Skip to content
Part 19 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Ɗakin yake kallo, babu abinda bai hargitsa ba, wanda zai fasu ya fasa. Wanda zai iya karyawa ya karya. Hannun shi duk ya fashe. 

Zafi-zafi yake ji da raɗaɗi da ba zai iya misaltawa ba, ƙirjinshi yayi nauyi kamar an ɗora dutse. Sam baya jin zafin ciwukan da ke hannunshi. 

Abu ɗaya ke mishi yawo cikin kai yana ƙona mishi zuciya “*EL”. Tun akan abinda Abba yai musu ya daina yarda da mutane. 

Ba kalar kokwanto da tantama da baiyi ba akan Yumna. Zuciyarshi ta ɗauki watanni da soyayyar ta kafin yardarta ta samu wajen zama. El a wajen shi wani ɓangare ne da bai taɓa tunanin ɗora ma ayar tambaya ba. 

Ba zai manta ciwon da ya ji lokacin da Mami tai ƙoƙarin nuna mishi abinda ƙaunar El ta hana ya gani ba. A ranshi ko da yaushe ya ganshi da Zulfa tunani ɗaya yake zuwa. 

“El ne. Zai kare mutuncin Zulfa da farin cikin shi in buƙatar hakan ta taso.”

Lamp ɗin da ke fashe a gabanshi ya ɗauka ya sake jefata jikin bango. Ba kayan ɗakin yake son farfasawa ba, ba komai na ɗakin yake son birkitawa ba. 

El yake son birkitawa sai ya faɗa mishi dalilin da zai yi musu haka. Bai ga rayuwar su a gurgunce take ba? Bai yi tunanin har yanzun ƙoƙarin fahimtar inda rayuwa ta ajiye su suke ba? 

Daga rasuwar Sajda yasan akwai abinda ya canza na rayuwar shi da ba zai taɓa komawa dai dai ba. Daga rasuwarta duk sa’adda ranshi ya ɓaci abu na farko da hannunshi ya kai kusa da shi yake lalatawa . 

Yadda yake ji gab yake da jima kanshi ciwo, hakan yasa shi soma kiran sunayen Allah duk wanda yazo mishi kamun. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…..”

Ta fito, ita ya ci gaba da jerowa yana jin da kaɗan-kaɗan hankalinshi na dawowa jikinshi. Wayarshi da sam ya manta tana jikinshi ya ji ta soma ringing.

Lumshe idanuwanshi yayi yana sauraran kiɗan, sanin kowa ke da shi kawai ya kara nutsar da shi. Hannu yasa aljihunshi ya fito da wayar tare da ɗagawa ya kara a kunnenshi. 

Cikin sanyin muryarta tai mishi sallama. Ya amsa muryarshi a dakushe.

“Are you ok?”

Ta tambaya da sauri, yana mamakin yadda a yanayin muryar shi kawai take gane wani abu na damunshi. Girgiza kai ya ɗanyi da yake jin yana mishi ciwo. 

Kamar ta ganshi ta ɗora da. 

“Ka faɗa min baka jima kanka ciwo ba. I can’t……”

“Ki daina damuwa da ni, kin ganni a tsaye a ɗakina, kina asibiti Yumna, damuwata zata jira har ki samu sauƙi.”

“Bansan yadda zan daina damuwa da kai ba. Za mu yi faɗa in ka sake ce min haka, matsalata taka ce, kai ka faɗa da bakinka, yaushe zaka yarda matsalarka ta zama tawa?”

Sauke numfashi yayi.

“Ƙirjina zafi yake sosai, bansan me yasa abubuwan da ke faruwa suke faruwa ba, bazan miki alƙawari matsalata zata zama taki ba. 

Saboda na ɗauki alƙawari da yawa ban cika ba, alƙawari ƙarami na kasa cikawa…..”

Ya ƙarasa yana jin kamar duka duniya ta taru a saman kanshi. Cikin sanyin murya Yumna ta amsa shi da, 

“Ba kasa cika alƙawarinka kayi ba, wasu lokutan muna ɗaukar alƙawura da suka shafi ƙaddara. 

Muna alƙawari kan abinda bamu da iko da shi, ka daina ganin laifinka kan haka, yau rana ce da za mu yi farin ciki ko na minti goma ne. 

Yau rana ce da ya kamata kai farin ciki koya yake, ka ajiye matsalar kowa a gefe.”

Girgiza kai yayi. 

