Skip to content
Part 18 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

A mota ya kira Tayyab da ya ce mishi suna hanyar gida shi da Dawud, bayan sun biya asibiti sun ga jikin Yumna. Sosai Labeeb yai faɗa kama zai ari baki. 

Juya motar yayi zuwa gida. Sai da ya shiga yai parking. Kafin ya fito yai ma Ateefa text 

“Ki kula min da ku, bana son yin faɗan anymore. I love you.”

Tukunna ya fito ya nufi part ɗin su Dawud. Bai ci karo da kowa ba har ya ƙarasa ɗakin Dawud ɗin. Inda yake zaune kan gado da alama wanka ya fito. 

“Nake jin Doctor ya ce kana buƙatar hutu?”

A gajiye Dawud ya kalle shi tare da faɗin, 

“Ni garau nake jina, beside yau ɗaurin aurena. Ko baka tunanin ya kamata in je wajen? And nima Doctor ne ko ka manta?”

Girgiza kai Labeeb yayi. 

“You are too stubborn Don . Doctor da baya bin doka.”

Ware mishi idanuwa kawai yayi. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Gani nake kamar yau mafarki ne, after duk wahalar nan zan samu Yumna. Ka ga Zulfa ma yanzun suka tafi asibiti da Mami , zazzaɓi take sosai….ni ya kamata in duba ta i know but….”

Dokawa zuciyar Labeeb ta yi da karfin gaske, kafin ta ci gaba da dokawa da sauri-sauri.

“Duk lokacin da na ɗauka komai zai yi dai-dai…….”

Kasa ƙarasawa Dawud yayi. Jiya tsoron rasa Yumna ne, yau kuma Zulfa da ƙyar take iya ɗaga idanuwanta. 

“She will be fine…… Tashi ka shirya, yanzun ka ga har goman ta yi….”

Miƙewa dawud yayi, Labeeb ya ƙarasa gefen gadon ya zauna, farar shaddarsu Dawud ya ɗauko ya dudduba ya cilla ma Labeeb ɗin nashi, don tunda suka karɓo kayan na haɗe waje ɗaya. 

Shi bai ma kula ba, saboda hankalinshi ba akansu yake ba, so yake ya ga an ɗaura auren nan an dawo, yana kallon lokacin da ya rage bom ɗin dake tare da Zulfa ya fashe musu. 

Har Dawud ya shirya yana riƙe da hularshi a hannu ya katse ma Labeeb tunanin shi da faɗin, 

“Da bandage ɗin nan hular ma zata zauna.”

Miƙewa Labeeb yayi, ya karɓi hular daga hannun Dawud yai dabara ya ɗan ɗora mishi ita, har lokacin bruises ɗin dake fuskarshi duk da kumburi. 

Hakan bai hanashi yin kyau ba, ya saba ganin shi da fararen kaya, sai dai yau ya fita daban, shima kayan jikinshi ya cire ya linke su, ya ɗauki shaddar shi ya saka. 

Bai ko saka hular ba ya ɗauki wayarshi yai ma Dawud ɗin pictures sannan suka ɗauki guda biyu a tare, did n yana jin shi ne hoto na ƙarshe da za su ɗauka for a long time. 

Ganin Dawud ɗin yai wani sanyi ya ƙara taɓa Labeeb. 

“Ka taho mu tafi.”

Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Aure na za’a ɗaura El…. Babu Ummi, babu Sajda….. Yau rana ce mai girma a rayuwata, ba zasu ganta ba….”

Ya ƙarasa da wani yanayi mai ɗacin gaske a muryarshi, Labeeb baice komai ba ya buɗe ƙofar ya fita. Yasan akwai abinda Ummi da Sajda ba zasu so gani ba tattare da yinin ranar. 

Yana jin Dawud biye da shi a bayanshi. Mota ɗaya suka shiga har Unguwar Rimi, gidan ƙanin baban Yumna inda za a ɗaura auren. Cike yake danƙam. 

Da ƙyar suka samu wucewa, ga Labeeb da mutane ke ta son gaisawa da shi. Ba ƙaramin daɗi Dawud ya ji ba da Abba ya bar ma Dadyn Labeeb wakilcin auren dawud ɗin. 

