Skip to content
Part 38 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Tun da Labeeb ya fita ya barta take kukan rasuwan Arif ɗin da ta taso mata da rashin Sajda da na Ummi. Hannu ta sa ta dafa ƙaddararren cikin da ke jikinta. 

Maganganun Labeeb na zauna mata. In ta fahimce shi yana nufin hatsarin da Mamdud ya yi ya sa ba zai sake samun haihuwa ba. Abinda ke cikinta ne kaɗai rabon ɗanshi na duniya. 

Wani kuka mai cin rai ne ya ƙwace mata, in za a bata zaɓi har ranta za ta zaɓi kar ta sake ganin Mamdud. Ba za ta iya misalta tsanar shi a zuciyarta ba. 

Sanin abinda ke jikinta na ƙara girma da duk numfashin da ta ja kawai tashin hankali ne mai zaman kanshi. Ta yaya za ta dinga kallon koma menene a kullum? 

Me za ta ji game da shi a ranta? Zai zamar mata tunatarwa akan abinda ya yi sanadin samuwar shi. Duk da ko da ciki ko babu ciki Mamdud yai mata tabon da duk zuri’arta bama ita kaɗai ba bazai gogu ba.

Amma in babu cikin, in babu shi akwai ranakun da za su zo za ta manta da abinda ya faru ko yaya ne. Ƙila wata rana ya zama tarihi a rayuwarta. 

Da cikin labarin ya sauya. Ko giftawar abinda ke cikinta ta gani sai ya tuna mata. Ita ba zata taɓa hutawa ba, haka abinda ke cikinta da suka ja wa gori bayan babu laifin da ya aikata. 

In har samun cikinta ya zo da ƙaddara, tana mamakin matan da ke yin hakan don son zuciyar su. Kunyar duniya akwai tashin hankali a cikinta. 

Bayan za ta tsaya ne a iya mutanen da ka sani suka sanka. Tunanin ta ba zai iya misalta kunyar da bawa zai ji ba a lahira. Gaban dukkan halittu. Haɗe kanta ta yi da gwiwa tana sakin kuka da ba ta san ranar da za ta barshi ba. 

Sallamar Mami ta ji ta ɗago da kai, sai dai yaron da ke riƙe a hannun Mami ya maƙalar mata da sallamar da take shirin amsawa. Zuciyarta ke dokawa a hankali a hankai cikin ƙirjinta. 

Kafin ta ja wani numfashi tana goge fuskarta, a tsorace take kallon yaron da kamar su har ta ɓaci da Labeeb. 

“Mami? Ina kika samo yaron nan?”

Zulfa ta tambaya cike da ruɗani. Ɗan langaɓar da kai Mami ta yi. 

“Kuka yake ta yi. Na kuma san yunwa yake ji. Mumyn su Labeeb a hargitse take, ina jin wani cikin ‘yan uwansu ya zo da shi.”

Mami ta faɗi, girgiza kai Zulfa ta yi tana kallon yaron da ya saki hannun Mami ya ƙarasa inda take, faɗawa ya yi jikinta yana kwanciya. 

A tsorace Zulfa ta kai hannu tana taɓa shi ta ji ko ɗan mutum ne. Har Mami ta fice daga ɗakin bata daina mamaki ba. Dankali da wainar ƙwai ta zubo a plate ta miƙa wa Zulfa. 

Ɗago yaron ta yi daga jikinta tana zaunar da shi tare da matso mishi da plate ɗin gabanshi. Turewa ya yi. 

“Tea..”

Ya faɗi yana kallon Zulfa, da ƙyar ta gano muryarta ta ce mishi,

“Tea za ka sha? In haɗa maka?”

Kallonta yake kamar baya gane abinda take faɗi. 

“I wan Mamma. Wanna go home.”

Ware idanuwa Zulfa ta yi tana kallon shi. Kafin dabara ta zo mata. 

“Mummynka ta je unguwa. Za ka sha tea?”

Ta buƙata cikin harshen turanci. Kai ya ɗaga mata alamar eh. Ɗago kai ta yi ta kalli Mami da ita ma mamaki ne a fuskarta. Mami ta koma kitchen ɗin ta haɗo mishi tea mai kauri ta kawo. 

Tana shirin juyawa suna cin karo da Dawud. Kallon su ya yi yana tsaida hankalin shi kan yaron da ke kusa da Zulfa tana fifita mishi tea a kofi da cokali. 

“Wa ya kawo shi nan?”

Ya buƙata. 

“Ka san shi ne dama?”

Zulfa ta tambaya. Girgiza kai ya yi. 

“Ɗan El ne…”

Ya amsa yana wucewa abinshi. Kallon yaron Mami da Zulfa suke yi kowanne da kalar tunanin da yake yi a ranshi. Mami bata ce kanzil ba ta fice daga ɗakin. 

Kallon yaron Zulfa take tana salati cikin zuciyarta don ta kasa fitowa fili. Ba sai an faɗa mata ba, ba sai ta tsaya tambayar inda Labeeb ya samo yaro ba. 

Wani tausayin ɗan ne ta ji ya kamata, wannan ƙaddara da ke samun su na tsaya mata a rai. Dole ta ga Labeeb a hargitse. Tashin hankalin ne yai mishi yawa. 

Tea ɗin ta gama bashi, yana shanyewa ya kwanta a jikinta, hannunta ta ɗora a kanshi tana jinjina wa ƙaddararsu. 

BAYAN KWANA UKU 

Cikin su duk wanda ka tambaya yadda ya rayu a kwana ukun nan ba zai iya faɗa maka ba. Da wani irin sauri komai yake zuwa yana wuce musu. 