“It’s bigger than you think, matsalar ba zata ajiyu ba….. Ki huta, zanzo when i can in ganki…”

Sauke murya tayi. 

“Ka kula min da kank. Akwai matsalar da ta girmeka, ka bar ma Allah, Shi zai baka mafita, auren mu misali ne.”

Hannun shi yasa ya murza goshin shi. Bai ce komai ba har ta kashe wayar, ko da ba damuwarshi ya faɗa mata ba, ya ɗan ji sauƙi-sauƙi. Muryarta ta sa mishi nutsuwar da zai iya fita wajen ɗakin ba tare da ya sake fasa wani abu ba. 

Tsallake kayan ɗakin yayi, ya kama handle ɗin kofar ya buɗe. Tayyab ya gani zaune a gefen ɗakin ya haɗa kanshi da gwiwa. A hankali ya janyo ɗakin ya rufe. 

“Tayyab?”

Ya kira cike da tambayar me yake yi zaune a bakin ƙofar ɗakin. A hankali ya ɗago da idanuwanshi da suka canza kala saboda tashin hankali ya sauke su kan dawud. 

“Me kake yi anan?”

Dawud ya buƙata yana tsare shi da idanuwa. 

“Ina buƙatar wani abu da ba sabo ba a kusa dani.”

Ya amsa shi da sanyin murya. Girgiza kai Dawud yayi yana nuna ɗakin shi da hannu. 

“Ƙofar ɗakin ne tsohon abu?”

“Kai da kake cikin ɗakin. I just need something familiar. Na gaji da sabon abu ko yaushe.”

Runtsa idanuwa Dawud yayi, ya buɗe su yana saukewa kan Tayyab. 

“Me yasa baka shigo ciki ba?”

“Bana son damunka.”

“Baka son damuna? Da gaske Tayyab? Waya faɗa maka haka abin yake tafiya? When you need me kai me n magana! Karkai wani abu stupid, kasan ina nan ai. Ko bana kusa zan zo saboda kai. 

Me ye ba zaka iya faɗa min ba? Ban ɗauki shekaru ina nuna muku za ku iya faɗa min matsalarku ba? Ko bazan iya muku wani abu ba zan saurara?”

Kallonshi Tayyab yake, yasan duk maganganun da yake faɗa, ba shi yake gayama ba, Zulfa yake faɗa ma, laifin yake ɗorawa a kanshi. 

“Yaya ba laifinka bane, karka ƙara wannan kan wanda ka ɗauka. Ƙaddararta ce ta zo da haka. 

Ba don ka kasa ƙoƙarin komai a kanta ba, i guess rasuwan Sajda ta canza mu fiye da yadda muke zato.”

Zama Dawud yayi a ƙasa gefen Tayyab, muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Bansan me zan yi ba Tayyab. Da ba El bane ciwo ɗaya zan ji da shi. Zan ɗauki matakin duk da na so akai. 

He is family…….why him?”

Shiru Tayyab ya ɗan yi, kafin ya sauke numfashi da faɗin, 

“Akwai tambayoyin da basu da amsa, duk yadda zaka duba ba zaka taɓa sanin amsar su ba, wannan na ɗaya daga ciki. 

Karka damu da ɗaukar hukunci akan Yaya Labeeb, abinda yayi ba zai barshi zaman lafiya ba, kasan shi, kasan haka.”

Wani abune tsaye a wuyan Dawud da ya kasa haɗiye wa. Ƙirjinshi yayi nauyi. 

“Bansan me zan yi ba.”

Ɗan ɗaga kafaɗa Tayyab yayi. 

“Fin rabin rayuwar mu bamu san me muke ba, kana nan, inda kasa ƙafa nan muke maida tamu. 

Zulfa na buƙatar ka, tana buƙatar yayanta, me kayi sa’adda muka rasa Abba? Kai ka fito da mu, haka Ummi, haka Sajda . Ka yarda da kanka kamar ko yaushe, mu mun yarda da kai.”

Har zuciyar Dawud yake jin maganganun Tayyab, don ya rasa ta inda zai fara. Kai ya ɗan ɗaga ma Tayyab. 

“Ni ban sani ba, bata buƙatata kamar ku tun da can.”

Ɗan murmushin ƙarfin hali Tayyab yayi. 

“Don bata nunawa kamar mu baya nufin haka. Ka je kai mata magana.”

