Skip to content
Part 24 of 33 in the Series Rabon A Yi by Fareeda Abdallah

Kafin a saukar da ko wace irin cuta, sai da aka fara saukar da maganinta. Sai dai idan bawa baiyi dace da magani ba sai ayi ta wahala, a faɗa cikin ƙunci da ƙaƙanikayi.

Cikin kwanaki biyu da Fatima ta fara amfani da magungunan da ta karɓa babu abinda za ta ce sai godiya ga Allah. Duk da basuyi arangama da Oga Mukhtar ba, ita kanta tana ji a jikinta e lallai fa an samu gagarumin sauyi.

Zo kuga baki har kunne, duk wani ƙunci da baƙin cikin da maganganun Mukhtar suka dasa ma zuciyarta ta kawar da su gefe ɗaya, jira kawai take su gamu yasha mamaki.
Kwanaki shida bayannan ranar girkinta ne. Mukhtar ya waiwayeta ba don tunanin jin daɗi ba sai don kawar da matsuwar da yake ciki, tunda ɓangaren Fareeda dai har lokacin sifili ne.

E lallai fa Mukhtar ya sha mamaki, har ma fiye da yadda Fatima ta so ya kasance. Mukhtar ya amsheta cikin haba-haba da rawar jiki, an kuma an sake kumawa an kuma ƙara kumawa. Ita kanta duk wannan zafi da raɗaɗin da take ji ko kaɗan bata ji ba.

Bayan kammaluwar komai bai juya mata baya ba, kamar yadda ta daɗe tana muradi, ruƙunƙumeta yayi a ƙirjinsa suna sauke ajiyar zuciya. A sannu a hankali kuma wani nannauyar barci yayi awon gaba da su, zuciyar Fatima cike taf da wani irin matsanancin jin daɗi da alfaharin da ko kaɗan bakinta bazai iya baiyanawa ba.

Ita kaɗai ji take kamar tana yawo a sararin samaniya saboda tsabar shauƙin soyayyar Haskenta.

A wannan rana, hatta sallar asubah ita da shi basu samu sararin gabatarwa ba sai ƙarfe bakwai da rabi na safe. Saboda tsabar soyayya ma a tare suka yi wanka, suka ɗauro alwala. Ta bi bayanshi yaja su sallar asubahi.

Yana kishingiɗe akan kujerarta mazaunin mutum uku wani nishaɗi na ratsa zuciyarsa ta kawo musu abin kari. Nan gefenshi ta zauna, ta ɗora kanta a kafaɗarsa suna karyawa cikin wani irin salo da soyayyar da ta ci burin ya faru tun a kwanaki ukun amarcinta, amma ko yanzu ma bai zo a makare ba.

“Fatina”
Mukhtar ya kira ta da sunan soyayyar da tun darenta na farko bai sake faɗa mata ba.

“Na’am Haskenah”
Ta amsa a hankali haɗe da sakar mishi fari da ido. Sai kuma ta ƙalle mishi ido ɗaya ta ƙara da cewa,

“Ya aka yi? Ko kana buƙatar ƙari ne?”

Farantin dankalin turawar da ke ajiye a gabansu ya kalla, sai yaga ko rabi basu ci ba. Nan take zuciyarsa ta tunano mishi ƙarin da take magana akai, sai yayi murmushi kawai, ya mayar da fuskarsa kalar zai mata magana mai muhimmanci ya ce,

“Wai ni ya aka yi haka ne? A gurin Fareeda fa ba na iya taɓuka komai. Anan ne kawai nake namiji lafiyayye. Ko kin san abinda ke janyo irin wannan matsalar?”

Wani irin tsallen baɗake zuciyarta tayi daga gabas zuwa yamma. Ta zazzaro idanu warwaje tana kallonshi tana jujjuya maganarsa a cikin zuciyarta, sai kuma tayi tsam ta ƙura ma guri ɗaya idanu, banda luguden daka babu abinda ƙirjinta ke yi.

“Kin yi shiru, ki ce wani abu mana. Ni kam na ma kasa tattauna maganar da Fareeda saboda ban san ta inda zan fara faɗa mata anan ina iya kusantarki ita ce ba na iya komai da ita ba.”
“Uhmmmmm!”

