ma da ya bar nan bai dawo ba sai da daddare da ya kawo min wata wulaƙantacciyar kaza.”

Tayi ƙwafa mai ƙarfi, ta cije gefen laɓɓa tana girgiza kai.

“Daga ke har Mukhtar ɗin zan nuna muku ku ƙananun ƙwari ne. Na fi ku sanin duniya da ajujuwan cikinta na kissa da makirci”

A haukace ta shige uwarɗakinta ta ƙara janyo jarkar da aka cika mata shi taf da tsumin ƴar gata, ta ɗaɗɗaka sosai kafin ta mayar da jarkar inda ta ɗauko.

Kicin ta wuce ta ɗauko kofi da madara ta sake dama kalolin magungunan mata masu yawa ta shanye. Gyatsa mai ƙarfi ta saki saboda yadda cikinta ya cika sosai da magungunan da tun ukun rana take sha.

Ta sha alwashin yau sai ta saka Mukhtar ihu a kan gado, sai ga shi yana neman ɓata mata lissafin da ta yini tana yi a ƙwaƙwalwarta.

Ko da ta koma falon a wannan karon ba a window ta tsaya ba, ƙofar falon ta buɗe tana leƙen ɓangaren Fareeda kwatsam sai taga fitowarsu, kamar wacce aka dasa tana tsaye ta kasa motsawa daga gurin har Mukhtar ya gama sumbace sumbacensa ya kamo hanyar ɓangarenta.

“Auchhhhh”

Ta faɗa tana dafe goshinta bayan ya turo ƙofar ba tare da sanin tana tsaye a gurin ba ya buga mata a goshi.

“Subhanallahi, na buge ki ko? Me kike yi a bakin ƙofa?”

Ya tambayeta cikin kulawa bayan ya janyo ta jikinsa yana mulmula mata goshin.

“Na zo rufe ƙofar ne.”

Ta amsa daƙyar cikin jin zafi, sosai ta bugu a goshin, hankalinta yayi nisa sosai har bata san ya iso bakin ƙofar ba da tuni ta kauce.

“Yi haƙuri. Sannu! Hankalina yayi gaba ban lura da ke a gurin ba.”

Sosai ya mulmula mata goshin yana jera mata sannu kafin ya sake ta ya shige banɗaki don ɗauro alwalar sallar magrib.

Ita kuma kicin ta shige ta fara fito mishi da kayan abinci tana jerawa a tsakar ɗakin.

Har yayi mata sallama zai fita masallaci ta nuna mishi kular da Fareeda ta zuba mata abincin rana ta ce,

“Ga abincin ƴan can ɓangaren fa. Ko za ka miƙa musu kafin ka wuce?”

“Ok!”

Ya amsa a taƙaice.

Har ya ɗauka zai fita jin kular babu nauyi sosai sai ya buɗe. Ƙanƙance idanu yayi yana kallonta bayan ya ga abincin can ƙasa, shinkafa ce da miya tayi, kuma miyar ƴar ɗugul akan shinkafar.

“Miye haka Fatima? Wannan abincin ai ko su Sayyid bazai ƙosar ba balle ace har da mamansu. Kuma saboda Allah sai ki zuba musu miyar akan shinkafa? Idan ba yanzu za su ci ba fa?”

Narai narai tayi da fuskarta cikin sallamawa ta ce

“Ayya Haskenah, don Allah kayi haƙuri. Na san Fareeda bata cika cin abinci da yawa ba shi yasa ban cika musu ba, kuma daman ƴar kaɗan na dafa saboda kar inyi ɓarna. Amma zan kiyaye gaba in sha Allahu. Kayi haƙuri.”

Bai ce komai ba. Inda ta jera nasu abincin ya nufa ya, ko da ya buɗe babbar kular sai yaga ta shaƙe musu taf da farar shinkafa. Ta miyar ma ta zuba a wadace ga mai nan nasha-nasha a sama.

Ajiye wanda ta zuba ma Fareeda yayi ya ɗauki wanda ta zuba musu ya nufi ƙofa zai fita da su.

“Zan kai musu wannan. Ke sai ki ci wancan, ko ban samu ba babu damuwa sai in sha tea.”

Ya fice da kulolin a hannunsa, ya barta daskare akan kujera baki buɗe. Ranta a ɓace, zuciyarta a ƙuntace. Tsabar baƙin ciki da takaici bata san sa’adda ta lailayo wani ƙatoton ashariya ta maka ma Fareeda da ƴaƴanta ba.