Miƙewa Dawud yayi, ya nufi ɗakin zulfa, zuciyarshi na dokawa kamar zata fito daga ƙirjinshi. Tunda yake a rayuwar shi yau ne karo na farko da ya taɓa jin tsoron yin magana da Zulfa. 

Saboda baisan ta inda zai fara ba, baisan me zai ce mata ba, duk maganganun da yai mata ɗazu rabinsu ba a hayyacin shi yake ba, har ƙasan zuciyarshi baya jin haushinta, badony bata yi laifi ba. 

Sai dai babu wajen a zuciyarshi. Protecting ɗinta da ƙaunarta ya shafe komai, su uku suka rage mishi, yasan Tayyab da Khateeb maza ne su, akwai inda zasu kai a rayuwa da ƙaunarshi kawai suke buƙata. 

Amma zulfa har ƙarshen rayuwarta tana buƙatar protection da ƙaunar shi. A yanzun gani yake kamar ya gaza akanta. Bakin ƙofa ya tsaya, yana jin zufa na fito mishi har cikin tafukan hannun shi. 

A hankali ya ƙwanƙwasa ɗakin, muryar Mami ya ji ta ce mishi ya shigo, da sallama ya tura ƙofar ya shiga. Kwance ya ga zulfa Mami na zaune a kusa da ita. 

Kallon shi Mami ta yi, ta rasa kalaman da ya kamata ta yi amfani da su. Gaba ɗaya tausayin shi ya kamata, yau rana ce da ya kamata ace yana farin ciki. 

Auren shi aka ɗaura, bayan tarin rigingimu da tashin hankali, gani take kamar ya kamata rayuwa ta barshi ya ɗan huta ko yaya ne. 

“Allah Shi kaɗai Ya san abinda Ya ɓoye a ƙaddararku Dawud. Hanyoyin jarabawar Shi yawa gare su, Addu’a, haƙuri da rungumar ƙaddara ta kowacce fuska ne kaɗai mafita. “

Jingina bayanshi yayi da bangon ɗakin, hannuwan shi cikin aljihun wandon farar shaddarshi ta ɗaurin aure. 

“Ba baƙon abu bane a rayuwar mu ƙaddarar mu na zuwa da yanayi mai wahala. Allah zai bamu mafita….”

Kai kawai Mami ta ɗaga mishi tana miƙewa ta buɗe ƙofar ta fice daga ɗakin. Don in ta tsaya kuka zata yi. Zuciyarta ta kasa jurewa. 

Inda ta tashi nan Dawud ya zauna gefen Zulfa. Ya jingina kanshi da gadon yana jiran ta tashi daga bacci su yi maganar da baisan ta inda zai fara ta ba. 

**** 

Zaune yake cikin motarshi, ya ɗora kanshi a jikin steering wheel ɗin yana fitar da numfashi a tsanake. Ya kai mintina sha biyar da shigowa gida amma tunanin fitowa daga motar ya fuskanci Ateefa na mishi wahala. 

Bai taɓa tunanin akwai ranar da zata zo ace shi Labeeb yana tunanin shiga cikin gidanshi ba. Gidan ma da Ateefa a ciki. Lumshe idanuwanshi yayi. 

Yasan Ateefa kamar yadda yasan kanshi. Baya tunanin zata ci gaba da zama da shi. Abu ne mai wahala, sai dai kamar yadda yasanta haka yasan in ya gaya mata gaskiya tashin hankalin zai fi ɓoye mata. 

A tsakiya yake tsaye, gefe Zulfa ɗayan gefen Ateefa. Abinda ke cikin zulfa yana buƙatar uba, a halayyar Mamdud ta baya daya sani, yasan ba zai taɓa karɓar cikin da ke jikin Zulfa ta daɗin rai ba. 

Balle yanzun da ƙiris yake jira ya gogama gaba ɗaya zuri’ar Maska baƙin fentin da har rayuwar su ba zai barsu ba. Bawai don bai riga da yayi ba. Amma za su iya ɓoye abin ya tsaya iya su. 

Ƙoƙarin da yake yi kenan, komai zaizo da sauƙi in kowa ya ɗauka shi yayi cikin, zulfa zata zauna ƙarƙashin kariyarshi. Zai mutu kafin ya bari Mamdud ya sake matsowa kusa da ita. 

Zafi ƙirjinshi yake mishi cike da kuna, laifinshi ne ya shafi Zulfa, a dalilin shi ne abinda ke faruwa yake faruwa, iya adalci yayi. Rabuwa da Ateefa ciwo ne da zai ci gaba da ji har ƙarshen rayuwarshi. 

