Skip to content
Part 23 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Cikin kuka mai bayyana tana cikin masifar tashin hankali take roƙon Aunty Ladidi a waya don girman Allah ta taimaka mata, tazo gidanta da gaggawa a safiyarnan, tana cikin wani gagarumin bala’i ne da idan ba Aunty Ladidin ba babu wacce za ta iya fitar da ita a cikin wannan halin.

“Allah ya raba mu da bala’i”

Aunty Ladidi ta faɗa cikin rashin damuwa da irin kukan da Fatima take yi.

Daƙyar Fatima ta iya tsagaita kukan ta amsa da

“Ameen”

Ladidi ta gyara zama ta cigaba da cewa

“Maman Ummee (Inkiyar da suke ma Fatima da sunan ƴarta ta farko) a halin yanzu gaskiya bazan iya sakin ayyukan da nake yi in taho gidanki ba. Ah toh iya zallar gaskiyar magana kenan, bazan yi ƙarya don ki so ni ba.

Amma idan kin ga matsalar za ta faɗu ta waya ki faɗa min, ina saurarenki. Idan kuma baza ta faɗu ba to ki jira ko zuwa nan da sati mai zuwa, kila in samu sararin leƙowa.”

Katse kiran tayi ta saka katin dubu ɗaya ta banki cikin ragowar kuɗin da suka rage mata, sannan ta sake kiran lambar Aunty Ladidi. Ba tare da ɓata lokaci ba ta zayyane mata irin matsalolin da take ciki ita da Mukhtar, tana maganar tana kuka. Idan ta tuna yadda ƙeƙe da ƙeƙe cikin dare ya iya sanar da ita yadda take sai taji zafafan hawaye sun sake ɓalle mata, zuciyarta sai wani irin suya da ƙuna take mata kamar ana babbakata ta ciki.

“Ashsha! Eh lallai Maman Ummee dole kiyi kuka. Miji ya fito ɓaro-ɓaro ya faɗa miki irin wannan magana dole hankalinki ya tashi afujajan ki fara neman mafita.

Amma na ce ba? Kin sha magungunan sanyi kafin ayi biki kuwa? Kin san shi ne babban ciwon da ke janyo matsala makamantan naki da wasu waɗanda suka fi naki. Kamar su ƙaiƙayin gaba, rashin sha’awa, jin zafi lokacin mu’amalar auratayya, rashin kuzari, ke ciwon sanyi har hana haihuwa yake yi. Kin sha maganin sanyi?”

“A’a!”

Ta amsa muryarta na fita da ƙyar! Ta ƙara da cewa

“Amma magungunan mata babu kalar wanda ban sha ba…”

“Shirme kika yi kenan! Ta yaya ga sanyi danƙare a jikinki za ki tsaya ɓarnata kuɗaɗenki a magungunan mata? Baza su taɓa yi miki aiki ba, dama maganin sanyin kika yi ko baki sha maganin mata ba in dai kin dace da maganin sanyi mai kyau ni’imarki da Allah ya halicceki da ita za ta dawo taf! Maganin mata ana sha ne kawai don bahaushe ya ce ko kana da kyau ka ƙara da wanka…”

“Yanzu ya zanyi Aunty? Don Allah ki taimaka min.”

Tayi maganar cikin marairaita da rawar murya.

“Eh to akwai yadda za kiyi mana. Amma fa in kina da kuɗi. Shi ciwon sanyi da kike gani balaƴaƴƴen ciwo ne da idan ba dace kika yi da magani ba sai dai kiyi ta wahala. Kuma an fi dacewa da maganinsa a ɓangaren magungunan gargajiya, na asibiti sai tsananin sa’a za ki rabu da ciwon gaba ɗaya. Amma na gargajiya idan Allah ya taimakeki kika yi dace da ingantaccen magani kamar na Zee Maman Mujaheed cikin ƙanƙanin lokaci za kiga biyan buƙata…”

“Wacece ita? Aunty Ladidi ina son maganin, a ina take? Nawa ne kuɗin maganin? Wallahi ko nawa ne zan siya in dai zan samu waraka daga wannan matsala.”