Hankalin shi ba kwanta ba, gani yake kamar za a fasa. Har sai da goma ta cika dai-dai. Kamar amsa kuwwa haka yake jin komai na ɗaurin auren cikin kunnen shi har aka shafa fatiha. 

Kallon Labeeb yake, murmushi yayi, abinda ya daɗe bai yiba. 

“She is mine…..”

Ya faɗi kamar ya kasa yarda da gaske Yumna ta zama tashi. Da gaske wani abu positive ya sake faruwa da rayuwarshi. 

Da murmushi Labeeb ya tabbatar mishi da faɗin, 

“She is yours Dawud. Yumna taka ce daga yanzun har ƙarshen rayuwarku.”

“Thank you.”

Dawud ya faɗi, murmushin shi na faɗaɗa, har ranshi yasan da babu Labeeb samun yumna zai mishi wuya sosai.

**

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shi ne abinda Mami ke faɗi tunda suka fito daga asibitin har suka koma mota, Zulfa kam kuka kawai take ta ƙi yarda su haɗa idanuwa da Mami. 

Driver ɗin da Abba yasa ya kawo su yaja motar, har suka kai gida Mami bata daina faɗin Innalillahi wa inna ilaihir raji’un ba. Don abinda ta ji ya girmi hankalinta. 

Ta kuma kasa yarda da abinda ta ji, hannun Zulfa na riƙe cikin nata tana janta har suka ƙarasa cikin ɗaki. Mami ta mayar da ƙofar ta rufe. 

Jikinta babu inda baya kyarma. Muryarta na rawa, idanuwanta cike da hawaye ta ce, 

“Zulfa……”

Ta rasa ta inda zata fara. Cikin kuka Zulfa ta zauna. 

“Da ga…da gaske ne Mami, ciki ne a jikina…..”

Ta ƙarasa da kuka mai cin rai, wani ɗaci Mami ta ji daga ko’ina na jikinta yana tattaruwa yai tsaye a ƙirjinta. Hawaye masu zafi na zubar mata. 

“Wacce irin ƙaddara ce wannan Zulfa?”

Sosai kuka zulfa ke yi numfashinta har sama-sama yake yi. 

“Mami……wallahi sau ɗaya ne Mami….. Na shiga uku…… Don Allah karki faɗa wa yaya….. Mami ya zanyi?”

Gaba ɗaya ta gigice, ta firgice, kamota Mami tayi, ta kwantar jikinta, su dukkansu kuka suke mai cin rai. Girman al’amarin Mami take kallo. 

Baƙin fentin da ya gogu a rayuwar Zulfa da zuri’arta. Da duk wani jini nata, baƙin fentin da babu abinda zai taɓa iya goge shi. Surutu da yadda kowa zai ma ƙaddarar Zulfa fassara shi ne abinda ya fi komai ɗaga mata hankali. 

Babu ƙaddara mafi girma a rayuwar ‘ya mace da ya wuce wadda ta sami Zulfa. Ƙaunar da take musu ba zata faɗu ba, shi yasa abin yake ci mata zuciya. Tana raba laifin har da ita. 

Gani take da ta saka idanuwa akanta fiye da yadda tayi, ta fi kowa kula da yadda rasuwar Sajda ra sauya ta, da ta jata a jiki fiye da yadda tayi da abinda yake faruwa yanzun bai faru ba. 

“Cikin waye Zulfa?”

Sake maƙale jikin Mami Zulfa tayi, maimakon ta amsa ta sai sabon kuka da ta saki. Tayi babban kuskure ta sani, sai dai tama kanta alƙawari ba zata sake wani ba komin ƙanƙantar shi. 

Tama Labeeb alƙawarin babu mai ji, zai gyara komai, ta yarda da shi har zuciyarta. Da basu je asibiti da Mami ba babu mai ji……zazzaɓinta ne ke ƙaruwa. 

Hakan yasa Mami kamata ta kwantar kan gadon, ta ja abin rufa ta lulluɓeta ta zauna gefe tana zubda hawaye da yanayin rayuwa. Ba zata taɓa judging ɗin abinda ke faruwa da zulfa ba. 