Daƙyar ta iya danne zuciyarta ta shige banɗaki tayi alwala. A gurguje tai salla ta sabunta kwalliyarta ta ƙame akan kujera tana jiran dawowarsa.

Yau ranarta ce, lokacin gaba ɗaya nata ne. Ko kaɗan ba ta son tayi abinda zai janyo ɓacin rai tsakaninta da Haskenta.

Ko da ya dawo daga masallaci bai shiga gurinta ba, sai tashin motarsa taji alamun zai fita daga gidan. Da gudu ta leƙa ta window sai bayan motarsa ta gani yana gaf da fita.

Turus tayi a tsaye, zuciyarta cike da tunanin ina kuma za shi a wannan lokacin da ya kamata ace tana zaune a cinyarsa suna ciyayyar abinci a tsakaninsu?

A sanyaye taja ƙafafunta ta koma kan kujera ta zauna, ta zuba tagumi da hannu bibiyu, zuciyarta danƙare da saƙe-saƙe mabanbanta.

Minti talatin da fitarsa ya dawo gidan. Ko da ya shiga har lokacin tana zaune inda take, ta amsa sallamar da yayi a sanyaye.

“Barka da zuwa”

“Yauwa!”

Ya amsa haɗe da miƙa mata ledar hannunsa. Ya ƙara da cewa

“Ga alƙawarinki na cika. Rabin kazar amarcin da kike bi na…”

“Haba Haskenah, wallahi da ma baka wahal da kanka gurin siyowa ba. Ai ka fi ƙarfin kaza a guri na.”

Ta ƙarasa maganar haɗe da kaɗa ƙwayoyin idanunta cikin salo tayi wani farrrr da su.

Sai da yayi dariya sosai sannan ya ce

“Kar ki damu. Ki ci kawai, hakkinki ne a al’adance matsayinki na Amarya. Ina dai ƙara roƙon afuwa kan jinkirin da nayi gurin cika wannan al’ada.”

Martanin dariyarsa ta mayar mishi sannan ta shige kicin ledar na riƙe a hannunta.

A faranti ɗaya ta juye naman kazar, ta sako cokula masu yatsu guda biyu ta fito tana rangwaɗa ta ƙarasa kusa da shi ta zauna a kujerar da ke gefensa.

“Bismillah Haskenah! Jin daɗin cin kazar amarci a ci shi tare da ango, daga nan ko me zai biyo baya zai taho ne a marmarce kuma cike da armashi. Ko ba haka ba Aban Twince nawa?”

“Wannan haka yake Amaryata”

Ya amsa yana dariya.

Tare suka ci naman kamar yadda ta buƙata, ta zubo musu abinci a faranti ɗaya suka ci tare. Duk da ɗarewa kan cinyarsa bai samu ba soisai ta ji daɗin yanayin da suka kasance ita da shi.

Saboda tsananin shauƙi har bai san ji sadda aka kira sallar isha’i ba, sai ji yayi ana raka’ar ƙarshe. Ko kafin yayi alwala ya fice har an idar da sallar. Anan cikin falonta yayi sallar yana jin babu daɗi na rashin jam’in da bai samu ba.

*****

Bai manta yadda ya tarar da Fatima a darensu na farko ba. Amma saboda yana so ya share ma kanshi tantamar ko ba shi da lafiya ne shi yasa tana fara tayawa ya amshi gayyatarta da gaggawa.

Wani irin salo ne taje mishi da shi cikin ƙanƙanin lokaci ta birkita shi, sosai jikinsa yake karɓar saƙonnin da take aika mishi.

Wani abin ban mamaki a gare shi, wani abin tsoro da firgici, wani abin tunani a gare shi shi ne yadda ya iya ratsa gonar Fatima ba tare da fuskantar matsala makamanciyar wacce ya fuskanta tsakaninshi da Fareeda ba.

Bayan kammaluwar komai gefe ya matsa a wahalce yana sassauke ajiyar zuciya. Ita dai Fatima har yanzu matsalar jiya na nan a jikinta, bai saba jin irin haka a jikin Fareeda ba, gaskiya bazai iya ba. Gara tun da wuri ya sanar da ita idan ma wani magani take amfani da shi da yake sakata bushewa ta daina, shi ba ya jin daɗi, ko kusa ba ya jin wani armashi a karo biyun da suka yi. Har ta fara barci ya tashe ta.