Har lokacin ko motsawa Mamdud bai yi ba. Ishaq ya yi wa Labeeb magana bayan angama addu’ar kwana ukun Arif. Yana so su tafi saboda wajen aikin shi ga makarantar Zainab ɗin. 

Da kanshi Labeeb ya shiga cikin gida, Zainab na zaune jikin Mummy da tai wata irin ramewa. Da hannu ya nuna ma Zainab ta zo.

Sannan ya wuce ɓangaren da ɗakinshi yake a gidan. Binshi ta yi babu musu. 

“Yaya gani…”

Ta Faɗi tana tsayawa tare da zuba mishi idanuwa. 

“Ki shirya za ku tafi…”

“Ina?”

Ta tambaya tana ware idanuwanta. 

“Ke da Ishaq. Ga aiki ga makarantar ki kuma.”

Hawaye ne suka cika mata idanuwa taf. 

“Ina zan iya tafiya Yaya? Yaya Mamdud bai ko buɗe ido ba… Arif… Kwana uku yau. Don Allah Yaya ku bar ni ko kwana bakwai in yi…”

Girgiza mata kai Labeeb ya yi. Kukanta ya tsananta, ƙarasawa ya yi yana riƙe mata fuska. 

“Look at me Zee Zee… Zamanki a nan ba shi Arif yake buƙata ba. Addu’a ce ƙaunar da ke tsakanin ku yanzun kuma a duk inda kike za ta same shi. 

Mamdud ɗin ma addu’arki yake buƙata. Kuma ai za ki iya dawowa in ya tashi.”

Ita dai zainab kuka take har ranta bata son tafiya. Ta kuma yarda da dalilin Labeeb ɗin na ƙin barinta ko kwana bakwai ta yi. Hannunshi da ke fuskarta ta ture tana nufar ƙofa. 

Da sauri yasha gabanta. 

“Zee Zee ki fahimce ni don Allah…”

Idanuwanta cike da hawaye da rikici ta ce, 

“Ba tafiya ba? Shiryawa zanyi…”

Ta ƙarasa tana ficewa daga ɗakin, ɗan dafe kai Labeeb ya yi, yana jin jiri. Tun da ya tashi da safe yake jin shi wani sama-sama. 

Yana fitowa daga ɗakin ya ci karo da Mummy. Hannun shi ta kama tana maida shi ɗakin. Ta zaunar da shi akan gadon shi, sai lokacin ya kula da plate ɗin abincin da ta ajiye. 

“Ka ɗan ci wani abu mana.”

“Bana jin yunwa Mummy… Zee Zee kuka take don na ce ta bi mijinta…”

Sauke numfashi Mummy ta yi. 

“Zan mata magana… Yaushe rabon da ka ci wani abu tsakanin ka da Allah?”

Dafe fuskarshi yayi cikin hannuwanshi. Tun ranar da Arif ya rasu babu komai a cikinshi banda Yoghurt. Shi ma da ƙyar yake rufe ido ya sha. Sam baya jin daɗin komai. 

“Kana buƙatar abinci, kar rashin lafiya ta kama ka.”

Kai ya ɗaga wa Mummy, bata tafi ba sai da ta ga ya dauki plate din yasa cokali ya soma ci, turawa kawai yake yana haɗiyewa ba don yana gane kan abincin ba. 

Ko rabi kasa ci ya yi, nan cikin ɗakin ya bar plate ɗin ya fice daga gidan ya tsaya waje yana jiran Zainab ta fito. Bai fi mintina talatin ba ya ga fitowarta. 

Ishaq ya taso daga inda yake ya karɓar mata jakar da ke hannunta. 

“Mu biya asibiti tukunna sai ku wuce.”

Labeeb ya ce wa Ishaq. Da kai ya amsa shi, mota ɗaya suka shiga shi da zainab, Labeeb ya shiga tashi daban suka nufi asibitin. 

Suna shiga Zainab ta kalli Asad. 

“Bai tashi ba ko?”

“Shiru har yanzun.”

Asad ya bata amsa. Ɗan yatsanta ta sa tana share ƙwallar da ta taru a gefen idanuwanta. 

“Tafiya zanyi…”

Miƙewa Asad ya yi. 

“Tun yau?”

“Asad…”

Labeeb ya kira cike da kashedi. Ƙarasawa Zainab ta yi tana ɗan ɗaga ƙafafuwanta saboda tsayin da Asad yai mata ta sumbaci kuncin shi. 

Haka ma Anees, tukunna ta ƙarasa kan gadon Mamdud ɗin. Ƙura mishi idanuwa ta yi, hawaye masu zafi suka ɗigo daga idanuwan nata zuwa kan gadon. 

“Allah Ya baka lafiya Yaya Mamdud… Don Allah ka tashi da wuri… Ba za ka barni ba yanzun… Karka tafi kaima… Ina buƙatar Yayana… Zan dawo in sha Allah… Stay safe… Su Yaya Anees za su kula da kai… Allah Ya ba ka lafiya. Ina ƙaunar ka sosai.”

Ta ƙarasa tana miƙewa saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Wajen Ishaq ta ƙarasa da ya rungumeta yana sumbatar kanta. 

“It’s ok.. It’s gonna be ok.”

Yake faɗi yana sumbatar duka fuskarta. Kafin ya ɗago kanshi ya kalle su. 

“Allah Ya bashi lafiya Ya ƙara haƙuri.”

Ishaq ya faɗi yana kallon su da jinjina wa ƙaunar da ke tsakanin su. Yana jin sun canza mishi wani abu a yanayin zamantakewar shi da ‘yan uwan shi. 

Zai ƙara ƙaunarsu, yana son kusancin su ya zama irin na su Labeeb. Har sun kai ƙofa Asad ya bisu da sauri yana riƙo hannun Zainab. 