Don ta gama tsorata da rayuwa gaba ɗaya, akan su Dawud take koyan darussa kala-kala, yanzun komai ya sake kwance mata. Ƙaddarar dake jikin Zulfa zata iya faruwa da kowa. 

Ita kanta tasan bata wuce ƙaddarar data faru da Zulfa ta faru da ita ba. Wasu sababbin hawaye ne ke zubar mata. Tafi jin Dawud akan komai. 

**** 

Duk abinda yake dannewa ne daga buɗe bakin Zulfa da kalmomi biyar jiya yake dawo mishi. Runtsa idanuwanshi yayi yana sake buɗe su don ganin da yayi titin na rabe mishi biyu saboda ɓacin rai. 

Yasan inda zai samu Mamdud a lokacin nan, saboda wajen zuwan su ne, yadda al’ada take da muhimmanci da wahalar bari haka zuwa Naf Club yake a wajen su shi da Mamdud. 

Shekara ɗaya da ‘yan watanni kenan rabon shi da ko hanyar sai yau. In har zai yi abinda zai yi yau. Dole ya ga Mamdud. Allah ne yakai shi lafiya a gudun da yake. 

Yana jin yadda wasu daga cikin ma’ aikatan wajen da suka sanshi suke binshi da kallon mamaki. Wasu kuma na kiran,

“Wallahi El – Maska ne!”

Gabakm ɗayan su babu wanda ya ko kalla balle ya nuna ya san suna yi, jikinshi sanye da farar shaddar ɗaurin auren Dawud. 

Yasan suna can gida suna tattara mishi family kamar yadda ya ce. Part ɗin daya san zai ga Mamdud ya ƙarasa. Yana zaune kan kujera da mace ɗaya a cinyarshi. Ɗaya kuma a gefen kujerar da yake zaune suna ta dariya.

Yana ƙarasawa hannu ya kai yai jerking wuyan rigar Mamdud ya fisgo shi. 

“Woo woo easy El – Maska…..”

Mamdud ya faɗi yana ture hannun Labeeb ɗin. 

“How dare you Mamdud……. Na ɗauka we are done. Na baka duk abinda ka buƙata! Why?”

Kallon shi Mamdud yayi daga ƙasa har sama tukunna ya kwashe da dariya. 

“Na san you are a brat, amma ban taɓa sanin you are stupid ba sai……”

Bai ƙarasa ba Labeeb yakai mishi naushin da saida bakinshi yai jini, securities ɗin wajen har sun taho Mamdud da ke goge bakinshi ya ɗaga musu hannu alamar ba sai sun zo ba. 

Kallon shi Labeeb yake yana mamaki, yadda duk tsawon shekarun da suka yi bai taɓa ganin halayyar shi na asali ba. Yau yake ƙara ganin Mamdud a asalin shi. 

Mamdud ɗin da bai sani ba, wani zafi yake ji a ƙirjinshi. 

“I loved you like my brother Mamdud……i was so stupid.”

Ɗaga mishi gira Mamdud yayi. 

“Ƙarya kake El-Maska, zaka iya miƙa rayuwarka saboda ƙannenka, na gani ba labari aka bani ba. 

You know i love her. Ka sani and me ka yi you bloody dog, na faɗa maka ka yi kuskure baka jini ba.”

Muryar Labeeb a dakushe ya ce, 

“She choose me, kana nan, ita kake so, saboda me zaka taɓa Zulfa?!”

Ya ƙarasa tambayar da hargowa. Matsawa Mamdud yayi gab da Labeeb yana kallon shi cikin fuska kamar mai son gano wani abu. 

Cike da mamaki yace. 

“Oh no…. Baka sani ba…..O. M. G…..you idiot……”

Ya ƙarasa yana dariyar da Labeeb ke ji tana ƙara mishi ɓacin ran da yake ji. 

“El – Maska ina da abinda zanyi, faɗi abinda ya kawo ka please…..”