“Don waraka fa za ki samu da yaddar Allah! Mata da ɗunbin yawa sunyi amfani da maganinta kuma sun ga biyan buƙata. Kuma wani abin armashin shi ne sam maganinta babu tsada, galan dubu huɗu ne. Nima ba ta hannuna za ki sayi maganin ba, akwai wata ƙawar ƙanwata da take sayar da ingantaccen haɗin gyaran nono da cikowarsa ita naga ana kawo ma maganin masu siye anan kaduna suna karɓa a gurinta. Ita Zee Maman Mujaheed ɗin a katsina take, amma duk sa’adda kika yi magana kina son maganinta a cikin yinin ko washe gari saƙonki zai iske ki har garin da kike zaune.”

“Maganin cikowar nono?”

Fatima ta tambaya cikin zakwaɗi, zuciyarta cike da tunanin yadda a fili Mukhtar yake tattaro suɗaɗɗun silifas ɗinta yana yamutsawa babu shauƙi ko kaɗan a tare da shi.

“Shi ma maganin nonon ina so. Nawa take sayarwa?”

“Dubu biyu da ɗari biyar ne ɗan ƙaramin bokiti. Kuma wallahi ina mai baki tabbacin maganin nonon da za ki siya gurin Farida ba nono kaɗai zai gyara miki ba, har ni’ima yana ƙara ma mace saboda nagartaccen haɗi take yi ba irin na ƴan kuci ku bamu ba. Bayan ni’ima zai sa jikinki yayi kyau, ki murmure, fatarki tayi ta sheƙi saboda kunun da kike sha na maganin…”

Jikinta a sanyaye jin sunan mai maganin ta ce

“Sunan mai maganin Farida? A ina take ?”

“Kinkinau, ta gurin masallacin musabaƙa.”

Kamar baza ta siya ba, jin sunan mai maganin ɗaya da na kishiyarta da ta tsaya mata a ƙahon zuci. Sai kuma wata zuciyar ta umarceta da ta siya, ai ba gurin kishiyar bace balle a ce tayi abin kunya. Kuma Fareeda nawa ne a duniyarnan?

“Ina son maganin Infection ɗin galan biyu. Shi ma maganin nono ina son roba biyu. Amma zan samu da wuri ko Aunty? Idan da so samu ne a kawo min tun yau in fara amfani da su.”

“Kar ki damu. In dai kina da kuɗi a ƙasa za ki samu magunguna akan lokaci. Bari in kira Farida in ji yadda za kuyi.”

Bayan minti goma sha biyar Aunty Ladidi ta tura mata lambobin waya guda biyu, da bayani kamar haka.

“Ga lambobin masu sayar da magungunan ki kira su, za su baki acc no ki tura musu kuɗi za su faɗa miki lokacin da saƙo zai iske ki 09077591726👈🏽Farida Maganin nono. 0816 285 9027👈🏽 Zee maganin infection.”

Akan gwuiwa take, don haka babu ɓata lokaci ta kira lambobin. Sosai ta saki jiki ta faɗa ma matan biyu halin da take ciki, saboda Farida da Zainab mata ne da suka iya kasuwanci, sun iya tafi da jama’a cikin haba-haba da fara’a.

Shawarwari sosai suka bata na yadda ko bayan tayi amfani da magungunan za ta kiyaye kamuwa da makamantan matsalolin in dai ba wata muguwar ƙaddara ba da ba’a fata. Sannan suka faɗa mata yadda za tayi amfani da maganin, kuma sai washe gari za’a kai mata maganin. Ita za ta biya kuɗin delivery.

Acc no suka tura mata ta saka musu kuɗaɗen siyayyar da za tayi. Yinin wannan rana haka ta ƙarasa shi cikin ƙunci da damuwa. Ko abincin rana sai gaf da la’asar ta samu ta dafa jallof ɗin taliya.

Bata ji kashaidin da Mukhtar yayi mata jiya ba, haka ta sake zuba ɗan cukul a kula tana zubawa tana ƙunci, ita wannan tsarin na yin girki ɗaya sam baiyi mata ba. Don dai kawai ba ta da yadda za tayi ne.

Tun safe ko wanka bata samu sararin yi ba, a taƙaice ma babu aikin da tayi a ɓangarenta. Tana kwance tana tufka da warwara, wani lokacin kuma ta cigaba da saƙa da mugun zare kamar yadda ta saba.

Gyale ta ɗauka ta yafa kan kayan barcin jikinta ta fice da kular abincin a hannunta, fuskarnan a ɗaure tamau. Ta nufi ɓangaren Fareeda tana tafiyar laƙaiƙaita za tayi baza tayi ba.