Sumbatar hannunta ya yi. Idanuwanshi cike taf da hawaye da tsoro yake kallonta. Ranar da Arif ya rasu bai runtsa ba. Haka yaita binsu yana sa hannunshi a hancinsu ya ji ko suna numfashi. 

Mutuwar Arif ta gama tsorata shi. Ta sa shi tunanin ko yaushe zai iya tafiya shi ma. Inba tashi mutuwar ba ta wani makusancin shi. Gani yake ko yaushe zai iya rasa su. 

“Ina ƙaunarki sosai…ki kula da kanki sosai… Ki kirani… No zan kira.”

Kai Zainab ta ɗaga mishi, Ishaq ya kama hannunta suka fice daga ɗakin. Labeeb Anees ya kalla. 

“Zan sake ganinta right? Za ta dawo?”

“In sha Allah.”

Labeeb ya faɗi, maganganun Asad ɗin na taɓa shi. Don ya sa shi tunanin ko zai sake ganin Zainab ɗin ko ita zata sake ganin shi. Babu wani abu da yake da tabbas a rayuwar nan. 

Wayarshi ya zaro daga aljihun shi ya kira Zainab ɗin. Ringing na biyu ta ɗauka. 

“Yaya lafiya?”

Ta tambaya da sauri, sauke numfashi ya yi. 

“Lafiya ƙalau Zee Zee… Zan faɗa miki ina ƙaunar ki ne… Sosai… Ki yi haƙuri na ce ki tafi… Kina da wata rayuwar yanzun… Kina da naki gidan da ke buƙatar kulawa.”

“Banda wata rayuwa da babu ku a cikinta yaya… Jinin dake yawo a jikina shi ne a naku… Kowace rayuwa tawa akwai ku a ciki.”

“Hakane. Rayuwarmu na tare a ko ina. Ki kula da kanki. Allah ya kaiku lafiya.”

“Amin. Ka kula da kanka da su Yaya Anees. Call me da zarar Yaya Mamdud ya tashi.”

“Na miki alƙawarin yin hakan.”

Ya faɗi da sauri, sai da ta kashe wayar tukunna ya sauketa daga kunnen shi. Ƙarasawa ya yi inda su anees suke, tunda suka zo asibitin basu koma gida ba. 

“Ku tashi ku je gida ku kwanta, ku huta. Zan wuni anan, da dare sai ku dawo.”

“A’a zamu kwanta anan Yaya.”

Anees ya faɗi. Asad na ɗaga mishi kai. Ɗaure fuska Labeeb ya yi. 

“Ba buƙata na yi ba. Cewa na yi ku tashi ku tafi gida. Kuma ku ci abinci, real abinci nake nufi.”

Kallon shi suka yi, ya sake ɗaure fuska sosai. Anees ne ya fara miƙewa yana ƙoƙarin ɗago shi. Ya ture hannun Anees ɗin. 

“Bazan sake maimaita magana ta ba fa.”

Labeeb ya faɗi yana jan kujera ya zauna. Miƙewa Asad yayi yana bin bayan Anees suka fice daga asibitin. Labeeb ya dafe kanshi a gajiye. Komai ya ishe shi. 

**** 

Zaune Zulfa take akan dining ɗin cikin gidan, sai da ta ga fitar Hajiya Beeba tukunna ta miƙe ta shiga kitchen ɗin. Duk wani abu da ta san za su ci ita da Abba take dubawa. 

Fridge ta buɗe, duk wani lemo da aka fasa aka rage sai da ta zuba zam zam ɗin da Mami ta basu. Yau kwana uku kenan suna wannan aikin. 

Tana fitowa daga kitchen din Abba ma ya fito.

“Bani ruwa.”

Ya ce ma Zulfa, juyawa Ta yi za ta koma kitchen Abba ya ce, 

“Ba ruwa ba ne a hannun ki?”

“Zam zam ne.”

Ta amsa shi tana kallon shi, yadda yake yamutsa fuska kamar wani abu na damun shi. Tana jin yadda duk in za ta ganshi babu abinda ke zuwa mata sai korar sun da ya yi. 

Sai yadda yai watsi da su har rasuwar Ummi. 

“Bani mana.”

Ya faɗi, ba musu ta miƙa mishi, dama abinda Mami take so kenan. Tana kallon yadda ya kusan shanyewa tukunna ya miƙa mata. 

Raɓa shi ta yi ta wuce tana nufar ɗakin Mami da ta tura da sallama. 

“Mami Abba ya sha…”

Zulfa ta faɗi tana gaya mata yadda aka yi, hamdala Mami ta yi cike da nasara. Tana roƙon Allah ya kawo musu ƙarshen jarabawar nan. 

Magana za ta yi Dawud ya shigo.

“Mami zo ki ji.”

Ya buƙata yana juyawa. Mami ta miƙe ta bi bayanshi, ɗakinshi ya nufa tana biye da shi. 

“Dawud lafiya dai ko?”

Girgiza mata kai ya yi. 

“An sallami Yumna daga asibiti, tana gidan Anty.”

“Alhamdulillah… Kai Ma sha Allah. Sai kaje ka ɗauko ta ai.”

Cike da damuwa Dawud ya ce, 

“Ni bazan zauna a gidan nan ba… Ina da nawa gidan…ina yake sa’adda nake neman taimako… Sai yanzun da bana buƙata?”

“Zauna…”

Musu zai yi Mami ta ce, 

“Ka zauna Dawud…”

Zaman ya yi agefen gadon shi, ita ma ta zauna. 

“Ko kasan akwai haƙƙin da ke tsakanin mahaifa da ‘ya’yansu? In Abbanku bai sauke nashi ba, baya nufin Allah ba zai kama ka da laifin ƙin yi mishi biyayya ba. 