“Haskenah? Ya aka yi? Akwai wata matsala ce?”

Ta tambayeshi tana mutsutsuke idanunta.

“Fatima, in faɗa miki gaskiya ko in ƙyale ki cikin duhu?”

“Faɗa min Haskenah, don Allah faɗa min. Allah yasa dai ba wani laifi nayi maka ba. Idan nayi laifi ne don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min, da alkhairai nake nufinka a zamanmu ba na so muna yawan samun saɓanin fahimta…”

“Dakata Fatima. Ni ban ce kinyi min laifi ba.”

Ya katse ta. Sai kuma yayi shiru ya haɗiye miyau sau ɗaya.

“Fatima. Ni fa gaskiya a yadda nake tarar da ke ɗinnan ba na jin daɗi.”

Ba tare da wani alkunya ko karantawa ba ya faɗa mata yadda yake jin ta a bushe ƙamas.

“Don haka idan ma wani magani kike amfani da shi da ya mayar da ke haka ina baki shawarar ki daina. Don wallahi ni bazan iya jurewa ba, shi yasa kika ga ko a wancan kwanakin na amarci tun daga sau ɗaya ban ƙara yunƙurin cewa zan wani taɓa ki ba.”

Yana gama maganar ya faɗa banɗaki, ba tare da ya saurari ko za ta mishi wani ƙarin bayani ba.

Hankalin Fatima a tashe ta saka kuka ƙasa-ƙasa, wani iri take jin jikinta gaba ɗaya, irin a muzancen nan. Anya a duniya akwai abinda ya fi wannan ban takaici da baƙin ciki? miji ya ƙeƙashe idanunsa ba tare da jin kunya ko karantawa ba ya faɗa ma matarsa ba ya jin daɗinta a ɓangaren auratayya?

A wannan dare ta ci kuka har ta gode Allah! Barcinta raba da rabi ne, zuciyarta cike da tunanin hanyar da za ta bi don magance wannan matsalar da gaggawa. Ashe shi yasa ko irin ɗokinnan na amare Mukhtar ba ya nuna mata? To menene amfani duk magungunan da ta siya ta hannun Ramlah da sauran masu magungunan mata? Duk sun tashi a banza kenan? Yaudararta suka yi ta ɓarnata dubban kuɗaɗenta a banza ko kuwa ita ce magungunan basuyi aiki a jikinta ba.

Shi dai Mukhtar juya mata baya yayi yashaa barcinsa hankali kwance, cikin nutsuwa. Domin ya gama sakankancewa a zuciyarsa tunda ya samu nasarar ratsawa ta gonar Fatima, tabbas babu wani abu da zai hana shi samun kyakkyawan mu’amala tsakaninshi da Fareeda.

Washe gari da wuri ya shirya ya fice, a gurguje ya leƙa Fareeda ya duba lafiyarta da yara sannan ya fice daga gidan. Gurin aikinsa ya nufa, hutun sati ɗaya aka bashi don cin amarci. Tun jiya Ogansu ya kira shi ya jaddada mishi lallai yau ya zo Ofis akwai wasu takardu da ake buƙatar ya duba ya saka musu hannu, da gaggawa ake buƙatarsu bazai yiwu a jira zuwanshi jibi da hutunsa zai ƙare ba.

Ko wanka bata yi ba ta ɗaga waya hankalinta a tashe ta kira wata makwafciyarta da suka yi zaman mutunci da amana mai suna Aunty Ladidi.

Aunty Ladidi irin matannan ne masu tsage gaskiya komai ɗacinta. Duk yadda take aminci da ke ko take ƙaruwa da ke ba ta jin kunya ko tsoron ta wanke ki tas idan taga kina neman kauce hanya.

Ko a batun aurenta da Mukhtar har gida Aunty Ladidi ta bi ta tayi mata wankin babban bargo, ƙal tayi mata sannan ta bar gidan. Ko a yanzu ta yanke shawarar neman Aunty Ladidin ne saboda ta san ita ɗin idon gari ne, tana da mutane sosai. Kuma tana sana’ar haɗa magungunan mata ingantattu waɗanda take haɗawa da hannunta, dangin kayayyakin ciye-ciyenmu da ganyayyaki masu amfani a jikinmu mata.

<< Rabon A Yi 21Rabon A Yi 23 >>

2 thoughts on “Rabon A Yi 22”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×