Cike da tausayawa Labeeb ya ce, 

“Taɓa Zulfa shi ne babban kuskuren da ka yi Mamdud….. Na yafe maka na baya…. Wannan ba zai yafu ba….. Kayi crossing line ɗin da bai kamata ba.”

Da hargowa mamdud yace. 

“Me za ka yi? Za ka faɗa ma duniya i raped her?! Ba rayuwata kawai zaka lalata ba har da tata, the scandal, the talk…. maganar zata zagaye duka garin nan. 

Kasan ko me yasa? Saboda ta haɗa jini da kai……zata wuce a nuna ta…. Babu wanda zai auri kwance na…..”

Tun daga kalmar “Rape” Labeeb ya daina gane komai, duk maganganun da Mamdud yake faɗa da wani shuuu suke zuwa kunnen shi, gani yake kamar a gabanshi abin ya faru.

Cikinshi ya yamutsa, nan take yaji zazzaɓi da wani ciwo da baisan ko na menene ba ya kama shi. Ya kasa shaƙar iska. Da baya-baya yake tafiya kafin ya juya da gudu yana fita daga club ɗin gaba ɗaya. 

Jikin motar shi ya jingina yana maida numfashi. Yasan babu inda Mamdud zai je, kare Zulfa shi ne babban abinda ke gabanshi. 

Kamar yadda ya faɗa, Mamdud yayi kuskure. Zai tabbata ya biya shi ta hanya mai wahala. Ya ga abinda yake so ya gani yanzun. 

Ya samu dalilin da yake nema, faɗansu yanzun ya fara da Mamdud. Bai kuma san ƙarshen shi ba, mota ya buɗe ya shiga. Tashin hankalin da yake ji yasa zufa keto mishi ko ta ina. 

Da ƙyar ya iya kai kanshi gida. Kai tsaye part ɗinsu ya wuce. Zuwa babban falo, bugun zuciyarshi ya soma tsananta ganin mutanen dake falon. 

Anees, Asad, Tayyab, suna waje ɗaya zaune, sai Jarood da Uzair a gefe suma. Abban su Dawud, Dadyn shi da Baban su Jarood suna zaune. Idanuwanshi ya sauke kan na Dawud da shi kaɗai ne a tsaye. 

Da ƙyar ya iya sallama. Abba ya amsa shi. Dady kam cewa yayi,

“Labeeb lafiya? Zaka tattara mu anan sai yanzun zaka zo kuma?”

Wani yawu ya haɗiya jin maƙoshin shi ya bushe. Tsugunnawa yayi kan gwiwoyinshi a gabansu, kanshi a ƙasa. 

“Labeeb ka yi magana, lafiya wai?”

Abba ya faɗa. Muryar Labeeb can ƙasa ya ce, 

“Ina Zulfa m? A kira ta”

Tayyab dake zaune ya miƙe. Wannan karon Dawud ne muryarshi cike da shakku ya ce, 

“El? Meke faruwa?”

Labeeb bai ko juya ba balle ya amsa shi. Tayyab ne ya dawo tare da Zulfa, Labeeb ya juya, kallo ɗaya yai mata ya ji ƙirjinshi na ƙara zafi. 

Idanuwanta tasa cikin nashi. Yana kallon hawayen da ya zubo mata, so yake yai hugging ɗinta, yai comforting ɗinta ya faɗa mata ba zai bari komai ya taɓa ta ba. 

Zai yi handling komai, abinda ya taɓa ta ya taɓa shi. 

“In ba so kake raina ya ɓaci ba Labeeb ka soma magana, ka ɗaga mana hankali.”

Cewar dady. Cikin muryar da Labeeb bai gane tashi bace ya ce, 

“Kuskure na yi dady, ba neman yafiyarku nake yi ba, saboda abinda nayi yana da girma. 

Kan hanyar gyara kuskurena nake, shi yasa nake so ku ji daga bakina. Maganar na da nauyi.”

Cikin tashin hankali Zulfa ke kallonshi, da dukkan zuciyarta take addu’a ba abinda take zato bane Labeeb ke shirin yi. 

“Cikine a jikin Zulfa wata uku, cikina ne a jikinta dady!”