Ba za ka taɓa sake shi ba. Duk yadda matsayin shi ya canza a zuciyarka kuwa. Don Allah kar ka yi musu akan wannan… Saboda ni ka zauna inda ya bakan.”

Kallon Mami Dawud yayi. 

“Saboda ke mami… Ku fa? Tare za mu tafi ko?”

Girgiza mishi kai ta yi. 

“Mu muna nan…”

Kallon Mami yake yi, yana jin yadda ba zai iya barin su ba. Cikin idanuwanshi ta ga hakan yasa ta faɗin, 

“Don ka barmu a nan baya nufin ba za ka dinga kula da mu kamar yadda ka saba ba. Komai ma ya kusan zuwa ƙarshe… Ko ba ka yarda da ni ba ne?”

Da sauri ya girgiza kanshi, yana kallon matar da ta basu ƙaunarta, lokacin ta, da kulawarta na sama da shekaru goma. Babu wanda zai taɓa maye gurbin Ummi. 

Amma Mami ta samu wajenta daban a rayuwarsu. 

“Ka shirya ka je ka ɗauketa.”

Kai ya ɗaga wa Mami, ta miƙe tana ficewa daga ɗakin. Tashi Dawud ya yi yana ɗauko manyan akwatina guda biyu, ya soma ɗibar kayanshi yana haɗawa cikin akwatinan. 

Ya cika ɗaya dam, yana cikin kwashe mayukan shi da turaruka, Tayyab ya shigo ɗakin. Da mamaki yake kallon Dawud. 

“Ina za ka je? Kayan me kake haɗawa?”

Kallon Tayyab yake yi. 

“An sallami Yumna ne… Zanje in ɗauketa.”

“Sai yanzun nake sani? Yaushe za ka faɗa min? Da ban dawo ba sai dai in samu ka tafi ko?”

“Tayyab… Zan faɗa maka dama.”

Girgiza kai ya yi. 

“Mu ina zamu zauna?”

“Nan tare da Mami. Mami ta ce a nan za ku zauna.”

Sosai Tayyab yake girgiza wa Dawud kai, ƙarasowa Dawud ya yi yana dafa shi, ya ture hannun shi. 

“Saboda kai nake zaune a gidan nan yaya… Ba za ka barmu ba… Muna buƙatar ka… Da yanayin Zulfa… Komai zai canza in ba ka nan.”

Kai Dawud ya dafe, da Yumna bata shigo rayuwar shi ba, bai ga abinda zai sa shi yin aure yanzun ba. Me ma yake tunani zai bar ƙannen shi tare da Hajiya Beeba su kaɗai. 

Ya rasa abinda ya kamata ya yi, wucewa ya yi ya buɗe akwatin da ya rufe ya soma ɗibar kayanshi yana maida su inda ya ɗauko su. Ƙarasawa Tayyab ya yi. 

“Me kake yi haka Yaya?”

Ba tare da ya bar abinda yake yi ba ya amsa shi da 

“Mayar da kayan nake… Bansan me nake tunani ba…Mami ta ce a nan za ku zauna… Bazan iya musu da ita ba. Kai ka ce ba za ka zauna bana nan ba. 

Zan ɗauko yumna duk mu zauna a nan.”

Kayan da ya ɗiba Tayyab ya karɓe yana mayar da su cikin akwatin, baisan me yasa yai maganar da ya yi ba. Ko yaya ne Dawud ya kamata ya samu farin ciki shi ma. 

Tsoro Tayyab yake ji, tunda aka sa ranar Dawud ɗin yake da tsoron a zuciyarshi. Bai dai furta bane ba. Yanzun kuma da ya ga Dawud na haɗa kayan shi tsoron ya ƙaru. 

Dawud kaɗai yake da shi, ya ga yadda mace ta ƙwace Abbansu, ba zai iya ɗaukar wata ta ƙwace Dawud ba. Kayan ya shiga ɗaukowa yana dawo da su cikin akwatin.

Riƙe shi Dawud ya yi, ya fisge, sake riƙo shi yayi sosai wannan karon. 

“Ka kalle ni Tayyab…”

Ɗago fuska Tayyab ya yi, ya kai hannu yana goge hawayen da ke zubar mishi. 

“Subahanallah… Tayyab…na fasa. Ba inda zani…ina nan tare da ku.”

Girgiza kai Tayyab ya yi wasu sabbin hawayen na zubo mishi, yana jin maraicin shi fiye da ko da yaushe. 

“A’a Yaya… Don Allah ka tafi… Kawai ina tsoro ne…kar kaima ka barmu kamar Abba.”

Tayyab ya ƙarasa kuka na ƙwace mishi, ganin yadda jikinshi ke kyarma ya sa Dawud kamashi ya zaunar. 

“Ku ne farko akan komai nawa Tayyab. Karka sake tunanin aurena zai taɓa ku…wallahi zan bar kowa akan ku. Har da Yumna ɗin. 

Zan haƙura da rayuwa saboda ku… Ku ne komai nawa.”

Hannu Tayyab ya sa yana goge fuskarshi. 

“Ka tashi in taya ka.”

“Ba inda za ni. Farin cikin ku shi ne komai nawa”

“In na ce maka muna buƙatar mu ga naka farin cikin fa? Ka tafi Yaya… Saboda farin cikin mu duka.”

Sosai Dawud yake nazarin fuskar Tayyab ɗin, ya ga gaskiyar abinda ya faɗa tukunna ya miƙe. Shi ma Tayyab ɗin sake goge fuskarshi yayi. Shi ya taya Dawud suka gama haɗa kayayyakin duk da yake buƙata. 

Ya ɗauko akwati ɗaya suka fito, Abba suka gani tsaye ya dafa bango yana maida numfashi. Buɗe baki Tayyab ya yi don ya tambaye shi ko lafiya. 