Tun daga nesa ta hangi Fareeda zaune akan kujeran roba a ƙofarta, daga ɗan nesa kaɗan kuma almajirin da yake yi mata wanki ne, ga kaya nan a gabanshi ya duƙa yana wankewa.

Ko da ta isa ƙofar Fareeda maimakon a mutunce tayi mata sallama, ko baza su gaisa ba ta ajiye mata abincin, sai kawai ta ƙarasa gurin almajirin kai tsaye. Sunan yaron Yusuf, ta san shi yake yi ma Fareeda wanki tun da daɗewa, a wasu lokutanma har ita tana kwaso kayan wanki daga gidanta ta kawo ma Yusuf ɗin ya wanke mata anan gidan Fareeda.

A fili ta kalli Fareeda ta galla mata harara. Irin yadda Fareedar tayi kyau cikin sakakken doguwar rigar jikinta shi ne abinda ya ƙara ƙuntata zuciyarta. Har baiken kanta ta gani, me yasa bata tsaya tayi wanka ta sha uban kwalliya kafin ta fito kawo abincin ba?

Taja dogon tsaki kamar bakinta zai taɓi ƙasa. Ta kalli almajirin ta ce

“Yusuf sannu da aiki. Karɓi wannan abincin ka miƙa ma wancan matar.”

Ta ƙarasa maganar tana nuna Fareeda a wulaƙance da yatsarta manuniya.

Tun isarta gurin, Fareeda tana kallonta. Tana kallon yadda take ta wani kallon komai a wulakance, tana kallon yadda ta galla mata harara, amma sai tayi kamar bata gani ba.

Tana jin yadda ta ja mata tsaki amma duk ta basar, kamar bata san da wanzuwar Fatima a gurin ba. Fuskarta yana kan wayarta da take dannawa a hankali, lokaci bayan lokaci ita kaɗai sai ta saki murmushi.

Karaf maganar da Fatima tayi ya faɗa cikin kunnenta, wani ƙayataccen murmushi ta sake yi. Ta ƙasan idanunta take kallon yadda almajirin ya duƙa har ƙasa ya gaishe da Fatiman, sannan ya karɓi kular abincin ya nufo gurinta da shi.

“Yusuf ka faɗa mata ta sake abincin yanzunnan ta baka kular ka miƙo min. Sannan sabbin kulolina na jiya da Haskenah ya kai mata abinci ta baka ka kawo min, tunda ba uwar mace  ta siya min ba.”

Fatima ta faɗa cikin tsiwa da masifa.

Duk da ranta ya ɓaci da jin zagin da tayi mata a fakaice, ko kaɗan bata nuna a fuskarta ba. Kanta yana ƙasa tana cigaba da shafa fuskar wayarta, duk da izuwa lokacin ta daina fahimtar rubutun da take karantawa a fuskar wayar.

Idan akwai wani abu da Fareeda tayi matuƙar ƙwarewa akai shi ne ɓoye ɓacin ranta. Bata iya riƙe baƙin ciki a zuciyarta ba, amma idan ba ita ta so ba duk yadda za ka so ka ɓata mata rai ko ta ji haushi baza ta taɓa nuna maka ba.

Har wannan lokacin murmushin fuskarta duk da ya koma na yaƙe ne bata bari ya ɓace ba.

Yusuf na isa gurinta ya duƙa har ƙasa ya ajiye kular a gabanta, kusa da ƙafafunta, a ladafce ya ce

“Aunty wai ga shi, ki sake ki bata kular da kulolin jiya.”

Irin yadda Fareeda ta janye ƙafafunta a ƙyamace daga jikin kular abincin da almajirin ya ajiye shi ne abinda ya fara dukan zuciyar Fatima. Bata gama farfaɗewa daga wannan takaicin ba ta ji Fareeda ta kira Yusuf da har ya miƙe zai koma kan aikin da yake yi.

“Buɗe kular mu ga jagwalgwalon da ke ciki.”

Fareeda ta umarci Yusuf.

Babu musu kuwa ya tsuguna da hannunsa duk kumfa ya kama murza murfin kular, daƙyar ya buɗe saboda santsin hannayensa.

Taliya ce dafa duka ta manja, da yake a gurguje aka dafa ta sai bata wani ji kayan haɗi ba, kuma sa’adda ta gama dafawar ba’a lokacin aka kawo ba sai ta wani irin sanƙarewa a cikin kular babu ko armashin kallo a idanu.