Ƙarar marin da Dady ya ɗauke Labeeb da shi ya cika falon kafin wani irin shiru ya ratsa, kamar wanda aka saka ma pause a rayuwar su haka kowa ya ƙame a inda yake zaune. 

Kafin cikin tsantsar tashin hankali Zulfa ta kalli Dawud, abinda ta gani a fuskarshi yasa ta jin jiri na ɗibarta, babu shiri ta dafa kujerar kusa da ita ta zauna a ƙasa. 

Tasan har ta mutu ba zata daina ganin abin ba, wannan karon zafin hawayenta a duk jikinta take jinsu amman sun ƙi zuba don ta samu sauƙi. 

Kallon Dawud take yi, hular shi ya fara cirewa ya ajiye gefe sannan babbar rigar ɗaurin auren da ke jikinshi ya yaddata ƙasa, takawa yake har inda Zulfa ke zaune. 

Matsawa tayi ta haɗe jikinta da kujerar wajen tana jin kamar ƙasa ta tsage ta haɗiyeta. Zama Dawud yayi ya lanƙwashe ƙafafuwanshi. 

Ya kai hannuwanshi ya kamo na Zulfa. Idanuwanshi ya sauke cikin nata, tun kafin ya buɗe baki ta ga roƙon da yake mata. 

Muryarshi cike da rauni ya ce, 

“Zulfa ki ce min mafarki nake, ki ce min maganganun El ba gaskiya bane, ki ce min komai ba gaskiya ne abinda ya faɗa.”

Kanta ta saddar ƙasa tana neman hawaye don ta samu sauƙi koya yake ta rasa. A hankali ta girgiza mishi kai. Ba duka maganganun Labeeb bane ƙarya. 

Kafin muryarta a dakushe ta ce, 

“Ina da ciki!!!”

Matsawa Dawud yayi yana girgiza mata kai. Yasan ƙanwarshi ba zata yi mishi haka ba, in bata duba shi ba zata tuna Ummi, ko da ƙasa ta rufe ma Ummi idanuwa ba zata yi musu haka ba. 

Da ƙyar ya iya miƙewa, gaba ɗaya falon an rasa mai magana. Har ya ƙarasa ya kama Labeeb ya ɗago dashi. 

“Tashi….”

Ya faɗi a hankali, goshin shi ya haɗa da na Labeeb ɗin yana jin duniyar na sakkowa tana ƙoƙarin haɗe shi waje ɗaya. 

Cikin fuskar Labeeb ya ce, 

“Na ga Zulfa bata da hankali. Take them back……. El take your words back….. Ka taimaka min ka ce min ƙarya ne…”

Labeeb shima ji yake kamar kanshi zai tarwatse, in har kare Zulfa zai ja mishi tsana a family ɗinsu na wani lokaci a shirye yake. Ba zai bar komai ya sake taɓa ta ba. 

“Ka yi haƙuri…….”

Shi ne abinda ya faɗa, dukkan hannuwanshi biyu Dawud yasa ya hankaɗa Labeeb. Yasan mutuwa da ciwo, rashin zaman wanda yakamata ya zauna a rayuwarka da ɗaci. 

Amma ko da wasa bai taɓa sanin haka zafin cin amana da ha’inci daga mutumin da ka yarda da shi da rayuwarka yake ba. Kallon shi Labeeb yake yi. 

Yana jin kamar ya karɓar mishi ciwon. Bai ƙi komai ya same shi ba indai family ɗinshi zasu zauna lafiya. Balle yasan zafin cin amana. 

Yana cikin ciwukan cin amana, tsofaffi da sababbin raunuka da yake jin kamar ana shafa musu gishiri. Wani gunji Dawud yayi. Ya ɗauki table ɗin dake gabanshi yai wurgi da shi da saida ya tsorata kowa. 

Kafin yai kan Labeeb ya shaƙe shi ya haɗa shi da bangon wajen yana jijjiga shi. Gaba ɗaya su Jarood sukai kan Dawud amma sun kasa ƙwace Labeeb ɗin. 