Ciwo ne da zai iya tolerating. Wulaƙantar Zulfa a idanuwan mutane ta sanadin shi ciwo ne da zai wargaza mishi rayuwa da kanta. Fitowa yayi daga motar ya nufi cikin gida zuciyarshi na wani irin dokawa da bai taɓa tunanin zata iya ba. 

Da duk takun da yake zuwa cikin gidan da rauni da kukan da zuciyarshi ke tsananta yi. Hannunshi na zufa ya kama handle ɗin ƙofar ya buɗe yana saka ƙafarshi cikin babban falon gidan. 

Yana jin kusancin Ateefa fiye da kowane lokaci, ƙarasawa yayi har tsakiyar falon da takalmanshi. Ya cire shade ɗin da ke fuskarshi ya ajiye gefe. 

Bai ji takun tafiyarta ba sai maƙale shi da ta yi ta baya. Lumshe idanuwanshi yayi yana haɗiye wani abu da ya tsaya mishi a wuya tare da ɗora hannuwanshi kan nata da ke ƙugunshi. 

Yana jin ƙamshin turarukanta sun cika mishi hanci, kwance take kan bayanshi. 

“Ka yi haƙuri na bata maka rai ko? Ka san ni El-Labeeb, kasan yadda nake kishinka, bazan iya haɗa soyayyarka da kowa ba. 

Sonka zai kasheni kafin ka haɗa min shi da na wata, I am sorry na ɓata maka rai, ka ji….”

Ta ƙarasa tana shagwaɓe mishi murya, tunda ta fara magana ya ji zuciyarshi ta tsaya waje ɗaya da wata irin nutsuwa. A da maganganunta basu taɓa mishi komai ba. 

Saboda yasan ita kaɗai ta ishe shi, ta tattara duk abinda yake so a jikin mace, da matsalolinta, da bauɗaɗɗun halayyarta, kominta yayi dai dai da nashi, bai taɓa tunanin wani abu zai canza ba. 

Yana jin yadda ta sake maƙale shi. 

“Kayi shiru ka ƙyale ni ko?”

Baisan me zai ce da ba zai lalata musu wannan moment ɗin ba, saboda yasan irinsu kaɗan suka rage musu. Sakinshi Ateefa ta yi ta zagaya ta fuskance shi. 

Sam ya ƙi bari su haɗa idanuwa, hannu ta kai ta kama haɓarshi tana nazarin fuskarshi, tana son ganinshi cikin manyan kaya. 

Farar shaddar ta mishi kyau sosai, sai dai ranakun Juma’a ne kawai in zai je masallaci in yana gida kenan take ganinshi da su. 

“Ka yi kyau.”

Ta faɗi, murmushi yai mata da bai kai cikin idanuwanshi ba, yana ƙin yarda har lokacin su haɗa idanuwa. Don haka ta sa hannuwanta duka ta riƙe fuskarshi. 

Idanuwanta ta sauke cikin nashi, har yau tana mamakin kalar baƙin ƙwayar idanuwanshi. Zuciyarta ta ji ta doka da yanayin da take gani a cikinsu. 

“Me yasa kake kallona kamar kana min bankwana?”

Wani yawu ya haɗiye,maƙoshin shi ya ji ya bushe, ture hannuwanta yayi daga fuskarshi yana nufar ƙaramin fridge ɗin da ke ajiye a falon ya buɗe shi ya ɗauko ruwa ya sha. 

Yana maida numfashi, sannan ya juya ya kalli Ateefa tsaye tana kallonshi. Ƙarasawa yayi ya kama hannunta yana janta. 

Babu musu take binshi har wajen kafar benen, suka taka har sama yana riƙe da hannunta, hanyar part ɗinsu su biyun ya nufa da ita. Ya tura ƙaton bedroom ɗin nasu suka shiga. 

Sai lokacin ya cire takalmanshi. Ya jata kan gadon. 

“Kai min magana El-Labeeb…..”

Bai ce komai ba ya jata suka kwanta. 

“Just hold me……. Don Allah ki yi shiru Tee. Bana son yin magana.”

Shirun ta yi tana kwanciya a jikinshi ta zagaya hannunta tai hugging ɗinshi, tana kallo ya rufe idanuwanshi. 

“Girki fa zan ɗora tunda ba zamu gidan ba.”