Fatima tana kallon yadda Fareeda ta kawar da kanta da sauri daga kan abincin, ta mele baki gefe ɗaya.

“Yusuf za ka iya ci? idan baza ta ciwu maka ba ɗauko robarka ka sake a ciki, idan ka koma makaranta sai ka ba waɗanda basu samu abinci ba. Wata ƙil su su iya cin wannan busasshiyar taliyar mai kama da ta ƴan fursuna. Idan ka sake ka miƙa mata kular…”

“Aunty sauran kulolin da ta ce ki bata fa?”

“Yusuf ka faɗa mata wanda ya kawo abincin jiya, idan ya dawo shi zai shiga kicin ɗina ya ɗauko ya kai mata.”

Tana gama faɗin haka a ƙasaice ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta ɗan zamo gaba kaɗan a kan kujerar da take zaune ta ɗaga wayarta ta cigaba da dannawa.

Fatima tana tsaye ita kaɗai sai huci take kamar kububuwa. Lallai wannan shi ne baki idan ya san abinda zai faɗa bai san abinda za’a mayar mishi ba. Tana kallon yadda almajiri Yusuf ya ɗauko robarsa ya kara saman robar daidai kan sabon kularta da ko Mukhtar bai taɓa cin abinci a ciki ba.

Ya dinga buga kular kan robar saboda taliyar ta fara sanƙarewa, shi kuma so yake ya kifa abincin cikin robarsa ba tare da ya saka hannu a ciki ba, zai iya kai bayan magrib bai koma makaranta ba, baya so ta fara saki.

A ƙoshe yake, tun ɗaya da rabi na rana Fareeda ta shaƙo mishi faranti da indomie da dankalin turawa, an zuba busasshen kifi wadatacce a ciki, duk loma ɗaya biyu sai ya ci karo da kifi. Da ya gama ya kora da ruwan pure water guda biyu, kun san indomie tana da riƙe ciki har yanzu dam yake jin sa.

Daƙyar abincin ya saku kirif a cikin robarsa, bayan kular ta gama shan buguwa da wujijjiga. Bakin kular jage-jage da manja ya rufe da murfin ya ƙarasa ya miƙa ma Fatima.

“Ga shi, an gode Allah ya karɓa.”

Ta kasa karɓan kular saboda ɓacin rai, ta kasa amsa addu’arsa don ba tayi niyyar sadaka ba.

Shi kuwa ya ajiye mata nan gabanta a ƙasa ya koma kan aikinsa.

Fatima da ta rasa abinda za tayi ma Fareeda ta huce sai kawai ta cire gyalen da ta rufa da shi taci ɗamara, idanunnan sunyi jajur don ɓacin rai.

Ta buɗe baki za ta fara zuba zallar madaran rashin mutunci na bala’i sai ga Mukhtar ya shigo cikin gidan. Da manyan ledoji biyu riƙe a hannayensa.

“Oyoyo Abee! Da fatan ka dawo lafiya?”

Fareeda ta faɗa tana kallonshi da yalwataccen murmushi a fuskarta.

Martanin murmushinta ya mayar mata. Ya amsa gaisuwarta da kulawa yana tambayarta ya jiki?

Idanunsa na faɗawa cikin na Fatima ya ce

“Ke kuma lafiya kuwa?”

Ganin rigar barcin jikinta shara-shara ga almajiri na tsugune yana wanki a gurin ya saka shi ƙanƙance idanunsa.

“Menene haka? Wani wawancin shiga ne wannan?”

Ya sake mayar da idanunsa kan Fareeda ya ce

“Me yake faruwa anan? Kamar akwai abinda ba daidai ba..”

“Komai lafiya kalau Oga. A huta gajiya. Ni daman zan shiga ciki ne.”

Tana gama faɗin haka tsam ta miƙe tsaye, ta nufi ciki hannunta riƙe da wayarta.

Bayanta Mukhtar ya bi. Itama Fatima a fusace ta bi bayanshi zuwa falon Fareeda.

Suna shiga ciki ta zube ƙasa gaban Mukhtar ta saka kuka.

“Haskenah! Menene laifina don na aure ka? Na zaci Aunty Fareeda za tayi haƙuri ta rungumi ƙaddara mu zauna cikin aminci kamar yadda muke a baya…”

“Don Allah saurara! Me yake faruwa?”