Ihu kawai Dawud yake yi yana haɗa shi da bangon ɗakin, fadi yake,

“Na yarda da kai…… Na yarda da kai El! Damn you! How could you do this to her!!…..na tsane ka….. Na tsani yadda na haɗa jini da kai!!!”

Labeeb baya ko ƙoƙarin ƙwacewa, in har abinda dawud yake zai sama mishi sauƙi bai ƙi a ƙyale shi ba. Tayyab ne ya taso ya kama hannuwan Dawud. 

“Ka sake shi, bai cancanta ba, saboda me zaka taɓa shi, ka barshi ya zauna da laifin da yayi! She trusted him….. We all do…. Kuskuren mu ne wannan.”

Sakin shi Dawud ɗin yayi, da gudu ya fita yana barin falon. Inda Zulfa ke zaune ta haɗa kanta da gwiwa Tayyab ya ƙarasa. 

Ɗagota yayi, yasa hannuwanshi ya tallabi fuskarta. 

“Thank you Zulfa. Yau na ƙara sanin wanda ya mutu ya samu rahma shi yake cikin kwanciyar hankali. 

Naso ƙasa ta rufe min idanuwa kamar su Ummi da ganin yau. Ba zance me yasa baki yi tunanina ba kafin ki biye mishi.

Ya za ki yi ma Yaya haka? Dukkan rayuwarshi…..dukkan farin cikinshi yana rataye da mu samu rayuwa mai inganci…

Bazan tsane ki ba, saboda ƙaunarki ka dai zuciyata zata iya yi. 

Bazan yi fushi da ke ba saboda ƙaddararki ce ta zo da haka, banda tabbas ko zan taɓa iya yafe miki abinda ki kaima Yaya. 

Na sallama ma Ya labeeb ke Zulfa. Shi kika zaɓa akan mu right?……..”

Ya tambaya hawaye masu zafi na zubo mishi. Girgiza mishi kai Zulfa take tana jin hawayenshi na buɗe ma nata hanya. 

Muryarshi na rawa ya ce, 

“Ƙarya ne. Shi kika zaɓa akan mu…”

Ya kasa ƙarasawa saboda zafin da zuciyarshi take yi. Har zuciyar shi yake jin kukan da Zulfa take yi, hugging ɗinta yayi yana lallashinta. 

“Komai zaiyi dai dai….. I just need to…..be…. Alone.”

Ya ƙarasa yana sakinta ya nufi hayar fita daga ɗakin. Labeeb ya kalla a hanyar shi ta fita. 

“Thank you……”

Sannan ya fice. Kallon Labeeb Dady yayi sai lokacin ya samu bakin magana. 

“Ka kyauta Labeeb. Wallahi ban taɓa zaton wannan daga wajenka ba, ka bani kunya.”

Abba ya kasa cewa komai, saboda in gaskiya zai faɗa ba wani alaƙa yake ji da Zulfa ba balle abin ya dame shi. Don haka kallonsu kawai yake yi. 

Uzair ne ya miƙe da faɗin 

“Allah ya kyauta.”

Ya bar falon. Kallon Labeeb Asad yake. Shi kuma Anees Asad ɗin yake kallo. 

“Na tambayeka, sai da na tambayeka ko kana sonta…… You said no….. Kai ka faɗa min da bakinka…..”

Kasa ƙarasawa Asad yayi ya tashi ya nufi side ɗinsu, Anees ne ya miƙe ya ƙarasa inda Labeeb yake. 

“Tun tashina, kai nake kallo a komai nawa, da duk lokacin da Mummy bata da time ɗinmu, bana bari yana damuna saboda nasan ba zaka bari wani abu ya taɓa mu ba. 

Sai yau ka tarwatsa rayuwa fiye da ɗaya a gabana. Kasan wacce ta fi min ciwo? Asad. A shirye yake da ya haƙura da yarinyar da yake so tun da ya fara hankali saboda yana tunanin kaima kana sonta. 

Ni da kaina nace mishi farin cikinka shine saman namu ya haƙura, da ka barshi a haka, sai ka tabbatar mishi yadda zainab take a zuciyarka haka Zulfa take. 