“Tee……..”

Ya ja sunanta, tasan yanayin muryar, tai mishi shiru yake nufi, shirun ta yi tana wasa da yatsunta kan fuskarshi, tana kallon mutumin da ta miƙa ma yardarta da zuciyarta. 

Mutumin da ta ba dama ya canza komai na rayuwar ta, sauke numfashi ta yi tana fatan abinda ke cikinta ya fito da kamaninshi sak. 

Tasan akwai abinda yake ɓoye mata tun jiya, akwai abu mai girma da zai faru dasu, har ko ina na jikinta tana jin tsoron abinda zai rabata da shi. 

Shi ne mutum na farko a rayuwarta da ya nuna mata tsantsar so, kuma shine kaɗai a duniya da ya rage mata, wanda ya karɓeta da ƙaddarar da ke tattare da ita ba tare da ƙyamata ba. 

“Bana so in rasaka, kai kaɗai ne abu mai ma’ana a duniyata……”

Ta ƙarasa maganar muryarta cike da raunin gaske da yake ji har ƙasan zuciyarshi. Ya hanata magana ne saboda yana buƙatar kusancinta fiye da jin maganganun da zasu ƙara mishi damuwa. 

Yana son jinta kusa da shi saboda yana jin agogon lokacin da ya rage musu kafin komai ya birkice yana wucewa da gudu. Buɗe idanuwanshi yayi ya sauke shi kan fuskarta. 

Yana tsoron abinda zai zama babu ita, ita ce sanadin haɗe El-Maska da El-labeeb waje ɗaya, ita ce sanadin ɓacewar El-Maska da yake jinshi kusa-kusa daga jiya zuwa yau. 

“Karki sani in faɗi abinda ban shirya ba, kibar min moment ɗin nan, ina buƙatar shi fiye da zaton ki.”

Ya faɗi yana kallonta sosai, yana kallon yadda take ware manyan idanuwanta da yake so kan fuskarshi. 

“I am scared……. Na kasa shaking cewan komai zai tarwatse mana.”

“Roƙonki fa na yi. You know i can shut you up……”

Ya faɗi yana haɗe space ɗin da ke tsakaninsu, yana zuba mata idanuwanshi da wani yanayi mai zurfi da ya sata runtse nata idanuwan babu shiri. 

“Good……”

Ya faɗi yana zame ɗankwalin da ke kanta, tare da sa hannu ya hargitsa gashinta da ke gyare, yafison ganinta hakan, nazarinta yake yana ƙoƙarin haddace duk abinda yake so tare da ita. 

Abin da yasa ya fara sonta, abinda yake burgeshi tattare da fuskarta, sauke ajiyar zuciya yayi. Ko Zafira ta fi Ateefa kyau shi ya sani. Akwai mata da yawa da suka fita komai da suka mace akanshi. 

Amma ita ɗin yadda kyanta yake a zuciyarshi ba zai misaltu ba. 

“You are perfect…..just for me Ateefa. “

Ya faɗi a hankali yana jin ɗacin abinda Mamdud yai mishi fiye da koyaushe. Ya ɓata rayuwa da dama, hannu yasa kan cikinta yanajin ɗan tudun da yayi. 

Can ƙasan zuciyarshi yana fatan Ateefa zata yafe mishi ko don abinda ke cikinta. Ƙarar wayarshi ya gauraye ɗakin , sai da zuciyarshi tai wata irin dokawa saboda yasan Asad ne ko Anees. 

Hannunshi ya cire daga kan cikin Ateefa da ta buɗe idanuwanta tana kallonshi, ya kai hannu cikin aljihunshi ya zaro wayar ya duba. Asad ne. 

Ɗagawa yai ya kara a kunnenshi. Ya ɗan daƙuna fuskarshi da mamaki jin dariyar da Asad ya soma tarar shi da ita. 

“Asaad?”

Ya kira cike da tambaya. Dariya Asad ya ci gaba da yi kafin ya ce, 

“Bansan me yasa mukai mamakin cikin jikin Zulfa ba, ashe har da wani jwan a waje. Well ka zo gida ka ɗauki ɗanka.”

Miƙewa Labeeb yayi babu shiri ya ce, 

“Wait…. What???”

Dariya Asaad ya sakeyi. 