Yayi maganar yana kallonta. Sai kuma ya mayar da idanunsa kan Fareeda da taja ta tsaya a tsakiyar falon, ta harɗe hannayenta a ƙirji tana kallon Fatima da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa.

A hankali ta sassauta kukan da take yi, ta gyara zama idanunta cikin na Mukhtar, har lokacin hawaye basu daina tsiyaya a idanunta ba.

“Haskenah kai ka saka dokar abincin rana da dare wacce take da girki ita za ta zuba ma mare girki. Yau tun safe yini nayi a kwance ba ni da lafiya, ban samu sauƙin shiga kicin ba sai ɗazu. Kuma ba don kowa na ƙuƙuta nayi girkin ba sai don ita da yaranmu. Kawai ina kawo mata abincin ko buɗewa bata yi ba ta fara saƙa min baƙaƙen maganganu, har tana cewa wa zai iya cin ƙazantaccen jagwalgwalon abinci na? Don ƙarin wulaƙanci a gaba na ko taɓa kular bata yi ba ta ce almajirinta ya sake a robarsa…”

“Me yasa haka Fareeda?”

Ya tambayeta fuskarsa na nuna ko kusa bai ji daɗin abinda Fatima ta faɗa mishi ba.

Ita kuwa Fareeda mamakin ƙarya da munafurcin Fatima ke neman kifar da ita a tsaye. Har wani jiri jiri ne taji yana ƙoƙarin kayar da ita. Daƙyar ta iya ɗaga yatsarta manuniya ta nuna masa agogo, ƙarfe huɗu da minti goma.

“Ni da yara baza mu iya jure har ƙarfe huɗu bamu ci abincin rana ba. Tun da naga ɗaya ta wuce na dafa mana indomie muka ci, ko na karɓi taliyar da ta kawo min ba ci zamu yi ba, shi yasa na ba almajiri. Ka faɗa mata, daga yau girkin rana idan ya wuce ƙarfe biyu ta dafa ita kaɗai kawai, bazan rasa ƴan dabarun da zanyi mu ci ni da ƴaƴana ba.”

Bata ƙara tsayuwan minti ɗaya ba ta shige cikin ɗakinta, ta barsu a gurin suna kallon-kallo.

“Yanzu saboda Allah da Annabi ke ko kunyar fitowa a haka baki ji ba? Dube ki fa? Dubi jikinki? a madadin ki saka ƙaton hijabi da zai rufa ma ƙasusuwanki asiri sai ki fito haka ƙozai-ƙozai kamar bulala? Kuma wannan ɗamarar da kika ci ta menene? Dambe kike shirin yi da ita?”

Da sauri ta fara warware ɗamarar da tayi ba tare da ta ce komai ba. Sosai ranta ya ƙara ɓaci, so tayi reshe ya juye da mujiya Mukhtar ya goyi bayanta yayi ma Fareeda gagarumin cin mutunci. Sai ga shi buƙatarta bata biya ba.

“Tashi mu tafi.”

Ya bata umarni.

Gyalen da ta warware ta rufa a kanta ta wuce gaba yana biye da ita a baya har zuwa ɓangarenta. Kamar tayi mishi maganar ledojin da ya shigo da su ya bari a falon Fareeda, sai kuma dai taja bakinta ta tsuke.

Nan falonta taja ta tsaya shi kuma ya wuce cikin ɗakinta, sai ga shi ya fito wuf kamar wanda wani abu ya biyo.

“Fatima? Wani irin iskanci ne haka za ki bar shimfiɗa kaca-kaca tun yadda na fita da safe na barshi?”

Ta fara kame-kame ya dakatar da ita ta hanyar daka mata wani gigitaccen tsawa da ya saka ta durƙushe ƙasa tana riƙe cikinta da taji lokaci ɗaya ya ƙulle a guri guda.

“Kin ga, ba na ciki da iskanci da rainin wayau! Kar ki kuskura ki ce za ki kawo min banzar uzurin baki da lafiya. Ƙazanta, shi ne babban abinda zai sa a fara jin kanmu da ke, ba na son ƙazanta ko kaɗan, ba na ƙaunar ƙazama, ko na minti biyar ba na jin zan iya jure zama kusa da wacce na san ba ta da tsafta. Minti ashirin na baki ki tabbatar kin gyara ko ina ƙalƙal. Kina ji na?”