Yana jiran ku gama rigimar bikin Don ne, kai yake jira ka nemar mishi auren Zulfa. Me kayi Yaya? I don’t hate you……i don’t feel anything ne kawai. 

So thanks!”

Buɗe baki Labeeb yayi, sai dai ya kasa fito da kalma ko ɗaya har Anees ya bar wajen, kallon jarood yayi yana roƙon shi ya taimaka mishi. 

Girgiza mishi kai Jarood yayi.

“I respect you, ka sani ai, nima na tambayeka, damn tambaya. Na ce maka kayi kuskure lokacin auren Ateefa. 

Nace maka zulfa ya kamata ka aura, yadda ka faɗa ma Asad haka ka ce min. Na barka ne ba don na yarda ba. 

Dammit Yaya Labeeb, na ɗauka son da kake mata ya girmi wannan matsayin. I am done here!”

Labeeb na kallo shima ya fita daga ɗakin. Dady ma miƙewa yayi, Abba na rufa mishi baya. Cikin tashin hankali Labeeb ke binsu da kallo. 

Baba kaɗai ya rage. Cikin tausayawa ya kalle su. 

“Abinda kai hanya ce ta gyara kuskuren ku, za su huce in sha Allah zamu sake zama sai asan yadda za a yi. 

Ita ƙaddara in Allah ya rubuta maka ita bata wuce ka, amma da addu’a sai ta zo da sauƙi. Taku ta zo ne da ga lokacin da kuka yanke hukuncin bayyana kuskuren ku.”

Kai kawai Labeeb ya iya ɗaga ma Baba, har ya bar ɗakin. Ƙarasowa yai inda Zulfa take zaune. 

Cikin kuka ta ce mishi,

“Me yasa za ka yi haka? Saboda me zamu raba zunubaina?”

Girgiza mata kai yayi, ba zunubanta bane suke rabawa, nashi ne yake bibiyarsu. Hannun ta ya kama ya buɗe baki ya ji an fisge hannun zulfan. 

Ya ɗaga kai. Tayyab ne. Ya ɗaga Zulfan ta miƙe ya riƙeta a jikinshi, kamar yana son kare ta daga Labeeb ɗin. 

“Sai ka ƙyale ta haka ai ko?”

Ya faɗi yana juyawa da Zulfa suka bar falon, numfashi Labeeb ya ja, bai fitar da shi ba ringing ɗin wayarshi ya daki kunnuwanshi. 

Zuciyarshi ta ƙara dokawa da ƙarfin gaske. Wayar ya zaro. Ateefa ce, zunubanshi yanzun suka fara fitowa ya sani.

*****

Ruwa Tayyab ya miƙa mata, ta karɓa, saida ta shanye tas tukunna ta miƙa mishi kofin ya karɓa ya ajiye gefe. Hannu tasa tana goge fuskarta. 

“Ya isa haka Zulfa, inba so kike ki sama kanki wata cutar ba.”

Ya faɗi a tausashe. Cikin shessheka ta ce mishi,

“Ina Yaya?”

Ɗan ɗaga mata kafaɗa Tayyab yayi tare da faɗin, 

“Destroying duk wani abu dake cikin ɗakinshi.”

Hannuwa biyu Zulfa ta sa ta dafe kanta tana jin kamar ta rusa ihu. Ta rasa inda zata tsoma kanta ta ji sanyi-sanyi ko ya yake. 

“Laifina ne, ni na ja muku abin kunya…ni ya kamata yai destroying…..”

Riƙota Tayyab yayi a jikinshi yana jin ciwo da ɗacin abinda ke faruwa da su, buɗe baki yayi zai yi magana ya ji an turo ɗakin. Ya juya don ganin ko waye, ya sauke idanuwanshi kan Hajiya Beeba. 

Ranshi ya ji ya ƙara ɓaci, ƙarasa takawa tayi, ta kalle su a wulaƙance. 

“Abin kunyar da aka ƙunso kenan ashe shi yasa…..”

Ƙarar mari Zulfa ta ji cikin kunnuwanta, ta ɗago kai da sauri, dai dai lokacin da Tayyab ya sake ɗauke Hajiya Beeba da wani marin. 