Taja wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Lokaci ɗaya kuma tayi narai narai da idanunta ta tara ƙwallah. Hannayensa biyu ta riƙo a cikin nata, tayi ƙasa ƙasa da murya sosai da wani irin matsanancin damuwa a fuska da muryarta ta ce.

“Haskenah! Ka roƙi Fareeda, ka roƙe ta. Idan ka damu da rashinta ka roƙe ta, idan ta kama ko durƙusa mata a ƙasa ne ka durƙusa, ka tabbatar mata da cewa aurena da kai ba shi zaisa ka juya mata baya ba. Idan za ka iya ma kayi mata ƙaryar kai fa tunda ka auro ni baka taɓa kusantata ba. Idan ta so, za ta baka maganin ciwonka, daman ita ta ƙirƙiri cutar da gangar ka ga kuwa makarin ciwon na hannunta…”

“Ban… gane..ba. Me kike nufi?”

Ya tambayeta bakinsa na rawa.

Hannayensa ta sake ta zuba tagumi da hannu bibiyu.

“Ta ya zan faɗa maka sirrin da daga ni sai ita sai Allah muka sani? Ko ni da ta san juyin juya hali irinna ƙaddara zai kaimu ga matakin da zan zamo matarka baza ta taɓa faɗa min wannan maganar ba.”

Cak ya ɗaga ta daga kan kujera ya ɗaura kan cinyarsa. Ya kamo fuskarta ya riƙe cikin tafin hannayensa. Ya ƙureta da kallon soyayya mai ratsa masoya na tsawon wasu daƙiƙu, sai da ya tabbatar ta nuna luguf, jikinta ya mutu murus, sannan ya fara magana a tausashe, da wata irin siga ta matasan da suka ƙware a soyayya.

“Fatina. Kin san ina bala’in son ki ko?”

Saboda yadda jikinta ya mutu ta kasa buɗe baki ta amsa mishi, sai kai ta iya ɗagawa.
“Ashe a duniya akwai wani sirri da za ki iya ɓoye min? Na zaci ni ɗin abokin sirrintakanki ne? Akwai wani abu ɓoyayye da yake tsakaninmu ne?”

Nan ma dai kai ta iya kaɗa mishi alamun babu.
“To faɗa min! Kin ji ƴar matata? Rabin raina, masoyiyata, abar ƙaunata. Kogin zuma ta…”
Kwantar da kanta tayi a hankali ta fara cewa
“Fareeda, ta taɓa rantse min da girman Allah duk ranar da mijinta yayi gangancin yi mata kishiya za tayi amfani da maganin da bazai ƙara samun damar da zai kusanceta ba.

Kai baka yi mamakin irin kwanaki casa’in casa’in ɗin da tai ta ƙara mana ba? Ta ƙara ne saboda ta san ko ka je can ɗin babu wani abu da za ka samu daga gare ta…”

“Fatima, kar ki faɗa min ƙarya fa”

Ya katse ta muryarsa na bayyana shiga cikin gagarumin tashin hankali. Sai kuma ya sake ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta a rikice.

“Na san ke aminiyarta ce, baza ki ƙirƙiri ƙarya ki faɗa min don kawai kiyi mata sharri ba. Faɗa min gaskiya don Allah, ki ce min wasa kike min. Ta ina Fareeda za ta sami irin wannan maganin?”

“Hmmm! Kana tantama ko? Kai baka yi mamakin yadda duk matsanancin kishi irinna Fareeda ko kaɗan bata tashi hankalinta jin za muyi aure ba? Ka tambayi masana magunguna ka ji, tabbas akwai maganin da mace za ta matsa a al’aurarta daga zaran namiji ya nemi kusantarta zai kwanta ligif.”

Tsam ta tashi daga jikinsa ta shige cikin ɗakinta, ta barshi zaune cikin zazzafan tunani.
Hannayensa biyu yasa ya tallabe gemunsa. Ya ƙanƙance idanu ya ƙura ma guri ɗaya idanu tsawon lokacin da shi kanshi bazai ce ga iyakarsa ba.

Tunani yake yi, zuciyarsa cike da ƙila wa ƙala. Ya kasa samun matsaya guda ɗaya. Idan wani sashen na zuciyarsa ya fara kore maganar Fatima, da saurin gaske eani sashen yake ƙara tabbatar masa da gaskiyar zancen, idan ya tuna yadda Fareeda take ta ko in kula da al’amarinsa tun ɓullar zancen zai aure ta har zuwa sa’adda aka yi auren.