Yayi mata tambayar cikin tsawa.

“Eh! eh! eh na ji. Kayi haƙuri. Zan kiyaye”

Ta amsa bakinta na rawa.

Ficewa yayi daga ɗakin gaba ɗaya ya koma can ɗakin baƙi. Ransa a ɓace, in banda ƙazanta irinna Fatima ko singiletin da ya cire ya aje a gefen gado ta kasa kawar da shi daga gurin balle tayi tunanin wankewa? Da alamun akwai wasu notocin kanta da basu gama ɗauruwa da kyau ba, shi kuwa zai ɗaure mata su gam don ta san shi ba irin sakarkarun mazannan bane da suke jure ƙazanta daga matayensu.

Ko da ta gyara ɗakunan zuwa falo ya leƙa bayan ya dawo sallar magrib babu wani walwala a fuskarsa.

Abincin Fareeda ya ɗauka da yara ya miƙa mata, ya kwaso mata waɗancan kulolin na jiya. Ya dawo ya zauna a falo yana ta daddana wayarsa. Ko abincin da ta jera mishi cewa yayi sai yayi sallar isha’i zai ci.

Haka ta rakuɓe gefe ɗaya, kallo ɗaya za’ayi mata a gane a ɗarare take. Allah Allah take gobe tayi a kawo mata magungunan da ta siya ta fara amfani da su, don ita a ganinta waɗannan matsaloli guda biyu su ne manyan dalilan da suka sa Mukhtar ya juya mata baya a lokacin da ya kamata ace yana tsananin tarairayarta.

Haka suka kwana zuciyoyinsu babu daɗi. Kamar yadda yayi sammakon ficewa gurin aikinsa jiya, yau ma haka ya fice bayan ya karta mata kashidin saura tayi lattin abinci, ko kuma ya dawo ya tarar bata gyara ɗaki ba.

Ƙarfe ɗayan rana aka kira ta a waya, kwatancen gidanta aka tambaya, tana faɗi babu ɓata lokaci cikin minti talatin ɗan saƙo yakai mata magungunanta ta bashi kuɗin mota.

Jiki na rawa ta shige can ƙuryar ɗaki ta kira Farida da Zainab Maman Mujaheed a waya suka yi mata cikakken bayani na yadda za tayi amfani da maganin biyu.

Saboda zaƙuwa tun a wannan lokacin ta fara amfani da su, sai fatan dacewa. Bata yi kuskuren yin lattin abinci kamar jiya ba, ƙarfe biyu saura kwata taje ƙofar Fareeda ta dangwara kuloli biyu a bakin ƙofar sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi sau biyu tai wucewarta, ba tare da damuwar Fareedan ta ji ko bata ji ba.

Inda Allah ya taimaki Fareeda a lokacin suna zaune a falo ita da yaranta. Ta jika musu Conflakes a kofi suna sha, taji wannan ƙwanƙwasa ƙofar.

Ko da taje ta buɗe sai kulolin ta gani. Tsaki taja ta kwashe su tayi ciki, kan dining ta ajiye, tana buɗe babbar kular taga farar taliya, a ƙaramar kuma miyar tarugu ce da aka soya ta ɗanye-ɗanye.

Rufe kular tayi ta koma gurin ƴaƴanta ta cigaba da kallon da take yi.

*****

Da ɗoki sosai a tattare da Mukhtar ya koma ɓangaren Fareeda. Ko a mugun saƙa irinna tunani bai taɓa kawowa a ransa matsala makamancin ta rannan za ta maimaitu tsakaninsa da Fareeda ba. Sai ga shi an kuma, washe gari ma haka aka sake maimaitawa.

Izuwa yanzu sosai lamarin ke bashi tsoro da kaɗa mishi ƴaƴan hanji. Duk tunaninsa ya ƙuƙe ne akan ta yaya za’ayi haka? A gurin Fatima lafiyarsa ƙalau a gurin Fareeda ba lafiya ba.

Me yake faruwa? A ina matsalar take? Ganin Fareeda ko a jikinta bata nuna lamarin ya dameta ba yasa shi kasa sanar da ita a gurin Fatima fa ba ya fuskantar irin wannan matsalar. Kawai sai ya bar zancen a cikinsa, zuciyarsa cike da tunanin wani irin al’amari ne wannan mai sarƙaƙiya?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rabon A Yi 22Rabon A Yi 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×