“Ke har kina da bakin da za ki jefi wani da gori?!”

Tayyab ya faɗi cikin hargowa, ihu Hajiya Beeba ta rusa tana faɗin, 

“Na shiga uku ni Beeba, Alhaji yaronka zai kasheni!”

Hannu Tayyab ya sake ɗagawa, Zulfa ta riƙe shi tana girgiza mishi kai, dai dai shigowar Mami ɗakin. 

“Meke faruwa haka?”

Tayyab na maida numfashi ya ce, 

“In na gama ƙirga abinda nake ƙirgawa cikin kaina matar nan bata bar ɗakin nan ba wallahi Mami sai na karyata!”

Hannun Hajiya Beeba da ke rusa ihu tana zagin Tayyab ta uwa ta uba Mami ta ja tana tirjewa tana komai ta fitar da ita daga ɗakin sannan ta dawo. 

“Wai me ya faru?”

Dafe kai Tayyab yayi yana jin wasu hawayen takaici na cika mishi Idanuwa. Sai da ya tabbatar zai iya magana tana nutsuwa sannan ya buɗe bakinshi, ƙirjinshi da nauyi marar misaltuwa. 

“Gori tai ma zulfa…. Mami gori tai mata… Ni bazan iya ɗauka ba.”

Waje Mami ta samu ta zauna gefen Zulfa tana dafe kanta, hawaye suka zubo mata. Gori kam yanzun suka soma sha. Abinda ke faruwa da Zulfa tambari ne da zai bi har jikokinta. 

Sai dai bata da zuciyar da zata faɗa ma Tayyab haka. Tana kallo ya fice daga ɗakin yana jan ƙofar kamar ita tai mishi laifi. Kwanciya Zulfa ta yi kan gadon saboda jirin da ta ji yana ɗibarta. 

Tana jin mami ta dafa mata hannu, tana son nuna mata tana tare da ita, sai dai ji take duniyar ta a yanzun babu wanda zai taɓa fahimta. Ga kanta ya mata nauyi lumshe idanuwanta tayi tana fahimtar abinda ake nufi da asalin tashin hankali. 

“Rayuwata ba zata taɓa komawa dai dai ba ko Mami?”

Shafa kanta Mami tayi, tana jin kamar ace tana da wani sihiri da zata iya amfani da shi wajen ɓatar da abinda ke faruwa da Zulfa, sai dai ba mai ƙarfin ja da ƙaddara. 

Muryarta can ƙasa ta ce, 

“Rayuwar mu gaba ɗaya Zulfa. Allah Yasan halin da muke ciki. Ba kowacce ƙaddara bace take zuwa maka da fuska me kyau. 

Inka karɓeta, in ka miƙa lamurranka wajen Allah sai ya sauya maka ita saboda baya ɗora maka abinda ba za ka iya ɗauka ba.”

Har lokacin idanuwan Zulfa a lumshe suke, tana jin maganganun mami na ratsa ta. 

“Allah na saki, lokacin da ya kamata na nemi kusanci da Shi, nafi jin ciwon har da ku a zunubaina, yaya ba zai taɓa yafe min ba ma…….”

“Shhhh…..”

Mami ta katse ta tana ɗorawa da, 

“Karki yanke mishi hukunci baki gwada shi ba….”

Tana jin hawayen da ke bi mata fuska ta ce, 

“Mami ki yafe min….”

Tarbe hawayen ta Mami take ta ƙoƙarin yi.

“Har wajen Allah laifinki mai yafuwa ne zulfa. Wacece ni da zan riƙe ki da abinda ƙaddara ta rubuta miki, ni kaina ban wuce ta faɗa min 

Kuskure ne da kowa zai iya yi. Ban riƙe ki ba……”

Sauke numfashi Zulfa tayi kafin Mami ta sake cewa. 

“Ki huta don Allah. Ko za ki ci wani abu?”

Kai ta girgiza ma Mami sannan ta yi shiru, kafin wani wahalallen bacci ya ɗauke ta. 

<< Rayuwarmu 17Rayuwarmu 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.