Bayan kuma shi kanshi shaida ne kan irin matsanancin kishin da take da shi. Da walakin goro a miya, lallai biri yayi kama da mutum.
Akwai alamun gaskiya dumu-dumu a cikin wannan maganar. Idan ya ƙara tuna ko a yanzu, shi kaɗai yake nuna damuwarsa idan lamarin ya sake maimaituwa. Ko sau ɗaya bazai iya tuna wani lokaci da yaga damuwa a fuskar Fareeda kan lamarin ba.

Karyawan da basu ƙarasa yi ba kenan. Ita tun da ta shige cikin ɗaki bata fito ba, shi kuma da yake ya gama shirin tafiya gurin aiki daga nan bai koma cikin ɗaki ba. Wayarsa da makullin mota ya ɗauka ya fice zuwa ɓangaren Fareeda.

A hanya sai saƙe-saƙe yake yi, ransa ya ɓaci sosai da jin wannan magana da ya gama haƙƙaƙe ma zuciyarsa gaskiya ne. Amma sai yake ta tunanin yai mata magana ko kar yayi mata magana? A ƙarshe dai sai ya yanke shawarar ya zura mata ido yaga iya gudun ruwanta, zai ga cikin su biyun wa zai fi shan wahala da jigatuwa? Shi da yake da wata matar ko kuwa ita da tayi ma kanta sagegeduwa?

Da wannan shawarar yayi ƙoƙarin faɗaɗa fuskarsa da murmushin yaƙe sannan ya buɗe ƙofar ya shiga bayan yayi sallma an amsa mishi daga ciki.

Tana zaune a tsakiyar ƴaƴanta tana biya musu ƙulhuwallahu ahad! Amsawa suke da hausarsu da bata fita tana sake maimaita musu.

Sun yi kwalliyarsu tsaf, gwanin ban sha’awa da burgewa. A guje yaran suka tashi suna mishi oyoyo, bayan ya zauna kan kujera suna jikinsa ta gaishe shi.

Idanunshi na kanta ya amsa, wani irin kallo yake bin ta da shi tun bayan shigowarsa. Kallon da ya jefa ta cikin tsarguwa, har sai da ta ce,

“Abee, irin wannan kallo Allah yasa dai ba laifi nayi ba…”
“Uhmmm! Laifi dai Fareeda? Wani labari ne na jiyo da ya ɗaga min hankali.”
Ya amsa yana sake ƙure ta da kallo.

“Tooo…! Allah ya kyauta.”

Ta amsa fuskarta ɗauke da yanayin jimami.

“Fareeda, wai da gaske saboda kishi mace za ta iya yin abinda zai hana komai ya shiga tsakaninta da mijinta?”

Ya tambayeta.

“Kishi fa ka ce Oga?”

Sai ta ɗanyi murmushi.

“Kishi halitta ce da Ubangiji yayi a cikin zukatanmu. Ko wace mace tana da kishi, sai dai na wata ya fi na wata. Baka taɓa jin labarin matan da saboda matsanancin kishin da suke da shi suna halaka mazajensu sannan su halaka kansu ba? Amma da yake komai na duniya yana da linzami, linzamin baƙin kishi mace ta tsananta addu’a, sai kaga komai ya zo mata da sauƙi. Allah dai ya ƙara sassauta mana.”

“Hmmm! Ameen”

Ya amsa a hankali, a zuciyarsa yake ta auna maganganunta, bai hangi komai a ciki ba face ƙara samun gamsuwa da maganar Fatima.

Bai sake wata maganar ba yayi mata sallama ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da mamakin wannan al’amari.

Ita kuwa ko bayan fitarsa bata ɓata lokacinta gurin yin wani tunani ba. Amsa ta bashi da zuciyarta ɗaya ba tare da tunanin da wata a ƙasa ba. Hidimarta ta cigaba da yi ita da ƴan ƴaƴayenta da ko kaɗan ba su da rigima ko ɗaga hankali irinna wasu ƴanbiyun.

Da ƙarfi ta ƙwanƙwasa ƙofar, ta haɗa da buɗe murya ta rafka sallama, fuskarta cike taf da murmushi.

“Alaikissalam! Ina zuwa.”

Ta jiyo muryar Fareeda ta amsa daga can ciki.