“Ka jini ai sweet Yaya….. Ɗanka zaka zo ka ɗauka gashi nan an aiko. And kaɗan yi sauri saboda Mummy na hanya. Kasan me zuwanta yake nufi……”

Buɗe baki Labeeb yayi, ya ji Asaad ya kashe wayar, zufa ke fito mishi ta duk wata ƙofa da ta samu. A rikice ya sauko daga kan gadon da wayarshi a hannu yana kaiwa da kawowa. 

Yana son fahimtar abinda Asad yake faɗi, ɗanshi ya ce… Ta ina ya samu ɗa. Babu yadda za ayi ace ɗanshi. Dafa shi ya ji Ateefa ta yi don ta masa magana ya kai sau goma bai ji ta ba. 

“Wai me yake faruwa? Kana tsorata ni fa.”

Kallonta kawai yayi, shi kanshi a tsoracen yake. Cikin kanshi yake jero possibilities na yiwuwar maganar da Asad ya faɗi, amma ya kasa. ‘Yan matan da ba shi da lokacin riƙe sunayensu yake ƙirgawa.

Shekaru uku kenan.

“No damn way…… No!”

Kama shi Ateefa ta yi ta girgiza shi cikin hargowa ta ce, 

“Wallahi ina gab da yin komai in baka faɗa min kome yake faruwa ba El-Labeeb!”

Ture hannuwanta yayi da sauri ya nufi ƙofa ya buɗe. Bin bayanshi tayi. 

“El-Labeeb……. El-labeeb!”

Ko juyowa bai yi ba, haka ta ci gaba da bin bayanshi, da gudu yake sauka daga steps ɗin benen, har ya sauka daga falon. Sa’adda ta ƙarasa har ya kai ƙofa ko takalmi babu a ƙafarshi. 

Dafe kai Ateefa ta yi tana jin kamar ta rusa ihu. Da gudu ta koma sama tana nufar ɓangarenta, changing room ta nufa ta buɗe closet ɗin kayanta, doguwar rigar da ta fara cin karo da ita ta ɗauko ta cire kayan da ke jikinta ta saka. 

Ta ɗauki mayafin ta naɗa a saman kanta, takalmi ta ɗauko flat ta saka bata damu da ko kusa da kalar kayanta baiyi ba. Ta fito. 

A bedroom ta ɗauki mukullin motarta, Da sauri ta fito ta sauko ƙasa ta ɗauki motar ta fice. Cikin kanta ta ɗauka Labeeb gidansu ya nufa don haka ta rufa mishi baya. 

Ta gaji, duk abinda zai faru sai dai ya faru, in har yadda take ji a jikinta aurenta na kan layi, ya kamata tasan meke faruwa.

****

Wata irin gigitacciyar ƙara Zulfa ta saki tana miƙewa, Dawud da ke kusa da ita ya riƙeta , amma gaba ɗaya ta ruɗe 

“Zulfa ki nutsu, kalleni ki ga, ina nan, babu abinda zai sameki….”

Yake faɗi yana girgiza ta yana so ta kalle shi, ko ina na jikinta ɓari yake yi. Gam ta riƙe hannunshi tana kuka mai cin rai. 

“Zulfa ki kalleni don Allah…. Babu abinda zai same ki, ina nan.”

Kai take ɗaga mishi tana sake riƙe hannunshi. 

“Yaya ka yafe min……. Don Allah ka yafe min ….. I hate myself.”

Ta ƙarashe tana sakin sabon kuka, riƙota yayi jikinshi yana jin kamar ya saka ihu saboda ƙunar zuciya. Me yasa Labeeb zai tarwatsa su haka. 

“Na yafe miki zulfa. Don Allah ki yarda dani…. Saboda me zan ji damuwarki a bakin El? Ban baku damar da zaku iya faɗa min matsalarku bane?”

Ya tambaya yana kallonta, abin na faruwa, yana shiga ɗakinshi yasan bai riƙeta a zuciyarshi ba, ƙaunarsu ta wuce na su yi mishi laifin da zai kasa yafe musu. Allah zai ci gaba da roƙon ya yafe mata. 

Girgiza mishi kai ta yi. Tana shessheka take faɗin, 

“Ka bamu yaya, wallahi ka bamu fiye da haka.”

Kai ya ɗaga yana hugging ɗinta a jikinshi, yana tsanar kukan da take da duk wani abu da yake da shi. Ɗumin jikinta yake jin ya wuce normal. Yasa hannu ya taɓa wuyanta. 

Zazzaɓi ne mai zafi a jikinta, da sauri ya ɗagota, yana duddubata. 