Sai dai kafin ya fito da maganar Abba ya soma amai, yar da akwatin Tayyab ya yi ya ƙarasa wajen da Abban yake da gudu. Amai yake, wani irin baƙin amai kamar zai amayo ‘yan hanjin shi. 

Dawud tsaye yake yana kallon su, yana kallon yadda Tayyab ke riƙe da Abba. Sosai yake amai, tun da sauran ƙarfin shi har ya soma laushi. 

Wani irin sama-sama numfashin shi yake yi. Jijjiga shi Tayyab yake yi. 

“Abba… Abba…”

Ganin ya wani yi shiru, jikinshi ya saki a hannun Tayyab ya sa Dawud ƙarasawa. Hannun Abba ya kama yana jin yadda bai ji nerve ko ɗaya ya harba ba. 

Daga zuciyarshi wani hadari-hadari ke tasowa, kafin ya furta kalmar da yai shekaru bata hau kan harshen shi ba. 

“Abba!”

Ƙarfin maganar ne ya jawo hankalin su Zulfa da Mami, da gudu suka fito, tsayawa Zulfa ta yi tana girgiza kai tana kallon Abba. 

“Abba… Banda kai…no…”

Take faɗi tana ja da baya cikin tashin hankali, tana kallon yadda Dawud ke riƙo Abba yana girgiza shi. Ko ina na jikin shi na kyarma. 

Wani abu Zulfa ta ji ya tsirga mata daga tsakiyar kanta zuwa cikin mararta da tai wani irin ƙullewa da ta sa numfashinta ɗaukewa kafin ta yanke jiki ta faɗi. 

Mami tayi kanta tana ɗago ta.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Zulfa… Zulfa…”

Mami ke kira, da gudu Tayyab ya tashi ya nufi inda suke yana riƙo hannun Zulfa. Dawud da ido ya bisu, in ya kalli Zulfa, sai ya kalli Abba. 

Ya rasa inda ya kamata ya je, ya ɗauka ya tsani Abba, ya ɗauka ya mutu a zuciyarshi. Bai taɓa zaton rashin shi zai sa shi jin komai ba. 

Don gani yake ya gama binne shi daga ranar da ya kore su. Sai yanzun da ya ganshi a kwance, ya ganshi baya motsi yasan cikin tashin hankalin duniya yanzun ya fara fahimtar ɗaya daga cikin su. 

Rashin iyaye duk biyun. Mami ta soma miƙewa tana faɗin, 

“Kamata mu tafi asibiti…”

Cak ya ɗaga Zulfa kamar bata da wani nauyi ya fita da ita. Rabon da Dawud ya ji shiru haka cikin kanshi tun rasuwar Sajda.

Yana kallon su har suka fita, Tayyab ya sake dawowa ya ɗago Abba da baya ko motsi a jikinshi yana fita da shi da ƙyar. Mami ta kamo Dawud ta ɗago da shi. 

“Taho mu tafi Dawud.”

Binta yake yana jin wani yanayi da bai taɓa sanin akwai kalarshi ba a duniya.

***** 

Hannun Tayyab ya ji kan kafaɗar shi yana janyo shi da faɗin, 

“Yaya fito…”

Tukunna ya kula da su Mami basa cikin motar, girgiza kanshi ya yi yana sake dafe shi saboda yadda yake jin komai ya mishi shiru a ciki.

Ɓangaren da ke fahimtar abubuwa cikin kanshi ya ɗauki hutu, sai da Tayyab ya girgiza shi sosai. 

“Yaya… Muna buƙatar ka don Allah… Bansan ya zanyi ba. Kamin magana!”

Numfashi Dawud yake ja a hankali yana fitar da shi, tukunna ya ɗan ɗaga wa tayyab kai tare da fitowa daga motar yana tura murfin. 

Bin tayyab yayi a baya. Sai lokacin ya kula da asibitin su ne ma Tayyab ɗin ya kawo su. Gaisawa yayi da wasu cikin likitocin kafin su wuce. 

Tsaye ya yi. Don baisan ina zai soma cewa Tayyab ya kai shi ba. Wajen Abba ko wajen Zulfa. Ganin hakan ya sa Tayyab faɗin, 

“Wajen Abba… Mami na tare da Zulfa.”

Binshi a baya Dawud ya yi har ɗakin, a bakin ƙofa Tayyab ya tsaya shi ya shiga ciki. 

“Dr. Dawud…”

“Dr. Amir.”

Dawud ya amsa shi yana miƙa mishi hannu. 

“Ka ce ku kuka kawo marar lafiyar.”

Kai kawai Dawud ya iya ɗaga mishi. Kafin yai mishi bayanin cewar babu abinda ke damun Abban banda gajiya. Sun yi sedating ɗinshi don ya samu hutu. 

Godiya Dawud yai mishi, kafin ya fita, kujera Dawud ya ja ya zauna a saitin abba. Yana jin shigowar Tayyab sai dai ba shi bane a gabanshi. Abba ya ƙura wa idanuwa kamar ba zai ƙifta su ba. 

Zuciyarshi na nutsuwa da tashin hankalin da ta shiga na tunanin rasa Abba. Ba zai iya ɗauka ba, fuskarshi ya sa a cikin hannuwan shi yana sauke ajiyar zuciya. Wata dariya Tayyab yayi da bata da alaƙa da farin ciki. 

Hakan ya sa Dawud buɗe fuskar shi ya kalli Tayyab ɗin. 

“Ina mamaki ne. Na ɗauka duka mun tsane shi. Na ɗauka mun haƙura da shi tuni… Kalle mu yanzun.”