Sai da ta kintaci ana daf da buɗe ƙofar sai ta buɗe murya ta fara waƙar
“Hooohotihoooo, hotihoooo, hotihoooooo, hotihoooo. Baaaaa ki da amfaniiiiii, sai dai zaman ƴaƴaaaa, ko in ce zaman hoooootihooooo hotihoo.”

Da mamaki Fareeda ta ɗaga idanu tana kallon Fatima da har lokacin da ta buɗe ƙofar bata daina rera wannan waƙa da ƙarara yayi kama da habaici ba.

“Lafiya dai ?”

Ta jefa mata tambayar da ɗaurarriyar fuska.

“Hotiho, au Fareeda uwargida. Me kika ce?”

Fatima tayi maganar tana wani irin dariya mai bayyana isgili da tsantsar wulaƙantarwa.
Wani kakkausan kallo Fareeda ta watsa mata, ta mayar da ƙofarta za ta rufe da saurin gaske Fatima tasa hannu ta tare.

“Saurin me kike yi Hajjaju? Abincinki na kawo miki, ki ci, ki sha, kiyi ƙaton kashi. Ko kina da wani amfanin da ya wuce wannan a gidannan Hotiho?”

Wani kakkauran miyau ta haɗiye, ta lumshe idanunta tana addu’a a zuciyarta haɗe da ƙoƙarin danne ɓacin ranta, ba ta son biye ma Fatimar, ita a tsarinta ko da miji bata cika son ta dinga yawan cece kuce ba balle kishiya. Tun rannan da suka yi a gaban mai wanki da ganin irin yadda Fatima ta nemi juya zancen bayan dawowar Mukhtar yasa ta shan alwashin in sha Allah ta bar ƙara biye ma Fatima suyi cacar baki. A karo na biyu ta sake turo ƙofar za ta rufe.

“Ke Hotiho, ki saurara min. Wallahi Tallahi idan kika kulle ƙofar nan komawa zanyi da abincina…”

“Kin daɗe baki koma da shi ba. Useless”

Baam ta mayar da ƙofarta ta rufe haɗe da jan dogon tsaki.

Tana jin muryar Fatima tana zazzaga tsiya a bakin ƙofar haɗe da kiranta da munanan sunaye, har tana cewa taje dai ta bincika cikin su biyun wacece mare amfani a gidan? Akwai ma ƙatotuwar hotiho irinta? Wacce sam ba ta iya amfanawa miji komai sai dai ta cinye mishi abinci…

Waɗannan jimlolin na ƙarshen maganganunta, su suka tsaya ma Fareeda a zuciya. Tayi tsai a tsakiyar falon tana tunani.

Sai kuma maganar da Mukhtar yayi mata da safe ya faɗo mata arai. Ƙirjinta ne ya buga daram!! Wani jiri da ya fara ɗibanta yasa da saurin gaske ta dafa kujera, a hankali ta laluba ta zauna.

“Kar dai ace Mukhtar ya faɗa ma Fatima ba ya iya komai da ni?”

Tunanin hakan kawai yasa hawaye gangarowa daga idanunta.

“Amma kuwa wallahi da ya gama da ni, kuma in dai yayi hakan bazan taɓa yafe masa ba. Zai dawo gidan ai, zan ji ta inda maganganunta suka samo asali, babu rami me ya kawo maganar rami?”

Daƙyar ta iya rage damuwar maganar a cikin ranta ta kwanta lamo akan kujera, ba ta son saka ma kanta damuwa. Ƙaramin ciki ne da ita, ba tun yanzu ba tasan ba ƙaramin illah damuwa ke haifarwa ga mace mai ciki ba.

Tana wannan kwanciyar sai ga su Sayyid sun fito daga ɗakinsu, hannun Shahid riƙe da sabon ƙwallo, ɗaya daga cikin tarkacen kayan wasan da Hajiya ta haɗo su da shi.

Har sun fara buga mata anan cikin falo sai ta buɗe musu ƙofa ta ce su buga anan harabarta. Ɗan sakaya ƙofar tayi ta koma kan kujera ta kwanta, a hankali ta fara addu’ar kau da damuwa da gaggawa a zuciyarta, a hankali ta dinga jin sauƙi sauƙi har wani daddaɗan barci ya fara kawo mata farmaki…

<< Rabon A Yi 23Rabon A Yi 25 >>

3 thoughts on “Rabon A Yi 24”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×