“Ina takardan asibitin da kuka dawo da shi?”

Ya tambaya, Yana sa hannu ya goge mata fuskarta.

“Bana son kukan nan zulfa. Baki da lafiya.”

Kai ta ɗaga mishi, tana ƙara sa hannu ta goge fuskarta, ya yafe mata, amma kunyar shi da muzantar da ta yi abune da zai zauna tare da ita har ƙarshen rayuwarta. 

“Yana wajen Mami, na sha maganin da aka bani.”

Sake kai hannu yayi ya taɓa jikinta ya ji shi da zafi. 

“Kina son maganar? How it……”

Kasa ƙarasawa yayi don amai kawai maganar ke shirin saka shi. Da sauri ta girgiza mishi kai alamar a’a. Kwanciya ta yi ta ja bargon da ke kan gadon tana rufe jikinta har fuskarta. 

In ta ce ga yadda abinda ya faru ƙarya take, sai dai tasan in kasa laifin za a yi zata ɗauki 80, Mamdud ya ɗauki 20. Babu inda akace ta ɗauki ƙafarta ta je gidan shi. 

Babu inda aka ce ta keɓe daga ita sai shi a waje. Ta kowacce fuska ƙafa ta sa tai fatali da darajarta ta ‘ya mace, tai watsi da dokokin Allah. 

Ba ƙaramin dace tasan ta yi ba, da Allah yake jarabtarta, wataƙila don ya wanke mata zunubanta ne. Runtsa idanuwanta tayi. Sam bata son tuna gaba ɗaya ranar. Inda da yadda zata yi ta goge ta daga cikin kanta da tayi. 

Ganin ta kwanta yasa Dawud miƙewa. Sauke numfashi yayi, ya ɗan yi tsaye yana kallon Zulfa na wani ɗan lokaci kafin ya fice yana ja mata ɗakin. 

A falo ya ci karo da Khateeb. 

“Don….”

“Khateeb ina ka ɓoye haka? Duk jiya banganka ba. Yauma haka.”

Murmushi Khateeb yayi. 

“Ina wajen Yaya Anees. Mun je wajen aurenka ma, da muka dawo sai na yi bacci a ɗakinshi. Wajen Mami zani, yunwa nake ji.”

Shafa kanshi Dawud yayi, duk yadda ranshi yake a ɓace ganin Khateeb ya ɗan sanyaya mishi wani wajen, yana kallon shi har ya nufi ɗakin Mami sannan ya fice daga gidan gaba ɗaya. 

Iska yake ɗan so ya sha, da zai iya da ya je wajen Yumna. Sai dai jikinshi ya mishi nauyi sosai. Waje ya samu kan ɗaya daga cikin kujerun da ke harabar gidan ya zauna. 

Yana zama ya hango mai gadi da wani matashin saurayi da ba zai kai Tayyab ba tsaye da yaro a hannunshi suna faman rikici.

Da yai niyyar share su, don yasan ba zai wuce ɗaya daga cikin irin mutanen da kan zo neman El ba. A yadda yake ji, duk wani abu daya shafi El baya son jinshi ko menene.

Ganin yadda yaron ke turo Baba Idi, shima yana turashi ga ƙaramin yaro yasa Dawud miƙewa ya ƙarasa wajensu. Matashin ya dafa ma kafaɗa.

“Bi a hankaki mana. Baka ga ba sa’anka bane.”

Yana wani buɗe hanci ya ce, 

“El-labeeb Maska nake nema.”

“To baya nan.”

Dawud ya faɗi cike da alamar takura. Yaron dake hannunshi ya miƙa ma Dawud tare da cewa, 

“Nan ne gidansu ai ko? To ga ɗanshi sai ku ajiye mishi.”

“What?! Wanne irin rashin hankali ne wannan?”

Murmushi saurayin yayi. 

“Ka ga ni ɗan aike ne. Yasan da ɗan ai. Ku ajiye mishi kawai.”

Matsawa Dawud yayi kamar wanda yake miƙoma Maciji . Kallon yaron yake, a ƙiyasce zai kai shekara uku, ba zaka kirashi fari ba, amma ba baƙi bane ba. Buɗe baki Dawud yayi yana ware idanuwa cike da mamaki. 

Baisan ta yadda akai ba, asalima ya kasa fahimtar abinda yake gani balle ya yarda da shi. In kasan El, ko gani biyu kai mishi ka ga wannan yaron zaka ɗauka ko ƙaninshi ne ko ɗanshi. 