Ya ƙarasa yana nuna kanshi da Dawud da ke zaune. Cikin wani sanyin murya Dawud ya ce, 

“In akwai abinda yake da tabbas a rayuwarmu shi ne cike take da sabbin abubuwa ko yaushe. Ka zauna tare da shi in duba su Mami…”

Dawud ya faɗi yana miƙewa. Ba tare da Tayyab ya ce komai ba ya jawo kujerar da ya tashi sannan ya kama hanya yana ficewa daga ɗakin. 

Gano Mami bai mishi wuya ba, don asibitin ba baƙonshi bane ba, a tsaye ya sameta, kallo ɗaya za ka yi mata kasan hankalinta ba a kwance yake ba. 

Tana ganin shi ta miƙe daga zauniyar da take. Ƙarasawa ya yi yana faɗin, 

“Mami… Ya jikin nata?”

Girgiza mishi kai ta yi, tana jin maganar na tsaya mata a wuyanta, saboda wani irin ɗaci da take ji. Da ƙyar muryarta na rawa ta ce, 

“Ban sani ba…jini take ta zubdawa kafin su shiga da ita… Ban sani ba… Bazan iya rasata ba ita ma… Bazan iya ba Dawud…”

Mami ta ƙarasa maganar hawaye na zubar mata, hannu Dawud ya sa yana goge mata fuska. Yana jin ƙaunarta har cikin zuciyarshi. 

“Ba abinda zai same ta Mami… Kukan ki zai ɗaga min hankali. In ba ki yi ƙarfin zuciya ba ina zan samu nawa? Ina buƙatar Mamina…yau za ta zo min da sauƙi in Mamina na tare da ni.”

Kai ta ɗan ɗaga wa Dawud ɗin tana jin shi kamar daga cikinta ya fito. Kamar ita ta haife su gaba ɗaya. Allah bai bata haihuwa ba, sai ya kawota rayuwar su Dawud ya zaunar da su a zuciyarta. 

Kama hannunta ya yi ya zaunar da ita kafin ya wuce. Office ɗaya daga cikin na wajen ya shiga, ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa ya dawo ya kawo ma Mami. 

Karɓa ta yi ta sha sosai. Numfashi Dawud ya ja ya sauke kafin ya taka, a hankali ya tura ƙofar don yana jin tsoron abinda zai gani. Juyowa likitan ya yi da duka nurses ɗin guda biyu. 

Ganin Dawud ne ya sa su komawa suka ci gaba da abinda sukeyi, ƙarasawa yayi, idanuwanshi kan fuskar Zulfa da ta wani dishe kamar babu wadataccen jini a jikinta. 

Yana jin likitan na magana. Wata nurse ta fita ta dawo. Amma ya kasa fahimtar abinda suke cewa, hankalin shi da nutsuwar shi na kan Zulfa. 

So yake ko motsi ya ga ta yi amma ina, ba ta ma san duniyar da take ba. Baisan iya lokacin da ya ɗauka tsaye a nan ba. Har sai da likitan ya dafa shi. 

“Jinin ya tsaya…cikinta na nan, sai dai bamu da tabbas akai. Komai zai iya faruwa a koyaushe.”

Kai Dawud ya ɗaga mishi, sannan suka fice daga ɗakin. Tsugunnawa Dawud ya yi yana kama hannun Zulfa da babu ƙarin ruwa a jikin shi. 

“Allah ka bata lafiya…Allah karka ɗora min wata jarabawar akan Zulfa… Allah ka sauƙaƙa mana rayuwarmu…”

Shi ne abinda Dawud yake faɗi kafin a hankali ya soma jero godiya ga Allah har sai da ya samu nutsuwa a zuciyar shi. Tukunna ya miƙe yana sumbatar hannun Zulfa. 

Fita ya yi daga ɗakin ya shigo da mami da ke zaune a wajen ɗakin bata ma kula da fitar likitan ba. Yadda yai wa Dawud bayani shi ma haka ya yi wa Mami. 

Hannu ta sa tana share ƙwallar da ta taru a gefen idonta. Tana jin ciwon ƙaddarar Zulfa. Ba za ta yi ƙarya ba akwai ɓangare na zuciyarta da ya yi fatan fitar cikin nan. 

“Allah Shi Ya san dai-dai. Ya san abinda Ya fi dacewa…”

Ta Faɗi cikin sanyin murya. Kafin ta ƙarasa ta zauna a gefen gadon Zulfa ɗin. Wayarshi Dawud ya zaro daga aljihun shi. Text ya tura wa Yumna. 

‘Kina raina. Ina asibiti da su Zulfa. Zan zo da zarar komai ya natsa. I love you sosai.’

Yana turawa, har zai maida wayar aljihunshi ya ji ƙarar shigowar sako. Ɗan kallon zulfa yayi da yanayinta. Wani abu na daban na tsaya mishi a wuya da ɗaci mai ciwo.

Kafin ya buɗe text ɗin da Yumna ta turo mishi sai da ya fara neman lambar Labeeb. Ya kamata ya sani tunda shi ya sa ta cikin wahalar. 

‘Muna asibiti da Zulfa.’

Kawai ya tura mishi sannan ya buɗe text ɗin Yumna. 

‘Subahanallah. Allah ya bata lafiya. Karka damu da ni… In dai ina zuciyarka nisan mu baya damuna. Ka sha maganinka, ka ci abinci don Allah. I love you more.’

Lumshe idanuwanshi ya yi, kafin ya samu damar feeling ɗin wani abu kiran da ya shigo ya katse mishi. Labeeb ne, ɗagawa ya yi yana faɗa mishi asibitin da suke da Zulfa din ya kashe wayar bai saurari komai ba. 

**** 

Tunda text ɗin Dawud ya shigo wayarshi yake tsaye ya rasa inda zai sa ranshi ya ji daɗi. In ya bar Mamdud shi kaɗai su Asad suka sani ba za su taɓa karɓar uzurin shi ba tunda shi ya kore su gida. 

In ya kira su don su dawo asibitin dawowa za su yi. Sai dai suna buƙatar hutun. Sai wani ciwon na daban ya shige su, ko makaranta cikin kwanakin babu wanda ya je a cikin su.

Yana buƙatar lafiyar su kamar yadda yake buƙatar ganin Zulfa a yanzun. Wayar Dawud ya sake kira har ta yanke bai ɗauka ba. Dabara ce ta faɗo mishi, Jarood ya kira. 

Ringing ɗaya ya ɗaga तार da yin sallama yana gaishe da Labeeb da ya amsa shi ya ɗora da faɗin, 

“In ban takura ka ba Jarood, Harmony za ka zo ka duba Mamdud zan je wani uzuri in dawo.”

“Ba damuwa. Gani nan.”

Jarood ya faɗi yana katse kiran kafin ma Labeeb ya samu bakin yi mishi godiya. Ba a yi mintina ashirin ba ya iso, amma Labeeb gani ya yi kamar ya fi awa huɗu. 

Yana shigowa Labeeb ya ce, 

“Na gode … Na gode sosai Jarood.”

Kallon Labeeb ya yi. 

“Ko me nake kasan zan zo. Balle bana komai. Kai kake cewa ba godiya tsakanin ‘yan uwa kuma kake min.”

Jinjina kai Labeeb ya yi. Karamci da ƙaunar da ke tsakanin su na zauna mishi da wani yanayi. Bai ce komai ba ya wuce yana ficewa daga ɗakin. 

Wajen motar shi ya ƙarasa ya shiga. Gudu yake da motar, cikin kunnuwanshi yake jin muryar Zulfa. 

‘Bana son gudun nan da kake da mota… Ko bana ciki. Don Allah ka dinga ragewa… Inda duk za ka je yana nan ba zai sake waje ba. Lafiyarka na da muhimmanci a wajena da ma su Arif.’

Rage gudun motar ya yi a hankali, sunan Arif a zuciyarshi na sa shi wata irin kewar yaron. Ko bai ga fuskarshi ba, in da ace zai ji muryarshi, ko na minti ɗaya ne. 

Numfashi yake fitarwa da sauri-sauri, sosai ya rage gudun motar yana fito da wayarshi daga aljihun shi, rabi da rabi hankalin shi yake. Ɗaya kan wayar ɗaya kan titi. 

Sai da ya gano folder ɗin da call recordings ɗinshi suke tukunna. Shiga ya dinga yi har sai da ya ji wanda yake ɗauke da muryar Arif. Connecting yayi da motar tukunna ya sake playing daga farko yana ƙaro maganar. 

‘Yaya ina wuni.’

‘Lafiya ƙalau Arif… Ya Jordan? Ya makarantar, komai dai lafiya ko?’

‘Alhamdulillah. Sai kewar ku… Sai abincin su da bana iya ci.’

Yana jin dariyar da ya yi. 

‘Za ka saba a hankali. Muma muna ta kewarka. In dai akwai matsala kasan kirana zakayi kawai ko? Like ko text kai min zan taho.’

Dariya Arif ya yi. 

‘Ba matsalar komai fa. Za mu tafi karatu yanzun. I love you… Ka ce ma su Yaya Asad, sun kirani ɗazu ina aji. Sai yanzun na yi free… Zan kira su in na dawo.’

‘To zan faɗa musu. Love you more… A yi karatu sosai.’

‘Alright. Ka kula da kanka.’

Parking ɗin motar Labeeb ya yi a gefen titi, ya haɗa kanshi da gaban motar, yana jin zai ba da idonshi guda ɗaya in dai zai sake samun ko awa ɗaya ne tare da Arif. 

Sai da ya tabbata yana da nutsuwar da zai iya tuƙi tukunna ya tashi motar ya sake hawan titi, a hankali yake lallaɓawa. Da ƙyar ya danne tunanin Arif da na Zulfa. 

Idan wani abu ya sameta ba zai taɓa yafe wa kanshi ba. Don yasan ƙaddarar da ke ɗawainiya da ita, shi ne sanadi, zunuban shi ne suke rabawa tare. Yana ƙarasawa asibitin ya sake kiran lambar Dawud don ya faɗa mishi ɓangaren da suke. 

Bai ɗaga ba wannan karon ma. 

‘Don Allah kai picking. Ɓangaren da kuke za ka faɗa min.’

Ya tura wa Dawud ɗin. Ba a yi mintina biyu ba ya turo mishi ɓangaren da lambar ɗakin. Girgiza kai Labeeb yayi ya mayar da wayar aljihunshi. Bai ga laifin Dawud ba, in da za su yi musayar waje baya jin zai iya jure magana da Dawud ɗin. 

Da sallama ya tura ɗakin, Mami ya gani zaune. Dawud na tsaye, idanuwanshi suka sauka kan Zulfa da haskenta ya fito mishi fiye da koyaushe. 

“Ina wuni Mami… Ya mai jiki?”

“Ba don kai ba da ba ta san wahalar nan ba. Wanne jiki kake son sani kuma?”

Dawud ya amsa shi kafin Mami ta ce wani abu. Shigowar Labeeb ɗin ta buɗe abinda yake ji game da shi. Tambaya ɗaya ke mishi yawo. 

Me yasa Labeeb zai musu haka? Ganin kallon da yake mishi yasa Mami faɗin, 

“Alhamdulillah Labeeb. Ka zauna mana…”

Ta ƙarasa maganar tana kallon shi. Ƙaddarar da ke kanshi na tsaya mata. Kallo ɗaya za. ka yi mishi ka san babu nutsuwa a tattare da shi. Ya rame, ya yi duhu. Duk ya fita hayyacin shi. 