Kamar da ke tsakaninsu ta yi yawa. Dariya yaron yayi, da sauri Dawud ya ƙara matsawa ganin har dariyarshi irin ta El ɗin ce. Wannan hukuncin ba shi zai yanke shi ba. 

Yana kallon Baba Idi kanshi na jinjina kai yana kallon yaron. Da ƙyar ya iya ce ma saurayin, 

“Muje ciki.”

Ya juya yan nufi ɓangaren su Labeeb. Yana jin yadda yake binshi a baya har suka ƙarasa cikin gidansu Labeeb din. Asad ne kawai zaune a falo. 

Yana ganin Dawud ya miƙe tsaye, kafin ya kula da saurayin. Ƙarasowa yai inda suke. 

“Wannan fa…..”

Kafin dawud ya bashi amsa ya ware idanuwanshi tare da nuna yaron da faɗin, 

“Tsaya….. Waye wannan?”

Ya tambaya a ɗan tsorace. Saurayin da ke riƙe da yaron ya sauko shi ƙasa. 

“Ɗan El-labeeb Maska. Ku kirashi ya ɗauka “

Mamaki ya hana Asad magana. Kallon yaron da ke tsaye ƙasa yake yana son fahimtar abinda ke faruwa amma kanshi ya kulle. 

Da gudu Asad ya juya ya shige ciki yaa faɗin 

“Dad! Daddy!!”

Binshi dawud yayi.

“Asad! Asad!!”

Amman bai ko juyo ba ya shige ciki yana kiran dadynsu. Dawowa yai jikinshi babu ƙarfi ya rasa abinda ya kamata yayi. Zuciyarshi ya ji ta doka. 

Ba kowa a falon sai ɗan yaron yana kuka, da gudu ya fita yana barinshi a nan. Waje ya fita yana ce ma Baba Idi, 

“Ina yaron nan?”

“Ya fita yanzun nan…..”

Bai bari ya ƙarasa ba ya buɗe ƙofa ya fice, amma ko alamun shi Dawud bai gani ba. Dole ya dawo. Sa’adda ya koma Dady da Anees sun fito. 

Cikinsu an rasa wanda zai ƙaraso inda yaron ke tsaye yana kuka, sun yi tsaitsaye suna kallonshi. Sai Dawud ne ya kamashi ya ɗauke shi. 

“In Aljani ne kuma fa?”

Asaad ya faɗi yana ware idanuwa. Lallashin yaron Dawud ke ƙoƙarin yi amma ya ƙi yin shiru. 

“Wai wa ya kawo shi?”

Dady ya tambaya. 

“Wani saurayi ne haka, bai ƙarasa su Asad ba, kuma ya gudu, na bi bayanshi banga inda yai ba.”

Dafe kai Dady yayi, yana samun waje ya zauna yana kallon Dawud daya bashi amsa. 

“Sai kuma ya ce ɗan labeeb ne?”

Kai Dawud ya ɗaga mishi, Asad Dady ya kalla, in ranshi yayi dubu ya gama ɓaci. 

“Kira labeeb ya zo ya daukie ɗanshi. Ka ce mishi Mumynku na hanya.”

Dariya Asad yayi, tashin hankalin ne da basu taɓa saninshi ba sai yau. Banda mutuwar Sajda da ya gani a gaban idonshi baisan komai ba sai yau. 

Ƙarasowar mumy ne babban tashin hankali. Cikin Zulfa kaɗai ya ishi Labeeb ba sai tazoy ta samu wani ɗan mai rai ba kiranshi yai ya faɗa mishi ya zo ya ɗauki ɗanshi. 

Da murmushi ya sauke wayar. Ko ba komai yana jin tsoratar da yayi a muryarshi kawai, ya kamata yasan yadda tashin hankali yake. 

Yadda Asad yake ji kamar ƙirjinshi zai buɗe, gaba ɗaya daga Labeeb ɗin har Zulfa baya son ganinsu balle zuciyarshi ta dinga gano mishi abinda suka aikata 

Tun yaron na kuka har yai bacci a kafaɗar Dawud. Ƙarasawa yayi ya kwantar da shi akan kujera ya zauna gefenta. A karo na farko da ya ga rayuwa ta canza fuskarta cikin gidan. 

Wannan karon kan Labeeb ta juya. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 18Rayuwarmu 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.