Girgiza mata kai yayi. Ba zai iya zama ba. So yake ya tambaya me ya samu Zulfan, amma yana tsoron sake tunzura yanayin da ke tsakanin shi da Dawud. Don haka yai shiru. 

“Bari in duba Tayyab da Abbanku.”

Mami ta faɗi tana miƙewa tare da fita daga ɗakin. Kallon Dawud Labeeb ya yi da mamaki ya ce, 

“Tayyab da Abba? Me ya same su?”

“Ba Tayyab bane…”

Sunan Abban ne yai mishi nauyi akan harshe yanzun kuma. Ya kasa furtawa

“Ba wani abu bane shi ma ɗin. Stress ne. Da ya huta za a sallame shi.”

Kai Labeeb ya jinjina. 

“Allah ya basu lafiya su duka.”

Kallon shi Dawud yake yi. Inda a bakin wani ya ji maganar cikin Zulfa shari’a ne za ta raba su don ba zai taɓa yarda ba. Zai ɗauka ƙazafi ne mai muni. 

Abinda ya canza a jikin Labeeb har yai abinda ya yi yake nema ya rasa. Ya rasa gani, ya kuma rasa gane me yasa zai musu haka. In ya nemi auren Zulfa ko babu lefe da sadaki ba su ba, Zulfa da kanta za ta yafe mishi su. 

“Ka daina kallo na haka… Don Allah ka bari.”

Ɗan ɗaga kafaɗa Dawud ya yi. 

“Ina neman dalili ne… Ina neman amsar tambayar da nake da ita…”

“Ba yanzun ba, ba yau ba don Allah. Ka barni tukunna…”

Labeeb ya ƙarasa da sanyin murya. Magana Dawud zaiyi Zulfa tai wata miƙa tana haɗe jikinta, ba tare da kula da yadda take fisgar ruwan da ke maƙale a hannunta ba. 

“Ya Allah… Wayyo Mami cikina… Cikina ciwo…”

Shi take faɗi kawai tana juye-juye. Da gudu suka yi kanta, Dawud ya riƙo hannunta da ke da ƙarin ruwa kar ta ji wa kanta ciwo. Gaba ɗaya Labeeb ya tallabo ta jikinshi. 

“Zulfa… Kalle ni… Kin ga… Za ki samu sauƙi… Dawud ka yi wani abu mana!”

Ya faɗi a tsawace, ba ta ma san suna yi ba, babu komai da Dawud zai iya yi, tunda ba kayan aiki a jikinshi, balle katin ta, ko ina jikin shi ɓari yake yi. 

Riƙeta Labeeb ke ƙoƙarin yi don juye-juyen da take za ta iya faɗowa daga kan gadon. Jikinshi data kwanto ya sa shi ware idanuwanshi. 

“She is bleeding… Innalillahi…”

Labeeb yake faɗi a rikice. Ai kamar maganar shi ke ƙara fito da jinin har bin kayan dake jikinta yake, da gudu Dawud ya fita. Ya dawo da likita. 

Takardar dake hannunshi yai rubuce rubuce a jiki ya miƙa wa Dawud. 

“Ka siyo wannan yanzu!”

Da sauri ya sake fita daga ɗakin, Labeeb ya kalla. 

“Ƙira min nurse…”

Kallon shi Labeeb ya yi yana tunanin yadda zai matsa daga kusa da Zulfa ko na minti ɗaya ne tana cikin wannan halin. 

“In kana son taimaka mata…tashi za ka yi.”

Likitan ya faɗi, dole ya zame Zulfa daga jikinshi yana gyara mata kwanciya akan gadon, ta yi wani luf da ita, tana ɗaga idanuwanta da ƙyar. 

Sa’adda ya dawo a ɗakin ya samu Dawud, likitan na ce mishi, 

“Jini muke buƙata ko leda ɗaya ne …Na ga O+ take da… Ko akwai wanda za a ɗiba kasan yadda yake wahala.”

Lumshe idanuwanshi yayi, daga ita sai Khateeb suke da O+ irin na ummi. Su dukkan su A ne kamar Abbansu. 

“Ku ɗiba nawa… Ko ya kuke so.”

Labeeb ya faɗi dan group ɗin jininsu ɗaya ne da Zulfa, nuni likitan yai mishi da ya bi nurse ɗin. Dawud ya bishi da kallo, can ƙasan maƙoshi ya furta, 

“Why? Me ya sa El? In kana sonta har haka?”

Girgiza kai Dawud ya yi. Likitan ya ɗan dafa mishi kafaɗa, 

“Ina tsoron faɗa maka… Babyn jikinta na fita… Ba zai zauna ba.”

Wani numfashi Dawud ya fitar da baisan yana riƙe da shi a duk kwanakin nan ba. Babu abinda yake faɗi acikin zuciyarshi da ya wuce, 

‘Allah ka rabata da ƙaddarar nan… Allah ka rabata da abinda ke cikinta…’

A fili kuma cewa ya yi, 

“Lafiyarta ce damuwata…”

Yana nufar ƙofa ya fita, iskar ɗakin ta mishi kaɗan. Ba don bai saba da ƙarnin jini da ke ciki ba. Wannan karon daga jikin ƙanwar shi yake fita. Baisan akwai bambanci ba sai yanzun. 

Waje ya samu ya tsugunna ƙafafuwan shi sun yi wani irin sanyi. A idanuwan Labeeb ya ga girman ƙaunar da ke tsakanin shi da Zulfa. Ƙaddarar da ta gifta musu mai girma cr, ta fi ƙarfin fahimtar shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwarmu 37Rayuwarmu 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×